DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   65 / 105

192K to 195K   out of 313.1K words

kifita hakkuri son Allah .
Kin sani ba saina fadi ba tunda muke kema kike baki taba jin anzo ana sasanta tsakanjn mu ba da mahaifiyar ki hakama wace ke rikonki a yanzu itama hakane kubura tana da hakkurinta daidai gwargwado.
Mijinki abokiyar zamanki ki rikesu ammana kada ki yarda koda wasa wani mugun halin da bashi ba ya fito daga wajenki kada inji kada ingani.
Ki tuna auren nan ba wani ya hadaku ba kune da kanku kuka hada junan ku da kanku don haka sai ayi hakkuri da juna son Allah.
Duk da bansan halin Aliyu na badili ba na zahiri na sani tunda ban taba zama waje daya dashi haka mai tsayi ba ba zance ga halaiyanshi ba a yanzu .
Saidai ina kyautata zaton alheri a wajen bawan Allah nan son halinsa na zahiri ya nuna na boyen nasa kadan don ko yaya kakan fahinci mutum a wajen dabi,unsa.
Nan dai baba ya fada min maganganu mai kama da fada nashi da kuma shawara inda ya saka inna inata ta tofa nata albarkancin irin na uwa tagari .
Mun dauki lokaci muna hakan kafin baba ya jefo min tambaya yanzu a wajen ki akwai wani shiri da kike sonyi ko wanda kike ganin mu a bangaren mu zamu taimaka maki dashi haka ?
Dukar da kai nayi ina fadin tare da girgiza kai nace babu komai baba yace haba zainabu ki fada ko kina ganin don babu da karfin zarahi ba zamu iya maki komai ba a yanzu .
Da sauri nace a, a baba ba haka bane wallahi kawai dai nasan cewa mum zatayi komai a bangaretane ba zata yarda ma kuyi wani abin ba.
Duk da haka dai wanan karon a matsayin mu na iyayyenki dole mu tabuka wani abinda muma nauyine a garemu wancan Alh ya tare komai don haka bamu samu tabuka maki komai ba.
Don ita hjy kubura tace min shi Aliyu ya saka komai a gidan naki bai bukatan ko tsuke daga bangren kowan mu don haka.
Ita hjy kubura tayi min bayanin cewa kayanki na baya sunanan basu komai a inda aka boyesu munyi da itacewa zata duba tagani koda ya kama a sayar ne sai abaki kudin ki rike a wajenki.
Da sauri na sake fadin a, a baba nabarwa inna komai idan mum ta cire duk wani abinda takeso a ciki sai inna ta dauka kawai.
Ayi haka zainabu ina innan ku ina wanan kayan zamanin a yanzu ai dai ki bari a sayar ko kasuwanci kya fara da kudin nan gaba tunda baka zama miji na baka kullum ai.
Baba a yanzu banson in raba hankalina biyu ga karatu ga kasuwanci kuma zan dai hakkura zuwa nan gaba idan Allah ya kai rayuwa tukun.
Gaskiya duba ga yanayin karatunku a yanzu dolene a mayar da hankali ga wanan matakin da kikai a yanzu ina alfahari dake sosai zainabu yadda kika dage kike kokarin fitar damu kunya nagodewa Allah da wanda yai sanadin wanan karatun naki Allah ya kara albarka amin muka amsa masa.
Nan ya kara min bayanin cewa yana da shanaye daya turke akauye ana masa kiwo yaso ya sayar dasu don inna dama ta fada cewa ba zan yarda suyi min komai ba don tasan halina.
Don haka zaije nasasu akasuwa in sayar sai in kawo kudin a raba biyu don nan ita Rabi zatayi dibula da cincin irin na mata tareshi nayi da fadin.
Don Allah baba ka barshi har nan gaba in bukin su Asiya ya tashi sai ayi wani abin amma nikan a barshi don Allah akwai kudi a wajena zan bayar inna tayi duk wani laluran nata.
Zainabu ina kika samu kudi baba ya tambaya dan murmushi nayi kafin nace baba wanda shi yaya yake turo min ne da kuma yaya Nasir dasu muhusin sukan turowa mum dani kudin.
To Allah ya kara rufa asiri baba ya fada ya mike yana fadin cewa zai tafi cikin gari ya dan zaga nace ina zuwa baba daki na shiga na dauko kudin danazo masu dashi na mika masa a cikin ladabi.
