DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   36 / 105

105K to 108K   out of 313.1K words

UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,


HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Daman banyi tunanen akwai ciki a jikin zeey ba don yarinyar nada baka,in hakkuri da dauriya baka taba sanin halin da take ciki a rayuwanta saboda dauriya.
For goods eighteen months tana zaune hakana babu komai daya shiga tsakaninta da hafiz amma bata taba kai karanshi wajen kowa ba don ban zaton ko hjy mum ta taba fadawa wanan zancen.
Anty Nafisace da muka fito daga office din likitan take wanan maganan da yaya Addil da suka jeru tare ni kuma ina bayansu nida hjy mum da mummy wace taga fadin nata zuciyan tun a office din likitan tana fadin.
Shike nan ai yanzu ba kare bin damo sai hankalin kowa ya kwanta dama ni nasan hakan yana da wuya ace wai hafiz ya tsaya har yiwa mama ciki yadda bai sonta din nan nasan abune mai wahala gaskiya.
Amma Alh yaki yarda yace dole sai azo ayi awo to anyi din yanzu sai hankalin kowa ya kwanta dama ai ba hankalin wanda yake tashe a nan kamar kowa don ba wanda baisan hakan yana da wahalan faruwa ba.
Allah ya hada kowa da rabonsa na arziki aka amsa da amin lokaci guda mummy din ta sake fadin yadai kare ai yanzu kowa ya tsaya matsayinsa kuma .
Haba mummy bai dace kina irin wanan zancen ba don Allah mutuwan aurene fa ba wani abu ba don Allah amma kina ta fadin zantuka haka mummy hafiz da zeey din duk nakine ai mana.
Wanan zancen da Nafisa tayi mata a gaban yan gida shiya kara sa hjy mummy hasala da yarta tana fadin aida daya suke ba,a goyon bayan maamah ita kadai ana aibata hafiz kan hukuncin da yake ganin shine mafita a garesu.
Mummy nidai na rabaki da irin wanan zancen akan aure shi aure ba,a shige masa gaba haka kayi kiri kiri kana goyawa naka baya idan kuma auren bai mutu ba fa ya zakiyi kuma ?
Tunda ga Addel nan yana ta kokarin neman hafiz din suyi magana dashi abin ya buwaya don Allah mummy kiyi shiru kamar yadda kowa yayi shiru yabarwa cikinsa zancen kowa a wurin nan ransa bai masa dadi ba ai da faruwan hakan.
Wanan zance sukeyi a tsakanin su har muka iso gidan da farko mummy din kin shiga tayi a waje muka barsu da yarta koda muka shiga Dada tana zaune a cikin damuwa muna shigowa ta mike tana fadin kun dawo to yaya akayi akwai cikin ko babu ?
Murmushi mum din tayi tace ba komai hjy asalimafa kamar ba abinda ya taba shiga tsakanin su duk dadewan nan na aurataya kingako babu zancen ciki ai anan.
Wanan da anyi dan banza a nan yaro da tauri kamar mutanen farko ke Abu kika zauna haka kina kallon katon banza kuna kwana a waje daya yaran nan lalai abarku kawai.
Shigowan su mummy yasa ta katse don mummy din kamar a cikin fushi ta shigo tana fadin bude dakin mu tsunce duk wani abin kwarai nasa naje dasu a adana masa.
Marka kina kalau kuwa da ace yar nan takice haka ya faru da ita hakan zakiyi ke nan ki dingawa mutane tabaran banza ko kinga munyi maki kama da barayine mu ?
Ba hakana bane hjy don naji Alh yace bashi ba gidan nan ne kuma to me zaizo yi kuma dama nan tunda shi ya zamo abinda ya zama a yanzu.
Ai,Bai zama ba tukun shirin zama dai yakeyi dai ai duk dan dayasa mahaifinsa kuka shima sai yayi na jini a bainan jama,a wata rana haba nan ran mummy ya baci ta fara fada kamar ta manta da waye Dada a wajenta.
Jin bakakem maganganun sunyi yawa yasa hjy mum kada baki a zancen tana fadin wai meke damun kine hjy Malka wurin nan fa kowa wanan abin ya shafa ba ke kadai bace zuciyar ki ba dadi a yanzu ba.
Aina sani nasan komai basai kin fada min ba ke kuma aure daine tun farko yace bayayi amma aka dage akan sai anyi naga ai inda namijine kowa na da dan nan aje a aura masu mana idan hakan yana da dadi ?
