YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 98

30K to 33K   out of 291.7K words

mamaki sannan ta fice bayan ficewarta Mama tace, “lallai ka cigaba da yima yarinyan nan duk abinda takeso muga ina ze kai ka da ita duka” banza da ita Baba yayi yaja Zeezee sukayi kwanciyar su.

*** A takaice ranan ba abinda Zeezee ta tsinana banda yima Mama rashin kunya da rashin ji, washegari ma da k’yar Baba ya iya tadata aka shirya ta school. Koda taje yau ma tayita kukan shagwaba seda taga Lubiee hankalinta ya d’an kwanta. Cikin sati Zeezee ta saba da school sede kullum kafin a tasheta se anyi drama ga zab’an wanda zeyi mata wanka, sa mata uniform, yi mata polish na takalami sa mata, do komi.

_Saturday afternoon 2:32PM_
Bajewa Zeezee tayi a tsakar gida tana kukan banza ita se an kaita gidan su Lubiee tunda yau ba school. Kota kanta Mama batai ba, hasali ma ignoring nata tayi ta shige d’akinta ta kwanta 2:40PM Baba ya dawo gida as always ya tambayeta whats the problem bayan ta irga masa ya share mata hawaye tare da fad’a mata ta kwantar da hankalin ta ze kaita gidan su Lubiee tunda yanada lambar Alhj. Maitafseer. Ba tare da b’ata lokaci ba ya kirasa bayan sun gaisa ya sanar dashi halin da ake ciki, cike da jin dad’i Alhj. Maitafseer yama Baba bayanin gidan sa dake Old GRA. D’aki direct Baba ya wuce ya tarar da Mama kwance “Hafsah! Hafsah tashi ko bacci kike?”
“Ya akayi Alhj? So nake in huta kafin La’asr please.”
“Hutu? Ai hutu be kama kiba.”
“Me kake nufi?” tayi maganan tare da miqewa zaune.
“Zaki shirya kanki da Zeezee yanzu in kaiku unguwa.”
“Unguwa? Unguwa a ina?”
“Zaki raka Zeezee gidan k’awarta Lubiee” yayi stating in an I-don’t-care manner.
“Lallai kuwa!” Mama tasa hannunta a kunkumi “ba inda zani, akan ganin k’awarta za’a tauye min hak’k’i, ina nan ba inda zani.”
“Semuga in zaman kanki kike a gidan nan na baki minti talatin ki shirya kanki da Zeezee wallahi in bakiyi haka ba ranki yana iya b’aci” nan ya sauk’e Zeezee k’asa, “karki damu kinji K’anwata zan kaiki gidan su Lubiee.”
“Toh Baba” anan ya fice. Mama tafi minti biyar a zaune tana hararar Zeezee sannan daga bisani ta mik’e ta hau shiri exactly after 30 minutes Baba yadawo d’akin ya tarar da ita sun gama shiri tsaf, dad’i sosai yaji “kaiii masha Allah, Hafsah ta bade kyau ba tsaya keda K’anwata in d’auke ku hoto.”
Dad’i sosai Mama taji dan yadda Baba ya yaba kyanta da kuma kwalyanta amman sede me? Batason nuna masa ta huce kan abinda yayi minutes ago, burning face tayi kan bataji me yace ba.

