DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   90 / 105

267K to 270K   out of 313.1K words

gidan dasu.
Na fito ina gaidashi ya amsa tare da fadin zainabu yaya yaran da ita gwaggonki dai nace lafiya muke baba tana gidan mum muka barta sai zamu tafi mu dauko ta .
A,a yau bata shigo mun sada zumuncin ba ke nan aina sameta gidan in gaida ita baba ya fada gun butan da baba yayi alwala ya nufa ya daga akwai ruwa a ciki baba na fadin a karo yace zai isheshi ai wanan muka shiga na barsu da yaran masu tafiyan zasuje sallah tare da baba.
Da Asiya na fara cin karo tana shanya kaya a haraban gida tace lah anty kuna tafe ashe tazo ta karbi yaron daya da sauri a hannnu tana fadin wai kina kokari anty yaran nan masu nauyi kika dauka haka ?
Allah dai ya kaimu mugani inkin samu yaya zakiyi ke kuma tace nikan banson tagwaye anty nace baki kaini ba ai yanzun ko dole na ruguma ai.
Ina inna na tambayeta ta nuna min daki tace yanzu tayi alwala ta shiga dakin na nufi dakin ta biyoni a baya tana fadin na zatafa jiya harda Rukky za azo ashe bada ita bane ?
Jin hakan yasa na juyo ina fadin haka kawai zata taso ta biyo maza tana dai tafe tace amma nasan sun dai fadane na shiga da sallamana inna na zaune tana jiran a kira sallah tayi muna sannu da zuwa na dora mata yaron a jiki na juya zuwa ciki don marana cike yake da fitsari a lokacin tun a gidan mum naji fitsari amma na kasa shiga inyi don fargaba.
Koda na fito inna ta tayarda sallah nima sallah nayi don na dauro alwala a lokacin bayan mun idarne muka kara gaisawa tana tambayana mama nace tana gidan mum.
Don yanzu kamar mum nason mama ta dawo wajentane nake gani ita dai mama dince taki yarda da hakan ba zata yardaba kuwa yadda take yabawa din nan taji dadi sosai zama daku tana fadi tana kari.
Toni bansan meyasa mum ke son tabar wajen muba amma kila shi yasani tae a dole shi ya sani ai koma meyasa shi bai rasa sani idan tace ta koma kada kice dasu komai ba ga yan aiki har biyu ta turo maku ba saidai yaran ne yanzu ba abin yarda bane shine amma yaya zakiyi dole kiyi hakkuri da hakan.
Inna na fahinci akwai wani matsala yanzu tsakanina da mum don yanzu take fada min sun yanke shawaran cewa matar yaya zata dawo dakinta.
Ita hjy din ta fadi haka nace yanzu daga can muke tace Allah ya kyauta saiki kara hakkuri don Allah ki kawar da idonki a zancen nan aishi malam din yasan abinda yakeyi inma wani abu a kasan hakan .
Haka kuma karki yarda ki nuna wani abu akan ita gwaggonki a yanzu kici gaba da nuna baki fahinci komai dake shirin faruwa ba kar kuma ki yarda har danta yasan hakan kin dai san tsakanin da da mahaifi ba zaiji dadin kasancewan hakan ba tsakanin ku don zaku raba mashi hankalinsa.
Shigowan baba yasa mukai shiru dagani har inna din dake magana ya shigo da yaran yana ba,s kafin yaya din shigo bayansu yana gaida ita inna a cikin ladabi.
Tayi masa murna da fatan alheri ga karuwan daya samu din dan wake sukayi aka kawo muna dagani har shi bamuci ba sai yaran suka danci kadan kafin mu taso zuwa la,asar zuwa gida.
Bayan naga sun kebe da baba sunyi magana na dan lokaci da zamu tafi baba ke fada min yana nan zuwa gidan namu ai insha Allahu.
Hanya ya dan tsaya ya sayawa yara kayan sanyi dasu chaculate muka nufo gida kai tsaye duk da muna dan magana sama dashi amma sai yake ganin fushi nakeyi dashi a lokacin a ganinsa.
Saida yayi sallah la,asar yashigo ina dakina kwance ina waya da Rukky ya shigo don ya gane nake fadin ai Asiya halinta sai ita kedai Rukky inna ma cewa tayi ba zata yarda ba ai sai dai in a nan kano zatayi karatun nata.