Au ta nan kuma kika fito min ai kuwa don tun farko banki ace a cikin yaran dakina Alh ya aurawa mama ba amma ila ya kai,shi son kai ya aurawa hafiz ita yana ganin yayi bajinta yanzu gashi ya barsa a ciki.
Dama na sani ai nasani tun farko ba son hakan kikeyi ba kubura yanzuma dadin zagin da akewa hafiz din kikeyi to saukin abindai zagin bazai lake masa ba insha Allahu.
Haka dai sukai ta fitinan su da kyar Dada ta izza hjy mum zuwa gida tace idan ita marka bataji magana taba kema ba zakiji ba ke nan ko jin hakan yasa mum tafiya tana fadin zata dawo.
Ita kuma sun shiga dakin sun duba ba wani kayan arziki nasa a dakin daya aje don hakane suka dan tattara takardun da sauran takarcensa a dakin suka tafi dashi.
Da kyat ya Addil ya sakeshi zuwa yamma ya dauki wayan nasa yana fadin Addel ya akayine yace anyi mana hafiz yanzu hukuncin daka yanke akan yarinyar nan kana ganin kayi daidai ke nan.
Hafiz ka tunafa iyayyen mu ba abin wasa bane a wajen mu kai tsaya Addel ya dakatar da ya Addel din daga maganan daya soma masa yace kunga takardan ke nan ashe ?
To haka naga yafi min sauki a rayuwana haka kawai za,a hadani da wata kucakar yarinya can kazama yar kauye dako kidayan dangi bata gama ba ace wai mata.
Yarinyat nan ankai ko ganinta a rayuwana bana son yi don me zan zauna da ita kan jin dadin wani ni nawa ran yana baci a kullum don haka na samuwa kaina mafitan abinda nake ganin zaifi muna sauki dani da ita.
Hafiz kayi gangaci da yawa kada ka manta har yanzu muna karkashin iyayyen mune fa tunda suna raye a doron kasa kuma su suka hada wanan auren naku daka daure kasawa kanka hakkuri da yarinyar nan sai Allah ya sa maka sonta kaga kaci riba biyu a wajen ubangiji ke nan hafiz.
Kai malam kana nufin wa,azi zakai mun a yanzu kome nace banayi dolene kaima ai namijine nawa Allah yace kayi kana iya karawa da ita ai tunda kana tsiron iyayye ko ?
Haba dai kada kaja zancen nan da zafi hafiz nasan ranka na a bace yanzu amma ka sani duk duniyan nan ba wanda zai tsaya ya fada ma gaskiya akan abinda kayi bayan ni .
Nasani ai shine nace kai kaje ka aureta don ka gyarawa iyayyen namu rai idan akan zancen wanan yarinyar zaka dinga kirana ina rokon ka daka daina kirana don Allah ko kuma ni in jefaka a black list na fada ma,.
Yana kaiwa nan ya kashe wayan nasa Addel din ya daga wayan yaga ya kashene ya sauke ajiyan zuciya mai karfi yana dago ido ya kalli mum data zuba mai idanu tace yaki tsayawa ya fahince ka ko yace yama kashe wayan nasa ai.
Tace kyaleshi zaiyi nadaman hakan ni yanzu matsalata shine kan mama din daya batawa kurciya duk da ba wani abinda ya taba shiga tsakaninsu amma mutane ba zasu gane hakan ba sunan ta dai a yanzu shine BAZAWARA awajensu.
Yanzu shi baba garba meyace ya katsewa mum din zancen da takeyi tace ban tsamani yasani fa don Akh yace bausab abinda zai fada mashi ba a yanzu.
To mum kuna ganin zamansu a wancan gidan ira da Dada shine mafita gara kawai ta dawo gida ta zauna a gabanku don har yanzu zainab yarince fa kada kuma azo a kara tafka wani kuskuren ga hakan.
Banyi tsamanin mama tanada wanan rayuwan da kake tunane kaidai kawai dawowan nata gaban mu shine darajanta na kyalene kawai don hjyce ta yanke wanan hukunci kaga banda abinda zan fada a nan kuma yanzu ai.
Ita Dada ai rudewane yasa tace hakan amma idan iyayyenta sunji gaskiya hakan ba zai masu dadi ba duk da suna tare da Dada a gidan amma ransu kan zai baci gaskiya.
Yanzu dai a jira aji hukuncin da Alh zai yanke don nasan ba zai kyaleta ba aita zauna a wancen gidan daga ita sai hjy ba dole nan dai din zasu dawo akarshe.
