DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   68 / 105

201K to 204K   out of 313.1K words

cincin din akeba yan zuwa ganin amarya ba.
To mum yadda kike fadin abinne kamar yayi yawa ai duba ga yadda baba basu da karfi suka kashe jiki haka da dawainiya shi nake nufi ai ba wani abu ba.
Wanan kuma sunga suna da zarahin yin hakan ne ai kuma wanan auren sun fifitashi da wancan na baya yasa sukayi hakan.
Aiko yau hjy Marka gidan nan kamar tayi hauka jiya don ba wanda ya biye matane ai yasa zancen ya mutu an kumax ce Nafisa ta dawo ta tarwatsa zancen yasa sukai shiru.
Akan me kuma mum ke fada ya tambaya cikin mamaki mum tace wai ba,a fada mata zancen tarewan ba don haka an munafunceta ita.
Shiru yayi ya mayar da hankalinsa ga wayansa muje kagani don hakkinkane ka gani din ya dago yana fadin in gani kuma aiba saina gani ba iya yadda akayi dasu mana mum .
Tace muje dai don ni ajesu a can hankalinna bai kwanta da hakan ba kuma yanzu a debewa kowa nasa a mika masa yafi ta mike tsaye don dole shima ya tashi don bin umurninta.
Sun samu daddy bai fita ba bayan sun gaisa mum ke fasin nace yazo yaga kayan nan ansan yadda za,ayi dasu abawa kowa nasa don hankalina bai kwanta da barinsu haka ba.
Me zai samesu wai kina gudun wani yai wani abu a,a Alh a dai raba a fitar masu da nasu abawa kowa nasa kason zance ya kare tunkan mutane suyi yawa kuma.
Mikewa ya Addel yayi yana fadin barin leka Nafisa kafinta fita ashe kowa ya santa da yawo har aunyi hutu bata huta ba ita kullum fita takeyi lamarin nafisa da yarinyar nan halima yana damuna sosai wallahi.
So nake a gama wanan sha,anin insasu gaba kowa ya fito da miji ita wanan dake zaman banza kota koma gaban iyayyenta su karata can zai fi sauki.
Lokacin danaso mata gata suka nuna ba hakaba a gareni hjy kuma ta kama masu yanzu sai su san yadda zasuyi da ita.
Ficewa yayi bai tsaya ba ya bar mum da shi a falin suna magana ya nufi bangaren mum a falo ya samesu ya shigo da sallamanshi.
Fuska daure har lokacin mum ta amsa mashi anty Nafisa na fadin angone kai ashe abu haka babu notices ba wanda ya sanda zancen.
To ya za,ayi nima haka zancen yazo min naso a barta ta karasa amma su daddy sunce ta karasa a gidana shine suke fada min ahekaran jiya nace shike nan ai Allah ya bada zaman lafiya ya amsa da amin kafin yace taso muje mana indan ganki.
Tana dariya ta mike tana fadin in kaji kira sa,ace akace yace har na yan sanda ta kara kwashewa da dariya ba wai fita sukayi ba anan falon ya dan gwaucewa idon mummy kawai.
Toke ya wani shiri zaki munane don yaran nan sunce wai zasuyi dinner kinga akwai bakin da zasu daga Abuja wanan kuma kena dorawa alhakin hakan.
Yanzun dai kiyi tunane abin breakfast da abincinsu na two days da wani hidima sai ki fada nawa zan tura maki duka tace wai lalai sai na zauna tunda kaga dole akarramasu ai.
Yace haka nake son ayi kafin tayi magana yace bari in turo maki dubu dari biyar mugani nan take a wajen ya tura mata kudin tace zasu kai su nawa yace zasufi goma ko ashirin haka don yan office din mu duk sunce zasu zo insha Allahu.
Dole odan wani abu za,ayi ke nan amma dai bari mu gani sun dan jima suna magana kafin yace zai tafi lokacin har ya juya ya juyo yana fadin.
Aff kin gani ko dana shafa sainn fita in tuna kuma mummy nace da in tura maki wani abu son bakin katsina nasan wasu a nan zasu sauka kada dawainiya yai yawa.
Ai daka barshi Addel don iyayyenka basu sani a zancen ba boye min sukeyi da sauri yace mummy kuyi hakkuri don Allah ba wanan zancen a tsakanin ku don duk daya muke daukanku mu
Nan ya tura mata subu dari biyu sai godiya takeyi kamar da gaske har ya fice daga part din zuwa wajen mum.
