Chapter 39 Reading DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc Arewa Novels

DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   39 / 105

114K to 117K   out of 313.1K words

yar nata tabbas wanan karon ransa ya baci sosai yana iya daukan ko wani mataki akanta kamar yadda yace din.
Don tsuki taja kafin ta mike tsaye ta fada bandaki ta dade aciki tana shiryawa yadda tasan zata gamsar dashi har ya manta da laifinta kafinta fito ta nufi dakin nasa kai tsaye dakin da duhu don haka ta fahinci daya kwanta ko.
A hankali ta taka zuwa bakin gadon ta zauna ta dan dauki lokaci kafin ta kira sunanshi tana fadin naga ka dauki zafi da zancena nida wasa nake maka ai nasan mum ce don e zan nuna wani abu akanta ?
Lokacin ya samu karfin halin magana yace baki da hankaline da zaki kawo zancen wasa da iyayye Aisha ban hada komai da mum ba aduniyan nan don haka kada ki kara min irin wasan nan.
Bata bari yaci gaba ba ta kwanto masa saman jiki tana manna masa kiss tun yana basarwa har ya biye mata suka raya sunna a daren washegari tunda safe suka fara shirin tafiya don ko tsayawa su karya a gida basuyi ba.
Karfe daya na rana suna cikin kano don haka kai tsaye ya kira wayana yana tambayan wani asibiti muke na fada mai ba,a dauki lokaci ba sai gasu sun baiyana a asibitin..
Lokacin nida Dada ne a wajen mum din ina tsaye ina daura mata ruwa suka shigo dakin bisa jagoran malam sani daya kawo muna abinci asibitin.
Mutanen Abuja kune tafe yanzu muryan Dada naji tana fadin hakan yasa na jiyo ina kallonsu don mun dade gaskiya rabon da mu hadu dasu don ita Aisha tun lokacin bukin mu.
Shiko yaya Addel tun zuwan shi gidan mu lokacin da yan uwansa ban sake ganinsa ba sai wanan karon don haka kowan mu ke ganin sauyi ga dan uwa a lokacin.
Cikin fara,a nake masu sannu da zuwa na kalli Aisha din nake fadin madam sannu da hanya naga ta matse fuska kafin tace dani wai zainab ce haka dama ?
Tunda naga sauyin yanayi afuskanta nima ban kara bi ta kanta ba adaidai lokacin ya Nasir kuma ya kira layina yana tambayana jikin mum din.
Ina aikina na dubanta ina bashi amsa nake fada mai ga yaya Addel nan ma ya iso yanzu ai kamar yadda halimatu bata gajiya da bina da kallo haka itama anty Aisha duk motsina yana idon ta don gaba daya taga na sauya mata.
Bata san training din anty hauwa bace don itace ke sakani gaba wurin gyara da kwaliya yanzu dama duk wani sauyin dana samu na rayuwa zama dasune ya sauyani a yanzu.
Muje waje inji zeey yaya Addel ya fada don haka nabi bayansa zuwa wajen kamar yadda ya bukata ina fita wata nurse ta shigo dakin tana tambayana da doctor zainab kt nake nema don Allah ?
Hakan ba karamin taba ran Aishan yaya Addel din yayi ba sai Dada ke fadin ta fita yanzu ita da yayanta ki duba waje don batayi nisa ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3?? 9??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Tsaye muke muna magana akan matsalan mum din dashi yadda ta hangomu tsaye din zakice tsayuwane na wani abu don yadda muke magana kan abinda ya shafemu din a lokacin.
Sam bamu san zuwanta wajen ba sai muryanta da mukaji tana fadin kazo nan ka tsaye kana naka ka barni can ciki ina maku gadi wanan yasa nake kin zuwa gun farko wlh.
Juyowa mukayi nike fadin anty Aisha kin fitone bata tsaya ban amsa ba sai cigaba da fadi tayi ni ka kaini gida in huta sai ka dawo kaci gaba ta fada tana kara daure fuskanta tamau a lokacin.
Kallon mamaki yayi mata kafin yace ai kinsam hanya zaki iya tafiya duk da gatse yai mata abinda ta fada ya ban mamaki don cewa tayi dashi aiba haka mukayi dakai ba tun farko kuma in nasan nan asibitin zaka fara kawoni da tun a round na sauka a junction din mu ai.
Gasu daddy nan sun shigo na fada cikin katse masu muhawaransu a lokacin duk suka kallo inda nake kallo din shiya fara takawa zuwa wajen su daddy din ya barmu a tsaye wajen.
