DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   51 / 105

150K to 153K   out of 313.1K words

dacen kunnun gyada muka dama da safe na zuba saura a flas don yai muna yawa nida mum da Dada da mukan sakawa abinci ko wani lokaci.
Sai ruwa da kofuna a cikin tire din na dire masa ban dago ba saida na tsiyaya masa kunun a cup lokacin yana text message a wayanshi.
Ina tsiyaya ruwa ya dago yana fadin wow wanan yasa nake son gida wallahi koba komai zakaci abincin gargajiya ka koshi wallahi ya mika hannu yana fadin thanks a daidai lokacin mum tayi sallama tashigo falon tana fadin.
Nika nace kaine danaga mota a waje don nasan ba motar hafiz bane don shi da jan mota naga yazo ya kallota yana fadin hafiz na garin nan kenan shima ?
Tace yayana nan tun shekaran jiya naga yazo nima a falon Alh muka hadu dashi jiya baka sanda zuwansa ba ke nan yace baj ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  fada min ba gaskiya.
Na mike na karbi jaka da ledan data shigo dashi zuwa cikin dakinta na barshi suna gaisawa da mum din ina dawowa falon naji yana fadin ranan zai koma Abuja ya shigo yin wani dan aikine dama a kano.
Mum tace nikan nayi mamakin ganin a yanzu din banji kace zaku shigo ba zama nayi mum ta kalloni tana fadin to ya jikin yau nace naji sauki mum.
Ga mamakina sai naji yai pretending din fadin baki da lafiyane zainab kasa nayi da kaina ina dan murmushi don dariya ya bani a lokacin nidai kai na gyada nakasa dago kai in kalesa don dariya.
Mutumin da muka gama waya dashi da asuba yake fadin dole zai shigo ya duba jikina nace masa ai naji sauki yace bai yarda ba sai yazo ya gani nace Abuja aiba kusa bane yace wasa na dauka ke nan kuma sai gashi din na ganshi gabana girshi yake wanan maganan yanzu gaban mum kamar baisan komai ba.
Mum ta karbe da fadin gajiyan jerabawane dai yake damunta amma ai ta dan ji sauki yau tunda gata zaune kinje asibiti ya tambaya yana kallona kafin nace wani abu mum tace kaiko dai ita kanta ai asibitin ne nan gida dai ta kula da kanta har Allah ya bata lafiya.
Mun dade a zaune muna hira saidai hiran wanan karon kan zancen sune da mum don ya matsa sai mum ta dauki mai aiki take fadin ita bawai me aikin bace bata son tsegumi ta tsana yace koda yarinyace a samo.
Take fafin wai kai mu biyune fa a nan wani aiki yar aiki zatazo tayi muna a nan kuma haba mum ai zaku so hutu yanzu da zainab bata da lafiya nasan dole ke kika mike kike komai ?
Tace a,a kasan mama da karfin hali haka ko take daurewa tayi komai koda na hanata kuwa baisan sanda yace what kina da hankali zainab idan kikajawa kanki wani matsala fa kuma ga haka ?
Yau naji iko Allah mai kaya ya daure sai me cira ke kuka nidai a,a kada ka karawa yata zuciya ta zamo ragguwa a gidan miji nan gaba kuma kai dai sha kunnun ka kaji da shirmen banja.
Mum ai gaskiya na fada fisabililahi bata da lafiya mene na wani aiki kuma koda ya fada ya dago don ya kalli mum sai yaga mum din ta tsure shi da idanu murmushi ya sake yaci gaba da kuba kununsa ina gefe ina kallon draman nasu.
In gulmane kakaisa in kayane ita ya mace in ba ciwo yakai ciwo ba an fadama tana son kwancine ko me da zaka kama min fada kamar wani ubana ko maigida can.
Dariya ya fara yana sosai kai ya mike tsaye tare da fadin akwai kaya a mota danazo dashi yarki tunda tana da karfi muje ta dauko min wasu a waje na mum ta kalloni ina zaune kamar bansan abinda sukeyi ba take fadin kinji wai kuje ku kwaso kaya waje dayazo dasu zaki iya ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

5?? 1??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Tare muka jero daga wajen dashi muna tafiya fitowan falon yake fadin ke baki san ciwon kanki bane zainab baki da lafiya zaki zauna kina wasu aiyuka idan jikin naki ya kara rabkeki fa,?
