DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   33 / 105

96K to 99K   out of 313.1K words

Hjy ina dai lafiya dai ko don a gaskiya ban tsanmanin ya fito koda bayana haka jiyan daya dawo ya dade zaune cikin mota bai fito sai can naga fitowan shi ya shiga ciki.
Da sauri na juya zuwa cikin nabarshi a nan gurin tsaye kofan dakin na nufa sai kuma naja na tsaya saboda har in yana ciki na shiga yana iya min cin mutunci da koran kare don haka nayi saurin komawa na zauna a inda nake da farko din.
Saidai zuciyana ya kasa shakat da hakan sai faman sake sake nakeyi a kasan zuciyana can dai na mike don na kasa zama saboda tunanen da nayi idan wani abu ya faru ni gida zasu fara dorawa laifin haka.
Kai tsaye dakin na nufa cikin karfin hali na tura saina jisa a bude ban yarda na shiga gaba daya ba saina dan fara turo kaina a hankali ina bin ko ina da kallo cikin mamaki.
Komai a dakin tsab yake don shima an kashe Naira a cikinsa don ba karamin kudi aka narkawa dakin nashi ba da kayan zamani na more rayuwa a cikinsa.
Mamakeken gadon na hango saidai babu kowa a samansa hakan yasa na juya da sauri zan bar dakin sai idona ya sauka a kafansa dake kasa yashe.
Bansan lokacin dana sakai zuwa cikin dakin ba gaba daya na nufi inda yake yashe kasa yadda na ganshi kwancen shiya ban tsoro yana kwance dagashi sai gajeren wando da yar singlet ya dunkule a waje daya alaman ciwo na damunsa.
Ga amai nan har kashi biyu ya zuba a gefenshi haka na daure na kai durkushe a gababsa ina kiran sunansa cikin tausayawa tare da kara ambatan sunanshi da ya hafiz baka da lafiyane haka ?
Da kyat ya samu ya bude idanunsa yana min wani irin kallo dana kasa fassarashi a lokacin ko tsanace ko na neman taimakonane yake min ban sani ba.
Yun kurin mikewa nayi niyar yi naji yace cikin wani irin murya ki taimaka ki kira min mummy ki fada masu banda lafiya ciwon cikine yake damuna tun jiya.
Ka bari na taimaka maka in gyara wajen nan da jikinka sai a kirasu amma bai dace aisu zo su sameka a haka ba na fada na mike na nufi hanyan bandakin nasa na bude nan ma yayi amai ya kasa flushing dinsa saida na tsaya na gyaro wajen na hada masa ruwan wanka nafito.
Da taimakona ya samu ya mike zuwa bandakin ganin yana kokarin tubewa agabana yasa na fito na jawo masa kofan aikin dakin nayi na tsabtace masa ko ina na saka kamshi a ko ina najuya fita daga dakin bayan na duba wardrobe na fito masa da wasu kaya masu saukin sakawa na dora saman gado.
Kitchen na nufa na dan dora mai abinda zaiji mai saukin hadi indomei na hada mashi sai dan albasa dana cika nayisa da ruwa sai tea mai zafi da kauri.
Ina shiga da cup din tea din yana fitowa daga bayin a lokacin kallo daya nayi masa na kawar da kaina gefe daya don tawulne daure a kungushi lokacin.
Saidau yayi wani irin rama sosai zakice ya dade kwance yana jinyane Allah yasa na gyara gadon don sama ya fada yana lumshe idanunsa.
Ka saka tufafi a jikin ka kada suzo su sameka hakana fada ya dan bude ido ya kalleni kafin ya kalli tufafin dana aje masa din haka ya daure ya saka a gurguje ya koma ya kwanta ina tsaye ina kallonsa.
Tea din mai kauri na kawo masa ina masa sannu nace ga ruwan tea ko zai walwalema hanjin kadaina amai, hannu ya mika min daga kwacen alaman na taimaka masa ya mike zaune, banki ba na kamashi ya mike zaune din na mika masa ya amsa ba mussu ya dan kurba zafinsa yai yawa yasa ya dan aje gefesa ya koma ya dunkule a waje daya.
Wayan nasa na zagaya na dauko mashi na mika mai yake fadin don Allah kira min layin mummy a raina nace dan iska gidahuma tayi rana ke nan ashe ?