Yace , a,a zainabu ga wanan hidimar tafe kin dauke muna kiyi wani wahala kuma yanzu haka ki barshi ki kara cikin wanda zaki bayar din zaifi nace baba don Allah ka karba baida yawa ai.
Bayan fitan babane ya rage nida inna sai yaran nan guda biyu inna ta shiga daki ta fito da wani leda baki ta zauna kusa dani tana fadin.
Ga wanan mamanki ta hado maki ya dade a dakin nan wajena ina boyonsa don tace sai zaki tare zan baki hadine namu na gida don ba boka ba malam amma muna karawa da gyara don jin dadin zama.
Tana kokarin bude ledan take fadin hakan kin gansu nan ko shekara nawa zasuyi hakan basu lalacewa a haka zasu zauna da wanan ake fadin muna gaje maza ba wani abuba muddin zaki yisa da kyau kafin ki shiga gidan banda sauran fargaba akanki saidai dan wanda ba,a rasa ba dai a gidan miji.
Na tsorace da kishiyar ki sosai yasa nayi mata bayani yaje har Agadaz ta hado makishi wajen kawun mu na can.
Don haka gasu a nan zaki aje ko zaki gidane dashi saidai idan kinje dole kiyi taka tsantsan kada hjy kubura ta gani son Allah banson wani zance da zai bata muna zamanmu da wanan matar ko kadan don dantane dole ayi taka tsantsan .
Allah yaga nufina ba don ki cutawa kowa ba saidon ki zauna a dakin mijinki ki tabbata a cikinsa har abada nayi hakan ba maison yau danshi na yawon gida kullum.
Abinda malam ya fada maki ki kula dashi karki cutar kuma Allah bai yarda a cutar dake insha Allahu kedai kiyi biyayya ki nuna so da kauna ga mijinki kamar baki son kanki kinyi dace yan uwasa dama yan uwakine don haka sai ki kara kama zumuci fiye da da can baya.
Baby ba komai ake muna kirarin kwancen miji ba sai narkewa narkewan mu ga maza shike ja muna hakan don bamu kunyan kyautatawa miji a gaban kowa kin sani.
Muddin kina hakan yanzu ne za, a fara zancen kin mallake miji sai yadda kikace alhalin shi miji a bangarensa yasan kyautatawan dake tsakaninku.
Maza kaman mage suke sunfi son mai masu shafa ko wani lokaci da wanan macen kwarai kanci gari kar kiji nace shafa ki dauka shafa na gaskiya nake nufi.
A,a kyau tatawa ta musanman dake tsakanin mata da mijinta wanda sai ma,aurata suka san wanan a tsakaninsu don Allah baby ki kula ki zage damtse don Allah.
Kin dai san waye Aisha tunkan ki kulla da mijinta son haka ina aon ki natsu ki natsu sosai ki karanceta ki san halinta ciki da bai kada ki yarda kije ku fara tsiya da tonawa juna asiri kuna tayarwa mijinku da hankali don Allah.
Har inkin biye mata kukai hakan ran hjy ba zaiyi dadi ba haka shima nasa kin sani sarai yana son matarsa badon baya sonta bane ya kara dake yanzu cikinsu .
Ki dauka dama akwai kaddaran aure a tsakaninku sai kin shiga cikinsu kunyi rayuwa a tare don haka ki natsu ki amfani da tarbiyan da aka baki a nan .
Da hjy ta zauna cikin natsuwa har yau hjy malka ta kasa cinma manufarta akanta saita fitar da ita gidan ku kina dai gani don haka sai kin kula sosai don Allah.
Kada kije kina sa ido akan abinda sukeyi da matarshi wanan ke damun mata da yawa yanzu aje a samu mace gidanta ace ai bata iya ba ina ta fito kingako ba zaman lafiya anan.
Kowa yaje yai kukan gidansu tashi ta fitar dashi a wajen miji ba sai kinje kina sakawa rayuwansu idoba don Allah saka ido bai barin mace zaman lafiya da mijinta kema kinsan hakan.
Gashi wanan daga yau zaki fara shafawa maranki iya mara idan kin gama ki shafawa goshinki ki murza da kyau kamar yadda kika murje mara dashi.
Wanan kuma turaren dan kadan zaki diga a hannu ki murza saiki shafe jikinki dashi kullum ki tabbatar da kinyi hakan da kyau haka wanan kada ki raina yawansa gaba daya zaki shanyesa tare da madara amma mai kyau amma sai ana gobe zaki tare a gidansa zakisha wanan.
