Chapter 64 Reading DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc Arewa Novels

DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   64 / 105

189K to 192K   out of 313.1K words

min bata daukeni yar uwa yadda na dauketa ba mum yanzu ace yaya ya dawo kasan nan kodai ba aure tsakaninsu ai zata kirani ta fada min.
Nace ba kinji ba yanzu saiki shigo mu bude tsaraban tawa tare dake ai sai naji mum na fadin baki kyauta ba mama ai hauwa ta wuce hakan gareki gaskiya mijin ki ya dawo sai ki sanar da ita.
Ni zan wuce ta fada wai tayi fushi da sauri naji mum na fadin keko hauwa ai ya kamata yanzu ki san halin mama dai hakana inda sabo aikin saba.
Amma daga zuwa zakice kuma zaku wuce yanzu kinyi fushi da kanwar taki ke nan to ayi hakkuri ke kuma ki fake gaba kada ki kara hakan ai hauwa ta zamo yar uwa yanzu gareki amma kada kice zaku tafi haka a cikin fushi ?
Ko zama bakuyi ba jeki mana ki kawo masu ruwan sha mum ta barshi kawai kinyi fushi ke nan har yanzu baki sauko ba mum ta fada tace ba hakana bane mum amma ba komai.
Ta juya wajen mum tana fadin sun dawo lafiya mum lafiya kalau suna can gidansu dazun nan ma yashigo da safe ya fita sun dan dade suna fira da mum kafin mu shiga ciki muna tafawa.
Lokacin nace wai yau kin rufa min asiri wallahi da mum tace son rawan kai har shelan mijin da bai damu da zamana nakeyi ai.
Na sani ai ni ina zan yarda in caza maki aiki kuma a wajen mum yanzu ya ake ciki yaushe zaki tare don mu san abinyi kada a girshe mu koda yake dole tun yanzuma mu fara shiri a bangaren mu tunda ya dawo nasan zancen tarewane yanzu.
Saidai kila sai ya nemi wajen da zaki zauna kuma ko tunda nasan gidansa ba zai isheku ba nan nake fada mata abinda naji ana fada cewa ya kara fadada gidansa yayi part biyu a gidan .
Kinga ke nan a gidan nima zan zauna tare dasu ke nan kai amma naso ace ya raba maku gidan zama don gujewa fitina ba komai Allah ya shige muna gaba na amsa da amin.
Waya ta dauke naji tana fadin yauwa Asabe don Allah kije kasuwa ki sayo min sassaken kuka da kayan yaji kayan yajin mai dan yawa don Allah ki dai sayo idan kinzo zan baki kudin ki.
Ya kamata mu fara shiri ina son in gyarakine duk da nasan su mum da mama ba zasu barki hakana ba amma nima ya kamata nayi nawa dana sani.
Sai bayan azahar ta tafi na fito in rakatane muka kuma tsaya jikin motarta muna magana da ita kafin a bude get aka shigo da mota ciki shine ya shigo kai tsaye idonsa yana kammu a lokacin.
Dole na tsaya har ya karaso wajen suka gaisa da ita tayi mai an dawo lafiya ya wajen madam kuma ya amsa da duk lafiya Alhamdullahi.
Ban ma san ka dawo ba saida nazo yanzu mum ke fada min ai ya juyo yana fadin ita bata sanar dake ba ke nan koda yake suna fushi danine daga ita har mum din kan laifin da bansan me nayi ba ?
Ka kyalesu yaya idan tazo gidanka ai fushi ya kare mum kuma ai zata huce itama barsu kawai dai sugama fushinsu nima zan rama ai ya kalloni ya fada yanzu kallonsu kawai nakeyi a yanzu.
Wai ace kazo gida amma ko irin taron nan da mata kewa mazansu ni ba a bari na samu ba wai ana fuahi dani .
Naji tace kamar da mamaki kai amma gaskiya zainab baki kyautaba duk da dai nasan kunyar gaban mum da takene ai amma haba kamar wata bagidajiya dai zeey haba don Allah.
Yaya kayi hakkuri komai ya kusa zuwa karshe insha Allahu muma mun matsu a tare din nan ai ya danyi dariya ya shige bata jima ba ta tafi na nufo cikin gida kai tsaye.
Ina shigo mum na fadin yauwa jeki gun ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hjy ta bani kanwar hausa don Allah sai ki biya gun antynku Jamila ki karbo min magani a wajenta haka na juya na fita yana zaune yayi duke da kai yana dakilan wayansa a lokacin.
