DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   60 / 105

177K to 180K   out of 313.1K words

a shiga tsakanin zeey da dada ko daddy ya fada ranan.
Don me za, a kyaleta tayi mata rashin kunya ina dai duk akan auren Aliyune kike wanan daga mata kan waya damu da auren ki na wahala yanzu auren da jeka nayishi kawai akayi har aurene da zaki dingawa mutane abinda kikaga dama a cikin gida.
Kije ai Aisha din itace maganin ku don yanzu ina mijin da kukai auren gaiya akanshi din ina matarshi ta dauke abinta tabar kasa dashima ke ke zaman wahalan dakon soyayyansa a nan yanzu ai.
Idon ta hafiz ne ya kama gabanshi shi tunda bakece autar mata ba balle ya tsaya ganin takaici kanki ga banza dama abin dai da namijine idan yaso.
Daga baya ke nan kuwa bayan yaki na fada yadda mummy sin zatajini son idona ya rufe a shirye nake ranan inba kowa amsa daidai da zancensa akaina lokacin.
Sam idona ya rufe har na manta da anty nafisa a wajen duk dadai ai tabani sukayi don kullum a cikin gulma ake gidan ai kan abu daya ana mun nune da dariyan gwai Allah.
Sai naji tace dani hold on zeey kiyi shiru kawai don Allah wanan abindai ya riga daya faru ko don Allah da hafiz da Addel daya suke a gidan nan banga abin tsayawa zaben wani ba.
Ke Dada na fada maki irin abin nan dama zai kawo fada a gidan nan gashi kuwa yanzu din anfara kai inda ba,aso don haka kowa yayi hakkuri yanzu.
Zancen barin gida bai taso ba a yanzu gareki Dada jikarkice kin fada ta fada shike nan don Allah zancen ya mutu a nan ayi hakkuri don Allah.
Au sai akace don jikace ta fada mata maganan banza ko da zai bata mata rai ba akan komai bane kowa ya sani don auren Aliyune towa zatayiwa rawankai kan Aliyu yanzu ?
Aliyun da baisan da zaman taba matar baban ennugu ta karbe zancen hannun mummy daga kin gaskiya sai bata dama kana ganin isar baka isa ba ta karshe da fadin hakan gareni don dama ita din ta hannun daman mummy ce kullum yanzu suna tare da juna.
Allah yasa dai nima ina da iyayyena ba a icce na fito ba yadda ake son kowa haka ake sona nima saukin abin ke nan ai don kwadayi bai kaini ga halaka ba inda ba asan darajan dan adam ba.
Ranan dai ba dadi don banji kunyar kowa ba a cikinsu sun taru sun min caaa a kai ni kuma na bada amsa daidai dasu din.
Bayan fitansune mum ta hauni da fada sosai ita kuka ni kuka nashige daki da niyar nasan idan daddy ya dawo ranan zan bar gidan don yadda mukayi dasu din ranan.
Saidai banji komai ba har safe har monday tayi na fice zuwa school gashi sama sama muke da mum don abinda nayi tace banyi daidai ba a wajenta ya zanwa manya rashin kunya haka su fada in fada.
Sai gidan ya koma min ba dadi alokacin nasan dai daddy yaji komai badai min magana bane kawai amma nasan dole a fada mashi abinda ya faru kodon ya tozartani naciwa dada mutunci.
Sai gashi baiyi magana ba kuma har aka share kwanaki hakan yasa na sake muka koma rayuwan mu ta normal da mukeyi kamar kullum nida mum din.
Abin farko da muka fara shine gyara tsarin rayuwata don anty hauwa tace dole sai na canza a yanzu ko banso dole in canza don in kwatowa kaina yanci.
Don haka na zuge jakata na fito da Atm dina na fara diban kudin da nake faman tsuminsu ina barje gumina dasu ta hanyan sauya suturu man shafa mai gyara fatan jiki da kayan kamshi.
Keda ganina zaki san na sauya a yan kwanakin sosai bisa ga baya da nake dabian gidadawa da faman tsumin kudi a marata don kudi kan ina samu gaskiya saidai ban abinda ya kamata dasune kawai.
Zaune nake saman dogon kujera a falon mum na gama cin abinci mum din tana gefena muna hiran katsina da sukaje buki satin daya shige.
