DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   73 / 105

216K to 219K   out of 313.1K words

kira kin fada min zuwanku ba in shirya taron ki yau uwar daki gidana ?
Rugumeni tayi tana fadin wata uwar daki can da kika manta dani, ai yanzu ga ubandaki kin samu anya zeey kuwa zaki bar bros ya koma gun aiki wanan irin soyayya hakan.
Yaya ina wuni halimatu take gaidashi ya amsa a yaya Addel dinshi da lafiya kawai yana basarwa .
Mun zauna aka gaisa a cikin mutunci sai mamaki kowansu keyi yadda wai dukkan mu muka sauya cikin dan kwana biyu sai zolayansa nafisa keyi da nima gaskiya bro auren nan zanyi kaga zeey din mum yadda ta koma in short time haka ?
Ina ita kishiyar naki Dada ta jefo tambaya nace tana wajenta Dada kila tayi barcine kinsan yau an tashi da ni,ima a garin kowa nason hutu.
Bari mana in mun tashi mu lekata ko Nafisa ta fada mikewa nayi a lokacin nace barin kawo maku ruwa ina jin tana fadin ruwa kuma jam da wanan sanyi haka wa zaisha ruwa.
Dinning naje na dauko masu sauran break fast din na kawo masu ina direwa sai fadi dada keyi meye kuma haka muka samu sa zuwan mu dadina da gidan amare ke nan akwai maiko.
Karshe na dire masu lemun kwali guda ukku ke indai ba abincin mijinki kika kawo muna ba son tsoro shiya zauna da yunwa yace No mun karya mu tun dazun ai ni kuma nace.
Wanda na dafa da safene ya saura ku fara tabawa kafin nagama maku abinci halimatu bude mu gani Allah yasa dai ta iya girkin inba shirme take maka ba.
A,a wallahi dada zeey mum bata da sa,a cikin mu wajen girki wanan kan kowa yasan da hakan anty Nafisa ta fada tana dan yunkurawa zuwa wajen bowl din dataga anyi raping dinsa da polls perpper tana fadin bari muga wanan.
Yana zaune sai murmushi yakeyi don yasan abinda dada keso kenan korafinta ke nan gareshi gidansa ana rowan abinci yau gata ga abincin gidansa ba shagube ko karafi.
Wai wai wai ke yar nan kai mai sunan malam kace in tare a nan sai an kare amarci dani haka don wanan dadin aiga yar zaman daki kun samu yanzu.
Ke tsohuwar nan da butulci kike meye daddy bai sayo maki don wanan zakice zaki wani tare a nan aci dake au au kinji almuri ko korata yakeyi da halima.
Yo nacene uban naku bai mun wanan dai na sabbin hannu nake sonci kuma yanzu ke zuba mata don Allah yacewa halimatu nan ta yunkura da sauri ta gurfana gaban abincin.
Dada wani zan fara zubal makine ta tambayi dadan tana kallon ta dada tace ai komai a nan sainaci sa halima kedai zuba min kifi na fara dashi nima in tayar da komadan amarci.
Lokacin ya mike yana fadin bari na duba maku Aisha nagani ko ta tashi ya dan fita sunaci muna hira nayi mamaki sosai yadda anty Nafisa ta zage ta kwashi abincin don komai saidata taba itama a wajen.
Sai gasu tare tafi yana gaba tana bayasa kamar dole ya tasota suka fito don yanayinta idonta akan girkin da suke kwasa lokacin ta dafa kujera tana fadin sannuku da zuwa dada.
Suka gaisa dada na fadin ai ya taso dakene yanzu nake fadin in mun gama muje mu gaidake ai sai akace kina barcine ehh ta fada kafin tace to sai anjiman ku a dadare ta fice suka bita da kallon gulma.
Dadace ta juyo tana fadin ina ba dai matsala a tsakaninku da ita da sauri nace wlh ba matsalan komai dada lafiya lau muke zaune.
Ikon Allah to ai haka akeson ji dama a zauna lafiya daga inda anty Nafisa take zaune tace matsalan me ina ruwanta da ita kowa na nasa bangaren .
Ba abinda zai kaiki can kiyi zamanki a part dinki ki tsare aurenki zainab kada ki yarda ki kula lamarinta balle har wani abu ya faru kedai yanzu ba karama bace kinsan komai.