Tsuki yaja ya dauki wayan shi yana latsawa kafin ya mike yana fadin zan tafi idan na fita zan kai gidan baba garba din amma gobe nake son yin sammako in koma insha Allahu dama zancen nan ya tsayar dani har wanan lokacin.
Idan kaje me zaka fada masa yace nikan ai gaidashi kawai zanje nayi don kar yaji nazo banje gidansa ba bayan wanan ba abinda zan fada a wajensa daddy ya kamata ya fada mai abinda ke faruwa ai bani ba.
Mum tace lalai kam idan kaje ka gaida min shi ya mike yana fadin zaiji ya fiice ta bisa da kallon yadda ya kara fadawa sosai a wanan karon ko ba,a fada ba tasan yana cikin wani yanayi da iyalin nasa fadine kawai baiyi .
Ina daki kwance don ko fali na daina fitowa Dada tayi fada dani da safe kan naci abinci saki kuma aiba akaina aka farashi ba don me zan zauna ina takurawa kaina hakane kan zancen saki injawa kaina ciwo kuma ?
Duk da hakan kona fito falo ba zan iya jimawa ba zan koma ciki in kwanta gashi ko karatu na kasa yi dana dauki takarda zan aje in fara tunane abubuwa daban daban a raina.
Kwana uku zuwa hudu ke nan ban fita school ba har hauwa ta kirani tana tambaya ko jikin ne har yanzu yasa basu ganni ba nace hakane amma naji sauki zan fito ai gashi gobe Friday naso ko yayane in fita din a goben duk da nasan kona fita ba komai zan gane a can amma fitan yana da kyau gareni dai.
Saidai washegarin kuma na tashi da mugun ciwon kai don haka ko dagawa banyi ba inda nayi sallah ina kwance tun safe Dada ce tayiwa mum waya tana sanar mata don akawo muna abin karyawa tunda ita bata iya girki da gas din da mukeyi.
Kwatsam babana ya fado gidan da sassafen suka gaisa da Dada din kamar yadda suka saba yake fadin ina ita zainabu din mama ?
Tana ciki yau bata tashi da dadin jiki bane tun safe take kwance kanta ke mata ciwo tace Dadan ta fada mai ina jin muryan baba din na samu na mike da kyar nafito wajen.
Kallo daya nayiwa baba din na sada kaina kasa yana zaune sama kujera shima kallona yakeyi har na karaso inda suken zauna da Dada na zube a kasa ina gaidashi kaina kasa hawaye na zuba min.
Shima baba din ido ya zubo min yana mai jin wani irin tausayina a lokacin bai taba jin tausayina da kaunana irin na ranan ba muryan Dada ce dake fadin.
Kaganta nan bataci bata sha uwarata ko yaushe tana kan waya tana rarashinta sai kace akanta aka fara kashin aure abincin safe yadda ta girka ba zataci ba saidai na safe ya taddana dare ni wanan abin ya isheni don banga amfanin zaman da nakeyi da ita ba.
Kuka na sake a lokacin sosai don nakasa controlling din kaina nina san irin abinda nake ji lokacin a zuciya su zasu dauka zafin sakin nakeji yasa nake kukan rabuwa da hafiz din a lokacin.
Muryan babane daya kira sunana a lokacin yace zainabu ban gane me kike nufi ba abinda mama ta fada gaskiyane kina son ki kashe kanki don auren ki ya mutunr ?
Ko kuma ciwon son mijinkine har ya tabaki haka kike son kashe kanki waima yaushe rabon ki dakije karatun kine ko har karatun kin yafene kina neman zarewa ayanzu ?
Shiya sakeki ya kama gabansa yana can yana harkan gabansa ya barku nan a cikin takaici keda iyayyen ki so kuke ku halaka kan kune da bakin cikinsa.
Wai ace har haka ya faru amma an rasa wanda zai kirani ya fada min ga abindake faruwa sai da musa ya kirani daga bauchi yana min jajen abinda ya faru.
Sannan nasan abinda ya faru din naje gidan Alh shi kuma na sameshi a kwance wai shima baida lafiya nazo nan kuma kema gaki a kwance duk akan abu daya ?
Why zaku zauna ku halaka kanku kan yaron da baisan ma kuna nan kunayi ba don Allah ai magana dan uwanki Aliyune dayace.
Yanzune zaki dage da karatun ki dama manufansu ke nan akanki na sakaki karatun nan don ki zamo anin alfahari ga zuri,an mu nan gaba yanzu kuma kin zauna kina son sakawa kanki damuwa da shiririta akan me zainabu ina daukanki me wayau wace tasan ciwon kanta ashe ba haka abin yake ba ?