Wayata dana dora saman table ya dauki kara na duba saida gabana ya fadi don ganin mai kirana alokacin don ba kowa bane sai ya Addel nayi mamakin hakan sosai dana ga kiran nasa.
Dan newa nayi nayi kamar ina receive na kashe tsoki naja na saka wayan a air mode nayi reject din kiran don yadda nake jin haushinsa a lokacin.
Ban jima ba na mike da wayan a hannuna nake fadin mum bari na dan dauko abu a daki ta amsa da to itama don tana tsabgan gabanta a lokacin.
Daga dakin ina kwance najiyo sauti wayan mum alaman kira ya shigo a wayan nata bayan an dan jima naji tana kwala min kira na amsa daga dakin.
Ina zuwa take miko min waya tare da fadin karbi wai ya kira wayan ki yana kashe ni wayana a bude yake waye mum ?
Na karasa da tambaya ina karban wayan daga hannunta bata ban amsa ba na kara a kunnena muryan shi naji yana fadin kin kashe wayan ne don ba zaki dauki wayana ba ko saboda kina fushi dani ?
Akan me zan kashe waya tana kunne kiran dainai bai shigo ba murmushi naji ya danyi a lokacin kafin yace dani da alama kema kina fushi dani ke nan ko ?
Fushi akan mefa kawai dai yanayine ina wuni na fada don a gaban mum nake lokacin kafin ya gama amsawa naga mum ta mike ta fice daga part din nan na samu daman sakewa don yin wayan a lokacin.
Shiru nayi kafin ya kara fasin hello nace ina ji kece kikai karana a gun mum ashe da har ina shakun hakan amma yanzu naga zahiri don yadda kike karba min waya a yanzu.
Akan me zanyi karan ka gun mum kasan wanan ba halina bane saidai idan neman laifin da zaka dora min kakeyi yanzu kuma.
Look zainab ina na fada maki tafiyan nan tunkan nazo na fada maki tsawon yadda zan dade anan ai amma yanzu sai gashi kuma kun hurawa mum wuta kun tayar mata da hankali akan rashin dawowana Nageria har ana kokaron dorawa Aisha wanan alhakin itace ta hanani dawowa saboda ke.
Ya Addel ban fahinta ba kace muna kokarin tunzura mum dani dawa kake son kace mun tunzura mum shine ban fahinci me kake nufi ba ?
Keda koma waye don kuna ganin na yaudareki tunda nazo da matana nan munyi tsawon watani a nan din ba tare da mun dawo nageria ba.
Don mum ta hanani sukuni akan lale sai na dawo ko don ke Nageria ko kuma Aisha ta zauna ke in tafi dake idan baki matsawa mum ba banga abin tayar da hankalinta ga barinki da nayi gida ba a yanzu.
Hakane kwarai don ko mum uwatace kai kuma a matsayin miji kake yanzu wajena amma da ace wanine nasan kaima zaka dauki mataki akan hakan a kaina.
Idan shekara dubu zakayi can in muna raye abinda kafi kowa sanine hakan ba zai taba damun rayuwata ba haka kuma ba mai cewa yaga gajin hakkurin zainab akan hakan.
Don na fahinci kana son kace nidasu babane mukai karan ka a wajen mum don tayima magana nagaji da zaman gidan da nakeyi yanzu.
Cikin mamaki naji ya katseni da fadin zainab ni kike fadawa magana haka har kina kokarin danganta zancen mu da baba kada kice zakiyi kokarin hakan a kaina dan nasan darajan iyayye sosai banson abinda zai batani a wajen baba don Allah please.
To yaya naji kace muka kai karankane ni dasuwa idan bada iyayyena da zancena ya shafa ba na fada a dan rage sautin muryana nima yace .
Look bar zancen nan hakana idan nine kuke son gani na kusa dawowa kasan insha Allah zan dawo ayi yadda mum keso ba shike nan ba nace yafi sauki nima na gani don hankalin mum ya kwanta da zunden da ake mata gara kawai a rabu zaifi.
You are very stupid zainab are you fool ke da bakinki kike kiran mu rabu kina cikin hankalinki kuwa ko kin samu matsalan kwakwalwane ban sani ba don yau sam ina jinki ba daidai kike ba ?
