DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   96 / 105

285K to 288K   out of 313.1K words

sameka a lokacin nayi ma bayanin komai ko ba haka akayi ba ?
Daddy ennugu yace kwarai kuwa aina fada mata a yanzu gabanta ni sam bansan da wanan zance ba tun farko wallahi da baikai haka ba ai.
A,a ita kubura ko so take tunda ina fakiri inje gabanta in gurfana in mata bayani dalla dalla yadda nayiwa Alh sannan ta gamsu ba kudin danta ciki.
Inma taimako ne zainabu gata ita da yar uwarta sune suka dab tataro abunda ke garesu sukace in kara nace su barshi ta rantse min ba hannjn mazansu a cikin zancen nan na karba son gudun haka.
Abinda yasa kuma ban fadawa kowa ba har yanzu takardun gidan nan basu shigo hannuna ba tukunna tunda maigidan baya gari magana yana gun iyalinsa suna kaiwa kudi.


ZAIINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

9?? 4??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,


Ana haka mama ta shigo don yasa umar ya daukota zuwansu dai yayi amfani za,ace don sun goyawa baba garba baya .
Amma duk da hakan yakafe akan sai mum ta fada mai gidan da danta ya saya mashi da shanayen da tace ya girke yana facaka da kudin danta.
Sai ni dasu muke juyashi yadda maga dama muke cin abun yaya yanzun mun hana ya kula kowa na tare da ita tota fada mai abinda yaya yayi masa na daukaka rayuwa.
Tuburan baba ya haukace masu akan ba zan koma ba su debi yara kawai sukaiwa kubura wajenta tunda har idon ta ya iya rufewa akan abin duniya haka.
Inga kara na dauka zainab takice har abada ashe ita ba haka abin yake ba wajenta da wata manufa ta rikeni a hannunta dama.
Daddy ya gyara zama ya kira sunan baba yace garba kana nufin kaima namiji zaka iya raba daya biyu yau a tsakanin mu ?
Idan ita mace haukansu na mata yasa tayi haka kai ina hankalinka na maza yashiga da zakai hakan sam Addel ba zaiji dadin hakan a rayuwansa ba kamar yadda mu nan duk bamuji dadin faruwan wanan abin ba gaskiya.
Kuskurene kubura tayisa ta yanke hukunci a cikin fushi ni yanzu haka komai ba zan iya cewa da ita ba don haka idan har na isa dakai a cikin garin nan ka ban yarinyar nan yanzu in mayar da ita dakinta don Allah a tare gaba kuma wanan ya wuce don Allah.
Kallon daddy din yayi kamar zaiyi magana sai kuma yai shiru yace to shike nan yaya amma a fadawa kubura ita bata kaiba wallahi afada mata nace batakai ba tayi min kadan.
Yau badon kuba Alh dana nunawa kubura karya take wallahi zan nuna mata ni bakatsinen gaskiyace don sai tayi bayani da bakin ta yadda tabawa diya sako haka zata karontasa da bakin ta.
Amma babu komai saidai ita har dan nata banga abin tsone ido ba indai nine ta kama kanta kafin mu hadu don tunda ta fara hakan watarana za a hade.
Sam mum batayi zaton abin zaikai haka basai gashi zance ya fashe don Nasir ya kirata yayi fada sosai ya nuna rashin jim dadin shi ga abunda ta aikata tare da umartanta da ta fidda bakinta cikin lamarin zaman mu idan ba Addel ya kawo mata magana ba game da gidansa.
Zata fara fada yace mum baki da gaskiya wallahi mutanen nan basuci haka a wajen ki wallahu baba garba masoyinmune a cukin dangi kaf.
Haka zainab din ina mamaki yadda a lokaci guda kika bari aka shiga tsakanin ki da zainab haka wallahi to ki bari a zauna lafiya mum wanan ai mu ake jawa a bin kunya wallahi.
Dole su daddy suka tasani gaba na koma gida ba abinda nakeyi sai kuka don na tsani auren a lokaci na yarda da wasu ke kiran auren zumici ko auren mugunta.
Don yau da mum ba zaman biyu take guna ba gata uwar miji gata gwaggo a wajena ba abinda zai hana in tsigeta a lokacin data sako iyayyena a zancenta.
Amma ina idan nayi hakan dangi da mahaifana zasu sani a gaba su tsotsigeni wanan ne ya ceci mum a wajena a wanan ranan don katsinawan sun hau ashe gaskiyane kunya garemu badai tsoro ba.
