DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   92 / 105

273K to 276K   out of 313.1K words

ruwan baya mun gaisa dasu suke fada min su yaya na massalaci.
Nake tambaya saboda nasan halinmu malama asibiti ko don aci kudinka yanzu za a kirkiro ma wani zance na daban duba yaron nayi kafin na fara fada da ita tace doctor ya bada umurnin a kara mashi ruwan ta dauko takardansa tana nuna min.
Karba nayi nan na hau fada zuwa wajen likitan nayi hakan ne badon komai ba son gudun kada yarona ya tashi a haka dan ciwo kadan idan ba drip aka sakawa mutum ba baya jin sauki.
Da can baya ba kasafai ake wanab karin ruwan ga mutum ba sai ciwo yakai ciwo ake sakawa mutum ruwa.
Yanzu ko an mayarda mutane kamar albasa idan ba ruwa aka daurawa mutum ba bayajin sauki koda ciwon baikai na hakan ga mutum ba.
Likita baya nan yasa na fito muka hade dasu yaya da suka biyo bayana nake masu bayani ganin yaron ya dan samu sauki yasa na dauki abina muka koma gida tun a cikin daren ba wanda yace dani komai dan kwana asibiti sai a hankali idan yakama mutum dole.
Amma tunda gani nasan kuma aikina akan me zan zauna mu bata lokaci mu kuma dole da mama muka koma a lokacin ban san case din da akayi ba tunda ban kusa.
Na dai zata saboda ciwon yaron ne ta biyomu a lokacin ranan zai dawo part dina dan haka ban damu da rashin fitan shi zuwa can ba tunda banda case dasu yanzu nasawa zuciyana.
Abinci na bashi da sauran yan abubuwa dana saba masa tun bayan dawowan mu dama dakina na shifide yaron ina kula dashi.
Hakan yasa har mama duk muna dakin fafir naki kula yaya a ranan dama haka na shirya yi a zuciyana .
Sai wajajen sha biyun darene mama ke fadin ba dakin mijinki zaki je ki kwanta ba tunda gani nace ai yana can wajen matarsa hakan yasa mama ta saka min ido muka kwanta a nan .
Sun dai samu barci su amma idona biyu ina zaune ina karatu ina kuma kallon yaron dake gefe a kwance don kulawa.
Naji massage ya shigo mi ina dubawa nasan yaya Addel ne batare dana bude ba na dan karanta heading din naga yasa ke nake jira tun dazun,,,,
Tsoki naja na dangwara wayan tare da mikewa nayiwa kofana key na kashe wuta ina aiki da dimligt wanda ba haske sosai .
Ashe yaji shiru yazo yaji kofan a rufe daya murda ya koma cikin mamaki don hakan bai taba faruwa a tsakanin mu ba sai ranan.
Washegari don banyi barcin kirki ba don haka ban makara ga sallah bama sai bayan na idar na sake komawa barci kodana tashi na samu yana daki suna magana da mama.
Dan tashi nayi ina duban inda nabar yaron a kwance baya wajen yana jikin ubansa kwance dake zaune saman kujera suna magana da mama .
Kin tashi Abu ai dole kiyi barci tunda baki samu barcin kirki ba jiya duk na falko zan samu idonki biyu kina karatu .
Wallahi mama saida na mike nayi masa ina kwana kafin na yunkura ina sauka saman gado na fice daga dakin.
Dakin yaran na nufa natayar dasu laura suyi sallah kafin na wuce kitchen kai tsaye dankali na debo na fara ferewa tare da dora ruwan zafi nacigaba da firan dankalin.
Banji motsin shi ba sai muryansa daya dan firgitani da yake fadin mene hujjanki nakin zuwa wajena bayan ga mama tare da daddy kinsan kuma ba zai taba damuwa ba idan mama na nan ?
Saida na dan juyo na kallesa na juya ina fadin bani da hujja illa a gabanka aka nuna min ba ason alakanka dani a yanzu kuma kaji ka kuma nuna min hakan me zaisa in nace ko don ana ganin banda gata sai na koma mabukaciya.
Wanan wani irin maganan banzane kike fada min yanzu don ban fahinci zancen kiba waye yayi maki kashedi a kaina din in sani da yace maki baki da gata.
