DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   29 / 105

84K to 87K   out of 313.1K words

Itama din karatunta takeyi hankali kwance har lecturan da zai dauke mu ya shigo ajin muka mayar da hankalin mu ga abinda yake koya muna din.
Ya dade kafin ya fita lokacin ta juyo ta kalleni tana fadin gaskiya ban fahinceshi sosai ba da zan samu karin bayani zanso ni dai banyi magana ba sai kokarin bin abinda ya koya muna nakeyi.
Tana kokarin jana da hira duk da basar da ita din da nayi a lokacin bai hana taci gaba da magana ba dani sai amsa da nake bata a takaice take fadin in taso muje wajen motarta mu karya don lokacin break yayi.
Sai lokacin na dan dago ina fadin nagode ban tare da yunwa saida na karya na fito ke dai yar uwa naga kamar baki natsu dani ba niko kaf ajin nan dake hankalina ya kwanta.
Nagode na fada tace kinsan komai gamon jinine na hango natsuwa a tare dakene sunana hauwa Garba daga Niger state muke aiki ya kawo mu garin nan duk da mijina uwarshi yar garin nan ne ita.
Sai lokacin nayi dan murmushi a fuskana ina dagowa nace surname din mu daya dake ashe nima zainab Garba katsina nake bearing a takarduna.
Tace shike nan mun zama sisters dake ashe shine mafarin sakewana da wanan bakuwar da yanzu take dan sakani magana koda ban son ba kuwa.
Don irin mutanen nan ne masu son asani nan halinmu yasha bamban da ita amma ba laifi tana da son naci ga karatu ga yadda na fahinta idan an koyar bata gane ba zatayi ta nacin da sai ta gane kome ake nufi wanda nima ina kara fahinta ga hakan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

2?? 9??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Haduwana da hauwa a yanzu yasa na dan sake wani lokaci har banson mu rabu don tana sakani dan walwala idan muna tare kobaka so hauwa saita saka magana ko dariya.
Sannu a hankali wata yar sokoto itama ta hade damu saidai ita auren ta ya mutu a lokacin duk da tana cewa damu zata komawa mijinta ai don ko yaushe tana maganan hakan haihuwanta daya dashi suka rabu ta dalilin kishiya sai yayanta ya daukota zuwa kano ya kadata karatu a nan kano din.
Sai Fatima kawata ta secondary da wani lokaci tana zama damu itama don haka ko ina mu hudun zaki ganmu a tare don department din mu daya ba yawa ke garemu ba kuma dama hakan yasa muke tare da juna.
Duk zaman mu basu taba sanin cewa ni matar aure bace don ban fada masu komai ba akaina sun dai san cewa ni yar jahar katsinace kawai .
Su a zatinsu ina zama da yan uwanane kawai a nan kano din duk da suna ganin malam isah driver na zuwa daukana kullum amma basu kawo zancen aure a gareni ba.
Don a lokacin bamu da lokaci karatun mu yadau zafi zamuyi jerabawan canza ajine ba wani wasa ko shiririta agaremu gashi sun gane ina da fahinta don haka suka kara like min muka hade sosai dasu.
Ban kiran kowa a gida yanzu saidai su kirani don tun ranan da nakira mum ta furta min kunyanama take ji a yanzu don bata san me zata iya furta min ba na daina kira saidai su idan sunjini shiru daddy kesa ta kirani mu gaisa.
Ya ban hakkuri yace na kara hakkuri akwai abinda yake jira yasa ban jisu ba amma insha Allahu komai zaizo daidai a garemu nikan ban damu ba don yanzuma da nake zaman kaina nafi jin dadin karatuna tunda banda wani takura .
Bamai sakani aikin komai gidane ni kadai ke cikinsa don haka kwana bibiyu nakeyi na bata lokaci tunda safe na gyara gida kafin malam isah yazo daukana.
Dan abinda zanci kuma wani lokaci a waje muke tsayawa hanya in saya in dawo gida dashi ba sai nayi girki ba a ranan gashi ban saka damuwa ba yadda mutane suke zata sai wani haske da kyau dana kara a yanzu din.
Ma,ana d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ai sannu a hankali na fara gogewa ina ganin kwaliyan gayun makaranta yadda suke dresse dinsu don haka nima ban bari an barni a baya ba duk damu kayan mu da lap cort a sama don a bambantamu da sauran dalibai.
