Chapter 81 Reading DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc Arewa Novels

DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   81 / 105

240K to 243K   out of 313.1K words

a wajenka kuma ka basu don Allah gone ai kawai ko kowa ya kama gabansa kuma.
Hakan yasa tun a falin na mum ya tura mata kudi da massage yace su sai abinda zasu saye don jama,anta kinga ai ya raba wanan gardaman a cikin ruwan sanyi.
Banda labarin zuwanta saida mum ta kirani tana ja min kunne kan kada in yarda in kula Aisha ko wani nawa ya kulata azo ana tashi da fitina mu nuna mata mu abin farin ciki ya samemu ba tsaya ba.
Don ba a san dame tazo take kokarin tara gaiyan tsiya ba gidan don suyi dashi tace bata zuwa sai gata kuma ta fado kwatsam an ganta.
Muna gama waya mama Azumi tace sheri dai ya kawota gobe ku barmin yaran nan a daki kona kwashesu zuwa gida wurin hjy har agama taro kowa yazo ya tambaya ace suna wajen kakansu ai yafi anty hauwa tace.
Don in an barsu nan dole wata saida dauka ba asan mugunta ba kowa zata turo don haka mama shawaranki yayi inma zasu sha nono sai a kawosu mu zauna a mota ta basu nonon su sha.
Don tun wajen suna ake samun kafan illanta maka da wani lokaci sai kiga an haifi yaro lafiya daga baya kuma sai yazo ya barkace ai kinga kabilu su basu yarda da hakan ba yawan taba jariri ga kowa mune dai hausawa masu yarda da sauri muke hakan har yanzu.
Shawaran mama din aka aje can gida gun hjy zata tafi dasu baki alaikum ba tare da kowa yasan da fitan mu har ni zanje can zuwa rana zan dawo gidan hauwa tace mu barsu da jama,a anan .
Aina tace tun dazun suke shewa tun shigowan su ni wata data daka min tsawa har saida na rude na kasa gane me take nufi wai na share bayan dakinta take nufi dani aka kwashe da dariya.
Dama ai kinsan dole a jefa ki wanan zancen don kina nan tare da zainabu kingako baki tsira a gurinta kedai ki zauna waje daya irin wanan sai su rude ka su rabaka da arzikinka daga baya kuma suzo su gujeka mama Azumi ta fada .
Haka maigidana ya fada min tun zuwana garin nan yasa in tazo gaisuwane kawai tsakanin mu da ita kuma bata amsa min.
Ko gaisuwan ki bari mana dolene tunda ba ita ta ajeki ba anty hauwa ta fada a hasale mama azumi tace gaisuwa ga musulmi ai wajibine ta gaida ita din tunda tana karkashin mijinsu ne bazai rageta ba ko ya karata sai ma lada da zata samu karshe.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

8?? 0??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Ance komai na babba yafi na yaro mama Azumi na wanan zance muna ganin kamar shirmen zancen sune irin na harkan kishin da can baya .
Ashe zancen mama da kamshin gaskiya a cikinsa don ko biri yai kama da mutum akace saboda matar da kusan sati biyu da haihuwa zuwa ukku bata taba bugu min waya ko mum tayi barka ba.
Sai gata da magariban farko sun shigo ita da halima da wata bakar mace gajeruwa wai sunzo yi min barka a lokacin.
Allah yasa duk kawayena lokacin suna gidan basu tafi ba muna zaune a falo an baje ana ta harkoki wasu sun sallame sallah suna kwance a wajen wasu kuma suna hira sai masu duban waya da lissafi.
Muna can muna magana da mairo ta fado falon bako sallama sai su na bayan natane da dan sallama suka shigo suna fadin tau ashe akwai mutanene haka a gidan.
To sannunku da zama yan ziza duk suka kallota na dan lokaci suka mayar da kansu ba tare da sun tanka masu ba kowa ya share sai anty hauwane ke fadin a,a uwargida sannu da shigowa ashe ana gari ke nan ?
Ta dago ta kalli hauwan data mayar da hankali wajen Aina da takewa bayani taga bata ma ta kanta a lokacin ta kasa fadan abinda zata fada din ta bata amsa.
Tana gamawa da Aina ta sake juyowa tana fadin ku zauna ga wajenan hafsat don Allah dan excuse su dan zauna hakan yasa wace ta kira da hafsat din dagawa da sauri wajen da take din zaune.