Yaya taya kake son ina zaune ina kallon mum tana aikin dani ya kamata ance nayi indai ba ciwo ya kaini kwance bane har ban iya tashi ?
Yadda muka jero muna tafiya kobaka da fahinta wanan zaka fahinci akwai wani halaka maigitma da daraja a tsakanin mu yadda yaya din yake min kallon kulawa da kauna.
Yayin da nake daga gefenshi ina takon nan nawa kamar bana son taka kwai ya fashe ko ina soron kasane daga gefen shi wanan tafiyan kuma haka Allah ya yini dashi natural ne gareni tun ina karamana amma sai mutum ya dauka yangane hakan gareni.
Yace tobe serious bana son kiyi komai zainab a yanzu bayan karatun dake gaban ki cikin wanan satin mai aikinku zatazo daga katsina don ranan da mukai waya dake naji muryan ki ba lafiya kika ce min kina kitchen kuma hankalina ya tashi ainun.
To yaya bakaji me mum tace ba aiki bai garara ya mace ai indai na gidane sai har ciwo yakai mata intaha ya tareni da fadin dake da mum din duk banson hakan agareku yanzu.
Meye amfanin samuna iyalina na cikin wahala ni ban yarda da wanan ba inma mai aikin daya bata isan ku sai a karo maku wata yar karama don dauko min miko min understand na gyada masa kai cikin gamsuwa.
A daidai lokacin hafiz da yake tsaye bakin window don yasha taba ya hangomu tsayawa yayi cikin mamaki yana kare muna kallo a lokacin don zuciyarshi ta kasa fahintan abinda idonsa ke gano masa a lokacin.
Sam baisan da zuwan ya Addel din ba kano sai ganinsa yayi girshi a tare dani cikin wani irin tsayi mai ma,anoni da yawa agaresa don wanan duk mai hankali ya ganmu yasan da wata akasa da bata fashe ba tukun.
Gabanshi ne yake wani irin faduwa lokaci guda fau fau fau a fili yacewa kansa be cool mana hafiz kada ka zamo sha sha sha ka natsu kada kayi abinda bashi ba mana.
Ya koma ya zauna yana tambayan kansa ta yaya Addel ya shigo kano by this hours be sanar dashi ba meya kawoshi kanon a wanan lokacin da yasan yana tsaka ga aikinsa yanzu ?
Mikewa ya karayi ya koma wirin windon muna tsaye muna fuskantar juna inda yaya yake min sherin ina ciwone akan rashinsa kusa to gashi a gabana ciwo ya kare na kwata saman motan ina dan dariya.
What ya fada da dan karfi yana sakin labulen ya kamo hanyar fitowa wajen da sauri saidai kafin yazo yaya din ya dauko cret din Apple guda biyu ya miko min yana fadin ko baki inma wanan na rage maki ?
Nace haba yaya aida abincin da nake ci kulum ya zamo na banza ya dora min a hannu na mika na karba ya juya ya dauko cartoon din lucuzed a daidai lokacin ya karaso wajen yana fadin.
Addel ya dago don jin yadda ya kirasa a ranan yace ohh na manta mum ta fada min kana garin nan ai yaushe kazone wai ?
Kwanaki ya bashi amsa a takaice ma,ana ba yauba ba jiya ba ke nan ya cicibo cartoons din har uku da niyar shiga dashi ciki hafiz ya soma magana yana fadin na hangoka da wanan yarinyarva tsaye ne nazo.
Ok wani abune ga hakan sai kuma ya rasa me zaice mai nikan na juya na shiga don ganinsa ban dawo ba a gaban mum din na dire kayan na zauna ina huci nace mum wai wanan mahaukacin me yake nufi danine wai ?
Ta juyo tana fadin wake nan nace ya hafiz mana mum wai tambayan ya Addel yake me nakeyi gunsa tsaye ?
Mum tace ga hauka kuwa zai hanaki tsayi da Addel ne ko ya manta halakanku dashine a kaddara ya manta din shiya isa ko gidansa yake yace ba zaki tsaya da dan uwanki ba ?
Nina sani mum wanan fa ya zare nake gani ta daga tana fadin yanzu ina Addel din yake nace yana can suna magana dashi nashigo tana kokarin mikewa ya Addel din ya shigo da kayan take fadin me yake karanto makane kuma shi ?