Da farko nayi rakin karatun nawa saidai yanzu ina jin dadinsa yadda muke samun shawara da kulawa yadda ya kamata sai nake jin kara son karatun likitan a yanzu.
Mahaifana da suka haifeni kuma kusan ko yaushe da dare idan na dawo nakan kirasu a waya mu gaisa mukan dade da baba yana ban magana har banson ya dauko min zancen auren hafiz dake kaina duk lokacin daya dauko min wai yana ban hakkuri nakan shiga wani yanayi na daban a lokacin.
Muyi hutu da kyar duk da hutun ba wani mai yawa bane dai amma mun samu dan sauki a lokacin saida nayi sati daya a gida ban leko ko get ba iyakata da waje in nafitowa maigadin gidan da abincinsa shine fitana.
Ranan na shirya don in kai masu ziyara gida a karo na farko ke nan wata shidda da auren mu kuma ke nan don a gaskiya nayi tunane kada wanan auren ya tabarbare muna zumuncin mu da iyayyena.
Tsab na shirya nayiwa malam isah waya tunda dare yazo da safe ya daukeni saiko gashi don inason inyi sammako in samu daddy a gida kafin ya fita kasuwa.
Don har zazzabi daddy din yayi amma yace kada a fada min shine baba ya kirani yana sanar dani don haka na shirya don zuwa gida din bayan nayi tunane akai.
Cake da zubo da kunnu ayyah mai dadi na hada nasa a basket sai gida da anty Nafisa na fara haduwa wani kallo take min zakice ranan ta fara ganina muka gaisa na shige part din hjy mum.
Ashe fasa fita tayi taje tana fadawa mummy shigowana dani da basket din ban ko zauna ba mum ta daukeni takaini falon daddy mu gaisa dashi muka gaisa ya nuna jin dadi da ganina din ba cikin mugun kama ba da sukayi zaton ina ciki.
Mun dan dade dashi muna hira kafin na mike don yafita don ba komai bane illa nasiha da saka min albarka kan biyayyan da nayi masu da suke min shida mum din har ya bada basket din yace a kaimai a mota kafin ya fito shida abokansa zasuci a kasuwa.
Yanawa mum sheri da cewa saidai ajin kamshin wanan hadin amma ba mai lasawa a gidan nan tunda diyana tayo min part din mum muka koma a can muke hiran karatuna da mum kafin na mike ina fadin mum bari nashiga nagaida mutanen gida.
Part din Dada na fara shiga inda na sameta a zaune ita kadai tana kallon tv na fado dakin ina fadin halan kina jin abinda suke fadane kin kurawa tv ido haka ?
Saida ta dago ta kalleni da kyau tace ja,ira yau kece a gidan namu ko angon naki ya dawone kuka shigo na kai zaune ina fadin ai kunfi kusa idan ya dawo kece zaki fara sani ai.
Watau Dada harke kika shareni kuka barni ni kadai kamar banda kowa ina rayuwa agida kamar manya kiri,kiri kikaki zuwa mu zauna tare ?
Tace bari yar nan karma kiyi magana don Allah nasan kaf gidan nan mu masu laifine a gareki ai amma don Allah ki yafe muna .
Da sauri na tareta da fadin haba Dada kin taba jin inda iyayye sukaiwa yarsu laifi kome kukai min ai a cikin gatane wata rana sai labari insha Allahu.
Allah dai yai maki albarka yau da ace ba jinin Abu kike ba watace da ba,asan yadda rayuka zasu baci ba da zancen nan lalai hakurima da kawaici gadonsa akeyi na yarda da hakan akanki.
Don kin nuna muna ke jinin Abuce da malam na cikin gida yadda suke kiran kakan mu dashi ke nan lokacinsu dan muskutawa nayi ina murmushi.
Tace yau abin nan da badon ke da iyayyenki masu hangen nisa bane bansan iya inda zancen nan zai tsaya ba ja,iri dan banza zai gama haukansa ya dawo hanya ai.
Bayace wai course ya tsayar dashi ba to wata shidda yanzu ai ya cika sai mugani wanan dan anyi la,anane a cikin zurian mu wallahi duk halin su Marka ya dauko babu halin zariya da dan nan ya dauko namu.
