DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   75 / 105

222K to 225K   out of 313.1K words

Nice kuma malama yau yaya nasan ka sani kawai dai so nake mu kiyayye kawai duba abinda kikeyi yanzu don anan zan karya kada ki bari ya kone ya fada yana juyawa.
Ina fadi cikin mamaki anan kuma yace ehh ba tare daya juyo ba yasa kai ya fice ganin hakan yasa na dan sauya abinda zan girka a ranan na dan kara mai amarshi kadan.
Nagama komai na shiga nayi wanka har lokacin ina mamaki wai a nan zai karya yace to ina matarsa da zata barshi yazo nan wajena ya karya ai yanzu dai gamu gani na fada a rai don nasan wasa yakeyi.
Saiko gashi na fito daki na sameshi a zaune saman dinning ya fara cin abincin tunkan infitoma kamar wanda ya kwana da yunwa a cikinsa.
La,illah wai dama da gaske kakeyi yaya nan zakayi breakfast kada kaja min masifa wajen uwargidanka fa yaya ?
Saidai ya gama tauna abincin daya diba yake fadin kika ganta ina tun shidda ai bata gidan nan wai zasuje danbatta ita da yan uwanta sun kumazo sun dauketa tun dazun.
Kamar ince ba gobe zaku tafi ba kai kumafa data barka bako abin karyawa saidai naja bakina nayi shiru kujera na jawo na zauna ina fuskantarsa.
Lokacin na kula da yadda yakecin abinci lalai da yunwa ya kwana bansan lokacin da nace ko in dafama wani abune ka kara dashi.
Ya dago ido yana fadin kinga inata loda abinci ko yunwa nakeji wallahi tun abincin da naci nan da rana jiya shine a cikina har yanzu.
Shiru nayi ban tofa ba sai a zuciyana nake fadin namiji ke nan kuma a haka ake soyayyan ba a san yadda za a kula da miji ba kuma a hakan itace yar gaban goshi.
Ki barshi zan fitane jiya ban samu zuwa gida ba idan na dawo da rana nasama kin gama zanci ya fada har ya mike sai kuma ya zauna yana fadin .
Narin tura maki komai a yanzu don anjima banda lokacin hakan kila kudin school da zaki biya sai wanda zaki dinga shan mai dana kashi kuma gasu nan yanzu zan turo maki a account dinki.
Ya fara tattaba wayanshi sai kuma ya dago yana fadin ko akwai wani abinda baki dashi kuma idan na fita in sayo maki don kila zan dan dade banzo garin nan ba wanan karon .
Saboda gabatar da abinda naje can nayi da zanyi yanzu idan nakoma saidai idan na samu time zaki iya ganina ko wani lokaci saidai yadda ya kama idan naje insha Allahu.
Idona yana akansa ina tunane jin shiru yana magana ban amsa ba yasa ya dago daga abinda yakeyi din don ya kalleni ni kuma lokacin na nisa ina fadin ina ganin ba komai insha Allahu komai ina dashi ai.
Ok ya fada ya mike daidai lokacin da alent din wayana yai kara ya gyara da kyau yana kallona tare da dan jan kujera ya furta thank for d food saina dawo.
Agaidasu mum zanzo insha Allahu tunda baka nan da sauri ya juyo yana fadin don't try it na fada maki banson yawon banza don Allah idan dai ina gari muje tare mugaidasu mu dawo gida.
Tunda ya fita na dade zaune wajen ina tunane ni kadai gadai kudi masu yawa kan an turo min amma kuma miji zaiyi nisa dan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i yanzu.
Idona na lumshe a hankali ina sauke ajiyan zuciya na kara kallon wayan ina mamaki irin kudin da yata din ya turo min a lokacin .
Na dai gaji da tunane na mike na kwashe kayan abuncin nawa da mukaci zuwa kitchen na wanke na dora muna girkin rana don na tabbatar ba lalai bane ta dawo din tayi masa girki da rana din.
Don haka nayi girkin tare dashi ban huta ba saida na gama na kamala komai na koma dakina don in huta kafin azahar tayi.
Da haka barci ya dan kwasheni mafarkin da nayine ya razanani don da Aisha din nayi mafalki mara dadi wai ta dawo da wani abu tana watsa min a jikina .