No ba komai mum shirmensa dai yakeyi a can waje din ya juya ya fita don bai tsaya ba naga mum din tabi bayansa da sauri har lokacin kuma hafiz din yana tsaye yana cicika a wajen daga nisa mum ta hangosa yana bala,i da dan nata ta karasa tana fadin kai wai meye hakane hafiz ?
Meke faruwane wai ya juyo yai wa mum din wani irin kallo yana fadin koma meye nace masa bana son hakan ai koma meye kuma laifinkine keda kike babba kike gani baki tsawata mashi ba.
Hafiz kanka daya kuwa kana cikin hankalinka kuwa ta fada cikin tsigar tambaya da mamaki a gareta kai don't try this your rubbish talk to mum ba zan dauki hakan ba na fada maka.
Idan an fadafa me zakayi muryan mummy da anty Nafisane ke fadin hafiz hafiz wai kanka daya kuwa me kake kokarin yine a yanzu mum ki shiga don Allah ciki ki barni da mara kunya a nan .
Kamar umurni haka mum din ta juya zuwa ciki cike da mamaki a lokacin Addel din ya kalloshi yace waiko ka mantane in tuna maka tunda naga ka zare a yanzu.
Kaface idan mun damu da zainab ce mu jika mushata a part din mu ka tuna yanzu to meye damuwanka don mun jikata muna sha yanzu din.
Impossible abinda ba zai yuyu ba ke nan dan akuya mai manta halarci a garesa tsayuwan mutuwan wacin gadi hjy malka tayi don shike nan ankai inda ba ason akai a yanzu danta ya bambaro mata wani fitinan kuma ke nan gidan nan tana fama da kanta.
Yaya ya gama shigo da kayan ina daki sukai magana a tsanake da mum taja masa kunne kan ya fita harkan hafiz don Allah tunda kowa yasan kamar zaucece yake yanzu.
Text yayo min akan na fito shi zai tafi kasa fitowa nayi don mum dake zaune a falo lokacin sai amsan da na mayar masa da Allah ya kashi lafiya mum tana zaune a falo.
Mikewa yayi yacewa mum din yana zuwa banyi aune ba sai gashi cikin dakin tsaye a kaina muryanshi naji cikin bacin rai yana fadin indon mum ce ta dade da sanin halakata dake ido kawai ta zuba muna taga iya gudun mu.
In zaki fito ki taka min ki fito ko in tafi abina ya fada daga inda yake tsaye wajen kofan shigowa dakin nawa da kyat na dago kai ina fadin gaskiya yaya ba zan iya ba haka kawai ba fadi naji yace OK ya juya ya fice daga dakin.
Saida akayi kamar minti goma naji muryan mum tana kirana hakan yasani fitowa ina fadin mum gani kin shige kizo ki kwashe kayan nan a nan don nasan nakine keya kawowasu.
Da sauri na dago ina fadin mum wani kuma nakine mana wayazowa dubiya bake ba nashiga uku ke kinga kwashe kayan nan a nan idan kina iyawa ni banson gulma da kilibibi irin naku ai yanzu dai zancen boyo naku ya kare tunda mahaukacin nan ya fasa kwan kowa yaji.
Sai ku jira jin sakamakon ku don nasan tana kasa tana dabo a gidan nan ke nan dama ido na saka maku naga iyakar boyon soyayyan naku.
Banda shirmenku daga ke har yayan naki ni banfi kowa farin ciki a duniyan nan da hadin kanku ba a yanzu tsoron me ko fargaba ya saura inji na wani a cikin gidan nan kuma yanzu.
Dukar da kai nayi ina murmushi cikin kunya na fara diban kayan ta dago ta kalleni da fararen glass din dake idonta tana karatu take fadin kinga kibar guda guda don a rabawa mutanen gida suma su sa albarka a cikin kayan nan.
Don haka halin mum yake abu ko kadanne sai ta tsankwarawa kowa a gidan yasa albarka ga wanda ya kawo din amma part din mummy ko duniya za a kawo mata koka gani baka taba ganin giccin abin saidai honkonsa idan sun yar sun gama amfani dashi ke nan.
Dakatawa nayi ina bin kayan da kallo don ba karamin kudi yaya ya kaso min ba tace zamani kayan zancen naki kike kallo a gabana don Allah ni dai dauki kije da rashin kunyanku na yan zamani.