Daddy ya hana yaya zuwa da yace zaiyi yace ya zauna yayi aikinsa kada kuma yayiwa mum zancen ya barshi da ita kada yaji wani abu ya bullo a tsakanin mu ko daga baya ya kashe wanan magana tunda an fahinci tsegumine kawai ita kuma mum bata tsaya bincike ba ta hau zancen.
Ashe abinda hauwa take hango min a idon mum ke nan a lokacin take yawa fada min sai nayi hankali da mum don zanga sauyi yanzu a gareta tunda aure ya kullu a tsakanina da Addel.
Gashi na gani hauwa kance min zamu koma dani da mum kamar makiya sai inji haushin zancen inga kawai tana son hadani da itace ta yaya matan data rikeni take kuma nuna min kauna zata koma tana kiyayyata gaba don kawai na auri danta.
Allah ya gani ina son yaya Addel don ba macen da zata kyalla ido a kansa bataji tana sha,awan aurensa ba a zuciyarta don komai da ake bukata ga namiji ya hadasu a wajensa.
To amma na auresane ai harda tausayin yadda mum ta koma akan matarsa dana fahinci dalilin kiyayyansu a yanzu ashe dama mum irin matan nan ne masu kishi da matan diyansu a fili.
Yasa da mun zauna take yawan maganan Aisha take yawan aibantata take yawan shiga damuwa da zaran ta kyalla ido akan Aisha taga wani sauyi na karuwa.
Kurciya ya rufe min ido a lokacin ya hanani hango hakan ga mum da yakamata ace na hango a lokacin don mum irin matan nan ne masu bakin kishin mumuke .
Ke mai karatu idan baki manta ba ai da mun zauna mum ta kama zancen hjy malka da diyanta ke nan a gida tana aibantasu a bakinta sai nagaji na share zance ko kuma wata rana a zauna dani ana tsegumin sai gashi yau ya kawo gareni.
Karfe goma safe hauwa tana gidan mu ina bata labari take fadin mena fada maki besty na hango hakan gun mum dinki tun akan zancen aurenki da yaya.
Irin matan nan da son diyan su ya rinjayi zuciyarsu suna da wuyan shani wajen surukuta donn basu sanin lokacin da suka soma kishin yayansu su koma makiya da matan yayan nasu.
Nasan dole sai hakan ya kasance tsakanin ku ita yanzu Aisha ce kuma ta koma tana kauna lalai mu mata a barmu sai ka zamo abin tausayi za a koma kaunarka watau.
Ki barta ba tace da Aisha zai tafi Abuja ba nace haka ta fada tace to su tafi mana kema ai kin san hanyar Abuja din.
Kada kicewa kowa komai barsu muga iya gudunsu suna isa washegari kema kina isa da yaranki da duk angayanki idan kunje yasan yadda zaiyi daku can din.
Sai kin isa zaki kirasu baba ki gaya masa nima zanje gidan ai in sameshi inyi masa bayanin komai kyalesu kawai muga gudunsu tunda kikaga ta fara hakan sai kin nuna mata kema yar zamani fa zaku zauna lafiya.
Inba haka ba haka zatayi tayi suna tauye maki hakkinki ana danneki da sunan zumunci don ana ganin ke baki isa kaiwa matsayin da Allah ya kaiki a yanzu ba.
Nasan gidan nasa ai babbane yana isan ku dukkan ku tunda gidane me dakuna hudu yabar wanan gidan yanzu ya koma na manyansu shine aiya rudata take son zuwa can ta zauna ita kadai.
Hauwa tace ke kuma kina nan kano kina shan haushi ko ta turata mzamu nuna mata muma yan zamani ai ki barshi a hakan mun dade muna hiran sai bayan azahar ta tafi na samu na kwanta don inyi barci.
Saidai hakan ya gagareni saboda tunane dan zabura nayi don tuno da wani abu daya wuce a baya mai karatu idan zaki tuna zaki iya tuno lokacin da yaya Addel ya saya min wata karamar mota a karon farko yaya mum tayi lokacin sayen motan.
Da farko ta nuna tana so amma daga baya dataga da gaskene saita hadani da tsohuwar motarta ina shiga gwaran gwaran ina jin dadi.
Daya sayo kuma meya biyo baya a lokacin dokokine da aka saka min ashe tun a lokacin nice ban farga da halinda mum ke ciki dani ba sai yanzu da hankali ya fara zuwa min a rayuwa nake gane haka.