Rukky ce ya tambaya daga inda yake tsaye na daga masa kai yace ke matar kabila da hadin bakinki akaki barin Asiya karatu ko taji muryanshi tana dariya tace yaya numa ba kun hanani yi ba lokacin.
Donshi kika shiryawa Asiya bom ko to zatayi na roki baba ya yarda tazo nan Abuja tayi karatun nata ai sun dan jima suna zance dashi yace dani karbi ban iya tabaran Rukky ni.
Abinci fa naga bakaci komai tun dazun ba ya juyo yana fadin cenake tare zamuci ai naga kema kamar tun fitan mu baki ci wani abuba ai.
Ban bashi amsa kai tsaye ba sai mikewa da nayi ina sallama da Rukky ina fadin ke bari zan kiraki zan bawa Abbani abincinsa don haka yaran ke kirasa nima nakama kiran hakan har ya dan zauna min a baki kalman.
Falo na fito na samu ya koma daki nan na tsaya muka gyara kayan abincin tare da yaran nan nake tambayansu idan sunci abincinsu sukace sunci tun dazun gaban Aina suka dibama.
Meye sai kun kira aina tagani idan zaku dibi abinci ku diba kawai kuci mai isan ku idan kun zuba muna namu ai ita Aina tasani ban hana kowa diban abinci gidan nan.
Nan ya fito ya samu ina wanan maganan dasu dinning din ya nufa kafin na kira yaran mu zauna tare banci komai ba don hankalina yafi karkata gun abincin yaran dashi.
Baya mun gama ya koma ya zauna a kujerun falon dama nasan yana da wuya ya kara fita tunda naga ya saka jallabiya a jikinsa ya fito.
Kitchen na shiga muna aiki don ina rage aikin safe saboda makara daddy ya fara sintirin neman mama ua shiga dakinsu ya fito har dai ya fara kiran mama mama da dan karba hakan yasa nafito dole na samesu.
Rarashin yaron na farayi ina fadin mama tana bayi tana wanka uban naji baice komai kan zancen sai dai karshe yacewa yaron yazo ya dauke masa hankali da game a waya.
Kafin ya dago yana fadin ina son a saka yaran nan makarantar islamiya amma ina tunanen sunyi kanana su kadai da zuwa ba wani babba a tare dasu don can inda yaran umar ke zuwa nake son sakasu.
Karfe nawa ake shiga yace ina ganin four na yamma su taso six sai na safe kuma idan ba,a boko yace eight na safe a taso eleven.
Hakan zai yuyu don banda time din kaisu a yanzu saidai idan na gama karatun nan yace No nariga nayi magana an samo min driver da zai dinga kaisu ya daukosu kuma.
Makarantar yana da kyau sosai gara su fara idan sun kai four years zasu fara boko haka na tsara banson yaro yayi saurin shiga school sai ya fahinci wasu abubuwan rayuwa daga addini dana tarbiya kafin ka mika yaron ka makaranta.
Dan shiru nayi kafin nace saidai idan da manira za,a sakasu kaga ita tanada wayau a cikinsu zata iya kula dasu ai cewa yarinyar karama da mum tasa aka kawo muna don dayan ta dan tasa gaskiya.
Suma din ina son ki sakasu a boko ai su fara karatu don zamansu haka kamar ba,a taimaki rayuwansu ba nake gani tunda duk yan gida kama.
Nayi wanan tunanen sai naga za,aje hutun karshen zango yasa banyi magana ba amma nima nayi tunanen hakan.
Nasan zakiyi tunda kinsan amfanin karatu kallon yaron nayi naga yayi barci yasa na mike nakoma kitchen din na barsu a wajen.
Dare yayi yaron ya saka muna kuka yana neman mama nan na falfaleshi lokacin uban ke fadin kiyi kokari ki saba masu zama ba mama don Allah don na fahinci mum yanzu bata son zaman ta damu.
Nu lurar da ita ba abinda zai faru tace a,a ta dawo wajenta dai ban san me hakan yake nufi ba don haka ko tambayan dalili kada ki somayi kyalesu kawai da ita a can.
Kwanansa biyu ya koma Abuja ya barmu monday yara suka soma zuwa makaranta bayan umar ya kwashe yaje yayi masu register da yamma driver da suka dauka ya dawo da yaran dan daddijone me neman abunda zaici da iyalinsa.