Layin uwar na nemo masa kira daya ta daga kamar tana jirace da kiran nasa dama tana fadin hafiz yanzu na kare zancen kafa a raina.
Mummy bashi bane ya hafiz baida lafiya sosai sai amai yakeyi yace nakiraki kizo cikin muryan rudewa naji tana fadin me kika bawa hafiz din ?
Cikin mamaki nace ni kuma mummy bari nazo gidan ta fada tana kashe wayan nata nabi wayan da kallon mamaki ina maimaita kalamun mummy din gareni na kalman data fada na me kika bashi yake amai ?
Me wanan kalma ke nufi a bakin mummy zuwa gareni yanzu nan na fara fassara kalman a zuciya saiga wayan nasa ta kara kara na mika masa yace ki dauka na danna muryan anty Nafisace tana fadin zainab meya samu hafiz din kuma ?
Anty yace cikinsane ke ciwo nima ban sani ba sai yanzu na sani to gamu nan zuwa ta fada ta kashe wayan ba,a jima ba ko sai gasu son kila dama suna hanyane ta kirashi din.
Tun daga falo nake jin muryan mummy na kwala min kira ita kuma anty Nafisa na fadin haba mummy abi abin nan a sannu mana ai hafiz ba yaro bane balle ace anyi poising dinsa bai sani ba.
Kada ki dameni haka kawai a halaka min da saboda son kai nasan halin hafiz ba abu kadan ne zai kaisa kwance ba haka muka hade a kofan shiga dkin nasa badon na kauce ba mummy bangajeni tayi niyar yi a lokacin.
Ta shiga tana fadin boy meya sameka haka me tabaka kaci har haka ya faru ya bude idanunsa da sukai masa nauyi yace banci komai ba fa.
Kafin tayi magana su daddy suka iso suma nagodewa Allah dayayini mai tsabta don ko gida namu tsab yake sai kamshine ke tashi a ko ina yana kyali don gyara.
Ni kan ban shiga ba don ganin su daddy a dakin na tsaya falon mu muryan anty nafisace ta koma kirana na amsa nazo take fadin tun yaushene baida lafiya wai ?
Nima ban sani ba don nazata ko yayi tafiya don abincin dana aje masa nagami baici ba kuma naga motansa a waje shine na duba dakn na sameshi a kwance cikin galabaita yayi amai ko ina a dakin.
Sai naga duk aun bi dakin da kallo ganin ai a gyare yake to nace shine na taimaka masa yayi wanka na gyara wajen tea ma yasha gashi nan na hada masa ya kasa sha tun dazun.
Ai kaji zancen banda naka wa zai maka haka daddy ya fada yace wa zaice haka ya faru dashi a yanzu yadda yarinyar nan ta gyara ko ina kafin kowa yazo .
Koma waye ai zata gyara tunda mijin tane aidai san abinyi yanzu a taimaka tunda yana wanan yanayin kada a tsaya ana wani yabon wani game ciwo akwance gaban mu mummy ta fada.
Dole ko ki bari a fada don halinsa ake fadi waya sani ma ko wani tsiyar ya dirka wa cikinsa ya tashi halaka daddy ya fada yana kara waya a kunnensa ya kira likita yai masa bayani har kwatancen gida yace gashi nan zuwa.
Nan daddy ya kashe wayan yaci gaba da fada inda yake shiga ba nan yake fita ba dole mummy tayi shiru wanan fadan da daddy keyi ya nuna min sun dade da sanin halin da dan nasu ke ciki bawai bakon abu bane a wajensu ke nan.
Shigowan likitan sukayi shiru yazo ya a,aunashi ya duba komai yana masa tambaya kafin ya dago yana kallon daddy ya juya harshe yana fadin yasha wace bai saba sha bace tayi masa karfi ta sake masa re,action haka anyi arziki data kashe shi lokaci guda da bai samu amayar da ita din ba ai.
Ina jin hakan na sulale na fita zuwa falo ns zauna saiga hawaye dama ashe aikin giya nayi ke nan na tambayi kaina har tsawon yaushe zan kai ina wanan wahalan kwasan giya a gidan nan.
Ya Allah kaimin mafita ta alheri Allah kaga zuciyana ya Allah ka kawo min dauki ga wanan laluran sai gasu sun fito dukkansu dakin duk kansu rayukansu babu dadi a lokacin.
Likitan ya fita ashe ruwa ya daura masa don naji yana fadin a dinga lekasa ana ganin yadda tafiyan ruwan yake kada kuma ya danne hannun nasa ruwan ya tsaya.
