DUBA MIN BAYA FAKON BIRI BOOK COMPLETE by Zainab Makawa.doc

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Hausa Novels 001

Chapter   32 / 105

93K to 96K   out of 313.1K words

cikin zolaya.
Murmushi nayi ina kawar da kaina gefe daya nace ni ai na dade da aure Rashida ko bakiga alaman aure bane tare dani na fada ina mikewa tsaye don bana son dogon magana a lokacin.
Bangaren mum kuwa a yanzu tana cikin damuwa kan zaman danta Addil da matarsa Aisha wace zamane na zamani mace ke juya miji yadda ranta keso agaban kowa kuwa zata bashi umurni .
Shiko bai dauki hakan komai ba zai bi umurnin nata a ganinsa duk cikin sone da kauna yake hakan gareta wanda su kuma mutane suke ganin ya koma mijin hajiya a lokacin.
Dayawan maza haka suke da sanyin rai amma mutane yan gaza gani zasu fassara hakan da an gama da miji don baida nacewa sai abinda mace ta umuceshi dashi kawai.
Wanda zancen har ya dawo kunnen iyayye ba kunnensu kadai ba don ko a gabansu sunsha ganin hakan sai abin ya fara damun mum don yawan tsegumin da akeyi kan hakan.
Missalin abubuwan kuwa shine agaban kowa zaice su bari adan kara time su tafi zatace No katashi mu tafi yanzu dai sai yabi umurnin ta din ya tashi a lokacin.
Ko kuma yace daga nan zamu wuri kazane sai matar tace ni bazanje yanzu ba hakan kuma zai tabbatan don ba za,aje gurin ba kamar yadda tace abubuwa da dama suke faruwa irin haka wanda su basu daukeshi komai ba a wajen su amma gun mutane hakan ya zama abin magana a garesu.
Sauda yawa hakan yana faruwa tsakanin ma,aurata sai a dauki hakan fin karfine kawai ga matar tashiga gaban mijinta ke nan sai abinda tace za,ayi a gidan .
Don hakane akeson sayawa agaban mutane don hakan ba wayewa bane zubarwa miji mutumcine agaban mutane kome zakiyi kiyishi a tsakanin ku biyu amma matan yanzu basa gane hakan yana ja masu illa ga aurensu sai suyi tunanen kome sukayi sunyi daidaine su.
Amma mutane saisu dauka cewa magani ko asiri matan sukewa mazan su gama dasu sai abinda sukace shine za,ayi duk da akwai dayawa masu hadawa da asirin don su mayar da mazajen nasu haka.
Ita kan Aisha wanan rayuwan yacita don ko babu kauna ko so tsaksninta da yan uwan miji datakewa gani gani a yanzu tana ganin dafisu miji mussanman anty Nafisa da sukasha soyayya dashi a baya na yarinta.
Gashi sun camfata cewa bata son yan uwa su rabesu don zata nuna bataji dadin zuwan dan uwasa garesu ba ko ta nunawa bakon mugun halin da zaisa ya bar gidan ba shiri.
Idan ana irin wanan maganan abin yana konawa mum rai sosai har wani lokaci takan kira dan nata ta fada masa maganganu aka matar nasa wanda baisan dalilin hakan ba.
Abu goma da biyu ya taruwa mum akanta ga zancena da hafiz ga kuma zancen gidan ya Addil dake son yafi karfinsu a yanzu don irin korafin nan yasa yanzu ya dauke kafanshi da kano tun bayan aurena da duka zo sau daya yazo bai kara zuwa ba har wanan lokacin.
Dama ance idan gida yai kyau hakan na samo mafarine daga jajirtatan uwar gida ko mai gida dole sai daya ya jajirce zakiga gida ya kafu har ya tsaya bisa tubali mai kyau.
Dayawa sukan dace da hakan a da zamanin baya namiji zai jajirce ya tsaya a gidansa yayin da mace ita kuma zata tsaya ta kafu ta taimaka masa wajen ganin gidan ta tafiyu a yadda tsarin yake.
Saidai a yanzu zamani yazo da wani nau,in da mata ke mulkin gida da kansu ciki da waje sai abinda mace ta tsayar ne umurni an kaucewa tsarin addini da karfi da yaji saboda boka mata sun koma juya gidajensu ba maza ba.
Wanan yake yawan kawo baraka a cikin al,umma inda dangin miji zasu shigo hakama wani lokacin dangin macen ba za,abarsu abaya ba sai zaman ya koma gashi nan dai agidan ba wani tsari maikyau da za,ai koyi dashi a wani gidan.
Wanda hakan yana cikin abinda ya taimaka wa yawan sakin aure a yanzu zakiga an koma tsarin zaman waje yafi dadi ga ma,auratan an rabu ana son juna bisa kan son zuciya da kaucewa ubangiji akarshe a koma a zaman waje kuma ana yadda badala a cikin al,umma.
Ya ubangijin Allah kasa mufi karfin zuciyar mu mu zauna a saman tsarin addani yadda ubangiji Allah da Annabinsa suka sharada muna muyi damu da zuri,an mu Amin ya Allahu.
To ankai dai inda ba,aso don ko har yakai Dada ta kwashi kafa zuwa gidan ya Addil din dake Abuja da sunan zuwa asibiti saidai ba,asha da dadi ba a zuwan nasu don ko sun sha tarin takaici da bakin ciki a gidan.