Sati daya da komawa Rukky ta kirani a bakinta naji wai ashe an mayar da auren yaya da matarsa dazun baba ke fada mata data kira ta gaidashi.
Naji zafin rashin fada min bda baiyi ba amma kuma na koma naba kaina shawara don haka na zuba ido inga gudunsu.
Na zata a ranan zata tare amma sai naji shiru banji sun shigo ba banyi kasa a gwiwa ba wajen sanar da aminaina zancen washe gari suka dai ban magana bai wuce inyi hakkuri ba.
Dama kuma shidin ne dai akansan me kishiya dashi mun aje akan mu tsaya muga gudunta hauwace ta dan kara hada min kayan gyara duk da ba damuwana sukayi ba.
Har sokoto ta aika aka kawo mata hadi na musanman ba suna ba kayan el,sutra shine karon farko da ta taba banso nasan sabon hadine wanan yanzu kuma ta binciko ta ganesu.
Ta yaba kayan sosai da takawo min tana fadin in dai gwada nida kaina zan nemesu daga baya hadine na musanman ba kissa a cikinsa tace .??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????
Na karba tunda naje na saka a cikin drower ban bude nagani ba komeye a cikinsa da kwana ukku Aisha ta tare a gidan bayan sun gama hayaniyarsu da gude gude can mukaji shiru alaman sun tafi.
Hakan yasa nasan oga zaizo ke nan kila ranan ko washe gari tunda ga matarsa ta tare saidai har dare bai shigo ba.
Kamar da can ba ruwan wani da wani haka mukai kwana ukku a gidan baizo ba sai gana hudu na fito pepper ya bugo min gashi hanya nace Allah ya kawoka lafiya.
Karfe tara ya shigo nasan kuma shigowansa ke nan yara sunyi barci a lokacin sai faman kame kame yake min ina dai amsa mashi duk abinda ya fada.
Can dai ya shiga dakinsa ganin hankalina ya dauke gasu Manira muna hada abincin da zasu school da safe don akwai haddan safe gobe asabar.
Sai gashi ya fito cikin jallabiya yana fadin ni zanje in kwanta don nagaji na juyo ina fadin Allah ya tashemu lafiya har ya juya ya soma tafiya kuma ya juyo yana fadin mama dai bata dawo bako ?
Bata dawo ba wallahi nikuma banje ba tunda suka tafi katsina buki jiya suka dawo saida safe ya kara min sai ya ban tausayi yadda yakeyi alokacin.
Saida na gama abinda nakeyi na shiga daki tare da yarana da yanzu tare muke kwana dasu don rashin mama a cikin mu da suka taso suka bude ido da ita a gidan cikin mu.
Barcine ya gagareni a ranan sai faman juyi nakeyi saboda sabo ance turken wawa nida nazo na sameshi da matarsa da fitanta har na saba da zama ni kadai ba kishiya.
Ni ke nan ina haka ita yaya taji a dan zaman da tayi na gwauronci a gida ba tare da shiba yaya taji balleni a yanzu ke zainan kiba kanki lafiya shiyafi na fada a karshe.
Abu daya zanyi kawai inci maganin zama da ita yadda muka fara in kawar da idona akan duk wani matsalanta don nasan halin bai canza zani ba har yanzu yadda ta dawo muna zaman doya da manja din nan da ita kafin ya dawo.
Da hakan har barci ya daukeni ban sani ba nadan makara da safe don haka ina sallame sallah na fada kitchen kafin wani lokaci nagama hada masu abinci laura kuma tayi masu wanka nazo na shiryasu.
Koda driver yazo na riga dana gama basu abin karyawa suka fito suka tafi hakan yasa na samu dan lokaci na koma barci don karfe biyu zan fita zuwa exam din mu na karshe da muke zanawa.
Karfe tara ya gama kimtsawa ya shigo Laura tana gaidashi yake fadin ina nake tace ina daki ina barci dama na fada mata hakan sai gashi ya shigo dakin barci sosai ya samu inayi ya dan bini da kallo kafin ya karaso bakin gadon yana ja min kafa.
Har yaran sun tafine ko na falko banso falkawa ba a lokcin ina sauke kallona gareshi nace ina kwana ya amsa yana kara maimaita min tambayasa akaina nace tunda safe yazo ya daukesu na gyara kwnciyana.
Sun karya ne ya tambaya nace sun karya na kuma zuba masu wanda zasuci a can don yau hadda zasuyi zasu dan jima kafin su dawo.
