DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   80 / 105

237K to 240K   out of 313.1K words

Abinda kika dauki kanki mana hummaira irin shashancin nan naki yakewa gudu ai gashi ko kin fara daga ji kin farawa mutane haukan banza hakan yasa takashe wayan cikin jin haushin kalamin mahaifiyar nata.
Ranan tayi kuka tayi kuka sosai kamar bagobe gareta karo na farko data fara nadaman tsarin iyali data dauki lokaci tanayi a rayuwanta.
Sai halima da Usaine suka kirata suka bata magana har lokacin kuka sosai takeyi tana fadin Aliyu munafukine dama ai ta fada masu munafukine munafuntarta yake intayi magana mama ta kama fada.
Suka dai bata hakkuri da rarashi ta nuna ta hakkura da hakan suka kashe wayan sukaci gaba da nuna wai ya Addel bai kyautawa Aisha din da bai fada mata ba.
Amma ta kasa hakkuri da hakan na dan lokaci tacigaba da kuka tana maganganu saida ta kara kiran haliman su suka aje kan taciwa Aliyun mutunci.
Bai dawo gida ba sai lokacin daya saba shigowa gidan ya dawo da ledan take away dinshi tunda ya shigo yaga yanayinta ya fahinci akwai fitina dake cinta a ranan.
Don haka ya shirya mata ko gaisuwa bai samu daga gareta ba a lokacin ya aje ledan dan nisa da ita ya kama hanyar shiga daki kai tsaye sai yaji muryan ta tana fadin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7?? 9??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Aliyu ashe matarka nada tsohon cikine har ya tsufa haka amma baka taba fada min hakan da bakinka ba don kada in zubar mata da cikin kome ?
In fada maki don kina wa agareta yanzun da kika sani shine me sai kije din kiyi abinda zakiyi ko kuma kije ki zubar mugani idan kin isa har ya juya yakuma tsaya yana fadin.
Wai ban gane bama Aisha so kike inzo ina fadin Aisha ai zainab nada ciki kome kome kika mayar danine wai a cikin maza ?
Mikewa tayi tsaye ta dubeshi dakyau tace ba zaka fadi ba ai inkasan kunya tunda ka iya yiwa zainab ciki a wanan lokacin.
Kunya wai tsaya Aisha me kika daukenine yau ina son insani don Allah kunyanki zanji don nayi maki alkawarin ba zanwa wata mace ciki ta haifa min daba a duniya tunda gaki ko me ?
Ko kuma a,a inajin kunya akan munyi harkan banza da zainab yadda kika saba fada nayiwa zainab ciki har ya tsufa na kasa fada maki har yanzu ko me ?
Don ban gane me kike nufi ba akan matana zainab dai matatace halal malak ciki kuma ko meye bata hanaki ai kema kiyi ba kece kika hana kanki yin ciki don wni naki dalilin .
Ita kuma bata da dalili saitayi ta zubo min diya ina dauka ina jin dadi iyayyena da yan uwana suna alfahari da hakan suna nuna nawa zurian a duniya kamar yadda nima aka nunani a baya matsayun dansu don haka meye ruwanki da zancen cikin jikin zainab yanzu.
Munafuki mayaudari kacuceni wallahi saboda sonka yasa ban yarda nayi ciki yanzu ba son haka kayi kadan kace zaka dauko wata mace tazo gidan nan ta haihu yanzu kuma ina kallo.
Nuna alaman bata da hankali yayi da hannunsa yana nuna kansa hakan ya bata haushi sosai ta rarumi flower vers ta jefa masa ya kauce ya shiga daki yarufe tazo ta kama dukan kofa tana zage zage.
Yana jinta yaki bude kofan duk da ransa yana bace da ita hakan bai hanashi yin duk wani abinda ya saba ba ya fito ya zauna ya shiga laptop dinshi na dan lokaci.
Kafin ya rufe don bai gane komai a lokacin don sautin kukan Aisha din dake zuwa kunnensa a lokacin saboda kofa ta zauna dirshatana kuka zakice mutuwa akai mata mai karfi a lokacin.
Hakan baisa ya bude kofa ba sai safe ya bude kofan ya fito don ya dauki ruwa anan falon ya sameta kwace ma,ana anan dai ta kwana tana jin fitowansa ta zabura ta mike ta hau bakinta tana zagin shi tare da nufoshi nan ya tsaya yace baki da hankali kika fara kika tako nan yau saina balbalaki a gidan nan da sai kin kwanta asibiti.
