DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   48 / 105

141K to 144K   out of 313.1K words

nace bansone yaya sallon din nan yanzu warning akeyi kansa don zafin nan na damage din brain saboda weather din yanzu ba irin na da bane cam baya yana cikin abinda ke kawo cancer da sauri ga mata yanzu.
Ohh amma baku fadakarwa mana ku malaman lafiya nace munayi yaya basu dai jine kawai don sun daukeshi ga wayewa suna ganin kamar cigabane.
Bandama yaran yanzu ina wani cigaba cikin wanan abin kina yar musulmai dake dole dai ana yowa kiyi alwala kiyi sallah shike nan fa ya tashi abanza duk wahalan .
Daidai lokacin waya ya dauki kara na dan jawo ina dubawa ganin mairoce yasa na danna received da sauri ina fadin hello tace ke ga mai abayan ya kawo muna yace 50k nace what gaskiya badani ba commom abayane har dubu hamsin ?
Magana ta fara zazzaga min ina murmushi can nace mairo nace maki ba zan iya saya ba don Allah abinda za a saka dai rana zanje kashewa kudi haka mai yawa .
Yadda na kali wayan zaisa kagane wace muke magana da ita lokacin ta kashe wayanta nake fadin mum wai abayan waliman dan anty hauwa fa ?
To ai kin gama magana tunda kince bakiyi saidai hauwa tafi karfin hakan gareki kin sani don yarinyar nada kirki sosai wallahi tana da mutunci da ita da mairo nan duk cikin kawayenki sunfi kirki sai wanan dayan bafilatan da kuke tare.
Lokacin ya mike yana fadin mum ni zan fita nace ko a kawoma abincine yace No ki bari da wanan kai naki mai yawa da aka kama zaki tashi debo min abinci kuyi abinku kawai ya fada.
Yaci bayan matarshi ta dawo dama kwana biyu ai bata gidanne yasa kike yawan ganinsa nan nace tafiya tayi ashe hannunsa ga aljihu yana ciro kudi mum tace tana dai gidansu tayi fushi.
Takowa yayi baice komai ba ya aje kudi a gefena yana fadin ga kudin abayan da kudin kitson mum kada ta turaki gun zawarawanki roko na biya kudin kada aje gurin wani roko.
Da dai yafi maku sauki don na fara gori ke nan a yanzu sai rai ya baci an daina zaunar dani yin kitso nace haba mum yanzu dai ga yayana ya biya dai sai a dinga mi kullun tace wace ni ?
Kafin in dago kai ina mashi godiya har yakai kofa cikin daga murya nake fadin yaya nagode ban koyi godiya ba kafita ya fice baice komai ba nan bayan fitanshi mum take ban labarin tafiyan matarshi gida har dawowanta.



ZAINAB IDRIS MAKAWA

DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

4?? 8??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Saida na gama komai na al,adan kwaciyana irin cin abinci, shan black tea dana koya wajen hjy mum na mike nashiga bayi na watsa ruwa nafito na zauna na dan shafa mai mai,laushi da kamshi a jikina kana na dauko wankakan rigar barcina na dan fesa mai turare nasaka ajikina.
Falon na koma mum tana zaune tana bitan karatunta na litattafan addini da takeyi na kwar da duk wani abin daya dace akai kitchen afalon nakoma dakina na haye gado.
Waya na jawo ina dan dubawa kafin naga miscalled din anty hauwan mu nasan Mairo yar zafi ta fada masu zancen nace bani sayan abaya din yasa ta kirani nayi murmshi ina kaiwa kwance.
Tare da fadin abu ba saukan alkur,ani ba kawai don yaro ya gama haruffa zai fara al,kurani mai girma shine da wanan karyan haka na fada ina juyawa.
Idonane ya sauka kan kiran ya Addel shima misalin karfe takwas da yan mintuna na dare don haka ba bata lokaci na daga waya na kirashi nima lokacin goma na dare ya dan gwauta da minti bakwai ban damu da hakan ba.
Don a zatona ko wani abu yake so a wajen mum yasa ya kirani lokacin ina kira yana dauka da sallama cikin muryanshi mai tsada da jan aji cikin husky voice dinsa na maza daba ko wani namiji kedashi ba yayi min sallama.
Na karba ina fadin ya Addel sai yanzu naga miscalled dinka muna falo nida mum yayinda shi kuma yake fadin dama zan tambaya ko kungama kitson ne ai ?