Yau ba zaki shiga school ke nan ba nace sai karfe biyu nake da pepper in Allah ya kaimu kunyi abin karyawa ke nan ya tambayeni abin daya ban mamaki ke nan na dago ina kallonsa.
Kina kallona kinsan halinta da shiririta yanzu ta tashi yaushe zatayi muna abun kari muci bauchi zan tafi tare da umar kada in makara.
Abincci na nan saman dinning na fada ya juya ya fita nan dai ya karya ban fito ba don kada hakan ya zamo laifi a gareni ko gareshi ya gama ya fita saidaya shirya ya sake shigowa don muyi sallama.
Ya sameni zaune a falo don barci ya gagareni komawa a lokacin yake fadin ni zan tafi gashi banga yaran ba aka turo kofan side dina.
Gaba dayan mu muka kalla itace tsaye a kofan batai magana ba sai tsayawa datayi kimkam tana bin ko ina da kallo hannu ya daga min alaman inyi shiru ya juya gareta yana fadin lafiya ?
Ina jiran ka fitone ta fada kai tsaye daga inafa ya tambayeta cikin rashin fahinta ina ka shigo yanzu ?
Wajen matana mana ko baki san hakan bane in maki bayani sai kawai ta juya ta fita ba tare data jira bayanin ba da yaso mata .
Ya juyo yana fadin please ki barni da ita ni ina ruwana da shirmenku ko wa yasai lariya yasan zatayi yoyo ai ba abinda ya ganoni cikin rikicun ni na fada ina daukan remote.
Ya fita kan ya barni da mamakin wanan sabon haukan na Aisha duk da nasan zai mata magana amma dolene in dauki matakin hakan ta bangarena nima.
Don haka na shirya mata tsab zan tunkareta duk ranan data kara shigo min da izigili haka part dina don ba zan dauki hakan ba gareta.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
[7/11, 14:55] Seenabu Makawa: DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

9?? 0??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,,,,


Nayi dakonta a wanan karkn saidai bata mainaita gangancinta na farko a gareni ba don har ya dawo part dina bata sake biyoshi ba gashi idan yana gida zai zo wajen yaran ko ya kwashesu zuwa can su dade tare dashi.
Tun banson hakan ina gudun su cutu a wajenta hardai na barwa Allah nakawo ido nasa ga hakan da ya dauko yi ga yaran wanda nasan ba komai bane kawai dai so yake su saba da ita wanda hakan yana da wuya gaskiya.
Don wani lokacin acan yaran zasu barshi su dawo su masu tafiyan saidai idan kananun ya diba shine sai yaga daman dawowa dasu karan kansa.
Ido kawai na kawo nasa masa don na fahinci nufinsa a lokacin magana zai iya kawo muna matsala wanan na daya daga cikin hakkurin da kowa ke fada inyi ke nan akan komen Aisha din kome koma ma halinka.
Da yake pepper rana nakeyi a lokacin sai nake dan samun hutu a gidan idan yara sun fita sai sha daya zan tashi inyi wanka in karya yauma hakane ina zaune bayan na gama karyawa Laura tana gefena tanawa yara wasa mukaji sallamansu mum.
Da yar fara,ata kamar kullum na mike ina masu sannu da zuwa tare da fadin lah mum kunzo banje na tare ku da dawowa katsina ba kun rigani zuwa kuma ?
A to aimu gamu munzo yanzu nasani ko fushi kike tunda nayi maki laifi nasa an dawo maki da kishiyarki da sauri na juyo ina kallon mum din a cikin mamaki don ban taba zato ko tsanmanin wanan zance a bakinta ba haka.
Sai naji mama tace wani irin fushi kuma hjy kubura kin taba ganin da yana fushi da uwarsa komai kikayi ai tasan daidaine ba abinda zai cutar dasu bane kawai dai mijjnta yace don jerabawane basu da time yanzu ai ta tura a gaimu ko ?
Murmushin yake nayi na kasa zama nabi kujera ina kara gaidasu Laura ma ta gaidasu na nufi kitchen na hado masu abin sha na kawo masu da kaina.
Wai ashe mazana sun fara karatu jiya yake fada muna daya shiga nace sun fara mama amma saida kyat yanzu ake fita sai nayi yaki kafin a fita wai basu zuwa.

90 / 105