Ya samu an fito da wanda zai tafi dashi gida ya aje wai namu don dole ya dauka ya tafi dasu andai fita wanan kunyan kuma mum ta fada.
A falon mummy kuma yana fita Nafisa ta kalli uwar tana fadin mena fada maki mummy indai Addel ne ba haka bane kin dai gani yanzu karshe mune da harkan ai dubu dari biyar fa ya turo min gasu.
Nawa zan kashe dan kayan hadi zan sayo mu hade dasu Raliya a dinga hada masu komai ba shike nan ba gasu antyn ku habiba ai sun iya suma to zance ma ya kare ai.
Suka shiga lissafi mummy don bata da kunya itace me tunawa da wani abin son Nafisa tace abincin alfarma zata dinga masu don gyara hanyan gobe.
Anty habibace ke fadin ina matarsa ba zatayi masa ba ita ta fadane da tsigar gulma amma sai mummy taga kamar hassada ta nuna meyesa aka basu suyi su ga matarshi.
Cewa mummy tayi ai yaga matarsa ya kawowa yar uwarsa aikin sai kije ki fada mata ai da sauri tace haba hjy ba abinda nake nufi ke nan bafani.
Ato na dai fada duk wanda za a fadawa aje a fada shiru anty habiban tayi akaci gaba da lissafin abinda za,ayi din itama mum a bangarenta ana ta faman shirine.
Yana isa gida suka hade da anty Usai ya fito suka gaisa ga mamakinshi hakkuri yaji tana bashi nan take fada mai ai zata dawo kafin a tare din shine mukazo mu dan gyara mata waje dama sai bamu sameka ba ya fito da key ya basu ya juya yana kwalawa habu maigadi kira bakin get.
Yana zuwa yace kwashe kayan nan ka shiga masu dashi nan ya juya yana kokarin nufar part dina ya budewa maigadi don yasa kayan ciki.
Shima shiga yayi ya zauna a ciki donsu Usaina dake gidan saman dogon kujera ya kwanta a falo yana tunanen duniya a haka barci ya soma daukanshi yaji bugun kofa ya fito maigadine yake fada mai bakinsa nason su wuce.
Ya fito sukai sallama dama yasan ba wani abinda zasuyi kawai zancene na mata kofan ya rufo ya koma dayan part din ya sake kwanciya.
Daga nan kuma ya fito ya nufi masalci yai sallah bai dawo gidan ba in Allah yana son bawa yakan kareshi daga duk wani sheri daka iya samunsa a cikin rashin sani.
Haka Allah ubangiji ya karesa a ranan don haka kawai yaji yana son zama a dayan fatan din kawai sai ya nufi can ya kwana wanan yasa duk wani kuli na Aisha akanshi baiyi tasiri ba.
Gashi ba karamin kudi suka kashe ba wajen wanan aikin amma kuma yadda akaso bai samu ba anyi hasaran kudi a banza rabon bokansu ya koka a ranan kansu.
Saboda karfin gwiwan malamin da suke dashi yasa ta fara shirin dawowa gidan with full confedence nacewa aikinta yanzu zai fara aiki sai tsiyan dataga dama ta tsulla a gidan kansa.
Sai Allah bai karba mata ba ya ingizashi zuwa kwana part din da sau daya ma ya shigeshi yaga yadda aka tsara komai a cikinsa .
Bai kuma tashi yabar part din ba sai misalin karfe biyu yayi wanka ya fito a can dayan part din nasu ya bar gidan zuwa samun abinda zaiciwa cikinsa.
Itako tana can ta hau ta zauna tunda tasan cewa ba inda zai kwana a yanzu dole sai gidansu ai nawa ba a saka komai a cikinsa ba tukun don haka dole maganinta zaiyi aiki a kansa ke nan.
Ina kwance kasan dakina son su Mairo suna saman gadon nawa sun baje a sama gadon suna iya shige shigowa yayi don yaci abinci don tun safe yana kwance bai fito ba kinsan.
Muryoyin mu da yaji yana tashi duk sun karade sashen mum din dashi haka ya daure ya shigo yana mamaki yayi sa,a mum suna falo tare da kawarta hjy Fattu .
Gaidasu yayi da wuni kafin mum ta dora da tambayanshi ina ya shiga tun safe baizo ya karya ba yake fadin wallahi ina gida kwancene.