Ni lafiyata kalau kawai amsa nabaka daidai da maganan ka OK kin kyauta tunda amsan da zaki ban ke nan amma ki iya bakin ki don watarana na fada maki naji ya kashe wayan.
Tsuki naja don naga yana kokarin dora min laifin daba nawa ba a cikin zancen nan meye nawa tunda ban taba korafin akai ba gaban kowa yanzu yazo yana son ganin laifina.
ko da mum ta shigo ta sameni a kwance na dora hannuna saman goshina ina tunane kallona tayi tana fadin ya akayi kuma na ganki haka ?
Ba komai mum na fada a dan sanyayye shine ko nasan dama akanki zai sauke haushina don ya kirani jiya nayi masa kaca kaca ban raga mashi ba.
Shi yana zaton nida babane muka damu ai mum don haka ya nuna min a zancensa ta katseni da fadin kai nakan rasa ina hankalin yaron nan yake shiga wani lokaci barni dashi ba yace suna nan dawowa karshen wani wata ba Allah ya kai mu a zuciya na amsa da amin.
Tun lokacin banji ta kara wani zance ba kuma ana hakan matar daddy enugu ta haihu bansan ya akayi ba sai gasu sun kwaso sun dawo gidan daddy wai sai bayan suna zasu koma gidan su da zama.
A tsohon part din da suka zauna wanan karon ma a nan suke gaba dayansu nan yan uwa da abokan arziki suka shiga ziriyan zuwa barka da arziki.
Tunda suka dawo ban samu shiga ba sai ranan friday da safe banji dadin samun Dada da halimatu a part din ba duk da mun dan shirya sama sama da Dada amma ban wani dogon wasa yanzu da ita.
Kamar hadin baki kuma sai ga mummy ta shigo sama sama nayi mata barka da arzki Allah ya raya yasa albarka ina fadin hakan nayi kokarun mikewa a lokacin aminiyar mummy kishiyar ita mai haihuwa ke fadin.
Ni kan tunda muka zo gidan nan sai yau zainab ta shigo ko don banga shigowanta ba ai zainab yanzu babbace ganinta saida ticket.
Halimatu ke wanan magana lokacin na juyo nace a haka zaki kare wurin haddasana yaushe nake zama a gidan tun safe idan na fita mummy ban dawowa sai dare
Sai irin ranan yau nake samun lokacin kaina ranan jumma,a nima sanin hakan ai yasa ban damu ba nasan baki da lokacine ai kuna kokari wallahi mai haihuwa ta fada.
Kai amma safiya kuna daurewa karya gindi lokacin shigowa tayi barka an samu karuwa a gidan shine wani abu kawai dai dama hakan ta nasayi zaizo kan kowa ai inma wani ke daurewa mutun yayi hakan.
Ayi hakkuri mummy na fada don baba yayi min fada sosai kan matsalan dana samu dasu a ranan don haka banson wani abu ya shiga tsakanina da kowansu yanzu.
Kuma dai kun damune yanzu ai gani take tafi kowa tunda take karatun likitan nan sam gaba daya ta canzawa kowa ko itace farau oho ?
Duk da naji haushin kalaman Dada ban nuna hakan ba murmushi kawai nayi nace mummy sai na kara lekowa inga baby kuma na fice ina jin mummy na fadin.
Dama haka dan cin arziki yake ai yafi dan gida iya shige idan ya samu wuri yarinyar nan da ace Alh ya haifeta da mun shiga uku da ita a gidan nan.
Ban tsaya naji abinda wani zai fada ba nasa kai dai na fice kiran da hauwa tayi min yasa zancen su bai tsaya min a rai ba don cewa tayi na shirya zata zo ta daukeni muje wani shigo da ita.
Da yake muna free sai ban damu ba don nasan mum ba zata hanani fita ba don haka a gurguje na shirya koda tazo ta samu na gama shiri muka fita tare.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAIINAB IDRIS MAKAWA

6?? 0??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Yanzu kan ko yaro ya laluba yasan banbanci da da yanzu ba daya bane a gareni don zainab din da suka sani wanan ta wuce sanin wacan ta farkon.
Abin haka yake ga mace in har tana cudanya da wasu a sanun zata juye ta zamo kalan su ba tare data sanda hakan ba yanayin ta zai sauya sannu a hankali ta koma zubin wa yanda take tarayan dasu walau wayewa ko kuma gida danci Allah yasa muci jerabawan amin.
