DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   98 / 105

291K to 294K   out of 313.1K words

fitowa dakin nima kuma ina bukatan mijina dama karfin haline namu na manta nakeyi a lokacin don inace dake banson yaya a gaskiya na fadi karya.
Allah yasa min sonsa a zuciyana saidai ban yarda yayi amfani da daman hakan ya cuta min don nasan ko yanzu dana tsaya ban dauki mataki ba dole yadda mum ta juyashi a kaina hakana zai bi don tace ai zai dawo ya sameta Abuja kuma da zainab za a badani ba.
Me zan tafi inyi da yara can na batawa yara tarbiyansu bayan suna karatun su anan a saukake ko so nake ala dole ace dani nima mazauniya abujace yada matan can ke tunkaho a gari.
Ire iren zancen da mum tayi ta jefa min ke nan a cikin fadanta ranan ta dai nuna banda wani volume da incin kaina kamar ba jin dadin aure nazo yi ba auren zumunci ke nan.
Shike nan idan ke ta gidace baki da power yin abu a rayuwanki sai yadda aka juya ki kina biye kamar matan dauri dole kome zakiyi sai kinje kin fadawa uwar miji ta sani kada kiyi laifi .
Don mum ta fito min karara da cewa bashi yasa ta yarda na auri yaya ba don inzo in nuna kamar nafi kowa don idan taso wallahi koda baba ya daura auren mu sai ta warwareshi ba aiki bane a wajenta da dai natane ita ta haifi abinta ta wahala dashi.
Saida na gama abin karyawa tare da Laura na hada dinning na sameshi a daki cikin shiga ta alfarma na sameshi a zaune bakin gado da alaman waya ya gama a lokacin hakan yasa ya falka.
Ina fadin ashe ka falka daga barci yace eeh yanzu umar ya kirani wai jirgin an sauya time karfe sha daya zai tashi nace ai ba matsala kafin nan ka gama komai insha Allah don na hada abinci wanka ya rage yanzu kayi.
Yace ehh shinake son yi ke nake jira ki kara min kafin in biya gaba daya don dole in biya wanan karon naja da baya ina fadib kai malam koka manta da cs ke gareni wai ?
Cs aiya warke tuni don Allah zoki dan bani kada in tafi ina jin haushi hakan a zuciyana don yanzuma ji nake kamar in fasa tafiyan nan inba don ya zamo min important ba dole inje din ba yadda zanyi.
Dan baya naja zuwa wajen drower din gado ina fadin ka makara kana gani dai har nayi wanka jn fito incewa mama me kuma yace ina ruwan mama damu ai tafison taga kina ban kullum indai mamace.
Ina dariya hannuna yakai saman kudin dayake ban ina dora mai saman drower ya kalloni yace ai kudin kine ba nawa ba na dauka tarawa kikeyi a nan ai ?
Na dan kallesa ya mike yana fadin yanzuma ga wasu na cefanen kinsan yanzu ku kadaine a nan don ita wanan tare zamu tafi yau da ita.
Ta matsa takai karana wajen mum da gidansu muje din taje ta dauki abunda zata dauka acan din dama zuwan nata yana da amfanine da take damun mutane ita sai Abuja Abuja dai.
Kallon da nake masa yasa yaja bakinsa yai shiru naso magana kuma naja bakina nayi shiru yakai kofa nake fadin to Allah ya kaiku lafiya yace amin zainab.
Kafin ya juyo gareni kuma yana fadin ki kyaleta nasan abinda nakeyi zainab kada ki dauki hakan komai don Allah.
Komai kamar ya ba mum tace kaje da ita itakadai ba ba matsala ga hakan ai abuja ba bakon zuwana bane na juya na fita don zuciya bata da kashi akace.
Saida ya gama shiryawa ya fito wajen mama suka gaisa yake sanar mata yau da Aisha zasu tafi itama mama Allah yakai lafiya ta fada a gurguje suka shirya koda na fito rakashi mun samu ta shige motan umar ko tana zaune.
Muka gaisa da umar din yana tambayan yaya yara nace suna lafiya yayi min fatan alheri akan exam nayi masa godiya har lokacin tana wayan karya zaune a bayan mota har motan ya daga suka fice daga gidan.