Ga rashin kulawa fa kuma yunwa ba zasu karya ba sai shadayan rana lokacin data gama barcin safen ta rafito lokacin zata tsaya girka masu abinci su karya hakama na rana zasu dawo asibiti a wahalce amma ba zasu samu abinci a gidan ba.
Sai dan kayan kwalaman zamani acewanta mijinta baya zama a gida don haka bata girkin rana da dare kuma sai wajajen tara za,a kammala abincin da zasuci.
Wanda suka dawo kano da takaici da bakin ciki wace ta je neman kafiya wani ciwon yunwa kuma yana son kamata a can sun dawo baki na fadi cewa ga abinda akai masu agidan.
Har yakai daddy ya kasa hakkuri ya dauki waya ya kira yaya din yai masa kaca kaca inda ya nuna baisan hakan ya faru ba don shi ba mai zama bane a gida.
Karshe da yaiwa matar magana fada ta hauyi tana fadin wanan yasa bata son yan uwansa suzo don basu zuwa sai sun samu sherin da sukaiwa mutum idan hakane kada wanda ya kara zuwa mata gida tunda gulma ke kawosu gashi yanzu anzo an mata munafuncin da akasaba kulla mata duk kokarinta akansu.
Tas,tas ya kwasheta da mari saida takai ga shirin faduwa a karo na farko daya taba lafiyan jikinta yace ahir dinki wallahi yana fadin ashe baki da mutunci Aisha kakantawace munafuka ko matan babana kike nufi ?
Ashe baki da mutunci da ake fadin baki dashi a gabana zaki kira kakata da munafuka ke wata irin mara mutuncine da har zaki iya kallon idona ki fada min haka ?
Tana dafe da kumatunta ta kalleshi tace honey nika mara yau akan yan uwanka dama ashe sunzo su kashe min auren da basu so Allah yayi tsakanina da kaine ban sani ba ?
Kika kara fadin maganan banza akan wani nawa zan maki abinda yafi hakan a rayuwanki don ban hada yan uwana da komai ba a duniyan nan haka kema naki koda yarone karami ina kokarin mutunta makishi sai nawane keba zaki iya daraja min suba har kina fadin magana a gabana haka don baki da kunya ?
Ta dan sake masa kallo mai nuna zaka san ka mareni ai ta juya a fusace zuwa dakinta ta barshi a wajen tsaye yana huci ya rasa me zaiyi akan hakan saboda bai saba hayaniya da yawa bashi.
Kwana biyu zaman tsami suke agidan kowa na harkan gabansa don ko Aisha ta dau zafi dashi akan zaisan ya mareta ai yayin da shi kuma yake mai matukar jin zafinta a zuciyarshi cewa tayi mai cin fuska bata bashi hakkuri ba.
Hakan ya jawo rashin jittuwa agaban shi ga mum ko zai kwana kiranta a waya bata dagawa har gwada kiranta yayi a wayan Dada amma taki karba don tana son nuna masa fushinta kowa na kokarin nunawa dan uwa darasi akan abinda yayi.
Wanan yasa ya soma tuna yar mum don da tana gida haka ya faru zatayi kokari ta shawo masa kan mum din har ta dauki waya don ko sa,an aurensu ba karamin gudunmawa yarinyar ta bayar ba ya sani kuma yanzu ko ta kara gaba tayi aurenta ko ya suke can da hafiz ma oho ya tambayi kansa.
Ke nan ko dan karema yana da ranansa son ko wani mutum da inda yake amfaninsa a sanaiya da wani ko a zama don hakane yake da kyau ka zauna lafiya da kowa a rayuwa.
Neman number na ya fara yi yayi sa,a number ya shiga lokacin na mike zuwa daki don haka ban samu dagawa ba har ya tsunke saidana dawo naga miscalled dinsa cikin mamaki na danna masa kira.
Yana zaune yana aikin a laptop dinsa kirana ya shigo ya daga yana fadin bari zan kiraki ai ya kashe Aisha dake daukan jakarta data bari falon ta kallosa.
Baima san tanayi ba ta juya zuwa ciki a fusace ita a zaton ta ya sauya rayuwanshi har ya fara harka da yan mata a gabanta hakan yasa ta cika tana batsewa har taje daki ta kasa zama ta juya ta fito tana cika da batsewa.
A daidai lokacin daya dauka yace yar mum aure ya boye ki a shagwabe nace dashi hai yaya wani aure kuma bayan kun mata da yar kaunar ku ya kwashe da wani dariyan da bansan yanayi ba yace.
Haka rayuwa yake ai zainab ke dai ki zauna da mijinki lafiya ki kara hakkuri nasan halin Hafiz zai zo ya sauko komai ya wuce insha Allahu ki dai kara hakkuri kinji.
Hakan yasa Aishan data kawo gab dashi dakatawa tana huci tana kallonsa ya dan dago ido ya kalleta kafin ya sauke yaci gaba da fadin karan mum na kawo maki yasa na kiraki jin hakan yasa ta juya ta koma daki tana tambayan kanta metaso ta aikata haka ba tare da tunane ba wai ?
Canko falon ya fada min abinda ke faruwa na nisa nace ita mum din haba dai meyasa zata dauki zancen wasu akan ka ka bari da kaina zanje gidan gobe muyi magana duk yadda mukayi zan kira in fada maka .
Yai min godiya ya kashe wayanshi yana furzo da iska tare da tunanen akan mum tasan halinsa da saninsa ai ba zai bari matarsa ta wullakanta kakarsa ba haka don ko har shiri yayiwa zuwan Dada din tunda daddy ya kirasa ya fada mai zancen zuwansu din.