Abu na biyo shine dana tuno ya tayar min da hankali lokacin shine nisantani da mum tayi da yaya lokacin daya dawo daga wajen course din yaje waje ina da aurensa.
Tambayan kaina nayi da me hakan ke nufi dama watau mum tayi amfani danune wajen cinma manufarta akan Aisha ko me ?
In dai hakane tabbas mum ko ba kaunata takeyi ba saina godewa Allah dana kasance me yawan kama bakina ina boye sirina a zuciyata sai kuma kawayena dana kan dan fadawa su ban shawara.
Lalai dole in koyi takon saka a zamana da mum yanzu gidan nan tabbas na fahinci mum nada wani irin hassada a rayuwa da ake kira da hassadan mumuke bata son kowa da alheri idan ba nata ba sai kanta.
Tunda har yakai ta iya min hakan kowama zatayiwa matar da nake kamar ya a gurinta yau itace take fitar da hassadanta a kaina haka toko Aisha nata sai yafi nawa wata rana.
Na fahinci abubuwa da dama na kuma gano yadda zan zauna da ita nan gaba har inyi maganin abin karan kaina ba tare da hayaniya ba.
Gidan daddy kuwa abin nema ya samu sai tsegumi akeyi ana murna da gwai da haka ya kasance a dukkan mu dagani har mum din.
Su anty habiba sai zuzuta zancen akeyi harda kari yayin da mummy ke faman sakin magana a cikin habaici don dukkan mu masu laifine a gareta dama.
Mummy don farin ciki har Hafiz ta kira tana labarta masa abinda ya faru shiko budan bakinsa yace.
Na fada maki saina auri zainab koda tsiya wallahi hakan yasa mummy din tace dashi kaidai baka da tunane wallahi kamata yayi ace ka samu wace tafita ba ka tsaya gareta ba tana bazawara ta biyu.
Mummy idan ban rama abinda Addel yayi min ba ai da takaicinsa zan mutu a raina yaron nan yayi min abubuwa da dama da nake da haushinsa dama.
Kaidai ka mayar da hankali ga yarinyar nan yar gidan hjy Asmau dana fadama na bincika akwai alheri sosai ga auren ku.
Baison wanan zancen yasa ya kawar da zancen ya dauko mata wani zance akan mum a haka suka gama wayan da ita don halin bai sauya ba yana ganin tunda yarinyar ba yar hannu bace gidan jiya za a koma yafi son wace zasu sha tare ba maiji ko kuma wace ba zata yada halinsa a gariba.
Jin dadin zancen labarin da mummy ta bashi yasa yayi statturs dinsa da hausa yana fadin SAURA KIRIS DAMO YAKAI GA HARAWA,,,,,
Nasir ne ya kira dan uwan yana fada masa abinda hafiz din ya rubuta kuma yasan da zancen yazo gareshineke nan yasa ya rubuta hakan don haka yake da zaran wani abu ya faru ya dinga rubuta habaici ke nan yana gogewa a wayarsa sai zancen ya wuce.
Ganin hakan ya bata wa Nasir din rai ya kira dan uwan nasa yace kaga abunda mum ta jawo muna ko duk yadda akayi zancen yakai ga hafiz don kaji abinda ya rubuta yau.
Wanan mahaukacine fita zancensa son Allah wake batun hafiz kuma don Allah bros komai mum zatayi akan Zainab ba rabuwa a tsakanin ku don Allah bros.
Yace Nasir ke nan akan me zan saki zainab saidai idan na mutu ko mutuwace kadai zai fidda zainab a gidana kaima kasan da hakan ai
Nasir ya amsa da ba yanzu ba insha Allah sai munga jikokin mu dake tafe insha Allah ni har yanzu na kasa gaskanta hakan daya faru tsakanin mum da zainab wallahi abu kamar almara .
Kabari zan bita a sannu in gano inda matsalan ke fitowa insha Allahu ita kuma zainab din dashi baba garba nasan yadda zanyi handling dinsu suyi cool.
Shiko hafiz ya kasa hakkuri don haka yakira nafisa yana babatu saida ta kwabesa da ranta ya baci ta zazzageshi yace dama ke munufukatace nasan bakya sona da alheri to ko ki mutu sai na auri zainab .
Saidai ka mutu da takaicin haka hafiz tunda kai wawane ashe mata da mijinta bai mutu ba bai sake taba kake kiran sai ka aureta ?
