Chapter 83 Reading DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc Arewa Novels

DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   83 / 105

246K to 249K   out of 313.1K words

wanan asirin baki dayan mu babu maijin ya akayi.
Nagodewa Allah da yajefoni cikin wa yan nan mutanen arzikin a yanzu don su sukai tsaye suke shige da yawancin abubuwan da za,ayi din hakan yai min daidai da shiga yajin aikin da malamai sukayi na jami,a a lokacin kusan shine yaji na farko da suka fara kasan nan mafi muni kan neman hakkin bukatunsu ga gwaunati.
Karon farko da cikina ya tasa na shiga gidan daddy shine muka hadu da Dada dasu mummy a haraban gida suna shan iska a waje.
Dole na dumfarusu da niyar gaidasu tun ban karaso ba Dada ke fadin me nake gani haka yar nan kardai ince neman kashe yaran nan kikeyi kika dauki wani ciki a yanzu kuma ?
Keko hjy idan rana ta haska ai gara kasha haskenta kafin wasu su rigaka shan hantsi dabarantane hakan ta cika gida da yaya kafin wata tazo ta rigata saukewa tayi nisa ita hannun uwarta kubura ta dauko mana.
Sai lokacin da mummy tayi wanan maganan na gano inda suka dosa donda farko na dauka wasa Dada ke min na jika da kaka a takanin mu duk da mun rage hakan yanzu sosai a tsakanin mu sai gaisuwa.
Mummy ashe dai kin gane dabaran don gunku muka koyi hakan yanzu ke Dada banda abinki meye na damuwa a cikin zancen nan idan ma cikine dani yanzu ni dake da uwaye ta ko ina masu kama min wa yan nan.
Yanzun dai ke hjy kinji amsa daga bakinta anty Jamila ta fada eeh nako ji tunda ba kunyane da itaba dama kunya hjy da mijinta ta fada tana dariya nidai na gaidasu na dan tsaya kafin in shige wajen mum yin abinda ya kawoni gidan .
Don nazo akan kayan da za,a wuce dashi Nasarawa ne washegari donta sani tunda an hada komai a yanzu nan take fadin zatazo da yamma ta ga komai kuma mama ce zataje can ta zauna da kayan kafin a kai amaryan.
Na,amsa da to mum don banso hakan ba don yara da yanzu suka saba da mama fiyema dani dana haifesu din don sun bude idone da ita a gidan komai kuma itace take masu yanzu ita da Rukky.
Kodana koma bancewa mama komai akan hukuncin da mum ta yanke ba saida yamma dasu mum sukazo take fadi nan mama tace haba dai ina zani kwana da keanaki in bar yaran nan a nan ai sai su shiga damuwa idan basu ganni ba.
Kin manta da zuwana katsinane tun basu kai haka bama da ubansu ya tayar min da hankali dole na dawo ba shiri yanzu kuma yaji na kwasa nayi nasarawa ai abin baiyi ba kubura ku barni nan a samu wata a dangin uwarsu taje ta zauna ai suna nan sun fara isowa akace.
Ba zaki je dai bane yaya amma don dan kwana hudu ko biyar a can me zasu baga mutane a gidan ba su zauna dasu gaskiya nikan ku cireni ga lissafin tafiyan nan don ba zani ba.
Nina sani don yaya kan zaiyi fada idan yaji hakan don yarankan zasu tayar muna da hankali bayanta haka kuma bai barta haka ba akwai hasafin da yake masu dukkansu su ukkun ko wani zuwa yayi don haka akwai kyautatawa a tsakani da zaisa mama ta guji zuciyanshi a yanzu.
Haka aka saka Rukky lalle duk da daga baya yarinyar taso ta bultse muna wai bata auren Faruk din ita garin yayi mata nisa dasu baba damu ita kadai zata je can ta zauna garin mutane ba kowa nagida a kusa.
Tun tana fadan hakan da wasa har na fahunci da gaske takeyi acikin zancen ta hakan yasa da yaya yazo nake sanar mai da halinda ake ciki.
Saida dare ya dawo ya samemu falo zaune mu ukku ina zaune na ishishire da kafafu yaran kuma mama na basu abinci sai naga ya nufo inda muken bayan mun gama gidashi ya zauna.
Suka fara dan hira da mama sama sama kafin yace Rukky sai naji dada ance kin fasa auren faruk kuma yanzu bayan an gama komai ana shirin aure.
