DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   85 / 105

252K to 255K   out of 313.1K words

dakata muje gaba daya sai na kalleta tace ina nifin duk da yaran kona zauna nan hankalina ba zai kwanta bane .
Gaskiya ta fada hakan yasa muka cicibesu da barci na rufe part din muka dauki hanyar gidan daddy bayan na fadawa su Aina a gurgije..
Nasan nayi gudu don safiyace sosai babu wani cinkoso a lokacin don hakane muka samu isa da wuri gidan inda muka samu gaba daya suna part din nasa hankali a tashe.
Gama zainab nan ta iso anty Nafisa dake zaune ta fada na karasa da sauri gabanshi a daidai lokacin da mummy ke fadin aida ganin wanan abin iskane ko jifa da aka hada da iska .
Tsayawa nayi na dan lokaci tare da kura masa ido na fahinci yanayinsa da kyau wayata dake rike a hannu na na fara kira na juya ina fadin .
Hello Doctor habib ya amsa duk suka bini da idanu na dan fita daga dakin nayi magana dashi yace ga mota nan za a turo muna yanzu bayan nayi kwatancen gidan.
Kafin na juya na koma cikin dakin nace mummy a dauki files dinsa na asibiti da yake zuwa awo dashi don yanzu zamu tafi dashi asibitin nasan kuma zasu kwantar dashine a can.
Ya akayine zainanb mum dake zaune ta rike hannunsa da yake dan son ya motsa a lokacin na dago nace mum a bari muje can su kara dubawa kamar ya samu koda yake bari dai muje can din muji me zasuce akai ?
Don Allah a dan rage a shiryashi kafin su karaso din na fada cikin sanyin murya don kowa har yaran daddy enugu suna cikin dakin hankali tashe.
Daddy jallabiya zaku saka mai kawai son ko anje can za a cire ina son don Allah zan masa yar allura da zai dan bashi relief numfashinsa ya dan sauko.
Wanan abu dai za ai gangancine don da ganin wanan aikin iskane mutum ga idonsa haka a bude don Allah za a kai dai asibiti a karasashi a can.
Jikinane yayi sanyi jin abinda mummy din ta fada sai naji Dada tace ta yaya za a bar mutum haka gida kamar wasu jahilai damu mu godewa Allah daya bamu Abu cikin mu yau ai.
Ballema hjy haka kawai mu tsaya aikin jahilci bamu san abinda yake damun mutum ba a barshi haka a gida tunda kikaji ta fada asibitin kawai zamu wuce dashi don ta fahinci abinda ke damunsa saidai halinsu na likitocine basu fadin abu kai tsaye.
Ajiyan zuciya nafisa ta sauke kafin ta mike zata fita ta kalleni cikin turanci tace dani follow me sister nace OK bari nayi masa alluran inzo.
Na ciro yar karaman alluran dana dauko don dama hasashena ke nan yadda yaya ya fada na dan gyarashi kamar kibtawa da bissimillah na dan dura masa basu ko kula nayi alluran ba don mummy dake mayarwa daddy enugu da Dada martani a cikin jahilci.
Sai ranan na kara tabbatar da mum jahilaci zaman birni ashe bashine wayewa ba wayewama yana amfani da ilimine wani lokaci.
A nan na dago nace don Allah a dan rage kadan zai samu lafiya insha Allah ko anyi wani abin tashin hankaline a gabansa ?
Ina kallon Dada nake tambaya tace lafiya aka kwanta dashima jiya ai muna nan ana murnan zuwan hafiz dashi gaba dayan muma a nan muke tare a falon.
Ok yaya hafiz yazo ke nan na fada a raina nan naji gabana yayi mumunan faduwa lokaci guda karan jiniyar motar asibitin ne ya karde haraban gidan namu suka shigo da nurses maza biyu sai driver da abin dauka tare da anty Nafisa.
Daddy enugu naji yace ikon Allah numfashin nasa ya koma daidai yanzu cikin damuwa nace eeh daddy insha Allahu zai sauka daidai fiye da hakan ma tunda an masa wanan alluran ai.
Nurses din ke gaidani na amsa nake masu bayanin yadda zasu daukeshi da haka muka fito dashi motar daddy ennugu yashiga tare dasu.