Har kofa daddy ya rakashi yana mika masa hannu ya dawo lokacin daddy Enugu ke fadin daina kuka mana mama tunda an gane meke damunsa aiba kuka zakiyi ba yanzun kuma.
No daddy kukanta nasan kan abinda mummy ta fada matane cewa meta ba hafiz anty Nafisa ta fada Allah yada mummy din ta koma dakin duba danta lokacin.
Kamar ya maitaba danta wai meke damun Malkane don Allah ke nan tana nufin guba ita mama din ta bashi don takasheshi don bata sonshi kome ?
Aiko daddy yashiga fada don dakin ya shiga ya samu mummy din ya hauta da masifa yana fadin da badon yarinyar nan ba wayasan yana cikin wani hali ke kenan kwakwalwanki bai taba aiki bai iya lissasfo maki alheri ko yaushe sai akasin haka ?
Mummy din tace don na fadi hakan aiba karya nayi ba tunda komai na iya faru ba ai bincikene nakeyi don sanin hakan zai iya faru ko a hada kai da ita din ma .
Au ke naki tunanem ke nan baki tunanen danki dake shaye shaye ba zai iya shawo abinda zai illantashi ko to gashi shi dai shiya sha abinda yafi karfinsa .
Yarinyar nan idan baki ga kokarinta ba to kiyi shiru bai kamata tana iya kokarinta ba ke kuma kina hattaranta da bakaken maganganu haka ita ma din haihuwantafa iyayyenta sukayi.
Kuma suna kaunar abinsu yadda kike kaunar danki bar ganin sun kawar da kai akanta yanzu kawaici da kara suke muna kinsan halin garba ranan da kika kaishi karshe zaki raina kanki wallahi don kinsanshi sarai ba dadi garesa ba idan aka cinwa karshen hakkurinsa.
Nidai naga dole in tambaya yanzuma data fada maka din meye wanan ba makirci ba tunda tasan ba hakan bane ai sai ta kyale amma ta fadama don kaimin fada ko ?
Ehh don ko yarki ta fada ba ita ba inma hakan ne ki tuhumi nafisa data fada muna abinda kikace don ita bata fadin komai ba tace ita nafisan ta fada ko ai yar banzace mai ruwa biyu zata aika indai Nafisace.
Shgowan mum data samu labari ita da Dada sukazo shiya katse wa mummy fadan nasu nan Dada ke fada don suna takama hafiz dansune suka fito gida basu fadawa kowa ba ko ?
To suma yanzu sun zo don nice a matsayinta na kakata itakuma mum uwata sunzo su duba jikin mijin jikar nasu idan abin ya koma hakane anyi dace hafiz din yatashivtun lokacin da daddy da mummy ke musayar baki.
Jin abinda Dada ke fadi yssa yaja tsuki yana gyara kwanciya yace tana damunsa da surutun nan nata don Allah ta fita daga falo shi baison hayaniya don Allah.
Ja,iri yanzu da kaji sauki zakace hakan Amir ne ya haye gadon zuwa wajensa ya shafo kan yarom yana f??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????adin boy kaima kazo ka dubanine ?
Nan suka cika dakin suna nuna masa gata muna falo da anty Nafisa da take faman surfa masa zagi akan baisan ciwon kansa yana daukan alhakin mutane ji yadda ya tayar da hankalin yan uwa saboda iya shege kawai ?
Saiga matan daddy Enugu suma sun shigo duk na rasa me zanyi don gaba daya a rude nake don haka na koma na takure a waje daya ina tunane taya zai bar abin nan bayan ana nuna mashi gata irin haka ?
Ji yanzu yadda kowa ya taso yazo donshi koda kuwa sun san dalilin faduwan shi ciwon nasan zasuzone don kawai yana dan gata ga iyayyenshi.
Har yamma suna sintiri akansa nidai ina gefe daya idan ba nemana sukayi in basu wani abu ban shiga koda dakin har ruwan ya kare lokacin anty da mummy ne a cikin dakin tare dashi.
Nashigo kawo ruwan datace nasa masu nakawo ta hauni da fada haba dai keko ba mai zafi haka ba mana na juya don in mayar race idan naje na hado da cups in kawo na amsa har nakai kofa yace ke kawo ruwan ki aje zaiyi sanyi kafin na tashi ai .