Da sauri na kwasa zuwa dan store din mum da muke adana kayan amfanin ci aciki nikan wani tarkacen ma basan shi ba sai yauvdin nan don duk abin amfanin gida nacine ya kwaso muna irin nasu na yan birni sabanin wanda mukan lissafa masa a nan ya sayo muna don amfanin mu.
Sai dana kai komai daki na koma ina tunanen zancen mum don gaskiya ban taba tunanen cewa ta dagomu ba duk abin nan dake faruwa tsakanina da ya Addel din sai wanan ranan.
Lalai babba babbane da akace abinda babba ya hango yaro ko yahau sama baya hangoshi ba karya bane wanan donko ga mum ta gano boyon da muke mata din a tsanake.
Sai bayan sallah la,asar zuwa lokacin nasha gwada number ya Addel ina jinsa a kashe lokacin bani dadara ajima kadan zan kara gwadawa still wayan nasa yana kashe.
Mum ta kwala min kira da mama zo mana ki kawai mutanen kayan nan tun ba,a barshi a nan ba wani wabda rabonsa ya koka ya shigo ya gani a wajen nan kinsan sai ki bashi ko.
Ina zunburo baki a cikin kunya na fito dakin zuwa nayi na tsaya mata ina tambayan ya za,ayi mum sai lokacin ta dago tana fadin niko kin samu layinsa don naji wayansa a kashe tun dazun.
Na kira bai shiga ba na fada a takaice tace Allah ya tsare ki dauki apple biyar nan ki kaiwasu hjy komai dai ki kwatanta ki mikawa kowa nasa yadda tace din hakan nayi da kayan na fara daukan na mummy don in kai mata.
Daidai zan shiga falonta nake jin muryan mummy din na fadin banda ya mayar da kansa dan banza har wace zainab can yarinyar dana tsana a duniyan nan kamar yunwar cikina zai dawo yace min wai ita yake son mayarwa yanzu.
Kwanciyan hankaline dai hafiz baida shi ko jaraba na cinsu ai aure ya harammanta tsakaninta da Addel din ko wani nafsi kuwa munafukan nan hjy kubura zata iya kawowa a zancen nan ba aure a tsakaninsu tunda hafiz ya aura ya saketa kuma yana raye daram.
Aina riga dana shamcesu tun farko ta yadda zan illanta ta in nisantata da gidan nan gaba daya komai jeraba saidai suyi ta watsewa a waje har su bar mata abin kunya.
Waini za aiwa ,,,,, sallama nayi na fada falon tana zaune da wata kawarta abokiyar cin mushen mummy din kenan na kud da kud nasan an kiratane kan abinda ya faru din.
Amsawansu yayi daidai da shigowana dakin sukayi kamar ruwa yacisu a lokacin suna bina da idanuwa kayan na aje ina gaidasu nace mum tace na kawo aje nan ki tafi cikin izza da isa ta fada.
Na aje na juya na fita suka bini da idanuwa kafin hjy safiya ta nisa tana fadin dama haka yar nan ta koma wana koba asiri dole dana hafiz ya haukace akanta ai ke kinga yadda yarinya ta sauya kamar ba ita ba ?
Ai dole tana hurda yanzu da maza kala kala ana fakewa ga sunan karatu meye ba zaki gani ba a yanzu wajenta ai fiyema da hakan.
Ke ta wajena banda sheri don Allah ki bari yaro ya kece rainin shi dkn Allah kada ki hanashi abinda zuciyarshi ke so don wanan ba duk namiji zai ganta haka ya kawar da kansa gareta ba.
Amma da nasan haka zaki zo kimun da ban nemoki ba dan shawara wanan ai in yana kusa yau ba abinda zai hana yai maki alheri don jin hakan da kike fada.
Sun dauki lokaci suna zancena kafin matar ta mike tana fadin wanan meye ta aiko maki dasu tace waya sani nasan tsaraban dan natane dai ta aiko dashi don in gani niko bata san wanan bai dameni ba.
Ashe bari mu taba da sauri tace wa waini Alh dai ya dawo in nuna masa in mayar mata da tsiyanta don ni mayar mata dashi zanyi ban iya abin gori ta fada son kada taba matar komai a cikin kayan.
Nikan kinga tafiyana ban son mijinku ya dawo gidan nan ya sameni don irin kallon tuhumar da yake min indan ya ganmu tare abin yana sakani tsarguwa sosai.
Haka ta fito ta raka matar ta

51 / 105