Lokacin na dago daga jikin mairo ina fadin sannuku da zuwa anzo lafiya sauran suka amsa da lafiya kalau barka fa ashe an sauka.
Allah ya nufa na mayar masu to barka da arziki barkaka dai sannunku nagode akai shiru can ta motsa a kasaice tana fadin ina yaran fa ?
Suna daki gun mama suna barci anty hauwa ta bada amsa OK ta fada ta sauke wani ajiyan zuciya da har ya dan baiyana a fili lokacin har wasu suka dan kallota.
Mama sun farkane ga mamansu tazo ganin su ta radawa maman da Aishace uwargida ta shigo mama din tafito tana fadin.
Kinsan fitinan su ai yanzu na samu sukayi barci ana tabasu kuma fitina zasu dorawa mutane gasu ai a daki sai gajeran matar da suke tare tace abarsu kawai tunda suna barci farir mama ta hana ko ganin yaran.
Nayi mamakin yadda ta kasa budan baki tagaida mama din har suka mike suka fita daga part din nan suka dora masu albarka irin na mata da ba,a rasawa watau gulmansu.
Mama najin fitarsu ta fito anty hauwa tace welldone mama ina son irinku wallahi ke kiji min yariya wallahi Allah nayi mafarkin hakanne kuma yadda sukazo din nan aka nuna min.
A cikin mafarki kenan tana da wata manufa ga hakan ke nan kinsan magariba irin haka sa,ar muguce idan ana son binka da sheri magari ake tara a turama sherin da sai Allah maganinsa .
Kowa dake falin yacewa mama haba dai ta shiga masu bayani don haka kowa yace ai ya karu sai ya kama kansa da dakinsa a wanan lokacin Allah ya tsare ya karemu amin mussanman yara har ma manya ana aon daidai wanan lokacin mutum ya zan mai kiyayyewa da abubuwa.
Ganin hakan shawaran mama yai tasiri don da gaskiya ban yarda wai aje wani wajen ba bansan ko mama tayi waya da mum bane ban tsamani hakan don ko waya mama keson yi da mum nice mai kira mata ita.
Amma saiga daddy ya turo a daukemu wai aje cen a zana suna tun wanan zuwan yaran basu dawo gidan ba gaskiya nice dai na dawo son abokaina akaci gaba da sha,ani.
Taro yayi kyau sosai anci ansha ba dai wani bidi,a da akayi komai yadda aka saba akayishi wajen sai ga sakon uwargida wai ba,a kawowa mutanenta abinci ba me nake nufi da hakan ta turo Aina.
Nace aina ta fada mata bansan da mutane a dakinta ba son ban fitaba ni aka shirya komai aka kai mata sai gashi tasa an dawo dashi wai basu da yunwa da za a kawo masu abinci a wullakance.
Nan dai dan fitina ya taso don basu kyaleta ba sun mayar mata da martani cewa tasan basu da yunwa suka aiko a basu abincin sunan ko dama gulma yasa ta aiko ?
Sai gata tafito da bacin rai aka fara musayan baki da yan wajena da nata Allah ya takaita saiga shi tare dasu umar kamar an kadonsu gidan daidai wanan lokacin.
Rai bace ya fito mota yana tambaya azotonshi daga wajena akaso a raina mata wayau ya watsa taron matan yan suna kawayena sai hauwa ce ke mayar masa da ba,asin abinda ya faru ya juya cikin mamaki yana fadin .
Aisha ina ruwanki da harkansu ina na baki kudin naki jama,an da zakiji dasu don nasan halinku koka ban banda hakkin abincin ne koba da kudinka aka sayaba da baza abamu ba ?
Ke ban baki naki ba da zakiwa mutanen ki don gudun irin haka meyasa ke baki son a zauna lafiyane wai Aisha ?
Ooh dama nasan haka zakace maciyi amana har nawa ka turo min da kake shalana cewa aika ban kudi har ina kudin yake da zakayi min gori a nan ?
Umar ne ya jashi suka tafi har ya juya yaji tana jefanshi da kalamai masu zafi da tonon asiri ya juyo ya dawo yana fadin ke Aisha nagaji haka iam tired of dis nuses kitafi gidan ku don Allah.
Wanan ya bata zafi don me zaice mata hakan agaban kowa don haka tace ba zan tafi ba idan ka isa ka sakeni Aliyu sanan isan an shanyeka ko an gama dakai yanzu OK haka kike so tace eeh.