“Haba Hafsah ta? Menayi kuma yanzu? Hoton ne bakiso?”
“Ban sani ba” tayi speaking up finally.
“Yi hak’uri toh ki tsaya” remembering that tana son ta tambayesa kud’in ankon bikin ‘yar k’awarta yasa ta saki fuska taja Zeezee ya d’auke su hoton. “Yauwa masha Allah, gaskiya in godewa Allah da yasa a beautacious woman like you ta kasance mata ta” yayi maganar yana editing picture nasun.
“Uhm! Alhj ba de zak’in baki ba.”
“Ai kema kin sani Hafsah, a kullum dad’a kyau kike.”
“Uhm Alhj nace bikin ‘yar Aunty SDY fa ya matso.”
“Toh Allah sa ayi a sa’a ya kuma bada zaman lafiya mu tafi ko? Inason in wuce kasuwa bayan nayi dropping naku.”
“Ameen kud’in ashobe nakeso.” Ai take mood na Baba ya canza, a rayuwa ba abinda ya tsana kaman a tambayesa kud’i.
“Ke shikenan kullum cikin tambayan kud’i kina ruining happy moments? Mu tafi da Allah.”
“Bangane ruining happy momnts ba daga tambayan kud’i seka haura min sama.”
“Toh ni banida tashi mu tafi kina b’ata min lokaci.” Komawa tayi ta zauna tace;
“Ai wallahi ba inda zani ina nan seka bada kud’in nan had it been matter’n ya shafi Zeezee da without a second thought ka cire kud’i ka biya mata buk’ata wallahi nima ko ka bani kud’in ashobe dana gudumawa ko kuwa kaida K’anwarka kuyi ficewar ku” tayi stating in a serious tone. Ganin eh fa dagaske take ba inda zata inbe bata kud’in ba ya nisanta yace, “haka zaku k’are ai mutane sun d’au rayuwan k’arya sun aza wa kansu wai ba’a zuwa gidan biki seda ashobe toh Allah ya shirya ku wallahi”Zeezee kam se raba ido take ta kalli Mama ta kalli Baba.
“Ameen ka fad’i koma meh nide ka bani kud’in kawai shikenan.” Dogon tsuka yaja “mschww! Nawa ne kud’in?”
“Dubu ishirin ne duka, dubu goma na ashobe goma na gudumawa.”
“Har dubu goma zaki kai as gudumawa saboda auren Aneesa ne?” (blood sister ta)
“Muna zumunci sosai da Aunty SDY da kunya in kai mata abinda ya gaza dubu goma tunda akwai kawai ka kawo.”
“Mschw! Allah shiryaki wallahi” hannu ya sa a aljihu yaciro wallet nasa tare da irga fifteen thousand (15K) “amshi.” Hannu ta mik’a ta karb’a tare da irgawa bayan da tagama taga be cika ba, “ya haka Alhj? Sauran biyar d’in fa?”
“Abinda nake dashi kenan in na kwashe duka kud’in na baki me zamuyi cafani dashi gobe? Ki cikata da kud’inki maza tashi mu tafi.” Chan k’asa-k’asa tace, “ko a babu na rage hanya” wardrobe nata ta nufa ta adana kud’in sannan suka fice.

~* ~* ~*
Dai-dai 3:07PM suka isa gidan su Lubiee bayan sun fito daga motan Baba dake daga ciki yace, “se bayan La’asr in shaa Allah zanzo in d’auke ku.”
“Kai balaka shiga bane Baba?” Asked Zeezee.
“A’a K’anwata keda Mama na kawo ku ba-bye.”
“Toh se anjima” cewar Mama tare da jan hannun Zeezee suka shige.

*** Cikin d’an k’ank’anin lokaci Mama da Ummin Lubiee suka saba se hira suketa zubawa wane sun san juna dama da jimawa, a yayinda Zeezee da Lubiee ke chan suna ta wasa, sosai Lubiee taji dad’in ganin Zeezee, su ci abinci ma sunk’i se wasa suke a tsakar gida kasancewar gidan nasu nada sarari sosai. Chan suka shigo ciki suka sami su Mama a parlour inda ake ajiyewa Lubiee motar wasanta wanda yake nan Babba sosai, ciki ta shiga ta tuk’a sannan tasa Zeezee ma ganin Zeezee bata iya ba tad’au remote control d’in tana driving nata dashi. A hankali Zeezee ta koyi driving d’in itama seyi takeyi ana cikin haka Baba yayi wa Mama waya kan gashi shigowa zasu gaisa da Abban Lubiee se su tafi.
Bayan sun gaggaisa Mama ta d’ibo takalaman Zeezee dan sa mata ai atafir Zeezee tace bazata koma gida ba anan zata kwana in ma zata koma chan gida sede in da motan Lubiee zata tafi.
“Shin motan naki neda zakice zaki tafi dashi?” Lectures Mama. Cikin kuka Zeezee tace, “ni wayyayi shena tafi dashi” tana shure k’afa.
Se hak’uri parents na Lubiee da Lubiee ke bata amman ina se kaman ma sake tinzirata suke, if only zasu iya cewa ta d’au motan, atlast Baba yayi speaking up “taso toh K’anwata irin wannan kikeso?” Nan ta gyad’a mai kai.