Mum kan gaskiya tana jin jiki wanan karon saidai abinda sauki tunda yanzu BP din an samu ya sauka sosai tunda take samun barcin nan amma jiya kan koda mukazo gaskiya tana jin jiki.
Oh Allah ko amma banga alaman wani abin tashin hankali ba a nan saima na dauka kawai dai normal ciwone haka na girma dayake kama mutum.
Yata ashe kun karaso sannunku da zuwa daddy ya fada ta dan juya tana fadin ina wuni har lokacin fuskanta a hade babu fara,a a tare da ita ko wani alaman girmamawa zuwa ga daddy din kosu daddy enugu.
Mamakine ya kamani lokaci guda ganin yadda ta gyaida iyayyen mijin nata cikin rashin ladabi ko da,a tadai amsa da lafiya lau a tsaye tana kawar da kanta gefe daya.
Abin ya ban mamaki matuka don ban taba tsamanin diyar bahaushe da wanan halin ba duba ga yadda dan bahaushe yake samun tarbiyan girmama na gaba gareshi balle iyayyen miji da yana cikin huduban da iyayye kewa ya mace idan za,a kaita aure.
Saiga wanan na gani da dabi,an dako cikin kabila nata tarbiyan daban yake don a gaskiya duk abinda akace wanan Aishan tayi zata aika don ta nuna hakan ga halinta.
Yaushe kukazone daddy Enugu yake tambaya ya Addel yake fadin dazun nan muka iso don sammako mukayi saboda hankalina ya kasa kwanciya ga yadda naji jikin mum din ya kasance.
Hjy kubura kan tanajin jiki amma abinda yau da sauki gaskiya Allah ya gyara kanwarku na nan tana kuma kula sosai da lamarin tun jiya tana tsaye a kanta.
Ni ina son in tafi nagaji ina son in huta ta kara furtawa lokaci guda tana nuna damuwa da tsayin da sukayi din na dan lokaci a wajen duban jikin sarakuwan nata din dake kwance alokacin.
Wanda ya kamata ace tafi kowa a lokacin nuna concerns dinta kan lamarin ciwon hjy mun din a lokacin nata amma saiga wanan halin da yanzu take nunawa a gaban kowa nako in kula da takeyi kan sarakuwan nata.
Koba a fada ba duk da yana cikin damuwa sosai a lokacin amma akwai bacin rai a tare dashi gaba nayi don in kai su daddy dakin don ba zasu bari a shigaba a lokacin saida wani mai jagora.
Lokacin ya samu daman mata tambaya a tsawace yana fadin Aisha wanan wani haline kikeyi anan ko kina son su kara tabbatar da zargin da suke maki kan rashin kaunar kowa da bakiyi a cikin ahalinane wai ?
Ya zakace min hakan bayan kasan tun safe ban samu mikewa ba hakan kuma yana iya jawo min matsala idan ban dan zauna ba bai iya cewa da ita konai ba a lokacin sai juyawa da yayi zuwa dakin yabi bayan iyayyen nasa.
Ya samu ina gyarawa mun din kwanci don ta falka a lokacin suna gaisawa dasu Daddy din da suka shigo sai kuma carnualer danake duba ko bayana ya dan tabu Dada ke fadin ciwo ai ya samu gata anan.
Ko motsi tayi idon yarta yana kanta tana duban uwarta ai mama akwai kulawa sosai wallahi wanan kuma ba aikin raggo bane daddy ya fada yana runtse idanuwanshi yana maijin wani irin takaici a lokacin kasan zuciyarshi..
Basu jima ba sukai muna sallama suka fita ganin yana dakin yasa nace zanjebin dawo nafita na dauka ta tafine ga mamakina saina hangonta azaune tana waya.
Saida na karasa wajen nake fadin ashe kina na nan zan dan je ward din mu na dawo na fada cikin nuna kulawa agareta saidai ko kulani batayi ba har na bace a wajen ina mamakinta.
Tare muka dawo dasu hauwa da mairo tun daga nisa ta kura muna idanu har muka shigo dakin suna gaidasu Dada din dashi yaya suna masa sannu da zuwa.
Yaya abokan karatunane wa yan nan tare mukazo practical dasu nan na fada ina zagayawa wajen filon mum din da take kwance mairo ta dan duba hannun mum din take man bayani dasu basu ganewa nace ina son zuwa safe ayi discharge din mune.