Sai kin kula sosai don irin wanan matan masu ji da kansu haka suke abinsu gadarance don ka kula karshe aga laifin ka donsu basa laifi wajen miji dama.
Me wanan yanzu tafi zainab dashi anty ni sai incema zainab tafita a yanzu a nawa ganin halimatu ta tsoma baki a katon fatko sai naji anty Nafisa tace ke rufa muna baki son Allah keme kika sani tukunna.
Aiba wayewan fuska bace maganan sanin kan duniya da gwagwalmaya tare da cudanya da masu budaden ido ake zance ita zeey ina idonta ya bude irin haka ?
A raina nace sanin da kikaiin kema gama kawai ki wuce duk inda zata bullo min Allah zai dorani akanta insha Allahu.
Muna hira ina mikewa zuwa kitchen ina duba girkina wani lokaci kuma in dan leka yaya daya koma dakinsa ya kwanta don su samu sakewa.
Suma din idan na daga suna samun lokacin yin wani zance da basu son inji daga garesu akan mu har na samu na hada git
girkina tsab na fito dashi falo misalin daya saura duk na kammala komai don ban yarda zuwansu ya bata min lokaci ba.
Sai faman bina sukeyi da kallo kowansu da abinda yake zantarwa a kaina cikin zuciyarshi ina dinning din tsaya ina shirya abinci ya fito daga daki banji zuwansa ba sai ji da nayi ya rugumoni ta baya yana kai min kiss hakan yasa nayu murmushi ina juyowa nace akwai baki gidan fa yaya aiko mukaji muryan anty nafisa na fadin.
To romeo muna nan dai a bari mu wuce acigaba don Allah kare rugumeni yayi a jikinsa yana fadin ai nasan kuna nan zaku hanani jin dumin matatace ?
Ta karaso tana fadin lalai bros ka zare yanzu a gabana kake faman rugumar min kanwa zanfa dauki abina in komawa daddy da ita gida.
Ya kwashe da dariya yana fadin ai itama ba zata ba yanzu ko kunce ku tafi gata kuma ki gwada Allah ya shiryeka bro wazaice zakayi hakan ta fada tana dafa kujera.
Zainab wani girki kika hada haka kuma bayan wancan da mukaci dazun dama na dora koda kukazo karasawa nayi kince kar dada ta tafi ke nan har ina zance zamu tafi yanzu ina son inje wanke kaina yau wallahi.
Kinsan monday za,a shiga school akwai aiki banda time din yin hakan idan na bari aka koma nace to ga abinci na hada sai kuci kafin ki tafi anty tace ko kuma na barsu nan in tafi ba.
Ba inda zaki kema sai kinci abincin nan tunda an dafa daku dama gashi na zuba maku tare bari na dauko nasu dada inkai masu.
Dadan tana kwancene sai halima dake zaune tana dan lekomu don kujera ya tare mata ganin mu dake na juyo na dauko masu cikin babban tire .
Ina fadin dada tayi barcine ga abinci na kawo maku zubur ta dan dago tana fadin abinci kuma bayan wanan da muka cika cikin mu dashi.
Na fada maki wanan wanda yacine da safe ya raga wanan shine abincin rana daga inda suke zaune Nafisa ke fadin wai bataci ko dama nasan ta koshi ai ki mayar da abincin kawai .
Zeey da sauri dada ta dago tana fadin banyi haka dake ba sarkin rowa nasan da kece ruwama in na samu nagode aje kinji yar albarka ba,a rasa inda akasashi ai.
Suka kwashe da dariya sosai kowa yaci abincin kafin mu kwasa zuwa dakina mu uku mu zube can daga sunan sallah muka kuma zauna hira Nafisa na muna labarin zaman gidan mijinta.
Koda ya dawo sallah nan ya samu dada falon ta idar suka kuma zauna hira da ita har akai la,asar nan ma shiririta bai bari sun fito ba sai five suka bar gidan inda nayu masu alheri mai yawa suna mamakina.
Bai fita ba wunin ranan yana gida don zuwan bakin mu sai bayan tafiyansune ina kitchen ina wanke uban kayan da aka bata ya shigo ya sameni yana fadin basai nayi wani girki ba don Allah in huta hakana bari ya fita ya dawo.
Hakan ya ban daman samun yin aiyukana na gyara gidan ko ina na saka kamshi kafin naji ya koma min daidai wanka nashiga dana fito na samu kananan kaya na dane cikinsu na dawo falo na zauna don magariba ya kusa lokacin.