Na juyo na dawo da ruwan na aje zan dago mummy na fadin jeki ki zo min da mai sanyi kada ki manta da cup mummy ku barta ta huta hakana mana ya fada duk saida suka kalloshi jin abinda ya fada din akaina lokacin.
Yes gani nayi tagaji da yawa ai ba wani abu ba don naga kun kalloni lokaci guda ya fada cikin rashin kunyanrsa ai mun sani amma da mamakine kana tausaya mata ashe hakan nan Nafisa ta fadi hakan.
Ban tsaya kulasu ba don nafahinci ba gadon kunya a idanusu don yadda suke abu haka kai tsaye gaban mahaifansu din na kawo masu cup din nashige dakina na dan kwanta.
Saiga anty Nafisa bayan magariba wai ciwon cikin ya tashi likita tace azo dashi asibiti suyi masa yan gwaje gwaje acan don haka zasu tafi shine tazo ta fada min.
Kodana fito har mummy tafita dashi ko ina tsaye kofa sukaja mota suka wuce da sauri takowa nayi zuwa ciki ban zauna ba dakin nasa na nufa na gyara ko ina har bayi nafito kafin nadan zauna.
Har sha biyun dare basu dawo ba basu kuma kirani ba balle nasan halinda suke ciki a can din ganin dare yayi yasa na kwanta abu ga mai gajiya sai barcine ya daukeni.
Muryan mummy dake fada dani sun dawo suna horn ban bude gida ba yasa na falka a lokacin ina masu sannu da dawowa tabi bayan danta dake rangaji zuwa daki.
Banyi gigin binsu ba dakina na koma har barci ya fara daukana naji muryan anty nafisa tana fadin kwanciya kikayine sis ba zakizo dakin mijinki ki kwana dashi ba ?
Ido na bude ina kallonta tace mummy sun tafi ni zan kwana a nan daku sai Dada da zasu turo muna da safe hafiz dan iskane saboda tabara yana son kashe kansa.
Wai abokinsa salis nefa ya bashi abu yasha da baisan kansa ba kuma shine yake wanan wahalan haka ai gobe ya kara tunda ya zama dan iska da kyar aka samu ya amaye abin duka tunda jininsa bai daukan karfin abin.
Ki tashi kije can ki kwanta ni sai na kwana a nan don dare da dai kin barni anty mu dinga yi muna lekasa zaifi tace mijin naki komai haukansa aiba zai koreki ba yana cikin wanan halin yanzu.
Dan shiru nayi hannunta naji akafadana tana fadin hakkuri zakiyi kije mijinkine fa kuma kowa yasan kinyi kokari akansa don wallahi danice ko kula dan iska ma ba zanyi ba .
Amma sai gashi kin tsaya kin kula da abinki ai yanzu dai mummy ta gani ita dashi da suka gaza gane manufar daddy akan hakan to yanzu sun gani.
Da ace wata barece ke aida zancen nan yanzu ya gama fita agari amma sai gashi iyamu na gida kawai muka san da wanan zance koshi ba kowa yasani bama.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3?? 4??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Kar tace naki zancen ta takaini gaba haka na daure na mike tsaye na jawo hijjab din sallah na da counter nafice daga dakin nayi niyar in kwanta falin mu sai naga tana iya fitowa ta ganin wajen .
Dole haka na doshi kofan dakin gaba sai faduwa yake ina anyana abinda zanyi a zuciyana da hasken wayana nayi amfani don dakin da duhu lokacin.
Hakan yasa nagane mummy bata bar gidan ba saida ta tabbatar da dan nata yayi barci sosai a lokacin kafin ta tafi takoma gida.
Har da tunane nayi araina nace aida ta karasa kwana nan din yafi min barin anty nafisa da tayi damu din don gashi yanzu tana son taja min wani aikin kuma bayan wanda nasha da rana.
Dogon kujeran dake dakin na gyara na kwanta a sama na dunkule cikin hijjab dina ina dan danna counter din na tare da hailala abakina.
A haka barci ya fara awon gaba dani a wajen barcin ya soma fisga na naga gilmawan mutum kamar aafalki hakan yasa na dan zabura a tsorace ashe shine ya shiga bandaki na sauke ajiyan zuciyana koma na kwanta.
A takure dai na kwana a dakin don ina jin kamar aman giyan nan da yayi har yanzu yana dakin

33 / 105