DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   49 / 105

144K to 147K   out of 313.1K words

Shiya fada uwarsa ta fada baki tsaye gaban kowa a cikin gidan nan shine yanzu zai dawo yana son hake maki don ya mayar da mutane sakarkaru irinsa ko ?
Ai banson hjy takai zancen gun Alh ne yanzu sai uwarsa ta fara sanin tabargazan da yakeyi ingani da wani ido zata kalli mutane dashi bayan bace bacen data dingayi a gaban kowa gidan nan a baya.
Wai dama haka ta fada mum amma mummy wani lokaci idan tayi abu kamar bata da wayau wallahi koda yake kan yaya hafiz komai tana iya yi dama ?
Har mun gama zan kwashe kaya nake tambayan mum wai yaya Addel yau bai shigo gidan nan bane mum ?
Bai shigo ba ta ban amsa a takaice kafin tace wani abune nace a,a dama zancen planing din mu nake son fada masa tace to bai shigo ba yau kila wani abin ne ya tsayar dashi ko kuma wanan jarabar matar nasa ya motsa masu ta hanasa fita yau.
Kai haba mum kamar wani soko can mace zata tsareshi a gida haka kila dai wani gun ya tafi yasa bai shigo ba yau di mum tace waya sanar masa in ance hakan ai ba karya bane tunda ya tsaya mace tana juyashi yadda takeso.
Shiru nayi na wuce kitchen nakai kayan na aje na dawo ban tsaya ba na shiga daki nayi komai kamar yadda na saba nafito kafin na kai kwance ina karatu a haka barci ya daukeni ban sani ba.
Misalin sha biyu saura wayana dake aje daga gefen kaina ya dauki kara da alama kuma kirane a lokacin yake shigo min dole na mike don wani lokacin sai dare muke passing information ga junan mu inda za,a hadu don haka na dauka cikin mate din mune ta kira.
Nakai wayan kunnena cikin kasala da mutuwar jiki irin na mai barci a lokacin naji muryan namiji hakan yasa na tsaya tunanen waye kuma haka a wanan lokacin ?
Yana fadin da fatan zakiyi hakkuri tayar dake daga barci da nayi a yanzu kasancewa nasan kun dade da barci yanzu tunda naga kun kashe wutan part dinku gaba daya tun dazun.
Na kasa samun natsuwane zainab akanki tsananin sonki ya hanani sukuni a rayuwata ballantana nayi tunanen wani abu barci a zuciyana yanzu.
Nasan na bata maki a baya zainab kiyi hakkuri ki bani dama karo na biyu mu fahinci juna a yanzu yana fadin hakan na gane ko waye a lokacin.
Don haka ban tsaya wani sauraronshi ba kawai naja tsuki na kashe wayan ina zaginsa a fili tare da tuno abubuwan daya faru tsakanin mu dashi a baya lokacin auren mu.
Ban kai ga karshen tunanen ba wayan ya sake shigo min again naja tsuki ina surfa zagi a fili na jawo wayan da zumar kashewa sai naga sunan ya Addel baro,baro a screen din wayan nawa cikin mamaki kuma na daga ina karawa a kunnena.
A zatona ko mum ne ta fada mai ai ina nemansa don na tambayeshi shine ya kirani a wanan lokacin duk da dare yayi nama dauka ko dayan darene a lokacin



ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4?? 9??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Da sauri na dan mike zaune ina sauraron dadadiyan muryansa wanda ya ratso cikin kunne yana min sallama cikin ladabi nima na amsa masa da tawa muryan mai taushin tare da irin sanadarin dakr tattare da zakin murya wanda a yanzu shine burinsa jin wanan muryan.
Na dora da fadin lafiya dai ko yaya ?
Yace me kika gani ?
Nace naga kiranka by this hours shine ya ban mamaki na tambaya don tsoro ya kamani wallahi katseni yayi da fadin don nakira naji muryan kanwata kuma laifine yanzu ?
Murmushi nayi na lumshe idona tare da kaiwa kwance lokaci guda ina fadin ni bance ba yaya kawai dai abin ne ya ban tsoro wallahi.
To ki daina jin tsoro kawai dai barcine baizo min ba nace barin kira kanwata ta tayani hira ko zan samu in runtsa.
Shiru nayi na dan lokaci ina mamaki har yakai ga cewa dani hello ya naji kinyi shiru ko da matsalane a hakan ?