Ruwan abin zai sauka min na kauce ina fadin La,illaha illa anta subba hannaka inni kuntu minal zalumin Aisha me kike shirin yi min haka sai na falka ina wani irin zufa duk da sanyin ruwan saman da akeyi ranan.
Tsorone ya kamani adduan nake maimaitawa a fili kafin na jawo waya ina duban lokaci zubur na mike da sauri ganin lokacin sallah ya gwauta a lokacin na nufi bandaki na dauro alwala.
Bayan na idar da sallah na dade zaune ina tunane kafin inyi shawaran kiran hauwa nakira mun gaisa kafin na kora mata komai.
Sai naji tace dama nasan za ai haka ai ki kwantar da hankalinki insha Allahu komai bata iyawa dake zainab kedai kawai ki kara rike Allah ga lamarinki.
Ai ko batayi ba wanan kungiyar nasu zasuyi don mairo tasan labarinsu ta fara bani labarinsu ranan amma kada ki damu zan kara turo maki wasu adduoi kafin mu hadu.
Bata iya komai dake insha Allahu kisa hakan a ranki nace nima nasani don inna ma ta fada min hakan shima baba dariya yayi da inna ke fadin hakan yace data zube a banza udan tace ni zata jefa da asiri.
Hiran da mukeyine ya dan dauke min hankalina da zancen take fadin gobe ma bazaki fito ba ke nan nace ehh sai sun tafi don nafi son inga tafiyansa na farko a gabana.
Hakan yana da kyau gaskiya kinyi tunane mai kyau a nan gaskiya mun dai kare wayan tana min shakiyanci bayan mun gama waya na sake dauro alwala nayi sallah la,asar kafin na fito ban ko kaiga zama ba ya shigo .
Maigadin mu yana biye dashi a baya yana fadin malam hamza don Allah a kula da tayar da injin din nan koda bata gida idan an dauke wuta kada kayan abincin su lakace
Sannu da zuwa nayi mai maigadin da bazaice ga fuskana ba sai ranan yana min sannu da gida don tun ranan dana raka su dada ban sake fita ba kuma ina ciki kumshe kamar lale .
Dama haka nake niko gida in muna hutu ban fita ko ina idan ba fita ya kamani ba a yadda nagani yana good time da maigadin gaskiya .
Don ranan dana fara ce masa ga abincin maigadinan ai ina jin shi kadaine ko wani irin dadi yaji sosai yana samin albarka har da godiya.
Hanyar kitchen ya nunawa maigadin tare sukaje suka saka komai suka kuma fito a taren nan naji yana fadin malam hamza yanzu zan fito idan naga sai muje ka dan sawo abin amfani ko koda yake bari dai infito din.
Saida maigadin ya fita ya zauna yake cewa dani zai dauko iyalinsa ga gobe yace zai kawota nan zan gyara masu dakunan nan boys quaters din su zauna aciki.
Don gidan nan yai maki girma da zama ke dai zainab hankalina bai kwanta da intafi inbarki a nan haka ba baba ya hana yaransa zuwa yace ai aure kikazo yi innama ita kadai tazo ai don haka kije ki koyi zaman aure.
Haka gida sai cewa sukayi wai saidai dada tazo kafan ya rufe baki nace a,a yayi murmushi yana fadin nima ai ban yarda ba sin inkin fita school dawa zata zauna son haka na rushe zancen dada don nasan kema ba zakiso zuwanta ba yanzu.
Mikewa nayi ina fadin don dai ka damune amma zan iya zama ni kadai din yanzu ai ga iyalin maigadi sai mu zauna din nidaba zama nakeyi bama.
Ruwa na kawo masa mai sanyi na tsiyaya masa ya karba yana min godiya nace ga abuncin can a dinning ya kara kurba ruwan yace thanks nagode da kulawanki zeey.
Tausayi ya ban ya dan dukar da kai kafin ya mike yaje gaban dinning din yana zama ina bayansa ina fadin amma a can ai baka da matsalan abunci ko ?
Yace da dama dama dai zeey idan naci a office wani lokaci sai kuma washe gari idan nakoma zan kara karyawa can din don abincin ba laifi gaskiya.
A raina nace koda laifi yaya zakayi tunda haka ka dorawa kanka jaraban leke kan wanan matar taka da baka iya takawa burki.