Bari na gaida mummy in dawo Dada na fada ina mikewa tsaye tare da gyara mayafin kaina da kyau na fice daga wajen Dada din.
Har nakai kofa na tuna da halimatu da ban ganta ba na juyo ina fadin wai halimatu fa Dada tace ke dai bari wata yar banza ke nan ai.
Tana katsina kusan wata ukku ke nan yanzu daga zuwa ta dubo iyayyenta taje can ta samu waje ta zauna ni banmasan ko sun rike abinsu bane can.
Sallama nayi har sau biyu ba a amsa min ba hakan yasa na zata basu falon a lokacin sai nasa kai nashiga amma sai ganin mummy nayi zaune tana cin abinci hankali kwance sai anty Nafisa dake fitowa daga daki.
Ban daddaraba na sake sallama a gareta ta amsa min a dakile na zube kasa ina gaida da ita kamar ba zata amsa min ba tadai amsa din tana fadin .
Ashe ina da darajan da zaki shigo gaidani na dauka ai ba za a barki ma kizo ki gaidani ba tunda nina haifi hafiz ai da sauri na dago na dan kalleta daga inda anty Nafisa take tsaye tana sauraron mu tace haba mummy haka ba kyau fa.
Ke ki min shiru don Allah ko yanzu ta shigo gidan nan watau ni banda darajan da zata fara zuwa wajena ta gaidani sai kubura ko don bata daukeni da muhinmanci ba a rayuwanta.
Koda yake ai dolene kiyi hakan tunda yadda akeso ba,a samu ba kinga ko dole ki hakan ina dai duke ban dago ba a yadda nake.
Taso sis ya exam anty Nafisa ta fada tana kama hannuna zuwa part din dakunan su mummy data bini da kallo taja uban tsoki tana hade rai tare da kawar da idanunta kaina.
Hijjab na rufawa mata asiri don haka hijjab din dake jikina ya hana mummy ta fahinci yadda na koma a lokacin sai take ganin ina nan yadda nake ai ban karu da komai ba sai bakin ciki da takaici kawai.
Na kasa sakin jiki da ita duk yadda take dan jana da hira akan exam din mu wai idan ina da matsala in fada mata tabi min case din nan na nuna mata banda matsalan komai ga karatuna ban jima ba na koma part din mum.
Kwatsam muna zaune muna hirane sai ganin mummy mukayi kamar an jefota tana shigowa take fadin hjy kubura yanzu ma din da zainab take matsayin sarakuwa a gareni ba zaki bari mu zauna lafiya da ita ba ?
Dan abinda ta kawo kin karbe kin tura daki koda yake ba mamaki ai don kinyi hakan dama donshi kikai dumu dumu a cikin rayuwanta ai.
Kaiya Allah waddan naka ya lalace inba lalacewa da rashin sanin ciwon kai ba har yaushe zakizo nan ki tsaya kina fada akan abinda mama ta shigo dashi gidan nan.
Au to haka kikace kina da wani manufa ke nan ashe watau lalacewane don na nemi sanin hakkina don yanzu mama a matsayin karkashin dana take ba karkashin ki ba ko wani a gidan nan.
Amma tunda hakane shike nan zan gwada maki baki da wani power yanzu akan yarinyar nan ke kuma makira zaki gane cewa kina wullakantani baki daukeni matsayin uwar mijinki ba ko kadan ko ?
Na dukar da kaina banyi maganan komai ba har tagama fadin maganganunta ta juya ta fita ban jima ba mum tace in tashi in koma gida wunin da banyi ba ke nan a gidan kuma.
Nayi niyar inje gidan mu sai na tuna da sharadin mahaifina akaina daya haneni da zuwa gida in dubasu sai idan mijina ya dawo yace inzo zanzo gidansu.
Wai ashe hakan bayan na tafi mummy bata bar fitinan akan zabcen zuwan nawa ba , acewanta wai nazo masu da abu mum ta boye a part dinta ita kadai don zalama.
Dole har gaban daddy dake zaune saida ya gama sauraron korafin mummy din ya dauki waya ya kira malam isah yace ya bude boot din motan ya dauko kayan nan da mama tazo mashi dashi da safe.