Ita Aishan ta dawone bata dawo ba jiya dai yan uwanta sunzo sunce wai sunzo gyara mata waje zata dawo amma bata dawo dinba tukun.
Ke nan baka karya ba har yanzu hjy Fattu ta fada cikin mamaki ya danyi murmushi yana kaiwa zaune yayin da hjy Fattu ke fadin don Allah ku bashi abinci yaci.
Wanan ai daukan alhakine hjy kubura gara da yaron nan ya kara aure yanzu Allah kadai yasan bakin cikin da yake kumsa a rayuwansa.
Wanan wace irin hatsabibiyan yarinyace haka wai ka daukowa kanka yaron nan hjy kiyi shiru don baya son ana aibanta ta a gabansa yanzune zai bata maki fuska mum ta fada.
Au hakane wai babana shidai yayi murmushi kawai kafin yace su waye haka ke surutu ne wai duk sun ruda gida da hatgitsi haka ?
Kawayen mamane sukazo su sun fara bukine ai don tun jiya suke yini gidan nan ina take tazo ta ban abinci don Allah ya fada.
Indai tashi in debo maka ina zan fito da ita wurin abokanta yanzu haba hjy kira masa matarshi ta bashi ai gara ta san hakan tun yanzu .
Ta san cewa yafi abokan nan daraja da kima a gunta ke zainab hjy Fattu din ta kwala min kira can naji na fito da sauri ina fadin gani.
Ganinsa yasa na dan noke son girshi na gansa zaune kallo daya nayi mai ina fadin ina wuni haka din don Allah kawowa mijinki abinci yanzu bai karya ba tun safe .
Yana da mata biyu a gari kuna barinsa da yunwa haka idan ita bata gida kin sani ke gari ya waye bai kamata ki kirasa ba kiji me zaici ki girka masa nan ?
Kai hjy Fattu akwaiki da daurewa karya gindi wani lokaci ai sai ku bari sai taje gidan nasa ki fadi hakan ba yanzu da yata ke gabana ba.
Hjy kinji ko haka suke min tunda na dawo kasan nan nidai na juya na tafi kitchen na hado mashi abincin ina dawowane nake jin hjy fattu din na fadin.
Kaikan ka huta baka biyo hakin masu sunan naka ba dama ance ba,a taruwa a zama daya yau na sheda hakan.
Na aje abincin na juya take fadi a cikin tsawa shi kuma zai zubawa kansa abincin da zaki tafi da sauri na juyo ina fadin zan dauko masa ruwane hjy don Allah zuba masa sai kije ki dauko ruwan haka zakije kina sanyin jikin nan naki da uwarki ta bataki dashi tun a nan.
Dole ka canza daga ita har wacan mara kunya gudan ya zama dole ka daukarwa kanka mataki akansu dukkansu narkakune ka tara.
Itama wanan din ai hjy ta sagartata da komai a gidan nan wucewa nayi don harga Allah zancen hjy Fattu bai mun dadi ba a cikin raina itako yadda na fahinta iya gaskiyanta ke nan ta??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ke fadi a lokacin.
Ba yadda na iya duk da ganin da nakeyi tana yarfani a gabansa amma kuma gaskiya ta fada ai ya zama dole in zage damtse na wajen kyautatawa yaya a yanzu don ta nan ne zai banbamce tsakanin mu da Aishan a rayuwa dama kuma shine kishin da ake fada a tsakanin mata.
Kodana koma zaune kawai nake amma bani cikin sukuni a lokacin saboda zancen hjy Fattu a kan mu don na rasa shawara take bashi ko nasiha.
Sallama akayi dakin daga inda nake kwance rakube na dago ina amsawa anty Jamilace ta shigo muna da drinks sai snack a wani leda mai tambarin shagon da ake sayar .
Gashi ango yace akawo maku kuyi hakuri au yaya ya shigone dama anty hauwa ke tambaya hakan naji tace ya shigo ya fita kuma.
Sunji dadin hakan sosai gaskiya zama suka min zakice wanan ne aurena na farko don sai motoci suke fakawa a gidan sai faman gaiyatan yan school din mu akeyi wajen masu class don kawai abin ya bada cita.
Aiko ba gidan daddy ba don ko unguwa ya sheda ana sha,ani nayi mamakin ganin yan katsina haka da yawa wajen tarewan nawa.