Ajiyan zuciya na sauke lokaci guda na juya zuwa cikin gidan mama da tunda ta fito masa a sauka lafiya tana falon zaune ashe take fadin.
Sun tafi ko nace eh mama a sake tace Allah ya saukesu lafiya basu mai da tafiya bakin komai basu yace da sun isa kuma anjima wani kasa zasu nace wallahi.
Mai nema ai baiga hutu ba dama dole sai an wahala tace Allah dai ya kara rufa asiri na amsa mata da Amin ina batun shiga daki naji tace dani .
Dada ita wanan sun tafi din kwada ya fada inma wani abu takewa dai yanzu gata taje ai sai tayi da tunshe nace mama gobe muma zamu tafi ai ina gani dama don tafiyan jirgine su yasa bamuyi tare ba.
Masha Allah gobe gobe nan hakan yafi mana zance ga yadda yaro ya tsara abinsa yanzu kuma ace lokaci guda haka an juye masa lissafi gara dai kuna kusa dashi din yafi nace kwarai mama.
Ke Laura ku fara hada kayan ku banson kuma shirme don Allah kiyi sauri don sammako zamuyi ga goben don mu isa da wuri mama na fadin tafiyan wueun ai yafi sa,a inji manya.
Na shiga daki ina fadin ina son ki mama wajen goyon baya waya na dauka ina fadawa hauwa yadda mukayi tace ki shirya har kowa har ita mama din ku isa goben nan.
Dadin abin ma ai baya gari koda zai dawo saidai ya sameku kawai a gidab tsarin yayi sosai yar iska samu take wasa watau ita gata matar birni ko kano yayi mata kadan.
Shegiya ina kano din uwarta da ubanta suke zaune idan ya koroku kada ta dawo kanon ita balle nasan in yayane kuje ke nan zama daram ta jawa kanta jamgwagwan damu in tace katobaran baki ta iya.
Batace bin malamai da bokaye ta iya ta daurewa mutane baki ba to mu ba malam ba boka muke kwatarwa kanmu inci mu zuba da ita mugani wallahi.
Kada kiji tsoron komai ko fargaba ki shirya kije ki samesu can din muga karyan kinshin nata a yanzu.
Akwati biyu na hada nawa sai na yarana dana dauki daidai gwargwado don bansan yadda tafiyan zai kaya muna ba amma duk wani abin bukatan mu a can na kammala shirina tsab kafin in tukari wajen mama in sameta ina fadin.
Mama naso a gobe mu wuce dake amma baki samu zuwa kinyi sallama dasu daddy ba yace daga baya zai aiko a daukeki goben in zamu wuce zamu saukeki a gidan mum mu tafi.
Ba zanje can ba dama ina da niyar zuwa katsina ko kuma ku barni nan tunda ga Aina har ranan da zai turo a daukeni nace.
Katsina kuma mama ai saidai mu barki nan mama tunda yace baison zuwanki katsina na fada tace kuma tunda ba a watse abar gidan hakana ba.
A raina nace yayi kyau mama don itace dama matsalata na samu kuma abin yazo min da sauki a gabanta na kira aina da dare ina fada mata ta kula min sosai da mama din girki kuma abinda take so zata dafa mata don Allah.
Naje na diba masu komai na amfani da zai dauki dan lokaci kafin komai ya dawo daidai gareni najawo store din na rufe sukayan shayi da kudi naba mama din tana tawa yaran ba,a da mutanen Abuja sai tazo.
Motana lafiya take tsab don haka ba wani matsala ga hakan na bar kudi hannun mama nace hauwa zata zo ta karba tace min to muka kwana da shirin mu tsab .
Duk da ina kule mama na zargin wanan tafiyan namu saidai bata tofa komai ba akan tafiyan do itama tana son mu bishi can din.
Waya take ta dannawa aka daga Usai na fadin mutanen Abuja kun sauka lafiya tace lafiya kalau anty Usai ashe kinzo gida yau ke nan ina mama ?
Tace ga mama in batane dada kwada ya fada kai Aisha baki da kyau watau ssida kikaga tafiyan nan ya yuyu dai ni nazo mama ke fada min wai kun wuce yau din nan.
Anty Usai ina zan zauna kano ina masa gadin gida ita yar iskan tana can mum barta baki ganta ba yau kamar ta dora hannu akai tayi ihu muka baro banza.