Umar na jansa idonsa ya kade yayi ja abu ga farin mutum da kyar umar ya samu kansa ya fara tafiya sai yaji tana fadin baka cika namiji ba ashe yan uwan suna ta tausanta hakan yasa.
A fusace ya juyo yace kije nasake ki Aisha ya juya yacigaba da tafiya rai bace abinci sukazo dauka sai hakan bai samu ba a garesu lokacin.
Don sun bar wajen da bacin rai sai mairoce ta bisu da abincin inda suke gidansu umar haka taro ya watse kowa da abinda yake fada don karshe dai kishi yasa Aisha hauka tajawa kanta abin fade ga gari.
Da ace tayi hakkuri ba wanda yasan me ake ciki a gidan yadda ya shirya har a watse wasuma ba zasu san tazo ba hakkuri nada dadi ga bawa ya gani ya taushe kamar ba,ayi ba.
Wallahi har ga Allah banji dadin abinda ya faru ba a ranan don ta dalilin diyana za ace haka ya faru da ita haka kuma wani sabon kiyayyane zai kara afkuwa a tsakanin mu yanzu da ita.
Wanan yasa har aka watse jikina yana mace da abinda ya faru don basu jima ba akace sun kwasa sun fita da yan uwan nata kosu da tabi ta nasu da hakan bai faru ba a lokacin gaskiya.
Nan dai labari yakai har gidan daddy don su anty nafisa da halimatu suna gidan abin ya faru zuwansu ke nan ba,a jimaba ta aiko da zancen a basu abincin a lokacin.
A gaban idonsu kuma akai komai don suma sun tofa albarkacin bakinsu a matsayinsu na yan uwana suna kare bangarena a wajen fadan.
Wanan yasa sukaje gida da labari hankalin mum ya tashi sosai a lokacin ta kira layin yaya bai shiga don haka ta kira layin daddy ta sanar dashi abindake faruwa.
Shima hankali tashe yabar kasuwa zuwa gidan namu saidai bai samu yaya a gida ba nan ake sanar dashi yana gidan umar can ya nufa nan basa gidan sun fita a lokacin hakan yasa ya dawo gida.
Yana fadin bai samesu ba ai duk inda yaje ko ina yaje aizai zo nan ya samemu an fada mashi ana daka ta matane ko wani lokaci.
Allah yagani tun farko banso malam da wanan yarinyar mara tarbiya ba son koni nan akoda yaushe muka hadu jira take in gaida ita sam bata da tarbiya don yarbiyansu da namu ba daya ba.
Don kada yace ban sonsa da alheri yasa na yarde masa alokacin yanzu gashi ta hanasa zaman lafiya agidansa kome take ji irin yau ai boyewa akeyi har a watse taro amma irun haka a bainan jama,a abin baiyi daddy ba gaskiya.
Daddy dolene bakaji irin zagin da take masa bane agaban jama,a nasan wanan ya bashi haushi har yakai ga saki yanzu dai ai tajawa kanta zagi.
Yau ta fara zaginsa yana hadewa hakan dai dama ya kullawa zuciyar shi sakin yar mutane tunda an hura mashi kunne ga mai haihuwa ya samu yanzu.
Mummy ce mai wanan maganan da mamaki Alh ya kallota yana fadin aiga irinta nan za,ace ke kika haifo wanan yar wurin mugun hali malka.
Yanzu wa zai hura mashi kunne ya saki matarsa don Allah inba neman magana ba irin naki ke kuma bansan meyasa baki tauna magana ba kafin ki furtashi malka ya juya ya shige yana tsoki akanta.
A dada dama zancen gaskiya yanzu daci garesa ai tunda Addel ya zamo dan gaban goshinka yanzu ai ba a fadan zancen yayi baki haka kowa yaja bakinsa ya watse ya barta tana babatu a wajen.
Kafin Aisha ta isa Usaina data fita da fushin zuciya ta rigata isa gidan take fadawa mahaifiyarsu abinda ke faruwa da yar nata.
Bakin ciki da takaici ya rufe uwar tace ai takai ga abinda takeso ya mayi hakkuri da aka kai haka ai wani namiji zai lamunci wanan iskancin na hummaira ?
Koda ta iso da kuka ta fara fadin mama wallahi Aliyu ya cuceni ya zalunceni uwar tace kika zalunci kanki Hummaira sonkai da aon duniya yau yaja maki zuban mutunci a gaban jamma,a.