Na tafi ina fadin mum ke nan watau dani da yaya din duk sai ta horamu da huluncinta ke nan a yanzu in ba haka ba tasan ai ban zuwa gun Dada yanzu don me zata aikeni can din kuma idan ba wani abu take nufi ba.
A kofan shiga part din suke zaune na samesu bayan mun gaisa nake fadin sakon tace halimatu ta dauko min kafin anty Nafisa tace dani.
Zeey kin boye fa da yawa yanzun ba,a ganin ki kuma ba school ake zuwa ba nace saidai asibiti shima ba kullum ba gaskiya.
Kinsan angonta yana gari dole ta boye halimatu dake miko min kanwa ta fada don angonta yana gari shi zaisa ta boye kawai dai kanmun kaine irin nata.
Kamun kai kan ai taje basarakan matar Addel na jiranta indai wanan matar tasane waya sanima ko tana ciki saurata takeji yace muna bata cikin gidan dazun anty Habiba ta fada.
Anty habiba idan naje yankani zatayi ko gasani indai ba hakan ai da sauki aure zanje yi ba kallon sarauta ba kowa dai ya iya allonsa kafin ya wanke.
Ke jeki inda zaki don Allah kuna jawa kanku raini ga diyan ku wallahi anty Nafisa ta fada har na wuce suna zancen ita anty habiba na fadin jimun yarinya fa ni zaki fadawa maganan banza ?
Idan ban iya allona ba na wanke kisa a dakeni ke har kiyi girman da zaki dinga fadawa mutane bakar magana irin haka kewa kike daukan kanki ne wai ?
Mun hadu da mum take fadin dawa ake hayaniya hakane wai nace anty habibace na gwautata na wuce zuwa part din mu nan ta karasa taji meya faru.
Kai gida dai inya wuce mace daya zuwa biyu babu sauran zaman lafiya tsegumi ya samu ke nan a gidan yanzu ina habiba ina kuma zainab don Allah ?
Tun yarinyar nan bata magana har yanzu yakai kowa yai mata saita tsaya ta bashi amsa ni kayi abinyi ta koma dakinta ta zauna ta huta da tsegumin gidan nan da bai karewa don Allah.
Dan dago kai yayi yana murmushi kafin yace mum ina da sauran lokaci kafin ta tare ko tunda ba, a gama shiri ba nake gani ?
Shirin me ya saura maka a yanzu banda lefe da inda zaka ajeta ka gyara ina shiya saura a yanzu mum ta fada kamar a hasale ta kafeshi da idanunta tana fadin ka iya gyarawa matarka gida don ka kwantar mata da hankali.
Amma ita wanan bakai tanadin inda zaka ajeta ba nagane so kake kaja min dai bacin rai akan zancen nan kasan baka iyawa ka shammaci mutane tun farko ?
Abinda nakewa gudun faruwa ke nan tun farko kuke ganin kamar banson alakankune da juna na sani matarka ba zata bari ku zauna lafiya ba kayi abin nan ne kawai don ka kara bata zumunci dai ba gyara ba.
Daka barta ta fita waje ta nemi mijinta da duk wanan tsegumin yanzu ai bai taso ba gidan nan har agabana yau suke sakin magana son kawai inji haushi in tanka ya zama fitina da zaisa ayi tashin hankalin da malka zata fada min abinda ke zuciyanta.
Ba laifinsu bane ai dama ance dan kuka mai jawa uwatai jifa ai ko ita maman nasan yanzu auren ya koma mata ciki ai tunda ka nuna mata jin dadin matarka kawai ka damu dashi.
Da sauri ya dago kai ya kalleta tace karya na fada kome naga ka kalleni wanan yasa da yawa yanzu suka daina aure hadin nan na gida wallahi.
Don karshe baya dadi wani lokaci saidai kawai ya bata zumunci in haka ya faru kuwa nika tonawa asiri ba mama ko iyayyenta ba a cikin dangi shiyasa tun farko banso hadin nan ba wallahi.
Kun daifi karfinane kawai kukai abinku babu wasu manya aciki shi kuma yaya Garba ya daure maku gindi yana ganin kai na kwaraine wai ?
Haka ita mama din sai rawan kai take tana wani boye min don tasan ba zan yarda da wanan ba amma kaddara ai yanzu ya cita kuma tunda an daura ga kuma yadda ya zamo ka koma jawa mutane rai.