Magana kikeyine nace a,a kina jin haushine kema ko na dago da sauri nace akan me yaya abunda mutum ya daukarwa ransa zanji hauahin ka.
Abincin dana bude ya kalla yana fadin masha Allah wallahi zainab ke matar kwaraice yanzu idan na tafi inba wurin abincin mu na hausawa naje ba wazai tuka min tuwo haka inci.
Banyi magana ba na gyara masa nace bissimila ina tsaye yake fadin keba zakici bane nace sai anjima yaya dana gama na danci dazun danaji yunwa.
Ok yace duk ya fedeshi wanda na zuba masa din na miko ruwa ya wanke hannusa tas zan dago ya dan watso min ruwa na danyi murmushi ya gyara zama yana fadin to Alhamdullahi.
Yanzu barin tashi in samu maigadi inji medame za a sayo ko in basa kudin nace kadai saya mashi na dole son ba lalai bane ya saya sin kasan mutum da kudi yanzu.
Iein katifa da bedsheets da filo da yan kayan aikin mata ko har abinci ko a nan n dinga yi dasu yace what kece zaki zama boyar su ?
Bari dai inje don ba time kin kawo shawara mai kyau a nan ya mike ya fita nabishi da kallo ina fadin Allah sarki shi bai ko damuba a hakan.
Da ban gidan yaya ke nan zaiyi yanzu haka yake fama da yunwa wani lokaci idan baison korafin mum don yakan daga lokaci baije tace abashi abinci ba agida.
Nidai ban samu ganinsa ba nayi barci saida safe nasan a ranan zasu tafi son haka na tashi da wuri a zatona sammako zasuyi sosai a ranan wai sai sha biyu jirginsu zai tashi ashe jirgi zasubi.
Nasan ya saba hakan tunda safen kuma gyaran wajen maigadi sukayi inda shi malam hamza din ya wuce kauye dauko iyalinsa din.
Nan matar yaya keji take tambaya yake fada mata maigadi zai dawo da iyalinsa su zauna nan don zainab kada ta zauna ita kadai.
Budan bakinta sai cewa tayi Aliyu me kake nufine wai don wanan zainab din zaka jawo muna wasu yan kauye a cikin gida su zauna damu ?
Yace ke meye ba yar kauyen ba ni ban gudun yan kauye don canne asalina kuma ban kyamar mutane kin sani don dan gidan yawane kinsani.
Idan kai kana so ni banaon haka ga wanan ka kwaso ka aje yanzu kuma zaka dauko wasu gidadawa ka kara sakawa gidan meye matsalankane wai Aliyu ?
Gidan kine ko nawa Aisha ko rainin yakai kice ni ban isa ba da gida sai yadda ke kikeso nan ta fara fada bai kulata ba har tagama buge bugen wayanta ta fice gidan wai zata gida tayi sallama dasu.
Bata dawo ba sai wajajen goma da rabi a gurguje suka fito yana fada sun kusa makara yaushe suka kai airport yanzu.
Ina tsaye daga kofana ya gama fadanshi ya nufoni ganin zaizo yasa na juya zuwa ciki anan tsakiyan falo muka tsaya dashi ya rugumeni yana dan buga bayana yace.
Take care zainab ki kula da kanki da gida son Allah duk wani abu ya faru kikirani ki sanar dani koma meye kiyi hakkuri da mutanen nan da zasuzo kinsan sai a sannu zasu waye.
Zanbawa umar key ya kawo maki idan ya saukemu airport sai ki dinga amfani da motana yanzu don ban yarda ki shiga nakin nan ba,a dubata ba.
Motarka kuma yaya ya daga min kai tare da fadin ko baki son,tane nayi murmushi har yana iya jina nace nagakamar tayi min girmane ai.
Ki daiyi amfani da ita nace har muga abinda za,ayi don Allah kiyi hakkuri da mutanen nan zeey na amsa da insha Allahu yaya muka fito rike da hannun juna tana tsaye jikin motar tana jan tsoki wai ya shiga ya dade ciki bai fito ba.
Sai gamu kallo guda tayi muna ta watsar shi kuma yaki sake min hannuna har muka karasa wajen motan umar na fadin Allah sarki yar kanwarmu yau za,a barki da kewa a gidan.
Nayi dan murmushin yake ina fadin Allah dai ya kaiku lafiya ta shiga gaba lokacin ya sakeni yana fadin idan kin zauna gaba ni baya kikeson in zauna ne kome ?