Iya wanan ma din ya isa sai zasuzo zata zo maki da sauran hadin don Allah ki natsu kiyi amfani da duk abinda na fada maki da wanda babanku ya fada Allah ya baku zaman lafiya na amsa da amin.
Jikina yai sanyi sosai da nasihan iyayyena don haka na karasa wuni na ba lakka a jiki har yan uwa suka dawo daga makaranta suka sameni nan na dan sake muna hira dasu.
Asiyace ke tambayana wai anty zak auri ya Addel kuma ance yanzu gidansa zaki koma da zama yanzu da wanan matar nasa da bata son mutane zaki zauna ?
Cabdi inace ba zan iya ba gaskiya don kallon banza da takewa mutane ko gaisuwa bata amsawa shiyasa muka bar zuwa gidan sai ta bar mutane a zaune bata fitowa har a bar gidan.
Yanzu ba gani ba ina ruwanku da ita tunda yanzu ba wajenta zakuje ba son zuwa ai har kwana sai kunyi gidan wata rana tunda ina gidan nima yanzu.
Asiya ta kallomu tace kekan kinji dadi mijinki mai kyau dashi wallahi kuma dan gaye idan yazo gidan nan har kwana da yawa kamshin turarensa yana yawo a gidan nan.
Ke kinsan mijin da zaki aurane kika sani ko Allah ya baki wanda yafi ya Addel haka ake addua kullum ba hangen na wani ba.
Muna tsaka da hira sai sallamanshi mukaji a kofa duk mukai shiru Asiyace tace muryan yaya Aliyu nace shine kila yaje gida mum tace masa kina nan ke nan Rukkaiya ta fada suka fita wajenshi yana gaisawa da inna.
Sun jima ina jinshi dasu yana masu tambaya akan karatunsu inda yake fadin ya kamata asa sauran makaranta hakana naji Asiya na fadin baba yace sai an masu kaciya wai ?
Kai Asiya ba dai surutu ba na fada a raina yace Rukkaiya ba ance antyku na gidan nan ba tace ehh gata nan dakin inna kwance mun dawo school mun sameta nan.
Kira min ita ko barci takeyine idonta biyu OK ya fada saiga Asiya dakin da sauri nace kece nayi barci don Allah tace bayan na fada mashi baki barci ba.
Kice gani fitowa mikewa nayi zaune sai kuma na samu kaina da jin kunyar fitowa dakin alokacin ba yadda na iya dole haka na daure na fito daga dakin tare da dan kare fuskana da mayafin dake hamnuna.
Sannu da shigowa na fada kafin in kai zaune a gefe bai amsa ba sai cewan da yayi meya samu motarki da bakizo da ita ba ?
Matsala take ban kwanan nan shine mum tace in ajeta har aduba yafi sati uku yanzu ban shiga ba towa kika fadawa abu baida lafiya ina gari baki fada min ba itama mum bata fada ba.
Saidai inta mantane amma naji tana magana akai zata sa a duba min yayi ya fada ya koma ya dan lafe saman kujera tare da dafe kansa kafin ya dago ya sake fadin waya kawoki nan da baki kirani ba ?
Mum tasa Isa driver ya kawoni da zai fita dazun shi isa yana zuwa gidane har yanzu nace yau yazo don daddy enugu yayi tafiya.
Shigowan babane ya taimakeni don ya shigo yana fadin wai wani yaro ya aje roban nan a hanya jin hakan sukai kansa suna fadin eehh baba baba baba sannu da zuwa.
Mikewa nayi nima na leka inawa baba din sannu da zuwa ya dago yana fadin a, a zainabu kina gidan nan har yanzu inji gwaggon naki bata fadan dadewanki dai ?
A,a baba na fada a lokacin Aliyu ya leko yana fadin sannu da dawowa baba yace , a,a Aliyu kaima kana gidan nan ke nan naga mota amma ban gane ba da yake wanu lokaci mutane na aje mota a nan don filin dake wajen.
Wallahi nine baba naje gida mum ke fadin tana nan tazo shine nabiyo in bata sako ai inba gaba kayi ba saika dauketa ku koma gida don yamma yayi yanzu.