Nan mummy ta fara wiki wiki da idanu kafin malam isah ya shigo da kayan yana fadin Alh ayi hakkuri na manta inshigo dasune yace ya aje nan gabansu ya aje ya fita.
Lokacin daddy ya kalli mummy din yace bayan wanan tazo da wasu kayane gidan nan ina tace ani tayowa cake din da abinsha na kumace ba zan ba kowa ba a cikin ku na fita dashi kasuwa mukaci koba haka ba hjy kubura ?
To ni me zance Alh mum ta fada tana dan murmushi amma ai kasan ba,a kyauta min ba ta yaya yarinyar nan zatazo da abu gidan nan amma ba zan sani ba.
Ke Malka kada ki manta har yanzu ba dan nakine ke ciyar min da ita ba saiki bari duk ranan da dan naki yazo ya dauki abinda mukai masa da muhinmanci sai kiyi wana barazanan naki a kanta.
Ya dai tawace nike da iko da abina kuma ta nunawa duniya na isa da ita ni yarinyar ta gama min komai a duniyan nan don haka ki dauki zancen ki na shirme ki nade ke yanzu bakiji kunyan fadan wanan maganan ba.
Lalai mlka baki da kunya da har kikazo fada kan wanan abin don da kinada kunya da bakiko daga kai kin kalli wanan abin ba.
Ni dama nasan don a cuta muna akai wanan hadin bawani abu ba yaron nan yace baison hadin nan amma ka nace akan hakan yanzu kuma nayi magana kace ina na fito ?
Ta mike ta fice ta barsu zaune a wajen kowa imani ya kashe masa zuciya sai mum ne tayi karfin halin fadin inba shirme ba keda kika iya wanab kika gazaki saka danki yaiwa mahaifinshi biyayya.
Ta mike itama ta fice don lokacin har mijin nasu takaicinshi take ji ganin ya gaza daukan mataki akan iya shegen da matar nasa da danshi sukeyi ya zuba ido kawai ya kasa magana.
Tun rana kuma ban koma gida ba haka na hakkura na zauna gida ni kadai don in maida kaina busy na fara karatu a lokacin kan abinda mukayi a baya ko kuma in kuna kallo ina bin episode.
Har hutun mu ya kare muka koma makaranta nan karatun mu yaci gaba bani marmarin zuwa gida saboda fahintar da nayi cewa zuwan nawa yana haddasa masu fitina.
Don Allah ya gani a lokacin ba, zan iya zama part din mummy na tsayin wani lokaci ba saboda ban saba hakan ba a rayuwana zama a part dinta don bata da dadi ko kadan.
Karatu muke babu kama hannun yaro don haka inna fita tun safe ban dawowa sai yamma lis cikin irin hakane ranan na dawo a gaji bakin get nake sauka don ban shigo ciki don kada in wahal da malam isah din.
Sai dai idan ina da kayane zai shigo dani ciki in sauke sai ya tafi duk da umurnine na daddy nima akwai kyautatawa a tsakanin mu don ina mutunta dattijon sosai saboda ya dan girmewa mahaifina ga shekaru.
Ina turo get din gidan na shigo na hango mutum zaune saman mota ya kurawa kofan idanu ga karan sigari a hannusa sai hayaki ke tashi a wajen baiko gudan yaja matsala wuta ya tashi.
Gabanane ya fadi rasa don ban taba kawo zuwanshi ba sai ganin nan da nayi masa da alama ya dan dade a wajen zaune don guntayen taban da nagani a warwatse a wajen.
Cikin karfin hali na karaso ina furta sannu da zuwa makin ya amsa min sai dirowa da yayi daga kan motan yana jan tsuki tare da kakabe hannayesa.
A zuciyana nace kazamin banza Allah ya kara nisantaka dani mugu kawai azzalumi na nufi hanyar kofan falo na dauko key ina budewa.
A daidai lokacin wani mugun warin taba ya shiga hancina saida na zabura na dan juya shine ke hawowa step din daidai inda nake fuskan nan murtuk dashi kamar abin tsoro.
Gashi yayi baki ya dushe gashi kuma kananan kaya ya saka a jikinshi rigace mai dan hannu daya fito masa da damtsen hannusa waje sai wando jeans na maza dark blue ni bama idona ke mun gizo ba

29 / 105