Har akai sallah kafin ya shigo gidan koshi ba yadda ya saba,ba son ya dan gwauta lokaci ga yadda ya saba dawowa.
Ina son in kira ina gudun kuma yaga zumudina ya dauka na kagu da yadawo kusa dani sai na share sai kuma ga hauwa ta kirani muka buge da hira da ita nake fada mata ya fita bai dawo ba ai kuma naga lokacin dawowansa yayi har ya wuce.
Take fadin ke me kikeyi da baki daga waya ki kirasa kiji halin da yake ciki ba zeey wai ke wace irin macece kamar gidahuma don Allah ?
Idan zaki zage damtse ki shigo system kamar kowa ki zage kin zauna kina koyi da halaiyan su mum tsofi na kunyar mutanen da.
Wlh ke din nan in baki hankali ba sai kin koma yar kallo a gaban kishiya don Allah ki rabani da zancen haushi sai naji ta kashe waya tana jan tsoki.
Hakan yasa nadaga waya nakirashi har wayan na batun tsukewa sai naji ya daga ina jin sautin muryan sheck jafar yana wa,azi a motan yace.
Zeey gani kusa da gida ai daga hakan ya kashe waya na zauna ina kallo sai gashi ya shigo da sallamanshi na dan dago ina mashi sannu da zuwa ya amsa yana fadin.
Zainab ina kusa da gida koda kika kirani yasa da kamar kada in daga sai kuma naga kada ki damu idan ban daga din ba wallahi naga har time din dawowanka ya wucene ai ?
Yace na dan shiga garine wurin Yahaya daga can kuma na biya nayi shopping ina zuwa ya fada na kara daukan kayan na aje gefe daya.
Saidai nayi mamakin kayan da naga ya sayo don muna dasu ai a gida basu kare muna ba ya koma shigowa da wasu kayan niki niki na sake mikewa na karba daga hannusa saidai bai miko min duka ba saboda nauyinsu.
Bai zauna ba a falon ya shiga ciki wanka yayi ya kimtsa ya fito nan ya sameni da mum muna waya akan zuwan su dada gidan da sukai min suka wuni.
Tace ai hakan yayi sosai sun dawo suna fadi kin kyauta masu sosai sunci sun sha yanzu kan gida yai kyau don ansan darajan bako.
Na danyi murmushi donji abinda mum ta fada fitowanshi da nace kafito yasa tace yana kusane nace yanzu ya dawo in bashi wayanne tace barshi ya huta ki gaidashi.
Mumce na amsa mashi da kai ya mika hannu yana fadin bani ita na mika masa daidai lokacin tana fadin saida safe.
Ka,idane safe in kirata haka kuma bayan sallah isha,i idan na kwatanci ta idar da lazumi da takanyi a wanan lokacin.
Magana sukayi akan Nasir dake Abuja naji yana fadin ranan talata zan koma zan sameshi can aga yadda za,ayi dai amma sun rikeshi da yawa wallahi.
Jin hakan yasa na dago kai da sauri ina dan kallonsa muka hada ido yayi min signal da ido guda shiru nayi da har hakan yasa na fada tunane zai tafi ke nan sai yaushe kuma zai dawo idan ya tafi.
Ya gama naji yana fadin eeheee magana nakeyi fa me kike tunane haka kuma ya kafeni da idanunsa yana kallona na dan murmusa ina fadin ba komai yaya.
Anywhere ga kaya nan na amfani na karo maki don kada ban nan ya kare don banson kina fita don Allah daga school sai wajen aiki zeey saiko gida idan haka ya kama koshi ba kullum ba.
Don banson kice zaki kwaikwayi dabi,an nan na Aisha kullum zuwa gida duk da nasan suma gidan ba zasu yarde maki da haka ba.
Kamar yadda kikaji hutuna ya kare zamu koma Abuja din ranan tuesday insha Allahu ina son ki tsare min mutuncinki kamar yadda kika saba.
Duk da nasan banda matsala a wanan fannin dake amma ya zama wajibi in kara jaddada maki hakan don ki kula.
Ina tunanen zuwa wajen baba don ya bamu yarinya guda daga cikin kannen mu ta zauna dake duk da nasan yana da wuya baba din ya yarda da hakan amma zan gwada in gani koda sa,a.