Wallahi dani take wasa ko nawa zan kashe zan kashene anty Usai sai naga bayan shigiyar yarinyar nan na samu Allah ya dorani kan uwarshi yanzu in kira ina mata ladabin shegu itako tana hawa gadar zarena bar shegiya batace shishigi ta iya ba zan nuna mata ita ba kowa bace wallahi.
Zataga karshen shishiga gareni banza kawai sai bude gindi take yana dura mata diya kamar karya yar iska daga gefe halima ta sako murya da weldone diyata inayinki sosai wallahi tace bari mum halima muna abuja wallahi.
Ke baku ga gidan bama wallahi ke kinga gida kamar a cikin villar mutum ya wala son ransa babu takura ko wani doka.
Suka kwashe da dariya suna yafawa nan uwar ta karbi wayan cikin jin dadi tana fadin hummaira an sauka lafiya tace mama lafiya kalau muka sauka wallahi .
To hummaira tunda burukanki sun cika a yanzu don Allah hummaira ki natsu ki zauna dakinki da mijin ki lafiya hakana kindai ga yanzu ba da bane da kike ke kadai kina yadda kikeso.
Ko yayanefa wacan yarinyar tana ransa itama kuma dole itama tana can tana nata kokarin taga ta burgesa ba kije ki kwanta sai barci da cin mutunci ba hummaira.
Me zanyi mama daya dawo zansa a kawo min mai aikina tunda ita har yara biyu naganta dasu wajenta nima dole ya bari in dauki mai aiki ai.
Ba dole idan yace baiso ki barshi a dai zauna lafiya shi muka jawa baki rasa ci ba baki rasa shaba me kuma zai dameki a yanzu kishiya bata gaban ki kuma sai idan yaje masu.
To mama aba anty halima waya zamuyi magana uwar ta mikawa haliman waya ta shige daki don tsakaninta da halima saidai Allah .
Ta raba ta raba suna dafe da junansu ba a gane sirinsu bayan sun gama kus kus kan kayan data karbo matane sukayi sallama aka kashe waya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

9?? 6??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,


Karfe takwas duk mun gama shiri muna waje driver yazo tun bakwai yana jiran fitowan mu ya loda kaya a mota yayi komai .
Maigadi yazo yana fadin hjy ashe tafiya zakuyi kuma yau mu za a bari mu kadai nace mama na nan kafin azo a dauketa itama.
Don Allah a kula min da mama a yan kwanakin nan da zatayi daku malam hamza yace insha Allahu na fito na shiga mota suna muna a sauka lafiya.
Aina har da kukanta nace haba Aina abinda zaki dinga ganin mu ko yaushe kika sani ko wata rana kuma ku koma can.
Haka dai muka rabu dasu nima raina ba dadi a lokacin ina jin wani iri a raina kamar ince na fasa tafiyan .
Amma zuciya ta damari aniyar yakin dake gabana na rainin wayau a yanzu wai a barni kano tunda ni yar kauyece ko na zamo matar gado da manya ke fadin.
Tun ina biyewa yaran dake dan hayaniya har muka bar cikin kano muka dauki hanya gadan gadan lokacin suka soma barci.
Hakan ya bani daman samun lokacin ambato Allah bakina wanda na fara da sallatin Annabi sai hailala na dora da istigifar na gama naja hasbunallah ko wani dubu nakeyi tare da bin hanya da kallo.
Mun tsaya a kaduna munga wata course mate din mu da muka gama school na karbi sako a wajen ta kafin muka dora hanya daya daidai muna cikin kwatas din nasu don driver namu kanin anty hauwane yasan kan Abuja sosai ciki da bai.
Don hakane bamu sha wahala ba shiya fita yaiwa security magana saiga mutum biyu sunzo suna duba mu tare da dan checking din motar kafin daya ya fara yiwa yarab wasa saboda ganin fuskan yaya din dayayi sak ga yaran.
A ka,idan wajen bako bai shiga haka kai tsaye sai gashi Allah ya bamu sa,a kawai sun yarde muna mu shiga tare da yiwa driver kwantancen gidansa.
Yana bin kwatance sai gamu har kofan gidan yaja ya tsaya na dago na kalli gidan da kyau na kada kai tare da fara jera addua a bakina wallahu galibun naja na shafa a fakaice yace dani duk da ya girmeni mun iso gidan anty ina ganin wanan nema gidan gashi nan housefour da suka fada.
