DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   71 / 105

210K to 213K   out of 313.1K words

mayar da ita sarauniyace irin wacan da bata girki sai taga dama.
Aiko da zaina batayi ba idan tai hakan muda muke tashi tun shidda angama dumame da koko har kosai duk wani abinda za,a karya dashi an tanada ko kafin hansi ya fito.
Banda yaran yanzu hjy suna can kwance suna barcin safe sun dauki hakan wai wayewane a wajensu basu san koma baya yake ja masu ba gun aurensu.
To ai gashi sai daya ko biyu wani lokacin yakezo muna nan yace wai abin karyawa yake nema tunda bai saba cin abincin wajeba kinga bai iya hakan ba da bamuji ba ai.
Ikon Allah to itafa me zataci idan bata girkaba mum tace yaya Azumi ke nan itama taje gidansu taci mana ai shine wayewan yanzu .
Kedai bari naga abu gun yarinyar nan kuma baison a fada tunda yar sarkin garice ita yarinya ba mutunci sai shaganta iri iri nayi mamakin samun irinsu a cikin al,umman hausa haka wallahi wayewa zaisa kabar Allah ka kama akidar banza da wofi.
Aidai jiya kun gani yadda tayi maku cin mutunci don kawai ankai mata kishiya zatayi wanan haukan gareku dayan tace a to ta hadu da daidai da ita ai don yaran basu kyaleta ba ai suma sun fadi son ransu.
Wayanshine yai kara da sauri ya dago yana dubawa mahaifin Aisha dince matarsa ke kiransa kamar ba zai daga ba haka ya daga da sallama a bakinsa.
Ya fara gaidashi da Abba ina kwana ai yaji yace dashi rike gaisuwan ka malam Ali don na kula kai baka san mutunci ba ashe mun matsawa yarinya ta koma shine kake ganin kayi galaba akanta har zaka nemi yanzu ka wullakanta min ya ?
Amma ai Abba sai ka tambayeta ita meya hadamu ni dai bansan munyi fada ba sai yaji yace akan me zan tambayeta zatayima karyane kome ?
Kai abin nan fa idan bai yuyuwa yanzu tunda ka samu yar uwaka a barshi kowa ya huta amma ba zan dauki ka wullakanta min ya ba don wata.
Sai yaji ya kashe wayan shima tsuki yaja yana aje wayan dago kan da zaiyi ya samu mum ta kuresa da idanunta haka ya daure yana basarwa a lokacin mum tace.
Wani Abban ne kuma cikin dauriya yace da ita mahaifin Aishane dai mum kinsan haka yake kamar bature akan yaya shi wai takai karana gunsane kuma .
Ikon Allah jiya jiya da akai mata me kuma mama azumi ta fada cikin mamaki mum tace ai zakiko sha mamaki indai wa yan nan mutanene kuwa aiba sai anyi ba.
Yanzu in sunga dama su riketa kwana da kwanaki ba matsala bane garesu sai taga dama ta dawo gidan duk lokacin dataso hakan.
Kai amma ko gaskiya basuyi ba kai malam anyi wani abune lokacin ya danyi murmushin yake yace dazun ne da zanfito na shiga mu gaisa dasu don yan uwanta anan suka kwana gidan.
Ina shiga ina fadin kun tashi lafiya sai cewa tayi akan zainab watsartsa data gama watsewa nake wani rawan kai har ina neman wullakantata kome ?
Shine nake fada mata watsarsuma na kwarai ba,a wullakantasu ba kuma an zauna dasu ai lafiya balle zainab da take cikakkar mace kamaila data rike kimarta.
Guntun murmushi ya hango a fuskan mum tana kada kafa tace tarbiya aiba daya ba su kuma suna fadin kinji jan magana ko hjy aiko yanzu dai bukatana ya biya Alhamdullahi wallahi.
Kwarai ma kuwa insha Allahu wanan abin haskene ga kowan munan hjy ai wani lokacin gara wanda kasani na kusa dakai din da hangen nisa gara dai da akai hakan yafi kowa hankalinsa zai huta yanzu mum tace Allah yasa hakan nake fata ai.
Can dai ya mike yana fadin barin shiga mu gaisa dasu mummy daga can zan wuce ba dai wani abu ko ya tambayesu ?
Babu komai mum ta fada inda ita mama Azumi take fadin kayi hakkuri kaji dana komai zaizo ya wuce insha Allahu Allah ya baka ikon aikata adalci a tsakanninsu ya amsa da amin ya fita.