Da sauri ta dago ta dan kalleshi kafin ta mayar da kallon kaina ta dukar da kai nace hakanafa tace harda kukanta ta sameni a daki ranan.
Assha Rukkaiyatu wanan wani abin kunya kuma kikeson ki jawa mutane yanzu yan uwa kowa na murna da farin ciki kinyi sace miji sai aji wani zance kuma ya biyo baya.?
Mama ta tari numfashin mu da fadin hakan sai yaya ya tare da cewa a,a mama yanzu dai idan ta shirya amsan ba baba da daddy sai taje ta samesu ta fada masu ta fasa auren donsu suka bada ita dama.
Ta dan sake dagowa ta dubeshi a razane kafin ta mayar da kanta kasa nagane su kike son mayarwa mutnen banza saida na zaunar dake nagaya maki komai game dashi kikace min kin amin koba haka akayi ba zainab.
Nace kwarai kuwa yaya nan dai suka koma bata magana shine har aka samu ta yarda zatayi sai gashi yanzu naga tana wani zagewa hakan yasa na fara zargin zugata akayi.
Cikin hikima nake dan tambayanta take fada min ai halimatuce ta zugata wanda hakan yai min zafi da ita na fara na sameta nayi mata tas akan ta rabu da halimatu ko waya ta dainayi da ita .
Dama kowa na gidan daddy ga baki daya don nagane dai mummy ce mai wanan bakin kule kulen akan ahalin baba so take sai taga bayan mu kota halin kaka a garin nan.
Anyi shagulgula nan kano yan uwa sunzo kamar yadda suka saba zuwa ko wani buki saidai da za,a kai amarya banso zuwa ba amma akasa dole in bisu aje dani ta jirgi muka je da abokaina da Amarya mu dai gomane aka biyawa zuwan don haka mama tana ciki da yara Aina muka barwa gida.
A can ma ayi dinner hadadde anci ansha an kuma taremu a cikin mutunci washe gari zamu dawo kano na tashi ba lafiya hakan yasa ya turo mota ya daukeni da mama da yara muka shigo Abuja.
Sai kawayena ne suka koma da sauran mutane da suka biyo mota su mama luba wanan karon jirgi suka bi suka koma gida.
Kacar na karasa Abuja zazzabi mai karfi ya rufeni a lokacin don haka muka wuce asibiti inda yake jiranmu kafin mu iso.
Kula na musan,man na samu don sun dora ni a bedrest irin na masu ciki nasan muna on strike hakan yasa ban damu ba a lokacin don muna matakin karshene da gamawa.
Sai gashi yar kai amarya an koma dubanta daga baya don haka yan gidan mu na daddy suka kwaso jiki zuwa dubana aaibitin.
Bayan sun koma kuma su anty hauwa sunzo sun dubani sun kwana anan wajen mama kwanan su biyu suka dawo kano.
Kulan da nake samu sosai yasa na isa nayi kyau na kara murjewa a lokacin ne kuma Aisha da danginta suka san ina da wani ciki ashe yanzu kuma.
Har an bani bed rest saboda jigilan da nayi na buki yasa cikin ya tashi barewa budan bakin haliman su sai cewa tayi yar iska Allah yasa cikin ya bare .
Subbahanallahi halima kina ko da hankali kuwa da ta tare maki me kike mata wanan fatan yau zakiso in hummairace ace haka ya faru da ita don Allah.
Itako ta tare min komai don saboda itace hummaira take gida zaune har yau shekara da yan kai yanzu saboda wanan kike mata wanan bakin fatan ta hana yarki zaman aurene.
Ita da taje da niyar aure ba gashi ta zauna tana zubo masa diya ba kai da kai ko ita ta hana yarki haihuwa shekaranta nawa gidansa ko bari bata gwada masa ba ?
Kafin ta tofa wani kalma Aisha din ta mike da kuka ta nufi daki har uban yaji yazo yana hauka da uwar bayan yaji maganan abinda ya faru yace wanan satin za,ayita ta kare ko ya mayar min da ya ko ya bata takardanta a hannu kowa ya kama gabansa.
Haka dai kake fada kullum kunce kun iya shi kuma ya nuna maku baku isa ba dakai da yarka kasan dai hummaira tana son mijinta Alh shima yana sonta amma ta kasa hakkuri da bawan Allah nan.