Duba da yadda auren namu ya kasance hakama gidan iyayyena yan uwan inna dana baba sunzu daga bangarensu suma ana can ana dafe dafe da soye soye kamar yadda gidan daddy ma ya dauki cida.
Kowa baiyi tsamanin hakan ba abune kawai daga Allah inya tashi ma daukaka second yayi yawa ga hakan ya samu ga bawa.
Wajen dinner haka yai jama,a daga Abuja da sauran wurare nan ne kowa yasan ni wanda kuma a bangarena basu san angon ba suka sanshi a wajen.
Ranan kuma matarshi Aisha ta dawo a haukace don labari ya isar mata kan zancen dinner da aka shirya din mamanta tace dama na fada maki ai.
Ko dake ko babu ke tunda yayi niyar ba za,a fasa ba ke baki san waye ake kira da namiji ba ke nan har yanzu.
Garama ki koma dakinki da wanan barnan sunan da kike son yiwa kanki tayi kuka sosai a ranan mahaifita dasu halimansu suka rakata har dakinta mahaifinta ya kaita yana bata magana.
Ba,a jima ba take ta ganin bakin Abujansu suna isowa wasu da matansu wasu kuma da taron abokai saboda suna jin dadin zama dashi wajen aiki mutum ne mai haba haba da jama,ashi .
Suzo su bata magana su wuce don ba fuskan wasa a gareta bata taba jin dadin shawaran mahaifiyarsu ba irin ranan donko shawaranta yai mata amfani sosai take gani a lokacin.
Ayi lafiya an watse lafiya don itama danginta sunje wajen amma ba wani hayaniyar da akayi tsakani kowa ya kama gabansa.
Saidai mutane suna mamaki yadda auren ya dauki lokaci haka amma ba,a sanda hakan ba sai yan kalilan ne suka sani muna dawowa mum take fasin a gidan baba zan kwana gidan mahaifana ke nan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6?? 8??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Nayi mamaki kwarai lokacin dana shiga gida na samu na samu gidan namu a cike da mutanen kauyukan iyayyena duk dani tunda muka barcan din ba zuwa nakeyi ba.
Naji dadi sosai haka na kama binsu ina gaidasu a cikin mutunci da girmamawa a garesu suna nuna jin dadin hakan tare da fadin.
Wanan zainace ta zamo haka lalai boko yayi nisa Zaina kece kika koma haka kin zamo wata babban mace haka dake tubarkallah masha Allah.
Kowa ya furta abinda zai fada saiya dora da tubarkallah masha Allah acewan su wanda bai fadi hakan ba yana da wani manufa akan mutum ke nan da zancensa.
Dakin baba na shiga don nan ne ba kowa anbar masa dakinsa sai inna kawai ke shiga yasa tace inje can in zauna din.
Kayan dinner dake jikina nake kokarin cirewa a lokacin zan daura zanin inna data ban in sauya kaya naji ana sallama.
Ya Nasir ne ya shigo don sun iso da yammacin ranan yana dauke da dan akwatina na kaya karami sun gaisa yake fadin ina amaryan take ga kayanta ance a kawo mata.
Inna ta fito suka gaisa tana mashi sannu da zuwa ya amsa tare da tambayan lafiyan kowa da taro kuma tace Alhamdullahi .
Bayan sun dan taba hira ta nuna masa dakin baba da cewa ina ciki ya karaso yana sallama na amsa ya shigo yana fadin.
To ga kayanki ance na kawo maki don angoki nacan suna bom da matarshi tace bai shiga gida ta hana maigadi ya bude masa gida.
Kai ya Nasir banda sheri gidantane da zata hanasa shiga ko tayi haukane naji yace kifada dai koma sai yau na tabbatar da yarinyar nan bata da mutunci wallahi.
Kinga irin yadda ta kunyatashi a gaban abokansa kuwa gaskiya ashe gara da hakan dai ya faru don yau kowa ya sheda halinta.
Ni nayi kundunbalan shiga gidan na samu na bude ta kori maigadi waje ta kulle gida ta ciki ita da wasu mutum biyu suna ciki yan uwanta.
Zata taso min nace wallahi tasanni sarai yanzu ta kawo haukanta a kaina harbe shegiya zanyi in kashe banza na fito mata da dan pistol dina hakan yasa ta jefo min key.
Bari yau naso in daki yar iska iya son raina amma aka hana har na fito din nan banji motsin yar iskaba kuma .

68 / 105