Duk hankalin mu na,a kan mun din muna magana kan jikin nata naji muryan yaya din yana f?din ke zainab zan kai Aisha gida akwai abinda za,azo maku dashine ?
Na juyo ina fadin a,a yaya saidai ina ganin ruwa za,a kawo muna don dazun ban tsaya dauko ruwa ba da zanzo saboda kaya yai min yawa kuma motar haya nashigo.
Likita dake haka babba baki da motar kanki wanan wata irin likitane haka wai ya fada yana mikewa na dan turo baki naji muryan hauwa na fadin ai kune da kunyan haka yaya kanwar maza bata da motar kanta ?
Murmushi kawai yaya din yayi lokacin har Aisha matarshi ta mike tsaye takai kofa ba tare da cewa kowa komai ba duk suka bita da kallo a dakin.
Sun fita mairo ke fadin wai dama matarshi ke nan nace ehh kin santane tace a,a ganinta dai nayi wata sinkinkin da ita da alaman rashin fara,a don tun shigowan mu take faman harare harare nace ke da wani ido kika ganta don Allah.
Barta ta fadi don abinda idonta ya ganine tun shigowanta dakin nan bata bude baki tayiwa hjy kubura sannu ba sai faman daure fuska data zauna tanayi.
Kila adole mijin ya tursasa mata zuwa nan duba uwar nasa yasa take sauke haushi haka akan kowa nace ni kallon da take min nema ya daure min kai ?
Dole ta kalleki mana ko babu aure tsakaninki da yayan nakine zainab kishin mijinta ya kyalla idonsa akanki takeyi mairo din ta fada a cikin turanci kada Dada taji a hankali wanda iya mu zamu iya jin zancen ta.
Wani kallon tsoro nayi mata tare da fadin don Allah bar wanan maganan don zunubine hakan na fada cikin daure fuskana lokaci guda fitowa mukayi daga dakin.
Anty hauwa ce tace wai naji kuna wani zance kina daure fuska duk wata mace a yanzu dole tayi kishin mijinta a kanki zainab kinga yadda kika koma kuwa ?
Don tasan akwai aure a tsakanin ku yasa take son nisanta mijinta daga gareki ayanzu saidai ta makaro ga hakan yanzu don dole dai zai ganki kuma kina tare da mahaifiyarshi ai ko wani lokaci bata isa kuma ta hana hakan ba akansa.
Don shine aida gangan na fadi zancen mota a gabanta taje ta mutu yau don Allah saboda bakin ciki zataga abinda yafi wanan nan gaba indai nice muje zuwa gamu gata a filin yaki.
Kallonta nayi ina mmakin kalaminta na lokacin saidai shiru nayi ina tunanen zancensu don gani nake basu da hankali da har zasuyi wanan tunanen akaina da ya Addel mutumin da nakewa kallon uwarmu daya kuma gatana a bayan iyayyen mu saishi .
Yanzu zasu furta wanan zancen don hakane ma banda amsan basu a yanzu din kan zancen din nasan shirme me kama da hauka da kurciyane ke fita daga bakinsu a yanzu.
Nasan ko wace mace burinta shine ta mallaki ya Addel a matsayin miji a gareta amma bandani da nake masa kallom babban wa mai kamar uba awajena,
A mota kuma shirune na dan lokaci a motar don kowa kamar ransa a bace yake da dan uwansa a lokacin kafin ta dan nisa tare da waigoshi tana fadin me wanan yarinyar take nufi ke nan da tace wai kune da kunya ai da zainab bata da mota ?
Look honey kada ka soma gangancin sayawa zainab mota don hakan wani zance zai dauko maka a tsakanin mu.
Kai kadaine a cikin yan uwa da zatayi maka roko a fakaice wai ita ga yar iska yar bariki no warder a yanzu zainab idonta ya bude haka lokaci guda?
Ashe da wa yan nan yan barilin take kawance a yanzu dama ta iya hakan ta bari har hafiz ya wullakanta mata rayuwanta a banza.
Idan na sayawa zainab mota sai me don naga kamar umurni kike kokarin bani ayanzu kan yar uwata.
Koma basuyi wanan maganan ba dama ina da niyar hakan ko basu fada ba kuma ai gaskiya yarinyar nan ta fada don mune da alhakin hakan a zainab tunda tana wahalan karatu dole saida mota tunda muna da halin saya mata kuma ,,,,,
Wai zainab din nan uwarku dayane da ita da komai ko wanin ku zaice zainab zainab haka ranan naji Nasir na irin wanan zancen shirmen .