Kaima kasan baba bai yarda da hakan koni don mum ne da daddy ba yadda ya iya yasa ya yarda na zauna a gida dasu amma ka gwada ka gani din.
Yace well iwill try ko zamuyi dace a hakan idan hakan bai samu ba dole gida zan koma ko dada ko halima din nan wata tazo ta dinga zama dake nan.
No zan ma iya ai ko can aini kadai ke zama bada kowa ba koka mantane yaya naji yayi shiru nima shirun nayi.
Kamar ba zaiyi magana ba yana ta danna waya sai can naji yace wanan ba gidancan bane wanan yayi girma da yawa ki zauna ke dai mace a cikinsa haka.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7?? 3??
GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.



Gaba daya nake jin kunci a zuciyana tunda naji zancen komawanshi Abuja bakin aikinsa sai nake jin kamar idan ya tafi ya tafi ke nan iri wancan karon.
Duk kokarin da nayi na danne hakan a zuciyana na kasa saida har ya fahinci hakan a gareni har yakai ga tambayan wai meke damuna ne ?
Nake fadin ba komai a sanyaye ya zakice ba komai gaki kamar kinyi weak nake gani nace haka kawai abin yazo min nima bansan ko me yasa hakan ba.
Oya zonan ya miko min hannu na mike da kyar zuwa gareshi saidai kafin na isa gunsa hawaye ya zubo min haka na karasa saiji nayi yana fadin subbahanallahi har da hawaye haka zeey ?
Jikinshi na kwanta sai hawaye nake kokarin dannewa don kada in fasa kukan har yajini amma inas na kasa controling kaina ga hakan saida na dan fara shesheka har yaji a hankali .
Ya Salam !
Naji ya ambata yana kokarin dagoni daga jikinsa mu hada ido dashi kara kamewa nayi a jikinsa ban yarda da yadda yake son muyi din ba a lokacin hakan yasa ya daukeni cak a hannayesa kamar ya dauki baby roba.
Sai dakin kwanana ya direni saman gadona na zata fita zaiyi a lokacin amma sai naji sabanin hakan a hankali ya fara kaimin kiss tako ina a jikina ina kokarin zillewa.
Har yakai na biye masa yadda yakeso na kawar da kunya idona a wanan lokacin yayi yadda yake so dani nima na more masa a matsayina na mace a wanan fannin.
Muna mayar da numfashi naji ya shafo kaina a hankali yana fadin kukan ya kare koda saura na kara lalashin babyn nawa agai ?
Da sauri na dan yunkura ina fadin ya kare wallahi yaya saboda duk juriyana na raina raina kaina a lokacin donko nagane kurena a wajensa ya nuna min shi namijin duniyane na sosai raga min kawai yakeyi ashe daman.
Shine ya fara tunkurawa ya mikena zata bandaki zai shiga sai naga ya fice daga dakin nabishi da kallo ashe kofa ya rufe don a bude muka bar gidan sai daga baya yaje ya rufe ya shiga dakinsa ya tsabtace jikinsa ya jima bai fito ba sai can gashi ya dawo dakin.
Lokacin duk da darene ya dan ja hakan bai hanani gyara dakin ba don na gyare gadon bakyace shine muka gaba yamutsawa ba a dan lokacin daya shude.
Cup biyune a hannunsa sai goran freshmilk daya riko ina tsaye ina dauko riga in saka naji shigowansa hakan yasa na juya ina kallonsa.
Wajen gado ya nufa kai tsaye inda ya zauna a bakin gadon yana tsiyaya milk din a cups din rigan na saka na rufe wajen kayan na nufosa kafin na karaso naji muryansa yana fadin .
Zainab kinsan wani abu kansa a duke yana kallon abinda yakeyi zama nayi kusa dashi ina mai girgiza kaina ya dago yana fadin na farko biyayya naga kinsan wanan kuma kina kwatantawa don kina kina son duk wani abinda nake so ko ban fada ba.
Don haka banda wani shakku ko kwankwanto a kanki zeey na fada maki tyn farkon haduwan mu kan banda ra,ayin aje mace fiye da daya a gidana.
Amma kaddaran auren mu zananene tun farko don haka ki cire a ranki cewa zan tafi da Aisha Abuja in barki nan don ban sonki ko wani abu a,a.
Da ace tun farko kece matana da ba abinda zaisa na kara wani aure a

73 / 105