Kungani ba yanzu kila can yayi zaije yana basu hakkuri yana dodofa karsu amshe masa ita sun gane takonsa yasa yake wahala bai sani ba ya mutu da sonta a zuciyarsa.
Haba hjy bari dai ita wanan ta zaunu watarana kyace bashi bane Allah itama yanzu duk iya shegen nan dainawa zatayi idan taga inda hankalinsa ya karkata.
A part din mum kuma gaba dayansu yan gidan da wasu bakin dabasu koma bane ciki anata zuba lokacin yayi sallama ya shigo akai tsit kamar ba kowa part din.
Nan ya gaishesu a cikin jam,i suka amsa suna masa ya gajiyan taro ya amsa da Alhamdullahi suma ya gaidasu da dawainiya ya fita aka kuma dauka.
Yan koran mummy na fasin ai yanzu dada anyi kowa ya huta sai a zuba ruwa kasa kuma asha dama abinda mum keso ke nan tayi wanan cin fuska babu ko kunya a ciki.
Ba wanan yake damun mummy ba sai irin arzikin da suke hirancewa an malala a gidan ya tsaya mata a zuciyarta har take tunanen ina nata dan yake shagar da samunsane yanzu ?
Wanan abin ke cinta tunda labari yazo mata hakan yasa yanzuma ganin Aliyu ya kara tayar mata da hankali ta shige daki tana kiran layinsa.
Tayi sa,a ya daga kiran yana dauka yake fadin mummy ya akayine duk da taji ba dadi hakan ta share tana fadin hazif ina kana lafiya dai wajanka.
Nan taji ajiyan zuciyansa ya amsa da lafiya kalau mummy ya wajen ku kuma tace duk muna lafiya jiyan nan akai bukin tarewan zainab da Aliyu ina kasani ?
No banda labari saidai naga yaran nan suna posting din photuna na zaci hakan wanan guy din watau saida yarinyar nan ta tare a gidansa ke nan ?
Tun jiya yaje yaita yi ai gata nan gashi shiya damu da ita nan ta fara bashi labarin abubuwan daya faru har tazo gun ginan da akace yayi min tana fayyace masa komai.
Sai cewa yayi ba wanan bane agabana yanzu mummy aikina dake barazana a nan shiya dameni yanzu yake dan mata bayani nan kuma hankalinta ya tashi.
Har take data sanin kiransa a lokacin don hakan ya tayar mata da hankali sosai wanda take danjin zazzabi na saukar mata a jiki.
Nafisace ta shigo a cikin shiga na alaman fita take fadin mummy zan fita amma ba zan jima ba zan dawo saita dawo kawai tayi mata ta fita ta barta cikin takaici da tunanen mum da iyalinta.
Don ita a iya sanin ta dai tana tsaye akan yayanta duk inda taji wani sharare komai nisa tana kai kanta ko sako amma kamar bayi takeyi ba lokacin.
Ta rasa ina mum ke samo nata malam da sukai mata tsaye kanta da yayanta haka komai nata yake tafiya ba lankwasa ko gargada ko wani lokaci.
Daga gidan daddy gida ya nufo kai tsaye ganin part din Aisha a rufe yasa ya gane bata gidan ke nan haka ya shigo da malolon bakin ciki a zuciyarsa.
Yana sallama ina tsaye gaban dinning da waya makale a kunnena hannuna kuma yana gyaran kayan abincin da hauwa muke waya lokacin ya shigo.
Juyowa nayi don ganin wanda ya shigo a lokacin shina gani a tsaye ya kura min ido a hankali na juyo ina fadin sannu da dawowa yaya.
Amsawa yayi daga inda yake kafin naga ya juya yanasawa kofan key ya juyo yana fadin idan kina ciki ki saba da rufe kofa duk wanda zai shigo kin sani.
Don yanzu haka ke kadaine a cikin gidan nan sai maigadi don ba kowa a gidan Aisha ta fita saike kadai kinga idan barci ya daukeki baki san masu shigowa ba ai.
Zan kiyayye yaya na fada tare da fadin kadawo ya amsa da Allah ya dawo dani zainab yana takowa kamshin falon dayasha gyara yana fisganshi kafin yaji ya taka laulausan carpet din tsakiyan falon ya lumshe idonshi lokaci guda yana maijin wani irin yanayi a zuciyarsa.
Zaune yakai yana lumshe idanuwansa abinda yake so ke nan a rayuwansa don haka ya taso ya samu mum tanayi a gida bakaiwa mum girshi a gidanta don ko yaushe gidan tsab yake a gyare don haka ya sabada hakan shima.