Mum ta rude a lokacin nake fadin dawa zamu tafi a cikin ku da sauri mummy tace dukkan mu mana tunda ba mai zaman gadin gida jiran gawon shanu.
Ikon Allah muje a motana don ina son na rigasu isa na fada a cikin sanyin murya don na fahinci hakan dataga daddy din bai hirgitata ba a lokacin don tafi yarda da aikin tsibbu inda zata samu kudi ya shigo mata.
Sai bayan mun shiga motan ne mun kama hanya mum tace shiya kiraki ko nace ehh mum ina yaran suke nace suna nan cikin gida gaba dayan mu ai mukazo hankalina yana kan hanya da nake tuki a lokacin.
Nifa na shigo inga koya tashi yayi sallah shine na samesa a cikin wanan halin mum ta fada nace damuwace ba komai ba mum akwai abinda ya bata masa rai ya kwana dashi .
To mudai lafiya muka kwanta dashi inma akwai dai bamu da labarin hakan saidai idan yanzune zai fada a san meyake damunsa din aji.
Mummyce ke fadin hakan gareni don dani da ita da dada ce a cikin motan nawa daddy ennugu ya hana saura zuwa duk da nasan zasu zo din su samemu a nan suma.
Ba wanda ya kara magana a motar ga baki dayan mu sai ita dake kokarin gwaleni tako wani hanya a lokacin muna isa aka karbeshi muka shiga dashi ciki don gata.
Sai lokacin na samu kiran baban mu ina sheda masa halinda suke ciki shima hankalinsa ya tashi sosai haka kuma nakira hauwa tayi min report kan matsalan da nake ciki.
Bayan aune aune da dabarun likitoci aka bashi gado don hannunun nan da yake son dagawa ya samu matsala dole sai anyi jiya ko Allah zai taimaka ya samu ya dawo masa har lokacin ba zaice ga wanda yake a kansa ba.
Saida na tabbatar da dakin ya hadu na samu fitowa can na hangosu inda suke zaune a cikin damuwa daga gefensu na hango yaya Hafiz tsaye dashi da Nafisan su suna magana.
Hakan ya hanani karasawa sai waya na daga na kira mum ina sheda mata su shigo gani nan in nuna masu inda yake can ta dago kai ta hangoni shine ta mike tana fada masu.
Suka karaso nayi masu bayani a gurguje nabar wajen na koma office din likitocin na dan zauna kafin a tura a kira daddy da anty Nafisa su mukayiwa bayanin abindake damun daddy din .
Hankalinsu ya tashi sosai a nan likita ya roki da a rage yawa don Allah abar ko mutum daya ko biyu da zasu tsaya ya nunani yana fadin ga doctor ktn zata bada duk gudun mawar da ake nema a nan insha Allah.
Hakan yasa daddy ennugu da babana daya iso zama sukace su koma gida don likita yace a rage basa son mutane da yawa a nan din don haka ku barmu nida garba zamu zauna.
Sun san halin daddy ennugu dama mum bata jaba ta mike tana fadin tunda ba,a bari ashiga sai zuwa gobe zaman me zamuyi a nan kuma ko ina dai dama adduan mu yafi bukata a yanzu.
Nikan babu inda zan tafi nan zan tsaya don me zan koma gida bayan Alh yana nan cikin wanan halin kiyi ta zama ashe da mutuwa yayi yau kema zaki bisa ke nan daddy enugu ya fada cikin haushi.
Banji bakinka ba amma ba inda zani gaskiya ta kara fada ina zainab take ta kaimu gida mum take tambayan daddy din yace tana ciki wurin likitan suna magana.
Ai dama nasan hadin baki akayi ba kowa ya kawo wanan shawaran ba sai zainab din ta kitsa hakan don ai muna wullakanci to ba inda zan tafi dama dan tallaka bai iya samun waje ba ai.
Kada ki kawo muna zancen banza a nan malka muna cikin wanan tashin hankali haka a yanzu ke in ga tunane har kinga wurin irin wanan magana a yanzu a nan Alh yana cikin wanan hali haka zainab ko tayi muna komai don an nuna muna gata da zuwan mu an karbe mu anyi komai donta kuma.
Wai yayane haka baba daya karaso yake tambaya don ya kebe yana waya da inna a lokacin akan su dakata zuwansu ba a ganin daddy din ko sunzo.