Hamdala nayi ya bude motan muka fara fitowa daga ciki yace mu shiga sai ya shigo muna da kayan mu daga baya idan nan ne gidan.
A hankali na dauki yaron guda laura ta dauko dayan shi kuma ya hauda su daddy da kansa don step din gidan nada dan girma da tsayi na danna bell kusan sau uku naji muryan ta tana fadin iam coming please.
A zaton ta yayane ko kuma wasu daga cikin makwabtane sukaji zuwanta sukazo yasa ta katse barcin da takeyi tazo ta bude kofa don da tasan mune wallahi nasan bata bude kofan nan.
Tana budewa muna arba tayi wani irin shock lokaci guda kafin tayi karfin halin fadin wai kune ma ?
Eh na fada nace kauce mu shige daga ciki sai ta jaye a kofan ta juya ta koma dakin nata daya bata kai tsaye tana fadin babban bala,i me sukazo yi nan kuma ?
Ashe akwaita ke nan kuwa ni wanan yarinyar zata ja dani wai ita yar iska sunnanta sorry don nasan ba zai yarda da hakan ba .
Tana jin hayaniyar mu ta kasa fitowa dama ibrahim ya tsaya damu a hanya munci abinci don haka bamu da yunwa na kuma zo da miya mai yawa tunda nasan ina da yara daren jiyan fa banyi barci ba aikace aikacena nayi.
Ban damu ba don anty hauwa tace kome nake so ga ibrahim nan ba zai dawo ba sai yaga komai zai faru akwai kuma yayanta da kanwarta sai ya kaimu gidansu ko su zo.
Zama nayi da yaran kafin na mike ina son duba inda zanyi alwala don azahar da yayi naji wayata yana kara Laurace ke fadin anty wayar ki na juyo ina dawowa wajen jakata da wayar ke ciki.
Aisha da sautin muryan Laura din yaje mata taja tsuki tana zunduma ashar ita kadai a dakin tana dauko wayanta dake yashe saman gado.
Na dauki wayan na duba anty hauwace a layin ina dauka tana fadin zainab yaya kuna ina yanzu nace gamu gidan zaune wallahi ta buga wani ihu tana dariya kafin tace.
Ita shegiyarfa nace tana sama ai ta kadu sosai data ganmu wallahi bata taba zaton hakan ba gareni tace share banza kina ji duba gidan dakyau ki gani nace sallah zanyi gidane me four bedroom da extra daki ta kofan shigowa.
Biyar ke nan tace good inma zai baku bibiyune yayi ta bin daki shiyasani kin dai je din yanzu ki kira gida ki fada masu kina abuja kada sai daga baya suji nace ina da niyar hakan tace good ina ibrahim fa nace bari ibrahim kam da badashi mukazo ba aida mu wahala yau amma lafiya kalau wallahi ya fita yayi sallah a waje.
Kitche na shiga nayi alwala duk ban damu ba a lokacin komai ya saya na abinci normal fa kamar dama ya shiryawa zuwata din gidan.
Kaina kada nafito nazo nan falo na tayar da sallah kadin na idar nacewa laura oya kuje kuyi alwala a wajen can akwai famfo nagani ku shigo kuyi sallah.
Ta kwashi yaran suka fita dama na saba mata hakan nan makwabta suka sanda zuwan mu don yaran da suka gani suka tsaya suna magana akansu.
Bayan na idarne na dauki waya na kira baba muka gaisa na sheda masa muna Abuja yace ikon Allah yaushe kukaje nace yau baba bamu dade da isowa bama.
Yace ina dai lafiya dai ko nace lafiya kalau baba mun dai zone mu dan huta a nan yace to madallah sai ayi ta hakkuri kinji mama komai na duniya dan hakkurine dama.
Kada kiga na kama maki wanan karon daurowa hakan yayi don in nunawa kubura iyakatar don bata kai min can ba wallahi anyi ta hakkuri ina shi malam din nace bayanan yana wajen aiki yace to a gaidashi idan ya dawo nace zaiji baba nagode a fadawa inna suyi hakkuri ban samu zuwa na sallamesu ba kafin muzo.
Yace haba mu dai in kuna lafiya ai wanan ba matsala bane agaida samarin su gayar min da mai

98 / 105