Saidai sabanin hakan yayi katari da Aisha malalaciyace sam bata iya irin gyaran nan ba kuma ta hana ya dauki mai ,aiki wai bata yarda da hakan ba don yawan sherin yan aiki.
Kitchen naje na dauko masa ruwa na kawo masa yana zaune ya mike kafa tare da dora hannunsa saman goshinsa yaji nace ga ruwa yaya.
Jin hakan yasa ya cire hannun tare da sauke idonsa akaina ina gurfane na fara zuba masa ruwa a cup lokacin yake bina da kallo don bakon yanayin da yake gani a gareni wanda yakezo masa kamar sabo.
Hannu naga ya mika min alaman nazo ganin hakan yasa na mike zuwa gareshi saman cinyarshi ya zaunar dani yake fadin.
Naji yace kinyi kyau sosai baby saidai matsalata dake bakya hutu don banjin bayab fitanama kin kwanta kin huta haka kike aiki da gajiya a jikinki ko ?
Duk da naji dadin hakan sosai wallahi kwana dayan nan da nayi dake zeey kin fara sanyani cikin farinciki mara misaltuwa a zuciyana.
Don na hango alheri tun yanzun nan a zaman mu ina son ki kasance mai hakkuri da kuma dauriya a gidan nan cikin zaman mu.
Insha Allahu yaya ba zaka sameni da wani matsala ba matukar zakai adalci a tsakanin mu Allah kuma ya bada ikon hakan ya amsa da amin yana matsan yan yatsun hannuna a hankali .
Dakyat na iya budan bakina nace taso muje kaci abinci don nasan ka kwaso yunwa mum kuma ba baka abunci zatayi ba yanzu .
Kema kin sani ya fada yana dagoni tare muka jera zuwa gaban dinning din dashi ya zauna na zuba masa daidai cinsa kafin na koma gefe na zauna nima bayan na zuba nawa.
Hankalinsa na a waya saida na gama zubawa yaga nazauna ya dago yana fadin ya naga abincin gida biyu kina nufin ba tare zamuci dake ba kome ?
Haba yaya idan wani ya shigo ya samemu hakan fa me zance ga dai naka nan na zuba maka ai na fada cikin danjin nauyisa yace kinga amfanin rufe kofan don haka ki taso ki ban abinci in kina aon inci abin kwarai.
Ba yadda na iya hakan na taso cikin kunya na fara bashi a baki bakunya ko ya karba yana ci kamar wani yaro saida na bashi kamar two spoon naga ya dauki spoon din ya debo abincin ya kai min a baki na noke kai yace karbi mana ko so kike inbar ci nima dole na bude baki ya zuba min.
A hakan mukaci mukasha a falon nidashi yanayi yana zolayana banda bakin bashi amsa lokacin don nauyi da kunyarsa da nakeji.
Sam ban taba zaton zan samu yaya haka da saukin kaiba don yadda aketa tsoratani akanshi da matarshi musanman yan gidan mu gidab daddy.
Sai gashi naga abin ba hakan yake ba yadda kowa ke tunanen Aisha zatayi min katanga tsakanina dashi dana shigo gidan.
Mikewa nayi don in tattara kayan naji yace ina kuma zaki dasu ai zaman nan da kikaga nayi ina jiran cikina ya dan sakene na kara wanan ferfesun .
Kinsan ina son ferfesu a rayuwata samune yadda nakeso banyi baka da matsala don nasan kanaso na hadama dashi ai barin dauka anjima din idan zakasha sai in dumama maka nafada baiki hakan na kwashe na gyara wajen nagoge komai tsab kamar bamu zauna munci abinci ba wajen.
Koda nagama yana dakinsa bai fito ba saida akai sallah la,asar ya fito falon waje naji ya fita ya dan jima kafin ya shigo ya sameni a falo zaune cikin dan wani riga dogo amless da dan mayafinsa nayafa saboda yanayin dan zafin da akeyi.
Nan ya zauna shima ya sauya tufafin jikinsa zuwa kananu ya cire yaddin daya saka da zai fita gab dani yazo ya zauna yana fadin.
Naso nayi magana daku biyun a yau saidai wanan tafita bansan dawowanta ko sai dare ba wanan yasa banson zuwa da ita garin nan .
Dama a abuja ko yaushe tana gida amma nan da munzo ko yaushe tana gidansu bansan uwar da takeyi can din ba kullum.