Jin hakan yasa taja ta tsaya a waje daya bata motsa ba daga inda take din amma taci gaba da zaginsa din tana aibantashi dani da munanan kalamai.
Har ya shirya ya fito ko kallonta baiyi ba zai fitane take fadin zaka dawo ka samu gidanka hakana don ba gadin gida nazo maka ba nan.
Lokacin ya juyo yana fadin Aisha duk inda zaki kije nagaji nima wallahi wanan abu ya isa ya isa haka don Allah kije duk inda zaki nima in huta yasa kai ya fice daga gidan kai tsaye.
Kasa magana tayi a lokacin don ba abinda tayi tsamani ji daga garesa ba ke nan a lokacin ta tsamaci zai zauna ya lalasheta tunda yasan ya saba mata yaiwa wata cikin haihuwa gata zaune.
Daga nan sai ta fito mai da plan dinsu na ya kaita kasan waje a dubata sai gashi kuma taji ba daidai ba gareshi ya barta nan zaune da mamankinshi ita kadai a gida.
Nan ta jawo waya ta bugawa halimansu waya ta fada mata duk yadda sukayi haliman tace kin kwafasa ai Hummaira wallahi kin riga da kin bata zance don a wanan lokacin yadda kikai masa din nan ba zai ko kalleki da wani zancen fita waje ba.
Keda mukayi dake cewa ki danyi masa barazana kadan don ya rude dole ya tausaya maki kije kin buge ga hauka irin naki yanzu sai ki san mafita ai kina dawowa gidan nan kisan yaya ba zata barki ba kema kin sani shiku kin zube a wajenshi ke nan kuma.
Muryan uwar sukaji tana fadin ko yanzu kin zube ai sai ki kwaso ki dawo gidan gaki ga gida ai dama dakinki na nan baki sakewa wani ba dama saiki dawo a share ki shiga tunda hakan kike so.
Tanajin abinda uwar ta fada ta kara fashewa da kuka mai karfi uwar taja tsoki tana fadin sakarai mara hankali kawai .
A nan ta zauna taci kuka ma,ishi kafin ta mike ta nemi abinda taciwa cikinta sai kuma zazzabi ya biyo bayan hakan wanda ya kaita ga kwanciya a lokacin.
Wanda har ya dawo tana fama da zazzabi dole ya dauketa zuwa asibiti aka dubata tare da yi mata allurai ta samu sauki suka dawo gida.
Ya kira mum ya fada mata halinda yake ciki da matar nasa mum ta bashi hakkuri tace kada ya kulata ya kyale son yana daukan mataki za,ace saboda auren zainab ya saketa don yaga ta fara samun ciki.
Shine daya dawo gida ya sameta a cikon wanan halin dole ya tausaya mata ya kaita asibitin a dubata suka dawo ya kuma bata abinci saida taci ta kwanta barci.
Tun wanan lokacin suke zaman yar tsama a tsakanin su ba mai kula wani irin yadda suka saba a baya tsakaninsu sai ya fice baice mata komai itama ko kallonsa batayi idan ya dawo.
Suna cikin hakan aka bugo mata waya cewa mahaifinta yayi accindent har ya samu kariya a kafasa daya wanan yasa suka zo kano a satin hankali tashe.
Ni dai ban ganta ba saida kwana biyune muka kwasa zuwa gaidashi nidasu hauwa sam basu san da zuwan mu ba don basu taba zaton zanzo ba ma gaidashi din.
Mu hudune sai kayan fruits da drinks don ban yarda na kai masu dafafen abinci ba saboda zargi kishiyar da baku zaman arziki ina kai ina zuwa wa nata da abinci dafafe yarda ke saka ka dafa abinci zuwa dubiya ai.
Suna zaune sun baje ana ta hira a dan dakin wasu nacin abinci girshi suka ganmu ita goganyan bata ko ganemu ba saboda kwarjinin da mukai mata.
Sai Usainace take fadin wai zainab ce ashe kuna hanya tafe sannuku da zuwa yauwa anty Usai ya mai jikin tace jiki da sauki wallahi zainab .
Abba su zainab ce kishiyar Hummaira sukazo gaida kai ba kunya uban ya dago yana fadin waye zainab din a cikinsu ?
Nice baba na bashi amsa ina kara matsowa bakin gadon da yake kwance din yana ganina ya maida kai ya kwanta nakarasa ina mashi ya jiki da kyat ya amsa da dasauki bayan hakan ko amin ban samu daga bakinsa ba.