Dan murmushi na sake kafin nace a,a kawai dai dama sai kuma nayi shiru naji yace ki fada mana dama me ?
Nace ba komai ina anty Aisha yace tayi barci itace matsalanki dama ko to gata kusa dani tana barci ko in tayar da ita in bata wayan ne ?
Da sauri nace don Allah yaya rufa min asiri kada tace zarginta akan mu kuma gaskiyane ta tara min mutane da daren nan ina zaune kalau.
Au ashe kanwar tawa matsoraciyace ke nan a,a ba hakana bane yaya kawai dai ance kar ayi kar a soma banan sunane banso irin nata.
Au to barin kashe tunda har kina tsoron wani a kaina yanzu na dauka duk abinda wani zai fadi akan mu zaki iya shanyewa yanzu ai ashe abin ba haka yake ba.
Nace ban damu ba yaya tunda nasan banyi abinda take zargina ba ai kawai dai ban son a bata mata raine don nima macece kada wata ta bata min wata rana.
Yace Allah sarki kin kyautawa kanki tunda kina tsoron shiga hakkin wani ai ni har kinsa na manta ina mum nace tayi barci tana dakinta OK da kyau.
Kinsan wani abune zeey mum nace a,a yaya yace har naji na samu natsuwa cikin dan second din nan da muke tare yanzu barin barki kiyi barcin ki kada in hanaki tashi gobe da wuri kizo ki makara.
Nayi murmushi nace ai mum tana nan bata bari in makara dama itace ke tayar dani kullum naji ya saki ajiyan zuciya tare da fadin ashe mukai till down ke nan har safe tunda mum tana nan ?
Wai yaya na fada cikin rikicewa naji yace meya faru kuma ya tambaya nace haba dai till down kuma kamar sai kuma nayi shiru na fasa fadan abinda zan fada din alokacin.
Yace ki fada mana ko wani ya hanaki fadan abinda kikai niyya you free kome kike son fada yanzu ai nace a,a ba komai sai naji yayi murmushi yana fadin nakiraki dazun naji kina waya keda waye a wanan lokacin ?
Dazun na sake tambayanshi irin namu na yan Africa yace ehh ai kin fahinceni sarai dazun na kira baifi yan mintuna ba naji kina waya you are busy by that time.
Wai dazun dan rainin hankalin nan ne yaya hafiz mana ni bansan inda ya samu number taba ya kirani yana min shirmensa ko ance masa ina da lokacinsane yanzu oho ?
Naji yace dani hafiz kuma cikin mamaki nace ehh shifa wallahi ni gun daddy zan kaisa kara kai tsaye don na fahinci yana son ya takurawa rayuwata wanan zuwan nasa.
No kada kikai karansa gun daddy yanzu nace cikin shagwaba to yaya yaya zanyi dashi dazun fa biyoni yayi da gudu saida na fada dakin Dada.
Subbahanallahi shi hafiz din yana da hamkali kuwa koya manta ke mace ce bayan haka a cikin gida kuma zai gwada iskancin nasa haka ?
Lalai dolene a saka masa burki ki barni dashi zan masa magana ya rabu dake ko ana so dolene wai wanan ai haukane da iskanci zai biki da gudu idan wani abu ya sameki kuma fa garin gudun ?
Nace mum ma haka tacewa Dada wai kada ta fadawa daddy ita da kanta zatayi masa magana ya daina ni babu ruwana dashi na fada masa in akwai wanda na tsana a duniyan nan bayansane.
No ki daina fadin hakan don Allah ko banza ai hafiz dan uwankine zainab idan wani abu mumuna ya sameshi aiba zakiji dadi ba kema don haka ki daina kinji .
Amma son kace hakane da wallahi ban daina fada mashi hakan ko yaushe in yayi zuciya ya barni mana so dolene koya manta cin fuskan da yai min a lokaci ni wallahi bani kaunar ganinsa har kasan raina.
Nasani amma dai ki daina ko don daddy da yan uwansa gaskiya ba zasuji dadin hakan da kike fada ba kinji ko nace naji yaya wasa wasa bamuyi aune ba har karfe biyun dare muna tare saida yaji ina hamma yayi min saida safe muka kashe wayan.
Maimakon barci yazo min saina tsunci kaina da kasa barci a ranan wani tunane yazo min don sauyawan da nake gani a gun ya Addel wanan lokacin.