Shiru nayi naci gaba da aikina yana tsaye a bayana ya kura min ido na dan lokaci kafin yace isan don zancen su mum kike son juyawa kin dai san ba abinda suke nufi ke nan ba.
Amma kuma ai ba a gaban Aisha yakamata a zaunar dani ana min wanan fadan ba haka matar da bata san darajan kowa ba har yaushe zata fahunci abunda ake nufi.
Zainab kada ki dauko min wani sabon rigima kuma ki barni da wanda nake ciki don Allah ba kaina bane farau din tara mata biyu a gida ba banson tashin hankali don Allah.
Nima ba tashin hankali naja ba gara kawai in kama gabana tun yanzu zaifi mun sauki don a yanzu ban daukan irin wanan abin kuma gaskiya.
Waini kike fadawa magana haka kai tsaye don kawai mum tazo tayi maku nasiha kome ?
Nayi shiru ban bashi amsa ba na dan lokaci ya karkada kai ya na juyawa yace zainab zainab kibini a sannu kada ki bari mu samu matsala dake akan wanan zancen don Allah.
Nan ma ba amsa ya fita saida ya shirya yake cewa mama kiyiwa zainab fada banson tashin hankali zan saba mata wallahi fiye da tunanenenta.
Me kuma ya faru sai bai tsaya ba yasa kai ya fice baiko karya ba ya bar gidan na samu banda exam na kwanaki hakan ya bani yin daman aikina a tsanake ban shigo daki ba saida muka gama har abuncin rana kafin na shiga wanka.
Na fito na shirya kafin na dawo falo wurin mama lokacin suna falo da yara a zaune suna hira nazo na zauna take gaimu da Aiki.
Nace mama bari yasha magani rana yayi ina cikin bashi maganin tayi sallama ta shigo wai gaida yaron suka gaisa da mama take tambayan ya mai jiki mama tace maijiki kan ai ya walwale .
Gashi har yana dan wasa oh Allah ya sauwaka ta sakai ta fita ni dai banyi magana ba dama nasa duk yadda akayi shi yayi mata fada ta shigo ashe ko hakan ne ya faru.
Da safe ya shiga yake fadin meye hujjanta na rashin zuwa asibiti ta duba yaro da baida lafiya yau koba dansa bane yake gidan nan har aka kwantar dashi ashe baici gaisuwa a wajenta ba balle dansa.
Tace banda kai waya fada min yaro baida lafiya ai uwarsa nagidan tana ganin bankai matsayin da zata fada min bane ko ?
Zainab tana school saidata dawo itama ta sani ta samemu a can bayan haka ina nan yarinya ta samemu take fada muna ashe ko don su mum a lokacin ba zaki fito ba.
Dakata Aliyu don Allah kada mu fara samun matsala aka yaranka tun yanzu yaran da tunda na dawo gidan nan uwarsu bata taba turosu nan ba akan me ta nuna bata son hurdana dasu zan lekewa yaranta son banda zuciya kome ?
Ok haka kikace to kada kije ki duba yaron ki tsaya min hauka a nan kiga abinda zan maki idan na dawo ya fada ya fito.
Yana fada ta kira uwar tana fada mata tace amma ke shashace waike meyasa kike dip ne kamar ba mace babu ko dan kissan mata komai a gadarance kikeyisa gaba gadine ?
Ke da wata mai wayauce ai saiki nuna kin fishi damuwa da zancen nan kiyi gaba ana komai dake akan yaran nan baki tsaya kina wanan wautan haka ba.
Wallahi mama na tsani ko ganin yaran nan akansufa na bargidan nan don me zanso ban kaunarsu har uwarsu wallahi banjin zan iya hakan wallahi.
Uwar tace ke kika sani kada kiyi inkinso saiki bari ya dawo din kiga abinda zaiyi ai Aliyune daine kinsan halinsa sarai ta kashe wayanta ta barta zaune tana shawara kafin taja tsoki tana fadin ni yama dawo inji yaushe zamu koma abuja in daina ganin yan iska ga baki daya wallahi.
Karshe dai ta mike ta saka takalma ta fito zuwa part din nawa gaida yaron ta samu yaji dama shine ta fito tana ayyanawa a ranta cewa harda yara kanana sun iya makirci don su tayarwa mutane da hankali a banza.
Mama ta kalloni tana fadib me kikaiwa mijinki Abu yakawo min karanki da sauri na dago ina fadin karata kuma mama ?