Kai gaskiya tunanen namiji dabanne dana mata ya fada a zuciyanshi mum dake muna iyaka a tsakanin mu shi kuma baba yanzu yanzu ya alakatani da ita don yasan hakkin aure da girmansa.
Ba matsala ta bari idan ta tashi saita kirani in mayar da ita gida ya fada don sai dare yake son dawowa ya daukeni lokacin yake son nuna min shina mijine fa iya iskancina a gaban mum ne kawai.
Yayi sallama da baba din yace zaije ya dawo baikai ko minti goma da tafiya ba saiga mum ta turo a daukeni haka na shirya na tafi bayan mun gama magana da baba da kuma inna.
Koda ya dawo sai samu yayi aina wuce din mum ta aiko an daukeni tunda yamma yayi mamakin hakan sosai a zuciyanshi.
Son haka ya nasa ba zai kara nemana ba zai hakkuri da duk wani hukuncin mum har sai lokacin dataga dama takai masani din gidansa.
Yana hanya ya bar gidan baba kirana ya shigo nake fada mashi cewa nabar gidan baba mum ta turo an daukeni zan dora muna sanwa na kirasa dazun yana busy .
A dakile naji ya amsa min da ba matsala ya kashe wayanshi ajiyan zuciya na sauke don nasan ba, a kyauta masa ba to ya na iya hakan hukuncin mum ne a gare mu don bansan nufinta ba na nisanta tsakanin mu da takeyi a yanzu din.
Don haka ni umurninta nake bi don kada wani abu yazo kuma ya faru tace aita fada min banji bane in hakan ya faru ko banjin dadi dani da iyayyena yasa nake kiyayyewa.
Ashe baba ya kira mum yana fadin bata kyauta ba son me mijina yace zai dawo ya daukeni ita kuma ta aiko bayan tasan yana gari.
Tace yaya kayi hakkuri girki nake son ta dora muna yasa na turo a dauketa yace kindai san matarsace don haka baki kyauta masa ba gaskiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6?? 5??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Hannu ya kai a hankali ya shafo fuska a hankali tare da dan sauke ajiyan zuciya yana maida hankalinsa a tukin da yakeyi.
A hankali ya karkata motarshi zuwa hanyar da zai kaishi gidansu Aisha matar shi da yasan tana gida yanzu haka ya rasa ya zaiyi da wanan dabi,an nata na rashin son zama a gidanta ita ko yaushe tana gidansu zaune sai dare ta dawo gidan.
Wanda hakan dole yasashi yawon gararanba a cikin gari da bai saba da shiba don idan ya gaji da zaman gidan shi kadai saiya shiya ya fito bai faye son zuwa gida a yanzu ba don da gida yake nufa amma tunda yaga mum tagane sai ya daina zuwa gidan saidai ya samu waje inda zaisha iska agari son dole ya mayar da kansa mai fita shima ko yaushe.
Ba motarta a kofan gidan nasu hakan ya tabbatar masa da bata gidan kenan a lokacin duk haka hakan bai hanasa karasa shiga gidan ba.
Ya shiga kamar yadda ya saba bayan an bashi iso ya samu iyayyen a zaune da alama uwar da matarsa take waya a lokacin don yadda yaji tana waya tana fadin kiyi sauri ki dawo gida na fada maki don gashima ya shigo.
Uban yake fadi a lokacin mah Aliyu kaine ka zagayomu ashe sannu da shigowa gashi ko ita hummairan sun fita tun dazun basu dawo ba amma naji mamansu na waya dasu yanzu.
Ehh Abba dama magana nazoyi daku duka har ita Aishan saidai ba matsala tunda gaku a gidan yanzu ai sai muyi zancen daku idan ta dawo sai a fada mata ba wani matsala bane ai.
To ai shike nan mahaifin ya fada yana washe baki yayin da uwar ke fadin bata dai jin maganane wallahi na fada mata tabar yin haka amma yarinyar nan kamar da dutse nake magana.
Wai me zaisa ya biyoni kuma nan ba zai jirani har in dawo gida ba koma meye to ai yace yazo magana damune dake duka yanzu sai a saurareshi aji ko dame yazo ai ?
Dukar da kai yayi yana Allah waddai da irin tarbiyan gidan su Aisha na self freedom babu tarbiya ko kadan a cikin zancen nasu yanzu saima kara tabarbarewa da yaga abin nayi masu kuma.
Dan dama uwar akwai dan natauwa sosaii a tare da ita saidai na banza tunda bata

65 / 105