Sam inba agaban mum ba baya fito min a yaya Addel din dana sani meke shirin faruwa dani kuma haka nake tambayan kaina ni kadai a dakin kwance ?
Ga wanan rikicin na ya hafiz ga kuma wani na shirin ya bullo min don na fahinci take taken ya Addel a yanzu kaina yana kokarin nuna min sone a boye.
Kaina naba shawaran na kiyayeshi don ba abu bane da zai yuyu atsakanin mu don haka kar ayi kar asoma tun yanzu harko inya fito min da wanan zancen danake zargi zan fito in fada mai gaskiya ya daina tun kan wani yaji zancen a zargemu.
Wanka ya fito yana tsaye yana shiryawa wayasa dake aje saman side drower ya dauki kara ya taka zuwa wajen ya dauka.
Sunan Victoria ya gani rubuce guntun tsuki yaja yana wurga wayan saman gado yana mejin haushinta a karo na farko.
Don gani yake yanzu duk ita taja masa wanan halin da yake ciki tunda a lokacin sontane ya rudeshi har ya bijirewa iyayyensa gashi yanzu alhakin hakan yana binsa.
Sake kira tayi again don kwanaki sunkai uku bai kirata ba kuma kota kira bai daukan wayanta yanzu daurewa yayi ya duka ya dauko wayan yana dauka ya kara a kunnensa yana fadin.
Hello Victoria how now ?
Ta fara magana a bangarenta tana fadin handsome meke faruwane wai kake kin daga wayata kwana biyu ?
Wai koka daina sonane yanzu Dad din ka yaki yarda har yanzu da auren mu cikin karfin hali yace No Victoria ba hakana bane kinsan a gida nake yanzu dole saina lalaba iyayyena tukun.
Ta saki wani dan murmushi kafin tace nasan haka don nima nayi fama da wanan matsalan kafin Dad dina ya amince dakai lokacin.
Matsala dai gudane shine Dad ya kafe da sai kin musulunta kafin ya amince min dake don kinsan halin mutanen mu da irin rikon addanin mu a nan.
A gagauce tace dashi ba wana maganan a alkawarin mu kaima kasani tun farko Dad dina kuma ya fadama ba sauya addini a auren mu kuma ka amince da hakan.
Gaskiya akwai matsala babba a cikin auren mu don ko Dad dina ba zai yarda ba ta katseshi da fadin kabar wanan zancen yanzu sai idan mun hadu zamu san yadda mukayishi dama na kira in fada ma Tuesday zan koma don nasan kai kana nan tukun.
Yace OK ina sane da hakan zanyi kokari kafin ki tafi mu shigo da yan uwana garin ku a sheda in Allah ya yarda sukai sallama ya kashe yana jan tsoki.
Ya rasa me zaiyi a rayuwansa yanzu don haka waje ya samu ya zauna yana tunanen samun mafita agareshi duk tunanen da yayi amsan dayane kada ka soma don iyayye maza ba zasu yarda ba koda zasu yarda sai ankai ruwa rana ga hakan.
Karshe dai ya yankewa kanshi shawaran da yake gani daidaine naya fara neman yardana ta ruwan sanyi da lumana kafin ya bijirowa iyayye da zance.
Zaune suke falon mahaifiyarsu don sallaman datazo masu saboda sammako zasuyi su koma nan suke hira ba abindake zuciyarta tun zamanta wajen sai zagi da cin mutuncin mijinta da zainab datasa abaki da zuciya yanzu.
Yarta Usaina ke fadin ni hummaira sai nake ganin wanan abin bame yuyuwa bane kawai dai yayi hakane don ya rudek ki gyara halinki amma kinki gane hakan.
Daga inda uwar ke zaune take fadin nima abinda na gani ke nan ai dabara kawai yake mata irin na maza amma taki gane hakan balle ta gyara.
In bashi ba wani namijine yake bidan aure ya dingayi a gaban matarsa haka baro baro wanan kina cutan kankine kawai komai da yake muna gidan nan bai fasa ba fa.
Shiru tayi tana saurarensu don zancen ya shigeta sosai wanan karon don biri yai kama da mutum gaskiya yar nata ta fada don wani lokaci muryan maza zataji amma yace da zeey yake waya.
Inda hakan gaskiyane yaci taji zancen wajen wani nasa koda acikin zolayace kuwa don ance a dangin miji ake jin labarin kishiya duk da ba damuwa tayi da kowa nasa ba don yanzu har yakai suzo su koma bame leko gidan da sunan zuwa dubiya a wajeb su.