To ina kake son in sha yace kinfi karfin shiga bayan motane kome ko umar zan tura baya taja wani tsuki ta bude bayan motan ta fada umar din ya shiga wurin driver ya zauna na danja baya ina masu Allah ya tsare ya kalloni yana fadin take care nace insha Allahu.
Yadda bata dago kai ta kallemi ba nima haka ban nuna nasan da ita za ai tafiyan ba a lokacin suka bar gidan naga sun tsaya bakin get yana magana da wani kafin yasa kai lokacin ina cikin part dina koda suka bar gidan.
Nashiga damuwa sosai ranan ga kadaici da damuwa sun taru lokaci guda sun min katutu a zuciya sai naji dabaran yaya yai min a lokacin na dauko maigadi da iyalansa ya saka gidan.
Koba komai sun cire min damuwanan da kadaici idan ina jin motsinsu a gidan koda ban shiga tsabgansu ba sun dai debe min kewa ai.
Sai yamma lis naji ana nocking din kofana ina falo zaune na mike zuwa kofan ina tambayan waye daga can nake jiyo muryan maigadi yana fadin.
Hjy nine hamza maigadi mun dawo jin hakan yasa na bude kofan da sauri ina fadin au malam hamza har kun iso sannuku da zuwa kunsha hanya fa.
Daga bayansa wata mace baka mara jiki ta dan leko da yara biyu daya goye dayan kuma mace data dan tasa tana gefenta dukkansu da cikwikwiyayyen hijan har da dan faci a jikinsa.
Sannu hjy ya gida mun sameku lafiya lafiya kalau wallahi ya kuka barsu can gida lafiya kalau wallahi tana hausansu na yan zaria.
Malam hamza hannu a hade kamar me kunyata yake fadin hjy nace ko Alh ya maki bayanin kafin ya tafi nace kwarai ya fada min zancen zuwan iyalinka nan tun jiya.
Allah ya bamu hakkurin zama da juna suka amsa a tare amin hjy mun gode Allah ya kara arziki na amsa da amin kamar zan juya na sake jin yace nace ko wurin bude yake nace ehh a bude yake ai bari na fito mu karasa mugani.
Nakoma nasa mayafi na fito tare muka nufi part din dakuna biyu da dan karamin falo tsakiya sai bandaki shima daga waje muka dan zaga ina fadin Allah yasa dai wajen yayi maku.
Da sauri mijin ke fadi hjy ina nataba mafalkin samun wanan dama ace irin wanan gidan haka nine zaune ciki yau da iyalina wallahi mungode ba abinda zance sai Allah kara albarka da daukaka muka amsa da amin .
Nan na juya dama na tanadi abinci dasu na koma na dauko masu sunata godiya nace to idan kin gama sai ki tashi ki dan fara gyaran wajen yamma ya somayi .
Ta amsa da godiya nafito na dawo part dina don in barsu su dan sarara a tsakanin su ban sake fitowa ba kuma don kule part dina nayi daga wanan lokacin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

7?? 5??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.

Kamar yadda na saba hakan na tashi na shirya washegari da wuri don zan fara fita zuwa school wanda nake fatan hakan ya rage min kewan angona da baya kusa dani yanzu .
Sam nama manta da zancen iyalin maigadi da sukazo saida na fitone na ga mace duke tana sharan haraban gidan abin ya fado min a rai inda itama ta dago tana min ina kwana har kasa takai wai tana gaidani irin ga matar oga din nan ko wata hjy mai jan aji.
Da sauri nace haba dai ya sunan ma tace Aina,u nake hajiya nace son Allah bar rusunna min haka ya gajiya baki hutaba kina wanan aikin haka.
To hjy ai gara inyi in huta sai in kama wani kuma ni zanje makaranta sai yamma zan dawo in Allah ya kaimu kuma.
Tayi min Allah ya tsare har na juya nace ina yaran tace suna wajen mu suna karyawa nayi mamaki kari tun safe haka amma su sun saba da hakanne.
Don ban mantawa haka muma mukeyi a kauye a baya tun safe inna ta gama koko baba ya sayo kosai kafin bakwai mun karya.
Na fara tafiya ta sake fadin hjy nace ko akwai aikin da zanyi maki kafin

75 / 105