Mum ni bana kwarai bane ke nan abinda naji ya fada ke nan tun zaman mum wajen da take magana a cikin bacin rai.
Auren ka da yarinyar nan gaba daya yanzu ya sauyaka Addel duk abinda takewa mutane aka fada baka gani kai gaka mr romiyo sarkin soyayya ko ?
Gara da yau akayi agabanka kaga halinda yar mutane ke ciki a gidan nan babu halin ta shiga sashensu yanzune zasu bita da fadan bakar magana abin haushi har hjyma da kanta don bacewa.
Yanzu mum ni kuke jira ko ku nake jira da zancen nan idan ba zan iya aje mace biyu ba a gidana mum ai ba zan nemi aure ba kuma auren yar uwanafa.
Mum koda wasa nakeyi sai in rasa inda zanyi sai agareku ban taba tunanen in cutawa wata daga cikinsu ba a rayuwana ko wace don ina sontane na aurena kowa kuma zata zauna a matsayin dana dauketa a zuciyanane a zaman mu.
To yanzu dakata ai zaka iyan idan kasa kanka koda hudune nasani amma yanzu tunda ka dawo wajen sati biyu ke nan ko ka taba zancen tarewan yarinyar nan don Allah ?
Ido nasama inga iya gudunka ai nakoga alaman ba zaka iya tabuka komai a hakan ba don kana tsoron matarka kada ranta ya baci ka mutu idan tayi fushi dakai ko ?
Ido ya dan runtse yana mayar da kansa baya kafin ya bude ya dan furzo iska daga bakin yai dan shiru kana ya dago yace mum yanzu meya rage min don Allah ?
Da sauri ta kalloshi tana fadin ban gane ba har meka tanada kan sha,anin koko kana nufin ba zakayi mata lefe bane wai in sani bayan hakan ina ka shirya zaka ajeta kuma ?
Duk wanan abin yakamata ace ka fara shiryashi zuwa yanzu amma kaja bakinka kayi shiru dan murmushi yayi kafin yace mum kune baku ban daman hakan ba ai.
In ma tsaya da ita in fahinci damuwanta mum kin hana hakan garemu tunda na dawo zainab taki ban hankalinta mu fahinci juna kuma kinsani amma baki magana ba.
Hakan yasa na biku a yadda kukeso aje mum lefe kuma da inda zata zauna na dade da gama wanan don lefenta na gidanta a jere tun kan in dawo kasan nan an gama komai.
Wani sanyayyen ajiyan zuciya mum ta sauke kafin tabi bayan kujera tana kara bayanta tayi shiru na dan lokaci kafin ta dago tana fadin yanzu da kai hakan waka fadawa ?
Ko wa zaisan kayi lefewa mama abin gidan nan tsegumine fa haka zasuyi ta yawo agari suna fadin maganan da bai shafosu ba sannan kuma ina fatan ba matarka kaba tayi mata lefe ba ta kwaso mata kayan banza.
Yayi murmushi son yadda mum din keta magana akan Aishan nasa yasan koma meye ita taja wanan a tsakaninsu da mum din don haka ko abin ya bata masa rai dole yai shiru don ita taja hakan ai.
Mum ko ita bata san nata ba saida muka dawo din nan tagani nida kaina na sayo komai na turo dasu nan Nigeria kafin na dawo.
Shiru tayi don ba abinda kuma zatace don haushin da takeji a yanzu nasa ya ragu a zuciyarta can yaji tace zan ga Alh muyi magana akai asa lokaci .
Daddy kuma mum na dauka ai ya fidda bakinsa a cikin zancen nan da sauri mum tace kada ka koma fadan hakan don Allah koma meye ai dole mu bashi hakkinsa na mahaifi ko .
Balle Alh bai rike hakan ba tunda shi ba mace bace mu mata aka sani da wanan tsegumin na anyi ance ba maza ba idan ya dawo zamu tatauna zancen muji.
Mikewa yayi yana kallon agogon hannunsu tare da fadin ni zanje inga umar ya kirani yana son mu hadu karfe shida shine zanje in gansa yanzu.
Allah ya tsare mum ta fada ina daki ina jin duk abinda ke wakana amma kafin mum ta nemeni sai barci ya daukeni mai karfi har tayi ta kirana ina barci a lokacin banji ba.