Yazo min rai bace yace in maki fada kada ku samu matsala dashi kingako ransa ya baci gaskiya yau nake gidan nan bai taba kawo min karanki haka ba ai.
Can ba dadi ko yanzu zuwan nan nasan shiya turota ke kuma a wajen naki baiji dadi ba yaya kikeson yayi don Allah ?
Nayi shiru kafin in dago da zuman magana sai kuma na fara hawaye nayi kokarin fadin mama gabanki fa mum ta nuna niba kowa bace.
Dama nasani nasan wautanki ke nan a yanzu bayan ita kubura din ta lashi zuman musguna maku dake harshi mijin naki a yanzu.
Na rasa munafukin daya labarta mata wai malam ya sayiwa Garba gidan da suke ciki shine tace za ku iya abu haka baku fada mata ba.
Na dago kai da sauri ina fadin wallahi a,a mama wanan kan ba gaskiya bane dama baba abinda yakewa gudu ke nan tun farko dana kai masa kudin yace a mayar masa saida nace wallahi baisan zan kawo masa ya kara bama.
To kin gani amma an fada mata shine ya biya yau ace shi dinne ai banga abin bakin ciki a zancen nan ba saima tayi godiyan hakan a karshe.
Nakan rasa wani lokaci inda tunanen kubura ke shiga wallahi tundai wanan dan takin gaba daya ta sukurkuce min saida na zaunar da ita ina tambayan meye damuwantane wai ?
Take ce min mena gani nidai ba haka na santa ba gaskiya tana da fada amma ba irin wanan ba na yanzu dole dai akwai matsala wani wajen.
Gaskiya duk zamana da mum bata taba nuna min hakan ba sai a wanan lokacin illa abinda dana sani shine ko nayi mata laifi kai tsaye take fada min tayi min fadanshi kuma akan kada in koma maimaita abin
Amma tun yan watanin da suka wuce nake hango sauyi sosai game dani a wajen mum din wanda ban saba ganin hakan tare da ita ba.
Sai muyi mata uzurin hakan tunda bamu san meke damunta ba a yanzu nima yadda muka kwasa jiyan nan bayan komawan mu sai banji dadin abinba yanzu duba ga yadda gidan su yake da har na bari kowa yasan da hakan nan take ban labarin abinda ya faru tsakansu da mum din nima gaskiya banji dadin hakan ba duk da akaina hakan ya faru koda ban sani ba son dole mama ta boye min wani abu yanzu.
Sai la,asar ya shigo ina dakina tunda nayi sallah ban fito ba mamace ta tura yaran su fada min dawowanshi don kada ta gane wani abu dai nafito na bashi abinci .
Shima ba walwala a fuskansa ya karba gaisuwa na ban jima ba naje gun Aina da take fama da laulayin ciki na subata kodana dawo baya falin na zata yana gun matarsane ashe yana cikin dakinsa saida zai fita sallah magaribane nagane yana gidan don bamu faye bude kofan gaba ba a yanzu munfi amfani da kofan baya wanda ke kallon part dinsu Aina.
Haka ita kuma ban taba ganin ta bude nata kofan na baya ba don haka bata amfani dashi ke nan a bangarenra saina gaban.
Already an gyarawa mama dakinta tsab don haka bata gane me muke ciki a lokacin don hakane bata gane ai ban kwana a dakin nasaba ma a ranan.
Washegari misalin goma da rabi ina daki ina waya sai gashi ya shigo yana fadin ni zan koma banyi mamaki ba saboda nahau a lokacin sai cewa da nayi Allah yakai lafiya.
Kamar zai fita sai kuma ya tsaya ya juyo yana fadin gobe idan driver yazo zai dauki yaran nan ace ya tsaya duba motan nan naji na fada ya kada kai ya fita cike da mamakina a zuciyarsa.
Ban ce min ga kudun wani abu ba numa kuma ban tambaya ba haka yasa kai ya fice an dan jima naji yara sun dawo suna fadin ya tafi.
Yadda bai nemeni ba yinin ranan haka ban kira nayi masa an sauka lafiya ba nima na sharesa yaje matarsa dake gabana din tayi mashi.
Har aka kwana biyu bai kira ba nima kuma ban kira din ba don ina son nuna masa nima macece ba auren zumunci aka kulla a tsakanin mu ba.