Ko driver daga wajen aikinsu ya dauko yaje masu don zirga zirgansu tunda shi baida lokacin hakan wanan yasa ma bai yarda da zancen ba ya dauka don basu son matar nasa ne suke kokarin mata sheri.
Sai gashi ta gwada masa kalan tsiyan data tsula masu din agabanshi ya gani wanda ko waye yaso muzanta masa yan uwa ba zai dauka ba balle matarsa da yake aure.
Naje gidan washegari tun ban dauko zancen tana fadin mama dake da yayanki kuna son kasheni da bakin cikin ku na dauka kunyi aure zan huta ta karkashin ku sai gashi abin ashe ba haka bane ?
Mum Allah na fada maki na daina zan gyara kuma wallahi mum ina iya kokarina duk da zagi da muzantanin da yakeyi mum ya zagi iyayyena duk na shanye ban fadawa kowa ba ranan badon anty nafisa datazo ta ceceni dukana ya tashiyi ya kulleni a daki saida,,,
Nasan zai aikata hakan mama amma ki kara hakkuri ki basa duk wani hakkinshi daya rataya akanki shifa lamarin Allah wuya garesa ga sauki kuma yi nayi bari na bari sai ka samu takarda maikyau a gobe kiyama.
Duk abinda akace min hafiz yai maki nasan zai aikata hakan don ni kaina sai yazo gidan nan gani gashi ba zai gaidani ba don yana dauka da hadin bakina aka bashike .
Ya zamuyi kana da magabata kuma sha,anin aurene baka zagewa dole in baki hakkuri mama don kowa da kike gani hakkurin nan yake adakinsa auren sunane kawai ba wani dadi garesa ba.
Shi nake son matar yayanki ta gane hakan amma ta kasa gane hakan wai ace hjy ce zatayiwa wullakanci a gidansu ta hora tsohuwa da yunwa ga wullakanci kuma ?
Da ace ya daukemu da muhinmanci ai bataga wajen yin hakan ba ban yarda na goyi bayan su ba saida na nuna bacin raina kafin nace amma mum kinsan dai yaya ba zai yarda da hakan ba agansa sherin matane kawai yasa tayi amfani da rashinsa gida ta dinga muzanta masu nan dai nayi ta kare yaya din har ta dan sauko tana fadin ai dama nasan bayan dan uwanki zaki goya mama.
Nadai bata hakkuri kuma naga ta sauko din sosai don ta koma yabon halinsa kuma tace dani ai inya kira zata dauka don tasan yana cikin wani hali a lokacin ban jima ba na gaida mutanen gidan na fito zuwa gidan iyayyena don banson mu hadu da baba yai min fada tunda ya hanani zuwa gidan idan hafiz bai gari.
Na dan jima a gidan kafin na barsu zuwa gida na dawo banjima da shigowabane naji mota ta shigo get din gidan da karfi kafin naji kashe motar ashe shine ya dawo a lokacin .
Ina kitchen ina kokarin hada girki da zanci don ban tsaya ba can balle inci abincin dare a gida saiji nayi mutum ya shigo don karan rufe kofan gidan da naji a lokacin.
Hakan yasani fitowa daga kitchen din na nufo falo shine da kaya niki niki yake shigowa ciki da sauri na hada kalman sannu da zuwa ina kokarin karban kayan a hannunsa.
Kaucewa yayi tare da fadi don't try torch my belongings iam worning you kada ki soma taba min kayana ya shige ya barni wajen tsaye sororo ina binsa da kallon mamaki tare da furta mai hali baya barin halinsa dai.
Nikan kamar yadda na saba na hada girki na dora masa saman table na koma dakina na zauna ban sake fitowa ba sai washegari koda na fito na samu ya ci abincin dana aje masa.
Na kwashe kayana na wanke na kawo masa na safe dana rana nagirke na shirya na fita nabar gidan kai tsaye sai school tun da nagansa na kama kaina tashin hankalina ya karu a lokacin da dawowanshi.
Don nasan dawowanshi gidan wani tashin hankaline agareni tunda gashi ya fara yaushe da zuwanka mace taje taron ka da kaya zaka kogeta ka fara fada mata maganan banza.
Nikan nasan da wuya zancen mum ya shiga son ko ba inda yake ban dama har na samu nashigar da kaina yadda ta fada a wurin shi zan daiyi kokarina naga na cusa din kamar yadda suke so amma ba zan zake da yawa ba insha takaicinsa.
Don haka ban fasa masa yan aiyuka ba kamar yadda na saba kula mashi kamar bashi abinci idan ya dawo ya zauna in kawo masa ruwa zan masa sannu da zuwa koda bai karba ba.
Zan dai gaidashi din in aje masa ruwa kuma zai dauka yasha din idan na aje zan kawo mai abinci da drinks duk dana kula bai damu da shan drinks bashi amma nakan aje saidai na kula yana shan hadin gida don haka na zage wajen hada mashi irin drinks din hausa kamar su zobo fruits salad kunun ayya pineapple juice da sauran hadi har kunun zagmkin dawo da ake sayarwa wani shago nakan sayo na gyara masa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