Data iya ta kwantar da hankalinta ta zauna lafiya da abokiyar zamanta da duk hakan ba akai garesa ba ai amma tace ita yar zamanice yace shi kuma ya fita
Komai ya faru ita tajawa kanta ba wani ba ni gaskiya nake fada idan zakubi sannu kubi a gyara in kuma takarda takeso ya bata takardanta a huta.
Zan zauna da ita inji idan zata koma dakintane sai inji ya fada cikin sanyin jiki uwar tace dadai yafi wanan zaman a gida haka abokiyar zamanta nacen da miji lafiya.
Ya dan juyo cikin jin zafi ya kalleta baice komai ba ya sa kai ya shige part dinsa uwar taci gaba da fada idan ance kuyi hakkuri a dakunan ku kuga kamar mutum shi baisan komai ba yanzu irin wanan me gari ya waya don Allah.
A wajen halima take jin abinda Abban nasu yace a dan marairaice take fadin gara na koma gidan Aliyu anty halima tunda ban rasa komai a wajensa ba.
Amma kinsan yanzun sai kinyi hakkuri ko tunda yar iskan nan ta samu waje ta baje tana iya shege a bayanki nasan ko bukin nan na kanwarta shi yayi komai.
Wallahi da nice ke ba zan koma gidan nan ba ai sai yaga kamar kin rasa manemane a yanzu sai shi sai a lokacin ta kara tabbatar da zancen uwarsu kan halima da take yawan fadin ba kaunarku takeyi ba ku rabu da dan uba wallahi.
Ita da kanta ta je gurin uwar tana fada mata komai uwar tace aina fada maki indai halimace tafi bukatan ta ganki a gidan nan kuna yawo tare kullum.
Nan dai uwar da taga ta lankwaso ta kira Aliyun karo na farko tana bashi hakkuri a gabanta yace ba komai ai dama shi ya barta ta koyi hankaline ai a gida.
Zai zauna da magabatanshi ko me ke nan zasuji insha Allahu a haka sukayi sallama dashi tana jin yadda yace tace shike nan nasan ba zasu taba yarda ya dawo dani gidansa ba tunda basa sona dama.
Uwar tace kinga halin naki ko ta yaya mutum zai zauna dakai baki ganin girman iyayyensa ko wani lokaci ko a gabansa kina aibanta masa iyayye.
Ta dai yi shiru nan uwar tayi mata fada sosai mai kama da nasiha taja mata kunne kamar yadda duk wata uwar kwarai keyiwa yarta.
Zaune take abin duniya ya dameta tun lokacin da sukaje abuja suga gidan ya Addel mummy ta dawo cikin bacin rai da kishi da kyashi a zuciyarta.
Haka kuma tasa danta a gaba da kiran waya tana masa masifa kan ya zo gida kome yake ciki a yan watanin nan haka kuma ta dinga bin malamai wai a karkato mata kanshi yazo gida.
Tare da yan wasu dabaru da irinsu keyi wajen bokayesunda malamai don hankalinta ya tashi matukar gaske a lokacin kan mummy da diyanta.
Gashi tana jin kishin kishin cewa muhusin zai auri Asiyan mu wai suma hadasu mum tayi rumas din da yazo mata ke nan a yanzu.
Wata ukkun da nayi abuja yasa nayi wani irin kara kyau duk da ba fita nake ko ina ba gashi muna batun komawa makaranta a lokacin za ai calling back.
Kuma haihuwana a cikin watan ne hakan yasa na fara shiri a asirce duk da yace ba inda zani koda an koma saina haihu a nan Abuja din tukunna saidai in maimaita aji daga baya.
Ga yan uwan karatuna sun sakani gaba akan in dawo ance monday za ai resuming to school hakan yasa hankalina ya dan tashi.
Har yakai na kira mum nakai karan yaya a wajenshi tayi mai magana ya bari in dawo tace ai yasan zafinkine zainab keda abindake cikinki yafi muna karatun ki amma zan masa magana ya bari ki dawo din.
Batama kai ga masa magana ba Allah ya saukeni lafiya na kara haifo yarana kamar almara aka cirosu su biyu don dayan yayi brege a cikin ciki ya toshe kafa kamar na farkon.
Wai tagwaye kowa yayi mamakin hakan don wallahi ko ni na dauka dayane a cikina lokacin don scarning din da nayi tun farkon cikin ya nuna da dayane.