Dan dariya na sake nace angama tun dazun ai yaya amma nasha korafi kafinta gama min yace don't mind tunda anyi kuma mun biyata abinta aishine dai na fada abangarena.
Sai naji yace dani kotace a kara mata kudin ne nace a,a wallahi dariya tayi tana fadin ko gobe in bamye kai indai za,a bata kudim kitso haka ?
Wani shu,umin murmushi naji ya sauke abangarenshi kafin yace mum ke nan wai kinsan me zeey nace a,a yaya ?
Wallahi duk na shigo na samu kuna hakan da mum wani irin dadi nakeji a raina mara misaltuwa hakan yakan man dadi sosai sai inji kamar ku dawama a hakan da nake ganin ku.
Lah nida mum ai mutu karaba badai mutum ba Allah ko ya fada a bangareshi nace to yaya waya isa ya rabani da uwata kuwa a yanzu.
Yace aure mana zeey ko gida zaki tabbata da uwar naki ko yaushe ni dai yaya ban son zancen aure gaskiya ku barni haka yafi min dadi a rayuwata na fada cikin shagwaba.
Wanan kuma ai kinsan abune daba zai yuyu ba don ko zuwan nan saida baba yai min magana akan zaman ki haka ba aure na basa hakkuri don karatun ki.
Kyale baba don Allah su da anyi magana shida inna sai sucewa mutum aure ni kuma auren nan ma wallahi ya fice min a raina baki daya yanzu.
Ke yar gidan mum banda dai cika baki da yanzu baba zai matsa ki kawo miji nasan zaki gabatar maida bazawarin ki ne da sauri koda yake dama akwai ai tunda hafiz ya dawo yanzun yace matarsa yake so.
Mahaukacine dan maye baida hankali na daukeshi ko kare ya cijeni me zanyi da wanan mutumin a yanzu don Allah mu bar zancensa don har naji farin cikina ya gushe a yanzu.
Au sherin da zakiwa dan uwan naki kenan kuma nace shida yai min fa yaya sai anjima a gaida anty Aisha na fada cikin karfin hali don ko raina har ya baci din.
To shike nan ki dai saka mayafi babba kada malam nan naku na jami,a masu kallon mata su rigani gani ganin kitson kanwata nidana biya ban gani ba.
A lokacin naji muryan matarsa na fadin kaidawa ke waya Aliyu cikin daga murya nayi saurin kashe wayana cikin fargaba da tsoron hakan don nasan akwai wata masifan ke nan kuma again.
A can gidansu kuwa kai tsaye yace mata wakika sani zanyi waya da ita yanzu bayan ke da zainab nake waya mana ko wani abune yana kallonta ido da ido.
Tace munafuki Allah ya tona maku asiri dan iska kawai dan akuya mai barbaran kanwarsa kai bakaji kunyan hakan ba har kana fada min kai tsaye zainab.
Dama ba ragowa bace ita ragowan dan uwanka kuma dan uwan nakama dan wanda ya rikeka Allah ma,aiki shine zakai masu butulci yace haramun ne hakan in haramun ne aurena da ita ki fada min inda aka fada.
Kadaiji kunya wallahi Aliyu duk matan nan dake cikin duniya sai akan wanan yarinyar zaka buge nina rasa meka gani a jikinta har ya rudeka haka ka makance lokaci guda.
Yace abinda kika haska min shina hango agun zainab Aisha natsuwa hankali tarbiya da sanin mutuncin kanta tace karyane wallahi karyane wanan .
Waye baisan tsiyan da suke shukawa ba a wajen karatun su na likitacin da kake prouding tanayi yanzu da kilama shiya rudeka ka fada sonta ayanzu.
Wanan ma in nayi hakan aiba laifi bane ko auren mace mai ilimi dana auri wace taje turai ta gama watsewanta tanawa mutane karyan karatu ashe bata karanto komai bafa kuma na zauna da ita a hakan.
Haba kamar ji tayi kamar ya watsa mata ruwan zafi a jikinta ta fara fada tana fadin bansan kai mayaudari bane sai yau don ka samu wata yar iska kake kokarin bata min suna.
Babu dadi bata suna kike batawa yar mutane suna magana kikayi na baki amsa daidai da zancen ki meye abin hasala ciki tunda bayani akeyi na tuna makine idan kin mantane yanzu ai.