Daddy enugu yace maganan banza take son fadawa mutane kasan ita bata girma don kawai sunce a rage a koma gida nace su sutafi su barmu a nan nida kai ga su bala kuma ,,,,
Hakan yayi ai zaman me zasuyi nan tunda gamu ita hjy dai a barta don hankalinta zaifi kwanciya idan tana nan tana ganin halinda ake ciki din da cewa Dada.
Nafa fada maku babu inda zani a yanzu wai menene kuma don Allah ance ba,a son hayaniya haka kuma kuna daga masu murya haka Nafisa data karaso ta fada.
Nan daddy enugu ke fada mata meke faruwa ita da hafiz din sukace me zaki tsayayi a nab mummy kowa fa nan a cikin damuwa yake abarsu suyi aikinsu mana.
Lokacin bala yayi magana an kirani nace ace su jirani wajen mota gani fitowa nan wasu nurse suka iso suna fadin don Allah malamai ku matsa daga nan baku ganin halinda majinyata ke cikine kuna daga muna murya.
Donshine fa bamu yarda azo asibitin nan haka sai time din ziyara yayi don doctor zainab ce da wallahi ko nan yanzu bamu bari ku shigo haka.
Sam bai gane wata zainab ake zance ba a lokacin saida suka kamo hanya uwar tace zainab face ta saka a mayar damu gida nasani wace zainab kuma mummy don Allah dai banson haka ki bari aji da abinda akeji yanzu yana zaune gaban motan yana jin yadda suke zance sai can yace wai wata zainan dai ?
Zainab din mu mana tanan gida nafisa ta bashi amsa ganin bai gane ba tace zainab dai na gidan baba garba matar Addel a yanzu tsohuwar matarka.
Wanan dogon kwantacen nakifa haka nagane mana tunda kikace ta nan gida kina min wani kwatace hardani a ciki matar Addel dai zakice to nasani ko baka gane bane.
Mum don't try it again don Allah komai dai a bisa a sannu shina gani amma har yanzu mummy bata kaunar yarinyar nan akanka wallahi hafiz duk irin kokarin da mutanen sukeyi akan mu.
Da yanzu zance tazo ga mummy wani abu ya sameta duk abindake gabanta bari zatayi tazo to shine me ba zan taba son wanan yarinyar ba kema kin sani.
Nasani mummy amma ki barwa cikin ki hakan don Allah idan na fitar me zatayi min ko wani nata me zaiyi min mummy wallahi na rabaki da zeey a yanzu kema kin sani.
Ita harwa take kome ta zama a rayuwa inba ku da kuka maida kanku haka ba ace dukka yara ba inda zaka dafa kaji sanyi ke kinki aure shi kuma wanan ya jawo muna tabara wai mata mata macen kabila ?
Kabilan ma kuma yarniya kafira da bata sallah kuma dai mummy ina son abina hakana tunda tana sona wataran zatayi sallah ai idan muna tare.
Kuka ta saka masu a motan inda take shiga banan take fita ba fada sosai takeyi dasu tana masu kwatance da yaran mum a yanzu.
Ni wanan ke kikasawa kanki mummy dama Allah ai baiyi daidai ba tunda ban hada kaina da Addel donshi komeyasa a gaba sai yacin ma abin ta katseshi da fadin kaine mashiririce da baka son kaga ka zamo wani abu a rayuwa ko ?
Har suka kai gida haka a hargitse wanan bacin rai yaja mata ciwo a lokacin don ta koma jiki ya tashi sosai sai ji mukayi da ance itama mummy bata da lafiya ai.
Yaya ya iso missalin sha biyun rana asibitin ya nufa sai su baba ya samu sukai masa bayani kamar yadda likita ya fada masu sai azahar yabar asibitin kai tsaye gidan daddy ya nufo don munyi waya na fada masa muna gidan wajen mum don musan tana cikin damuwa alokacin.
Bayan mun gama waya mum ke fadi dada sai kukaji hafiz yazo na kallo mum ina fadin inba dazun nan ba wallahi bansan yazo ba mum.
Aikuwa kwatsa muka gansa ya fado muna kamar daga sama kowa yayi mamakin ganinsa ai don ba wanda yasa rai da zuwansa don banga tana irin rawan kan da takanyi ba idan zaizo da.