Wai zai saya masu jewelry's iri daya da budurwansa wanan wani irin shashancine da rashin sanin abinyi don Allah ?
Dolene wai sai kun mayar da ita yar mum kome ko ita mum ai banga tana wani daukaka rayuwan taba haka kamar yadda kukeyi da kai da dan uwanka saidai idan da wani manufa kuke kokarin hakan akanta dama .
Bayan yarinyar nan ma bazawarace haka kuma dan uwanku ne fa ya sake donshi yafi sanin kissa ya gane me suke kullawa ita da iyayyenta ya sakota ubanta kuma ganin ba riba ya dauke abinsa a hannun mum ku duk wanan bai saku natsuwa ba dolene sai tayi kama da kune don Allah ?
Murmushi yayi yana juya sitiyarin mota kafin yace na kula zaki dauko wani sabon zance a yanzu Aisha waiko kinsan irin zumuncin dake tsakanin mu da yarinyar nan da iyayyenta kuwa ?
Koma ba zumunci tunda take a karshin mum dolene mu kulata don farincikin mun din mu don kuwa tana bata lokacinta itama akan mum din.
Na sani mana dangice ita kamar kowa kodon kawai ta zauna da mum kuka dauki son duniya haka kuka dora mata well koda yake dama kwadayin iyayyentake nan ai dama ba yau ba nagane hakan ni.
Aisha enough don Allah don banga abinda ya shafoki a zancen yan gidan mu ba haka kwanaki kan Nafisa da uwani muka samu matsala dake ko kin mantane koda yake yanzu na fahinci komai ya danna horn maigadin gidansu ya bude madu get ya shiga tana fita bai tsaya ba yaja mota.
Ban gane ba kai ba zaka shiga ku gaisa da hjy bane kome yace ina da abin yi a yanzu yayi ribas da mota tabishi da kallon mamaki har ya fice gidan nasu.
Juyawa tayi ta nufi cikin gidan nasu da yan aikinsu ta fara fada wai sun bar gida da kazanta haka ba gyara wanan ai iskancine hakan.
Jikinsu yayi sanyi don sunsn zuwnta ba alheri bane garesu don da zaran tazo gari duk sukan shiga taitayinsune saboda azabanta da masifa ga hattara komai sukayi baiyi ba a wajenta.
A falo ta samu mahaifiyarta zaune tana waya da yarta shigowanta uwar ke fadin ke kuma kedawa da zuwanki kike masifa haka ?
Mama wallahi yan aikin nan naki kazamaine sai yaushe zasu wayene don Allah ji yadda suka tara kaya kofan shigowa gidan nan haba ki barsu suda suka zuba su zasu kwshe ai ke nifa wanan bakin tsabtan naki ya soma damuna wallahi.
Bakin tsabtan nan naki yana iya hanaki haihuwa fa Aisha don manya sunce idan mace ta faye tsabta yana da wuya ta haihu a rayuwanta koda ta haihu din kalilan nema zata haifa din don yawan tsaba bai bari ta tara iyali masu yawa a rayuwanta.
Mama wani haihuwa kuma yanzu don Allah har yaushe nayi auren da ake kira min wanan haihuwa haka nikan gaskiya ba yanzu ba agurina shima din ko yaji zugin uwarsane wai rana sai gashi yana min zancen haihuwa wai wani muje muga likita.
Aisha kanki daya kuwa haihuwanne kikewa wani fisge fisge haka kamar an ambaci makiyin ki to tsaya kiji riban aure shine haihuwa .
Duk macen arziki tasan da zaran ta wuce yan watani ba haihuwa hankali zai fara tashi ga ita da yan uwa amma ke zaki zauna kina wanan zancen kamar mara hankali.
To bari kiji in fadama ki Aisha idan ma wani abun kikeyi ki daina kinga tunda ya fara zancen nan to wallahi ki natsu kiyi hankali don hakan na iya kawo maku matsala a cikin auren ku.
Yanzune zakiji ya fara neman aure a cikin dangi nawa akayi muna ganin haka a garin nan kuma muna gani don Allah mama ki bar zancen nan Aliyun ne zaiyi aure haba mama bakiji da kyau ba kan ta koma ta kwanta a cikin fushi.
Kaiya ta yaro kyau take baya karko ke yanzu kina ganin bai isa ya karo maki kishiya ba ko don kina autar mata shine ba zai iya ba ?
Don Allah mama ki bar zancen nan

39 / 105