Ranan dai fitina suka kwana sunayi a gidan nasu gar washegari suka tashi dashi dole ya fito ya bar mata gidan kan masifanta don baison ya biye mata yakai ga aikata abinda zai jawo masa cikas ga lamarinsa.
Kasuwa yaje ya samu daddy a nan ranan ya zauna yana taya daddy kasuwancinsa tare da kara fahintar cigaban da shagon tsohon ke bukata a yanzu don juyawan zamani dole sai da abubuwan zamani ga harkan kasuwancin yanzu.
Daddy yaji dadin hakan sosai yadda har yanzu sukan bushi iska shida ya Nasir su lekoshi shago suyi harkan kasuwanci dashi wani lokaci kuma ysna karuwa da hakan sosai idan suzo shagon don suna cikin irin mutanen da hannunsu keda albarka kome suka taba sai anga albarkan abin a rayuwa.
Nan suka zauna yana ba daddy din shawaran abinda ya hango shagon nasa yana so a yanzu a ciki harda gyaran shagon a fadada masa girma don ya matse suna wahala a hakan da suke.
Sai yamma ya baro shagon kai tsaye gidansa ya nufo har lokacin tana kan zancen bai kulata ba ya shige dakinsa ya rufo yasa key ya shiga wanka ya fito ya shirya zuwa massalacin unguwan da yake bi sallah in yana gari.
Bai shiga gida ba daya dawo kai tsaye ya shiga motarsa ya fita gidan gidansu Aishan yaje yakai karanta daya fito ya dan biya wajen abokinsa Abdul sun dan jima tare kafin ya juyo ya dawo gida don haka yinin ranan bai leko gida ba wajen mum ke nan.
Ina dawowa wanka nayi nashiga kitchen na hada muna abinci sai bayan magariba na gama na hadawa daddy nasa na fito nakaiwa Dada nata lokacin mum tana daki don bata tashi idan batayi isha,iba bayan magariba.
Na fito na nufi part din a daidai part din da daddy Enugu yai zama da iyalinsa kafinsu koma gidansu a nan muka hade dashi da farko bansan dashi a wajen ba don kaina na kasa ina gyara rigan jikina alokacin.
Kamar ance in dago kai yana tsaye yana waya da alama daga part dinsu ya fito don yai waya anan din haka ya zubo min manyatattun idanuwansa sai kace tsohon maye ina dagowa kawai na dora idona akanshi yana tsaye yasa hannunsa a aljihu yana waya.
Kamar in koma baya don hangoshi da nayi a wajen amma saina dake naci gaba da karasowa inda yake don dole ta nan zanbi in shiga part din Dada din na karaso kusa dashi ya sakar min murmushi a fuskanshi.
Naja masa tsuki mai karfi ta yadda zai iya jina saboda na dade da sanin ya tsani hakan ga wani yai tsuki a kusa dashi hakan na kona masa rai sosai.
Madadin inga bacin ransa wanan karon sai naga sabanin hakan agaresa ba bacin rai saidai murmushin daya kara sakar min alokacin na kawar da kaina daga bangaresa da sauri.
Muryansa na tsunkaya yana fadin zainab wai don Allah ya kike da rikone haka ke baki yafiyane wai kan abinda akayi ya wuce abaya na fada maki a shirye nake yanzu dana baki ko wani irin hakkurine ma.
Har sau nawa kikeson in baki hakkuri jan abinda ya faru a baya tsakanina dake amma kinki ko saurarena mu sasanta a tsakanin mu.
Haba zainab ya kamata ki tausaya min kan halinda na tsunci kaina a ciki yanzu game dake mana nasan nayi kuskure amma kuma yanzu nayi nadaman hakan aure nake so dake.
A fusace na juyo gareshi ina fadin ya hafiz ke nan daka tsaya matsayinka na yayana a yanzu zaifi ma mutunci a wurina yanzu don ko da can da aka tursasani na aureka bisa umurnin iyayye ban taba jin digon sonka a zuciyana ba.
Balle yanzu da kaina ya waye nasan me ake nufi da soyayya ko kusa baka cikin jerin kalan mazan da zanso zaman aure dasu a rayuwana yanzu.
Don haka abadan ba zan taba jin ko digon sonka a zuciyana ba balle har zancen zaman aure ko wani abu maka mancin hakan yazo ya shiga tsakani dakai.
Ka dubi kanka ka dubeni don Allah nayima kama da tsaran aure kai kanka kasani zainab dake gabanka yanzu ba zainab din da bane don haka ka kama kanka dani don Allah.