Dakin mum tashigo ta kira sunana da karfi na amsa a zabure fada take min akan barcin yamma kafin tace dani yau ba zamu girka abincin dare bane ?
Wayata na jawo da zuman duba lokaci tace barshi ma zanwa Addel waya idan zai dawo ya riko muna wani abu muci ki huta da girkin nan tunda yamma yayi sosai yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

6?? 4??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Yan uwa mubi yan uwan mu musulmai dake RAFAH da adduan samun sauki daga Allah akan gallazawan da issalirawa ke masu a halin yanzu Allah ya shige muna gaba baki daya amin.

Na dai ga an fito da kayana ranan wanda nayi zaman wacin gadi dashi gidan ya hafiz sai kuma aka mayar nasan mum ta duba dan abinda zata iya dubane a ciki da zai mun amfani.
Amma kuma naga an mayar ba, a dauki komai ba daga cikin kayan har wanda mum din tayi min ba, a taba ba sai da darene mum ke fada min gobe in shirya inje gidan mu in dubasu.
Dama ina son zuwan don na kwana biyu banje na dubasu ba hakan yasa washegari na tashi da zumudin zuwa gidan don tunda safe na shirya na tafi na samu baban mu agida.
Muka gaisa yan uwana suna makaranta sai inna da kannen mu biyu da basu fara karatu ba ayanzu gidan ba dadi idan ban samu su sadiya agida ba yasa bayan mun gaisa na shige dakin inna na kwanta.
Bayan baba ya gama kintsawane yasa min kira na fito a falo na sameshi zaune yana karyawa koko da kosai yake karyawa dashi alokacin ya dago yana fadin zainabu ina dai kin karya kaf0in ki fito ?
Da sauri nace Alhamdullahi baba saida na karya na fito yace hakan yana da kyau ba, a son mutum ya bargidansa bai karya.
Manya sunce kaddara yana saurin fadawa mutum ga wanda ke barin gida bai karya ba kin gako abinda bahaushe ya camfa wani lokacin yana zama gaskiya.
Insha Allahu zan kiyayye baba na fada cikin ladabi ina dukar da kaina kasa don girmamawa ga mahaifina din a lokacin.
Sai kuma ya juya tambayana karatu nake masa bayanin matakin da nake a yanzu na kare da fadin yanzu dai hutu mukeyi muna dan lekawa asibiti lokaci lokaci.
Madallah ya kara fada a daidai lokacin da yake rufe jug din kunun nasa dake gabansa yasawa kanne kira suzo su dauki wanda ya rage su kara kafin ya dago kai yana fadin.
Kinsan shi yaro yana son suden mahaifinsa koda ya koshine zakiga yana rawan jiki wurin karba yaci saidai kash a yanzu mu iyayyen duk mun watsar da wanan dabi,an mun dauki hakan kamar kauyanci don rashin sanin fa,idansa ga yayan namu.
Fa,idace baba wajen yin hakan mu alokacin da da zaran uba yazo cin abinci zamu rakube muna jiran ragowa don munsan ko yaya yawan abincin yake sai an raga munashi munci.
Yanzu kan ai saidai abawa almajiri na fada daga inda nake zaune yace Allah ya barki almajiri ko shi zai kwashi wanan albarkan yayi gaba.
To zainab nace gwaggonki ta turo mani kene don naji bukatanki don Alh ya kirani yai min zancen tarewanki nan da wani jumma, a mai zuwa insha Allahu idan ba wani abu.
Donshi nace sai munyi shawara dake na kuma zauna dashi Aliyun mun kara magana akan zancen don tunda aka daura aure bamu samu kebewa dashi ba wanan tafiyan yazo ya girsheshi da bai dawo ba sai wanan lokacin.
Kaina dukar kasa ganin kamar yakai aya a zancenshi shima shiru yayi na dan lokaci kafin daga bisani yaci gaba da fadin tau zainabu duk daba zance kinsan kan aure ba a yanzu duba ga yadda wancan auren naki na baya ya kasance a lokacin.
Don haka baki san komai a cikin zamantakewa ba har yanzu manya sunce zomu zauna zomu saba haka zaman rayuwa yake dama.
Banson kiyi duban wai aini dan uwana nake aure don haka bari nayi abinda nakeyi a gida a, a zainab yau a kadara ma baida mata dole kisan wanan aurene bautansa daban da zaman gida.
Don haka don Allah ina rokonki zainab kiyi hali irin na uwarki inma da hali

64 / 105