Bayan mijikin ya baki kudi kiyi naki sh??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????agalin wani rashin hankali yakaiki zubarwa kanki da mutunci zuwa tambayar abokiyar zamanki abin wajenta kuma ?
Kinbar yan uwanki a zaune kinki ki saya masu abinda kuma zakuyi a part din kamar yadda yace kiyi masu amma kikaki kika tura kuma tabaki amma son jan fitina saida kika nemi tashin hankali son kawai ke baki da kwabo.
To yau kinkai ga yadda kikeso kin a rayuwanki ga daki can a share saiki shiga ki jira Abbanku ya dawo shidake kama maki iskan cin dakikeyi din baison a kwaba maki toga irinta nan yau ai.
Usaina tace mama nifa shawarana kawai ta koma dakinta tunda bai furta ko saki nawa bane yayi mata uwar ta dan kallota cikin harara tana fadin ko nawane ma ita tajawa kanta.
Yanzu dole ta jira ai ya dawo kada yazo yai fada daga baya kuma jin hakan yasa ta kwasa tayi daki cikin fushi ta barsu a falon suna mayar da yadda abin ya faru.
Ban samu kaina ba sai shadayan dare su Rukkaiya da Aina sun gama gyaran ko ina na gidan kamar bashine aka jagalaba a dazun muka zauna muna hiran abubuwan da akayi nan mama ke fadin.
Yanzu ita yar nan ta tafi gidansu ke nan nace haka akace wai ta rufe gida tun dazun sun fita dama abinda kubura kewa gudu ke nan gashi kuma ya faru.
Tace zaman ta can shine kwanciyan hankalinta a yanzu ayi bukin nan lafiya don da taji bata zuwa taji dadin hakan sosai a ranta sai kuma kwatsam gata tazo ashe da fitina tazowa mutane.
Don in kawar da zancen nace mama kun tuna kun anso maganin a wajen mum kuwa tace kin gani ba gaba dayan mu mun manta daga ita har ni yana nan kuma faloun bari ai tace gobe zata shigo ta ganeku.
Nayi dariya ina fadin mum dai zatazo wajen mazajentane kila amma ni ko yau naje gida ai ta ganni sallamanshi mukaji muka amsa mashi.
Abinka da wanda bai saba sa manyan kaya ba yana rataye da babban rigansa a kafada alama dai ya nuna ya gaji ko kuma zuciyarsa ba dadi a lokacin.
Saida ya zauna ya fara gaida mama da gajiyan taro itama tayi mai yaya jama,a yace Alhamdullahi ta dora Allah ya raya muna su ta farkin addinin musulunci ya amsa da amin mama.
Kallonsa nayi nace ko a kawo maka abincine a kasalance yace dani No iam OK banda bukatan abinci yanzu dama dan ruwan tea insha in kwanta son ko abinci banci ba dazun.
Ina zakaci abinci malam ga jama,a ga kuma wanan tashin hankalin daya faru abinda hjy kubura ketawa gudu ke nan tun farko wallahi tana saman bakinta ayi lafiya a watse lafiya sai ga haka ya faru kuma.
Matsalantane mama a cikin mutane Aisha zata kama yankan kauna haka me nayi mata for god sake muna gudun zuciyarta tana ganin kamar tsoranta ake ji yasa ban iya daukan mataki akanta.
Mama kin sani yarinyar nan ina tauyeta da yawa akan Aisha wanda duk na fadawa tun aurena da zainab ban taba zuwa da ita abuja ba koda sunyi hutu zaiyi mamakin hakan ?
Aiba bata son zuwa bane mama amma tayi hakkuri bata taba fada min wani magana ba kan hakan har yau sai ita don samun waje.
Zaki yarda mama har yau bakina dana Aisha bai hadu tayi min barkan zuwan yaran nan ba wai ita ta nuna min iyakana akanta nayi hakkuri mama amma hakan bai isheta ba sai tazo nan ta tayarwa mutane da hankali abanza.
Akan me nagaji wallahi fitinan Aisha ya iaheni mama gara a rabu kowa ya kama gabansa yafi mama tace ai zainab tana da hakkuri dan zaman nan da nayi da ita nagane hakan.
Haka kuma akeso da mace ta zauna iyakarta karta wuce gona da iri amma hakkuri zakayi ka barta tasha gidansu na dan lokaci ta gane banbancin

81 / 105