Muka danyi tsatsaye muna kallonshi na dan lokaci daga inda muke zaune mukejin suna warning dinta da a,a hummaira kada ki fara ba haka akeyi ba don Allah.
Anty hauwa ta juyo tana fadin to Allah ya sauwaka muka aje ledojin fruits din mukai masu sai anjima muna fita muka hadu da uwar Usaina din ke kara gabatar damu itama kallon tsab tayi min na second mata mai haba haba kamar yarta Usaina dai .
Itako goganyan tana fadin na gayyacetane a harkana don me zata zo min nan tafita hanyanafa banson yawan shishigi a kaina ?
Aiba ke sukazo gaidawa ba ko Abbaku su kazo gani donshi tazo bake ba mara hankali kawai ai dole wanan tafiki hankali jita cikin natsuwa don Allah ?
Halima ta dan kalla tana kullawa azuciyanta hanyar da zataci kudin Aisha din a saukake kafin tace ni ban ma taba sanin haka Zainab din take ba ai.
Lalai hummaira akwai aiki ja agabanki gaskiya wanan kamar ruwa biyuce ai nake gani kamar tana da surki da buzaye dai ?
Haka uwarta da ubbanta suke farare suma ta fada a,a lalai dole Aliyu ya haukace a kasa gane kansa mana yana ganin wanan abin a gidansa yanzu ke kingansu kuwa cabdijam ta nisa irin akwai magana din nan kowa yayi shiru dakin na dan lokaci suna karatun zuci.
Can tace jifa kamshi don Allah yan iska sun fita amma kamshine tako ina kamar yanzu suka shigo dakin nan cabdijam.
Ran Aishan ya kara baci sosai da zantuntukan da halima din ke fadi cika tayi tana batsewa ta kasa yiwa kowa magana don yadda take jin takaici a lokacin.
Saida mama din ta fita ita halima ke fadi kasa kasa yadda sai hummairan zataji ta ki bari mu samu lokaci akwai magana gaskiya dole musan abinyi kan yar banzan yarinyar nan don wanan sai kinyi da gaske gaskiya.
Muryan Usainace ke fadin amma Hummaira kina da matsala gaskiya kada fa ki zama cikin matan da basu amfani da iliminsu wanan abin ilimine irin kishin nan baki zauna kina wanan shirme haka.
Idan zaki kama jiki ki kama don wanan iskancin da sakarci da kikeyi yanzu ba namijin da zai daukar maki hakan kin ma gode Aliyun nada sanyin hali sosai bai biyo sunanshi na Aliyu ba don dakin gane kurenki wallahi.
Kamar bada ita suke zancen ba saida yammane Aliyun ya shigo gaidashi shima kafin ya koma gida yana tsaye bakin gadon ya kalli dattijon yace amma ance kafan nan dorin nan baiyi ba don yana kamar dan haushi daga kasa.
Nima dazun da rana nake magana fa amma na nuna ma yan asibitin sunce ba komai yana hakan wani lokaci idan yana son hadewa.
To amma gaskiya da an duba don zainab tace kafar da dan matsala gaskiya wacece zainab da zata kawo muna sallon banza dama abinda ya kawota ke nan sheri.
Aisha ke fadin hakan daga bayansa ya juyo cikin mamaki yace sheri kuma meye abin sheri a nan don taga matsala ta fada kuma .
Ba matsalan komai data fada tunda aikintane uwar tace ta dora da fadin hummaira ina rabaki da hakan wallahi baban yace ta kyaleta bai jima ba yayi masu sallama ya fita.
Aikuwa sai gashi bayan kwana biyu ta kirasa tunda safe tana kuka wai kafan Abba ance dorin baiyi ba sai an sake anje dashi theater yanzu asake dorin don ba ai kwana dashi da dadi ba jiya.
Yace gashi tafe ya samu likitan nata fada dasu na rashin fada mashi dasu da nurse din da basuyi da wuri ba nan tayi tsamo tsamo agabanshi cikin kunya.
Wanan ciwon na mahaifita yasa ta jima a kano inda hakan ya basu dama shige da fice suna yawon malamai da yan tsubbu ana faman cin kudinta suna shara mata karyan abinda ba zai yuyu ba don Allah ya tsareni.
Takai wata kafan mahaifin yaki lafiya karshe da zasu kawoshi nan asibitin mu akayi dace muna wajen Ramla da muke tare itace ta karbi aikinsa sukayi don haka nasan komai sai gashi tana jin bayani a bakin maigidan abinda ma ita bata sani ba akai.