Don ni zainab a yanzu sai tsadaden namiji wanda yasan ciwon kansa yasan darajan ya mace dana iyayyenta ba namijin dako iyayyensa baisan darajan su ba balle na mace.
Aiko take idonsa ya kade lokaci guda kamar yasha abin nasa yana fadin ke ni kike fadawa wanan maganan ke wacece me kike daukan kanki a yanzu ?
Oho dai ina son ka sani wallahi babu wanda na tsana a duniyan nan bayan kai hafiz don tsanarka da nakeyi banko son in bude ido inganka a duniyan nan don kallon ka kadai yana sa min wani irin kunci a ziciyana.
Wani irin yunkurowa yayi yayo cikina na kwasa da gudu na fada falon Dada ta mike tana fadin lafiya wanene me kika gani ko wani ya biyoki ne ?
Nace ya hafiz ne mana
Tace hafiz kuma garin yaya zai biyoki haka da gudu ko yayi haukane wai dama ina kule da take takensa gidan nan mara kunyar banza kawai ai Allah ba azzalumin kowa bane dama.
Kasake yayi daga kofa yana sauraren Dada din dake fada ga wani kunci da yake ji a zuciyarsa game dani tunane barkatai yayi a wajen kafin ya koma da baya ya wuce zuwa part dinsa kai tsaye cikin bacin rai.
Ranan tunane barkatai yayi a zuciyarsa game da maganganun dana fada masa din don bai taba tunanen hakan daga gareni ba wai yana me shawaran ya tunkari Dada da zancen yaga karshe na.
Sai kuma yayi tunanen irin lalashin da Dada tayi mai ya mayar da aurensa lokacin yaci mata mutunci sosai a waya don haka yanzu yasan da wuya Dada ta kama masa wasan dadi kan zancen.
Har cikin part din mu Dada ta rakoni tana yanka fada hjy mum ta fito tana fadin lafiya hajiya kedawa kuma tace dan banzan nan hafiz mana ko yasha abin mayen nasane ya biyo maki ya da gudu falona.
Hafiz kuma mum ta tambaya cikin mamaki kafin ta kalloni tana fadin meya hadaki da hafiz kuma mama cikin tsureni da idanuwanta tana son amsa daga garen????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? i.
Nace nima bansan dashi a wajen ba zan kaiwa Dada abinci nagansa yana waya shine yace wai in tsaya da naki shine ya biyoni da gudu ni kuma na sheka na shiga falon Dada din.
Dada tace kinji dan banza har ya kara maki ya wajen shanshancinshi da wani yace ya sakeki tun farko yanzu ya dawo yanawa mutane iya shege a cikin gida.
Zan fadawa ubansa ya dauki mataki a,a hjy ki bari zan tsawata masa kan hakan don yanzu dakin fada wani sabani kuma sabo zai shigo tsakaninsa da Alh rayuka suzo suna baci karshe.
To shike nan amma idan ya koma nida kaina zan fadawa ubansa yaja masa kunne dan banza mara kunya ya kita a baya shine yanzu zaizo yana sun,sunanta waje ko don yana ja,iri.
Nikan daki na nufa ban tsaya ba naje nayi alwala nazo na tayar da sallah koda mum ta leko ta samu ina sallah ta koma falo ta zauna a lokacin.
Saidana gama nafito na sameta zaune nake gaida ita da wuni na wuce kitchen na dauko abinci zuwa falon na aje agabanta har saidana gama hada komai na bukata na samu waje na zauna a genta.
Lokacin ta juyo take fadin uhum lalai sai yanzu na tabbatar da namiji baida isasshiyar kunya nayi saurin kallo inda mum din take tace hafiz mana ina yaga kunya kuwa.
Wai yau hafiz ne zai dawo yana binki haka to uban wa yake nema yanzu a gareki don yaga kinyi clean ko yanzu bai dauka zaki taba zama haka ba a rayuwansa shine haukan mazansa ya motsa ko ?
Nace wai tatsuniya ke nan mum ni me zanyi dashi yanzu don Allah don tatsoniya naga yanayi a yanzu nan na kwashe yadda mukayi kaf na fadawa mum din don ban fada agaban Dada ba lokacin.
Mara hankali kawai ya mayar da kowa irin uwarsa ko duk yadda yake so haka za,ayi mai wawa ya manta da cin mutunci mutane da yayi abaya harda fadin ai ina da diya maza idan na isa in hadaki aure da daya mana acikinsu.

48 / 105