.DUBA MIN BAYA FOKON,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

3?? 3??

GA MAISON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

No
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO.


Ya kasance asabarne don haka muna gida a ranan hakan yasa ban tashi da wuri ba sai wajajen tara na fito don in gyara gida in dora abin karyawa sai dai ina zuwa falo naga kayan abincin kamar tunda na ajesu ba,a bude ba.
Matsawa nayi kusa na bude suna nan a yadda na ajesu din bai taba ba na dan ja tsuki ina fadin miskili yai tafiya fadin rai ya hanasa fadawa mutane cewa zai tafi ji yadda yasa nayi barnan abinci don Allah.
Kwasa nayi nakai kitchen daga nan na tsaya na dora girki breakfast da gyaran kitchen din har zuwa su falo kafin na koma na zubawa maigadina nasa abincin na fito don in kai masa.
Har na dan zauda na wuce idona ya sauka ga motarshi dake packe a haraban gidan tafiya nake ina mamaki ya akayi yabar motarasa bai tafi da ita ba ?
Nadawo wanka na fada dana fito na zsina ina shiryawa sai lokacin tunanensa ya kara fado min a rai ina mamakin yadda ya fita ba mota idan tafiya yayi.
Har na shirya din nafito na zauna na karya kafin na bude tv ina kallo nan na mike zubur saboda tunanen da nayi a lokacin .
Waje na leka na hango maigadi zaune yasa tsohon redion sa a kunne yana saurare na dan daga murya ina kiransa ya taso da sauri nazo gareni.
Nace niko baba wai maigidan ya tafi bada mitarsa bane ya dago yana kallona yace gaskiya banga fitansa ba tun jiya daya dawo ya shiga ciki aibai fito ba kuma ya fada yana kallon kofan shiga gidan kafin ya mayar da kallonsa gareni yace.

32 / 105