Tayi wata daya dole ta koma ba biyan bukata a ko ina bukata dai bai biya ba kuma bata hakkura ba don dole take shigowa da biyu kano da sunnan duban Abbansu ta biya tata bukatan ta kuma.
Ban kara wata ko kwanaki ba a yadda watan haihuwa ya nuna ranan na fara jin alaman nakuda don haka na kira anty hauwa na sheda mata a dauki lokaci ba sai gata gidana.
Bayan ta duba tace muje asibiti kawai ayi komai yadda ya kamata acan din ban kira kowa ba sai mama Azumi da muke tare hauwa ta dauka tasa Rukkaiya tayi min girki lafiyayye da zanci.
Muna zuwa asibiti suka shiga dani dakin haihuwa ya zo da dan matsala yasa hauwa fita ta kira yaya Addel take fada mai halinda ake ciki yace gashi zuwa kano din daddy da baba zasuzo ayi abinda ya dace dani din kafin yazo.
Inda ya dawo gida hankali tashe saida ya shirya ya shiga dakinta tana barci ya tayar da ita yana fadin kano zan tafi yanzu insha Allahu.
Bata wani damuwa ba don tasan donni zai tafi tace dashi ka gaidasu Abba inka samu zuwa yayi mamakin rashin tambayansa dalili.
Sai cewa da tayi wai ya gaiyar mata da mahaifanta idan yaje ya kada kai ya fita ya barta bayan ya aje mata kudin da zai bar mata don amfani.
Koda yazo an ciro min babies dina lafiyayyu har an kaini resting room ina barcin wahala yara masu kyau tun suna jariren zaki gane cewa ya Addel suka biyo da tsayi da komai mazane duka biyu.
Har mum saida tazo asibiti ranan matan gida na fadin ba kara tace in Addel dan farinane ita kuma zainab ai autanace don me zan tsaya gida auta ta haihu.
Ai kuwa nan yan gida suka cika asibitin ya koma kamar gida ake mahaifan Aisha ya kira ya fada masu zancen haihuwan nawa sukayi mai fatan alheri.
A bakin mahaifan nata take jin zancen haihuwa nawa don haka ta danne haukanta sai uwar ke fadin Hummaira nasanki da hauka kada inji kinyi wani haukan banza zan saba maki batace komai ba ta kashe waya kawai cikin kunnan rai.
Shiko tare dashi ake jinya duk da ga kawayena ga yan gida amma yana nan dakin koda yaushe haka mummy dazo don daddy da yayi fadan rashin zuwanta har kwana biyu dole ta shirya ta tafi .
Ta samu za,a sallameni a ranan don haka bata wani jima ba a wajen sukai sallama suka fito suna gulma da suka sabawa kansu.
A nan gida naci gaba da jiyana sai yan barka ke faman shigowa barka mahaifiyar Aisha din taje asibiti dubana tare da Usai da halima haka kuma dana dawo gida tazo ta kawo muna abin arziki.
An sallamoni da kwana daya ya shirya ya koma abuja don daddy yace a dage taron suna sai na dan kara samun karfi sai dai an radawa yara suna yusuf mahaifin ya Addel sai kuma dayan yace sunan daddy musa.
Aka fara kiransu da Abba da daddy kinsan mutane da bata suna nan da nan Anty nafisa ta saka masu wanan sunan aka fara kiransu dashi haka.
Koda yaushe muna waya yana jin lafiyata suna saura kwana hudu ga yadda daddy yasa ya dira kano da uban sayayya shake a mota.
Lalai manya sunce haihuwa alheri ne ga bawa don ba karamin abu nasamu ga wanan hauhuwan ba haka su yaya nasir da yan uwansa sukayo min aiken kudi masu yawa saida na girgiza dasu.
Gaskiya yan uwa da abokan arziki sunyi min kokari sosai sai sam barka a wajen mutane daren sunna ta diro garin bayan tasha zugi a wajen kawayenta da halima.
Sam baisan da zuwanta ba don sunyi da ita tace dashi me zatazo tayi shida buki ya sama Allah saukeshi lafiya yace amin ya gode da adduanta.
Don haka dawowa yayi kawai ya samu mutane an cika part din wai suma zasuyi nasu taron ido yasa mata kawai ya tattara kayan amfaninsa ya kulle daki ya fito.
Gidan mum yaje yana fada mata abinda ke faruwa tace kayi hakkuri kasa masu ido duk abinda suka bukata

80 / 105