Wanan ne ya faru da yar gidan malam Garba dan hassan kt don ko ga baki daya na sauya yanzu dole makiya su kamu da hawan ruwa akaina lokaci guda idan sun gani don ko likkafa taci gaba a wajena karatu yai min rana yana kuma sahirin yiwa iyayyena da yan uwana rana insha Allahu sanadin mayar da hankalina ga karatu da nayi nake kuma samun ci gaba wanda bansan da hakan ba sai a wanan ranan.
Kallo daya biyu take min sai ta kawar da idanunta na gane ta sarai saidai banyi saurin nuna hakan ba don bansan da wace zata tareni ba a lokacin tunda na auri mijin yar uwarta na tashi daga kanwar mijin sister din ta a yanzu.
Muryanta ya katse min tunane da take fadin niko kamar zeey ko nace anty Usai ina wuni tace haba tun dazun nake satan kallon ki a zatona ko bake bace sai naga kema kina nuna min idon sani.
Nice wallahi na fada muka sake gaisawa da ita don na santa tun lokacin auren Aisha da ya Addel muna kuma yawan haduwa don halaka ya hada a yanzu.
Dawowan wace suke tare yayi daidai da zuwan anty hauwa dake fadin kinga turaren ita kuma anty Usai na fadin kanwar mijin humairace au Allah muka gaisa da dayan matan itama.
Anty Usaina din ke fadin sunce zasu dawo a karshen watan nan ko na amsa da ehh haka yaya ya fada tace ko jiyan nan mun gaisa dasu ai yanzu ma haka ita ta turomu muyi mata sayayya don tace a nan kano zasu dan kwana biyu.
A dadirce nace ehh wallahi sun dai sha turai kan tace dama mutumiyar ancan ta saba dashi ita bataki su tabbata can ba ai.
Muka daiyi sallama kowa ya kama gabansa a cikon katafaren kantin da kowan mu yazo sayayya sai bayan wucewan tane anty hauwa take fadin ina kika santa nace sister din matar ya Addel ce fa sai naga ta juya da sauri tana kara kallon su.
Kafin tace dani amma baki kyauta min ba aida datace siater din mijin humairace zance da ita amaryansa dai ko ?
Allah ya kyau anty aida ba zata tsaya tayi min wanan sakin fuskan ba ni sai ina ganin kamar basu ma san da zancen ba fa son sam bata nuna min komai ba.
Koda ta sani ya zatayi tunda an zama daya yanzu babu abinda zasu iya dake zainab ke barin fada maki duk iskancin nan idan kin iya tako zai zamo shirme da tarihi a wajen mutane.
Kece da makamin farko a yanzu makamin yana a hannunki kowa ya sani saidai idan kece kikai sakacin da ya fita hannun ki wanan kuma matsalanki don mata da yawa dadin aure na saka su watsar da daman su kan dadin miji.
Kallonta nayi ina fadin wani makamine a hannuna yanzu din tace mum kai tsaye kallon da nayi mata mai nufin tambaya da mum kuma ?
Tace kwarai mum itace makamin mu na farko a yanzu don haka ki kara zagewa sosai wajen kyautatawa mum fiye da wanda kike mata a yanzu.
Don dole ki nuna kin fishima kaunarta fiye dashi data haifa kada ki yarda ko shedan ya rudeki zainab kije ki sakaci wajen kyautatawa wanan boyar Allah da itace sillan kawo shi duniya don badon itaba yaushe zaki san wani Aliyu can.
To ki godewa Allah kedashi duk abu dayane haka kuma mum tana da hope samun saukin kuncinta daga wajenki ke zainab kada ki yarda ko da bakin allura wata rana ace za, ajiku da mum kan matsalan danta.
Ma,ana kan wani dukiya nasa haka yan uwan haihuwansa ki rikesu tankar kece kuka fito ciki daya dasu abaya kin dai san komai ba sai na fada maki ba zainab don haka a tanan zamu fara takon namu.
Ajiyan zuciya na sauke kafin nace yanzuma ai lafiya muke da ita tace umm, umm zainab na rabaki ke yarinyace har yanzu baki san tsakanin da da uwa ba.
Ai ki bar ganin yadda kuke nan

60 / 105