Nidashi muka hada kan mu banga abinda zaisa in tauye kaina a yanzu ba kuma shima yasani ko rabuwa yayi dani a wanan takin banda wuyan auruwa ga wani don me zan tsaya suna juyani yadda ransu keso a tsakaninsu abinda nake fada ke nan a zuciyana.
Shima a bangaresa hakane ganin kwana biyu baiji komai daga bangaremu ba gashi yana son jin halinda danta yake c???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?iki yasa ya kira layina is swichup yaji lokacin ya tuno ina exam ranan.
Sai da ya kwatanci mun fito daga exam ina hanya zan tsaya insaiwa yara kayan bukatunsu naji kira ina daga wayan naga shine a layin ya kira na dauka murya ciki ciki nake gaidashi ya amsa shima somehow gareni tare da fadin ya jikin shi daddy yaji sauki ko ?
Nace da sauki jikin bai kara tashi ba kuma tun ranan mamafa suna lafiya nace kowa lafiya yace shike nan sai anjima ban tsaya amsawa na rigashi kashe wayan.
Yayi mamakin hakan sai dai ya share zancen baice komai ba ya barwa cikinsa shima yana kiyastawa a ransa zaiyi maganinane.
Sai wajen kamar sati nashiga dakin in gyara na samu ya aje min kudin cefanen mu saman gado da dan note nagama karantawa na mayar inda yake bayan na gyara gadon ban dauka ba.
Na gama na fito na rufe kofan tunda ba mai shiga dakin dagani sai shi a gidan nasan in Allah ya dawo dashi lafiya zai samu kudinsa wajen daya ajesu din yaga ban taba ba.
Na fitone muna zaune muna hira saiga wata ta shigo da sallama duk muka bita da kallo gaisuwan sama sama tayi muna tana fadin anty tace in karbo key din mota zata fita dashine.
Anty wace anty na fada cikin mamaki tace anty Hummaira ta wancan part din ta aikoni nace ba a ban key din mota ajiya ba ta juya ta fice an dan jima sai gata ta dawo tace dani.
Wai key din motarcan dake bude zata fitane nace yara za,a kai school dashi yanzu driversu zaizo sai ta sake juyawa ta fita.
Na zata mai sakon zatazo da kantane sai naji shiru har dan dattijon drivern yazo suka tafi hakan yasa nasan ta hakkura da karban key din ke nan a ranan.
Duk da nasan ba hakkura tayi ba kawai dai jiran ya dawo akwasa tayi don da a bayane dauka kawai zanyi in mika mata shi kai tsaye ba tare da wani abu ba don haka nima yanzu jiransu nakeyi ga baki dayansu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

9?? 1??
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,


Sam bansan meke faruwa ba kodana dawo gida na samu su laura a zaune jigu,jigum cikin damuwa nake tambaya suke fada min suna aaibiti da yaron dashi tun bayan fitana.
Na kira wayan bai shiga ba yasa na shiga daki a cikin damuwa kayan na kwabe zuwa wani dogon rigan shan iska a zatona zasu dawo ai zuwa yamma da yaron sai naga sabanin hakan ya dan fara tayar min da hankalina.
Ina sallame sallah magariba yana kiran wayana yake fadin kin dawone nace eh nazo gida suke fada min kuna asibiti da daddy kuma.
Gamu nan sun bamu gado muna nan dasu mama da su mummy ta baci ke nan nasa a zuciyana lokacin na tambaya yake fada min nace dashi gamu nan zuwa.
Abinci na shirya da zan kai masu Laura kawai na dauka nabar sauran gida tare da ja masu kunne kada su yarda su bude kofa idan ba muryana sukaji ba.
Mun isa asibitin kai tsaye dakin yara na nufa tun a nan na fara haduwa da yan gidan mu muka gaisa suke fadin ana karawa yaron ruwane nace akan me ciwon har yakai hakane ?
Na shiga dakin na samu staff nurses din dake kara ruwan baya mun gaisa dasu suke fada min su yaya na massalaci.
Nake tambaya saboda nasan halinmu malama asibiti ko don aci kudinka yanzu za a kirkiro ma wani zance na daban duba yaron nayi kafin na fara fada da ita tace doctor ya bada

92 / 105