Ganin zancen ya dan shigeta yasa suka bata shawaran da suke ganin shine mafita a wajensu suka dinga tausanta har abinda take ji ya dan ragu a zuciyar ta game da mijin nata.
Shawara dayane zata gwada yanzu da yar nata tace tayi kokarin jana a jiki don ta gane gaskiyan zancen tasan abune mai wahala gareta yadda yake jin zafin yarinyar a yanzu.
Amma zata gwada ta gani don shine ma yana shiri tasan gida zaije kila donshi ba wasu abokaine dashi ba haka dayake ziyara.
Kalloshi tayi tana fadin sai ina yanzu cikin mamaki ya dago ya kalleta yace gida zanje na sallamesu nima zanje nayi sallama da mum kada mu tafi tayi fadan hakan.
Yayi mamaki sosai a zuciyan shi saidai baiyi magana ba amma yana tunane a zuciyarshi cewa wani rashin kunya ko wullakanci take son zuwa yi a lokacin don haka ya hake ta a zuciyarshi.
Tare suka shigo gidan sun samu mum ita kadai a falo ta gaida mum cikin mutunci a rana ko mum din tayi mamakin ganin wanan sauyin na Aisha din amma tabarwa cikinta zancen.
Sun zauna ke nan ta dago tana fadin zainab fa mum ko tana asibitine jin hakan a bakinta ba karamin mamaki yaba kowansu ba lokacin.
Hjy Mum din tace tana ciki yau jumma,a bata faye fita aiki ba tana hutu daga nan mum din ta daga murya ta kirani daga falon na amsa lokacin ina kwancene.
Na fito saye da wani dogon wando tied iya wuyan kafa sai dan rigan dana dora daidai cinya ya tsaya min fararen kafana sun fito santala santala a kasan wandon sai kaina babu dan kwali kitson kalaban da mum tayi min sun zubo min har baya na rike hulana a hannu.
Gaba dayansu ukun ido suka dora min lokacin dana budo labule ina fadin mum gani sai ganin su nayi girshi min a zaune don bansan shigowansu gidan ba lokacin ganin su kawai yanzu nayi a zaune gabana.
Aisha din ta nuna min tana fadin matar yayankice ke tambayan ki na juya ina fadin ina kwanan ku a cikin jam,i ga mamakina sai naji tace kina jin dadin ki fa kin shige daki kin bar mum ita kadai a falo zaune.
Murmushin dole na kakaro a fuskana ina yake nace gyaran daki nakeyi ban jima da shiga ba ai yayane ya katse mu da fadin zainab yi min list din abubuwan da kuke bukata in sayo maku kafin mu fito wajensu Dada.
Yana fadin hakan ya mike tsaye yana fadin muje mu sallamesu itama cikin sanyin yanayi ta mike don ganina yaso ya tarwatsa mata rayuwa a lokacin.
Don ba karamin firgita mata zuciya nayi ba a lokacin kishi da jin zafine suka rufe mata zuciya lokaci guda na yadda mijin nata ya ganni a hakan dana fito a lokacin.
Abinda bata sani ba shine shakuwa da yarda tare da mahaukacin soyayya shine tsakanin mu dashi yanzu don yaya yayi dabaran manna min so da sabon shi a zuciya wanda kullum muna manne da waya muna abu daya a yanzu kamar zolaya.
Suna fita nakai zaune ina fadin mum meta zoyi ne tace ina na sani yadda kika gansu haka nima ina zaune suka shigo min nace Allah bansan suna falon nan ba da ban fito ba memo na jawo a gefena na shiga rubutu a cikin sa sai bayan na gama nake karantowa mum din abinda na rubuta take fadin.
Baki rubuta kayan kwalan dinki ba da abin sha kin dai san ban zaman sai maki yanzu tunda yace ki rubuta gara dai ki rubuta din komai da kikasan sai mun saya a bayansa inya tafi yanzu sai wanda ya gansa kuma ai .
Basu wani jima ba sai gasu sun dawo daga tsaye ko zama basuyi ba yake fadin ke kin rubuta nace ehh na mika mashi bi yayi da kallo yana rubutawa kafin ya dago yana fadin banga su cuscus da irish da kwai bamana a ciki na daiga kayan zaki da yawa na meye su kuma ?
Da sauri na dago ina fadin a,a bani bace mum tace

49 / 105