Saidai wanan dayan yazo da dan matsala kadan na zazzabin da nayi fama dashi a lokacin don haka muka zauna asibiti har na sati daya ana curing din mu.
An sallamoni da kwana daya muka kwasa zuwa kano sai lokacin naga sauyin ginan da muka samu a yanzu a gidan don sauran filin nan duk an hade ya koma cikin gina a yanzu part din ya kara fadi sosai fiye da da nake zaune a cikinsa.
Saboda jikina banyi wani taron sunna ba a wanan karon andai radawa yara suna da Abdulraham dayan Abdulrahim babansu Nasir ya rada masu wanan sunan daga can Spain dinsu da yake zaune.
Don haka kowa ya kama kiransu da sunan abu daya nayi wanda yazo za a bashi kayan suna wanda namane sai snacks da drinks a leda indan zai tafi.
Amma duk da hakan bai hana yan uwa da abokan arziki shigo yi min barka ba a lokacin ciki kuwa harda su anty Usaina da zuwansu ya ban mamaki lokacin.
Bani ba harsu mama duk munji mamakin hakan don zuwan nasu suka kuma ce mahaifiyarsu tana min barka bata jin dadine yasa bata zo ba.
Radau radau muka rabu lafiya dasu hakan ne ya bamu mamaki matuka saida hauwa tazone nake labarta mata zuwansu naga mike zaune tana fadin.
Don Allah zainab ki bari suka zo gidan nan barkafa cikin mamaki da jin abinda nake fada mata nace Allah sunzo kinga leda can suka kawo muna.
Lalai namiji sai a barshi duk yadda akayi sun shirya da yayane ko suna neman shiri dashi a yanzu amma haka kawai zikau ba zasu taso zuwa gidan nan barka zainab indama ace akwai haihuwane a tsakaninsu kinga hakan na iya sa suzo barka din .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

8?? 3??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Kishi kummalon mata manya sukace hakan kuma ba karya bane don ban taba zato ko tsamanin zanji zafin dawowan Aisha gidan wurin mijinta ba a zuciyana ba sai gashi hiran mu da hauwa yasa abin tsaya min a rai ina jin zafin hakan.
Har nake ganin idan yai min hakkan da gaskiya shi mayaudarine kamar yadda ita Aisha kan fada mashi wani lokaci idan ranta ya baci dashi.
Haka na kwana ina sake sake da jin zafi da kunci a zuciyana har yakai na furta hakan a gaban mama muna zaune muna hira har Aina tace .
Abdulrahaman uwarku ta gudu ta kasa zuwa ganin ku sai sako tayi nasan dai wanan sokon na gyaran hanyane wajen ubanku ?
Nace mama ashe kin gane kema nima naga kamar zata dawo gidan nan ne su wa yan nan mazajen naki ai na farko ai basu samu hakan ba wajenta a lokacin.
Ban taba tsamanin yaya zai iya dawo da Aisha gidan nan ba ai duba da irin abinda tayi masa ranan cikin mutane koda yake ma ai sunfi kusa.
Ke na rabaki Abu kada ki soma ki tsoma baki cikin zancen nan nasu idan zai dawo da matarshi ya dawo da ita mana saman kanki zata zauna ke meye ruwanki dasu yanzu kuma.
Ita Allah ya mayar baya ita data neme wullakantamu Allah bai yarda da hakan ba wayaci baya yanzu idan ba ita ba.
Balle tsakanin miji da mata sa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i Allah inma zata dawone iyakanki dasu idanu ba ruwanki da zancen su kada ki yarda inji kin tsoma baki cikin zancensu ko kadan ki saka masu ido kawai ki gani ai mai hali baya barin halinsa kowa da halinsa ake zama dashi.
Balle wanan mai bakin halin yanzu yadda kika saba mashi din nan da komai yadda akeso gidansa na zaune lafiya ina zai dauki wanan iskancin nata kuma a yanzu kedai ki zuba ido idan ma dawowanne ta dawo gaki ai.
Ke yanzu kin zama iccen gamji saranki kuma sai an shirya don sara da sasaka bai hana gamji toho inji manya suka fada duk da wasu mata na karanbanin cewa .
Cire icce har saye baida wuya a wurin su to wani iccen ko an jijigashi baisan ma anayi ba balle ya girgiza kedai kara halin kwarai a wanda kike dashi da don kin

83 / 105