Ni a zatona yanzune zaki zage ki dage akan karatunki tunda harda jahilci cikin abinda yasashi sakinki a yanzu amma sai gashi don kina dakikiya zaki watsawa muna kasa a idanun mu gareshi.
Shigowan hjy mum baisa baba ya fasa fadin abinda yake fadi ba a lokacin har ya cigaba da fadin dukkanku kunsan yaron nan a yanzu baijin duk wata nasiha ko shawara da za,a yi masa balle yana ganin uwarsa tana bayansa tayaya zai ji wani shawaran ya mayar dake a yanzu ?
Jin abinda baba ya fada din yasa nina dago ina kallonsa yace kwarai kuwa lokacin nayi karfin halin girgiza kai ina fadin baba ba hakana bane abinda kuke tunane wallahi bashi bane a zuciyana a cikin kuka.
Yace to menene zainbu cikin kwantar da harshenshi a gareni lokaci guda yace banda abinki ai mutum bai boyewa nasa kukan zuciyarsa ai.
Ki fada min meke damun rayuwanki a yanzu gani ga kakarki ga uwarki hjy kubura a zaune tare damu meye damuwanki har ya saka kikeson halaka kanki a yanzu ?
Baba ni gidan nan ne banson zamansa ka maidani gidan mu in zauna wajen inna don Allah idan ina gidan nan ukubar danasha a wajen ya hafiz acikin gidan nan ba zai fita min a raina ba wanan shine abindake damuna a yanzu.
Nisawa naji baba yayi yana fadin na fahinceki zainabu zaki bar gidan nan don abinda ya kawoni ke nan a yanzu dama in tafi dake gida tunda su basu son ki koma gidansu a yanzu.
Ba hakana bane yaya don Allah kayi hakkuri hjy gata nan itace ta roki hakan a garemu nikan tun ranan da abin ya faru amma sai ga hjy takawo bukatanta nasan zakayi wanan tunanen a karshe wallahi ba haka abin yake ba..
Shi Alh yace bausan fuskan da zai kalleka dashi ya soma maka bayanin komai ba a yanzu don haka ya nuna isansa da ikonsa akan hakan yabi umurnin hjy gata nan.
Amma garba in kayi wanan tunanen bakai muna adalci ba a nan don dan uwanka yana iya bakin kokarinsa da yarinyar nan idan ba yau din nan dayake kwance ba garin Allah bai wayewa baishigo gidan nan ba.
Mama dole inyi tunanem hakan tunda ina gari mutuwan aure ba karamin zance bane fa tundai na yaran nan dayazowa mutane da wani irin fassara ace shekara biyu ake nema yarinyar nan na gidan nan ba wani abinda ya taba shiga tsakaninsu sai ukubu a kullum ?
Hakkuti za,ayi yaya wanan abin ya riga daya faru ko kuma yazo da sauki tunda basaida ya bata mata rayuwa ya rabu da ita ba shine idan na tuna zuciyana yakan yi sanyi hjy mum ta fada.
Duk da hakan da sauki din amma kuma ai ya bata mata suna don ya mayar da ita bazawara a idon mutane bakowane zai yarda cewa hakan gaskiyane ba ai baba ya fada a cikin takaici.
Yanzun dun dai tunda ta fadi shakuwanta zan tafi da ita can gida don gara ta zauna kuma a wajena saboda zamabta a wajen ku yana iya kawo wani fitina kuma nan gaba wanan ne ya kawoni dama wajen ku yanzu.
Don da niyar tafiya da ita nazo gidan nan saboda abin ya taba min zuciya wanan gidan dai na mahaifisane kunga ke nan zai iya dawowa nan ya sameta yai mata cin mutuncin daya saba muna abaya.
Nima nayi tunanen hakan duk da Alh yace yayiwa uwarsa kashedin kada yaji ya tako masa gida amma idan yazo ai dole nan dai zai nufo tunda bai zuwa can gida din mum ta fada.
Idan yazo ke nan tunda kunya bai isheshi ba ai banyi zaton zai dawo nan maza ba dole sai ya dauki lokaci kafin yanzo tunda yasan barnan daya shuka a nan Dada ta fada.
Duk da hakan mama a dai bari ta koma gida din tunda hakane kwanciyan hankalinta damu duka baba ya fada cikin ladabi ga Dada din daya fahinci itace matsala a yanzu yasan kuma rudewan tsufane ke damunta ga hakan.
Amma yaya sai nake ganin idan kayi hakan ka mayar da ita hannun ka kayi da wata manufa kuma abinda akr gudun daine zai faru don zumunci

36 / 105