Ban raba daya biyu ganin hafiz din ne yadda ya koma ya jefa Alh cikin wanan halin rashin lafiyan yau don ko kai bari dai ko uwar taji zafin yadda ya shigo haka a jiya.
Haba dai sai kace shi kadaine dansa da daddy zai wani damu har hakan sai naga mum tayi murmushi tace dolene zainab don shi suke saka ran zai zamo kamar mijiki a gidan nan.
Kinsa Allah ba ai masa dole ai shike hissabinsa yadda yaso dolr yanzu suji zafin hakan mijiki ba karamin abu ya gani ba a gidan nan.
Sallaman yaya din yasa mukai shiru aka koma yi masa sannu da zuwa yana amsawa a gajiye ya samu wuri ta zauna tare da kara gaidasu mum din daga nan suka kama zancen daddy din.
Nake fada masu gaskiyan abinda likita yace ke damunsa budan bakin mum sai cewa tayi inma wani abune tsakaninshine da wa yancan yaja mashi hakan.
Amma kinji munafuka yanzu wai bata iya barin asibiti kota zauna a gida bayan Alh na cikin wanan halin ko inta zauna wata uwar zata tsinana masa oho ?
Mikewa nayi ina fadin a kawoma abincine don mun samu mama ta dafa abinci nan mama ke fadin keko dai aida ganinsa baici komai ba an taso da tashin hankali tafiya bana dadon raiba akayosa.
Nashiga kitchen na hado masa abincin na kawo masa har lokacin yaran suna leke a jikinsa mum tace karbesu yaci abinci mana .
No ta barsu kawai bama wani ci zanyi ba ai zanje gida indan watsa ruwane in dawo ya fada aiku kuka saba masu da jiki ko yaushe yara na leke daku a jiki.
Ikon Allah meye nako a ciki yanzu mama ta fada mum tace me kuwa yaya ban dai iya ganin nama jan karene ai dan Allah diba makin ka fara ci ka tsaya kana basu.
Yakai abinci ga baki kafin ya dago yace mum ashe hafiz yana garin nan kun hadu ke nan ta tambayeshi ?
Yace No yanzu dai Nafisa ke fada min da zan shigo nan ta soma bashi labarin yadda yazo shima a raina nace shidai kishi baya tsufa ke nan a wajen mata duk da mum nada dama amma wani lokaci saita maganta
Ya danci abincin ya mike yana fadin zai tafi gida nan mum tace tashi kibi mijinku kije koki dan huta gida a barsu wanka kawai zanyi in fito ya fada .
Me zasu tsaya yi kuma ku dai je gida hakan yasa muka nufi gida gaban dayan mu har mama din son bata yarda ta zauna wajen mum ba ita.
A mota mama ke ta kara masa bayanin komai nidai ina kurum bace komai ba a lokacin har muka isa mun samu aina ta gyara gidan tsab kamar kullum tayi muna sannu da zuwa da yaya mai jiki nace da sauki.
Dakinsa ya shiga nabishi na hada mai ruwan wanka kafin in fito zuwa dakina nima wanka nayi na tsaya gyara jikina lokacin ya shigo dakin nawa yana fadin.
Zainab waya bude daya part din can nagansa an shiga ba yarda na barshi ba waye ya shiga cikinsa bayana ?


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

8?? 5??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Ashiru nayi cike da mamaki tare da jin haushin tambayan dayayi min din na rainin wayau a gareni ta yaya zasu shirya da matarsa bai fada min ba sai ganinsu nayi kwatsam a gidan yanzu ya dawo yana tambayana kuma.
Jin shirun da nayi yasa ya kara maimaita tambayan cikin bacin rai yace bakiji me nace bane waya bude dayan part din nan ya shiga bayana ?
Nikan ina ruwana da wanan sashen kaje ka tambayi mai part din mana ita da kai daine kuke da key din wajen ai.
In tambayi Aisha kike nufi nace haba yaya ta ya zanje in bude wanan part din haka kawai me zan nema a ciki matarka dai da yan uwanta suka bude basuko shigowa gidan nan bada sanin kaba yaya?
Suka bude ya maimaita tambayan suka budefa akan wani dalili zasu shigo min gida haka kai tsaye ba tare dana sani ba har su shiga basuyiwa mutane magana

85 / 105