Gidane fa yaya idan ta wuce kuma sai lokacin da suka sake ganin ta balle wanan karon kun dade basu tare dole ai ta dinga zuwa kullum.
Kishingide yakai yana daukan remote ya halbo Africa tv three yana fadin barta kawai nasan maganinta ai da kaina zanyi maganinta gidan nan.
Yanzu ke idan kece a kullum kina hanyar gida daddy ko mum ko baba zasu brki kije yau kije gobe don Allah ?
Da sauri nace rufa min asiri garama daddy ai baba har gidan nan zaizo yayi duka kila mum ko harara kawai ya isheni da ita ba sai ta tsaya bata baki bama.
Balle itama anty din wata rana zata daina hakan ai kafin na rufe baki yace yaushe ke nan baki san komai ba don Allah kiyi shiru kawai kinji.
Allah zata daina idan ta tara iyali ko ance ta fita ga hanya ba inda zata fita ai don laluran iyali ya isheta a lokacin kadai kara hakkuri kawai damu don Allah.
Zan mata biyayya iya yadda zan iya insha Allah tunda na riga dana san wasu halaiya nata ai abin zaizo da sauki naji yace zainab na amsa mashi da na,am yaya.
Yace kinsan wani abu a hankali na girgiza kaina yace na farko ina son ki kasance mai biyayya a gareni ko yaushe yi nayi bari na bari.
Haka kuma na biyu don Allah banson yawan fitina a gidana ki zamo mai kawar da idon ki akan komai idan kinyi hakan zamu zauna lafiya dake anan.
Saina ukku ina son ki kasance mai daraja iyayyenmu ki zamo mai kara dirani a yan uwa don kinsan korafin da nake fama dashi akan yan uwa.
Wanan abin yana kona min rai bana jin dadin yadda kowa ke korafin nan akan gidana har da wanda baizo gidan nan ba yana wanab korafin kin sani to yanzu a gyara don Allah.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7?? 1??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Nagama shirina tsab cikin wata yar rigar da bata gama rufe min cibiyaba duk mai dan siririyar hannu kamar shimi sai dan wandon jins namata tiet ne wandon don yana dan budawa idan kajasa.
Ya tsaya min iya wuyan kafa wanda hakan ya fito min da santala santalan kafana fili farare sol dasu zakice ban taba taka kasa dasu ba don taushi da santsi ga haske kamar wata jinsi ba yar rumawan katsina ba dani.
Dan kalaban dake kaina na gyara parking dinsu sai kwara biyu na rage afili suna rito ta gaba na daure kamshi na dinga lakata ina murwa a jikin tufafin jikina sin masu taushi da ladabtar da zuciya ga wanda ya shaka ajikina duk odan hauce wanan.
Dan sarkana na dauko na manna a wuyana da dan kunnensu a kunnena sai hakan ya kara fito min da shwkin fuskana shar a fili.
Lokaci na duba hakan yasa nasan duk inda yake ya kusa dawowa gida lokacin don bai wuce takwas da dan kai a waje ka,idane wanan wajenshi.
Yaune zan karbi girki tunda yaya yayi min kwana huduna irin na zawarawa acewa uwargida aini bazawarace ba budurwa ba.
Yaya zaiyi gardama nace muje a hakan wanan ba matsala bace a wurin zainab indai kwanane ba matsala tunda ina gidan matsayin mallakinsa yanzu hakan ya kwana gidan sauki a waje.
Wanda hakan kuma yaja min girma a idon yaya sosai don yaji dadi a karshe rashin yi masa gardama da banyi ba din a lokacin.
Don haka tunda ya tafi ta hanashi shigowa part dina don haka nake zato saidai da safe zai shigo yai min ina kwana sama sama ya fice sai kuma dare zaizo a gurguje muyi saida safe wani lokacin kafin yazoma na rufe part dina na kwanta saidai ya koma hakana.
Duk ko da gangan nakeyi takone da kaidin mata son kafin ya dawo wurina zai matsa indai akwaiso a hakan dole namiji ya matsu ya dawo gunka.
Saidana fito na shiga kitchen na kula da garin ashe hadarine ya hade sosai sai walkiya akeyi ko ina yana haskawa tare da dan cida lokaci guda.
Madaran peak na dauko na fasa na juye a cup dake da hadin da hauwa tace in tabbatar da na shashi a ranan daidai lokacin juyashi da kyau na shaye na daureye cup din na kife.

71 / 105