Karka mata yau ko zainab tabar gidan Addel ubanta ba zai taba baka aurenta ba wallahi idan kaika manta da cin mutuncin da kayi masu aisu basu manta hakan ba.
Suka kare wayan da zage zage dama sun saba shine ta kira yaya tana fada mai yadda sukayi da hafiz din cikin bacin rai.
Yace ta fada mai sai yajira inya mutu ya auri zainab din amma shi da zainab kuma har abada sai dai tarihi labarin auren zainab gareshi .
Ni duk bansan anyi hakan ba a lokacin don muna zancen rubuta final pepper din mu mun kuma rubuta lafiya sai fatan alheri a yanzu garemu.
Ranan da muka gama yaya ya sauka gari zuwan bazata yayi muna son sai ganinsa kawai mukayi daga sama .
Duk da dadin da yake ciki na yanayi hakan bai hana a hango damuwa a tare dashi ba a jikinsa don ina daki naji yara na ihun zuwansa yadda suka saba.
Shigana daki kenan ina zama naji yara na ihun Abbani oyoyo harsu laura dake kwaso kayan shanyi a baya part dinsu Aina hakan yasa nasan ya iso garin shiba mutum bane mai tafiya da mota tsakanin kano to Abuja jirgi yake bi ko yaushe don haka ba zancen wani tsaraba a gurinshi.
Sai yazo kano yakeyin duk wani sayayya da zaiyi a nan don haka yar briefcase dinsa yakan riko inya iso umar ya daukoshi daga airport zuwa gida ko wani.
Wanan zuwan kan nasan zuwane da abubuwa da dama zasu faru a gidan don haka na karanto addu,oin tsari da duk na iya a bakina lokacin na shafa a fuskana.
Kana na mike na fito zuwa falon mu inda yake tsaye ya dauki yaran yana masu wasa su kuma masu tafiyan suna lake a kafansa sun rugumeshi.
Nakan ji dadin hakan idan na gansu a cikin wanan yanayin don ba kasafai zaka samun hakan ba wanan ma baiwace gareni daga Allah
Daga bayansu na tsaya ina fadin sannu da zuwa jin hakan yasa ya juyo da sauri saitin inda yaji muryan tawa yana fadin yauwa zainab kuna lafiya ?
Idonsa a kaina kyam yana son yayi nazarina a yadda na fito taronsa din lafiya nace tare da juyawa zuwa kitchen don in bashi ruwa duk da nasan ba lalai bane a wajen mu zai sauka a ranan.
Tunda bai karasa wancan kwanakin nata ya tafi son haka sauka a wajen mu yanzu zai iya jawo wani tsegumi a garemu kuma.
Amma hakkine in basa ruwa tunda da alama nan ya fara shigowa da ya iso har lokacin yana tsaye tare dasu suna masa shirme irin na yara .
Dama shi akwaisa da son yara haka yake kamar baban mu nake ganinsa a wannan yanayin idan yana abu wani lokaci kan yaro.
Kai ku barshi ya huta mana na fada a bayansu na kalli laura nace kwasosu don Allah kutafi gun mama ki fada mata ga Abbani ya dawo.
Tazo da sauri zata kwashi yaran ya dakatar da ita da fadin ki barsu kawai jeki abinki yace wa Laura din .
Ya dawo da kallonsa gareni yana fadin yaushe rabonsu da ganina zainab ki barsu nima nayi missing dinsu ?
Ruwan na aje masa saman table da cup nace ga ruwa hankalinsa naga gwalancin yaran ya dago tare da fadin thanks naga yaran nan sun rame mana ya dago yana tambayana hakan ?
Da cewa nagoyen nace teeth problems ne kasan indan sun fara fidda hakori dama haka suke zama ya fara kokarin zama har lokacin duk suna jikinsa.
Yana binsu da kallo mai cike da kauna da kullawa kafin ya dago yace dani an basu maganin daya dace ko ?
A,a malam ashe kana hanya mama data fito daga daki ta fada ya juyo gareta yana gaida ita cikin dan ladabi irin na hausa fulani na asali tare da fadin mun sameku lafiya mama tace ?
Alhamdullahi yaya aiki kuma ta kara jefo masa tambaya yace da godiya Allah mama.
Wanan karon kan kun dade bakazo gida ba mama ta fada yace wallahi mama banma kasa ga baki daya yasa kuka jini shiru haka

96 / 105