_Bade sai mata zakace zakayi ba?_ Mama tayi maganan unbelievably a zuci.
“Toh shikenan za’a saya miki” Baba ya fad’a tabbatar wa Mama da zarginta.
“Alhj a ina ne ka sayo wa Lubiee?”
“Anan Central...” nan yama Baba kwatancen shagon.
“Toh thank you.”
“You’re welcome incase ya ganka Alhj ya bugeka price d’in is 42K.”
“Haha toh nagode mu tafi Hafsah” ya k’are maganan yana sharewa Zeezee hawaye. Baki Mama ta tab’e batare da tace komai ba, har gun motansu parents na Lubiee sukayi masu rakiya akayi ba-bye sannan Baba ya kunna mota suka tafi. A maimakon yayi hanyan gida seya kama hanyan kasuwa da Mama ta gano hakan se kawai ta girgiza kai “bade central d’in zaka wuce siyo wa K’anwarka motan ba.”
“Toh ina ruwanki? Ke bakiga kukan datake tayi bane?”
“Toh wallahi in haka ne nima se ka cika min dubu biyar d’in.”
“Se mugani ai” haka Mama naji tana gani Baba yaje ya siyawa Zeezee motar itama sede nata har yafi na Lubiee ma girma, her’s costs 50K. Ba rigimar da batai wa Baba ba amman yak’i cika mata wai se k’arshen wata itan da za’ayi biki tsakiyan watan yau.


*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com

PAGE 11



Isarsu gida Baba yasa Ibraheem ya ciro motar Zeezee daga mota, duk yaran se bin motan suke da kallo sun kasa zama gu d’aya a babban parlour ya dire motan Yasmeen da couldn’t hold it in anymore tace, “Baba motan waye?” Kafin Baba ya amsa Zeezee ta amsa, “nawa ne.”
“Ja chan gefe waze sai miki wannan k’aton mota?” Baban dake jinsu ko k’ala bece ba.
“Baba kaji Yashmeen wai ba nawa bane.”
“Seta hanashi zama nakin ai muga.”
“Baba wai dagaske motan Zeezee ne wannan?” Asked Omar.

*** Around 9:23PM
Zeezee fa ba wasa se tuk’i take ta shiga d’akin Mama ta fito tayi d’akinsu Mariam tayi parlour, ba inda bata shiga da motar tata har bathroom, Yasmeen da takeson tad’an d’ana itama taje ta samu Zeezee kafin ta baro parlour. “Zeezee ta d’an ara min motarki na nad’a kinji?”
“O’o manya bashuwa chiga.”
“Manya erinsu Adda Mariam da Ya Ibraheem ba? Yi hak’uri.”
“Ni o’o banasho.” Da k’yar Yasmeen ta iya shawo kanta ta yarda ta bata dan d’anawa, dududu da shigan Yasmeen befi minti d’ai ba Zeezee ta soma k’iriniya ita a bata motan ta Yasmeen da mota ya mata dad’i kuwa tak’i. D’an karen banzan ihu ta saki tare Baba ya shigo yana tambayan ko lafiya “ya haka? Me kikeyi k’atuwa dake cikin motan Zeezee?”,Yayi tambayar wa Yasmeen dake ta raba ido bayan ta fito daga motar. Nan Zeezee tamai bayanin komi, “yi hak’uri K’anwata kekuma ki sake shiga mata mota kiga k’atuwar banza kawai.”

Washegari da safe bayan sun karya Yasmeen ta saci jiki tayi store room da ledarta a hannu, gongonin madaran Zeezee ta bud’e tana d’iba tana cikin haka Zeezee ta shigo d’aukan juice ta ganta “laaaa!! Yashmeen!” Ihunta yasa Yasmeen b’arar da madaran dake hannuntan. “Wayyayi sena gayawa Baba kina d’iba min madala” nan danan Yasmeen tashiga tarawa “yi hak’uri Zeezee dan Allah karki fad’a mai zemin masifa.”
“Wayyayi shena fad’a” nan ta juya
“Tsaya kiji, zan had’a miki naki kema a leda seki sha da akwai dad’i sosai.”
“K’alya kina shon kimin wayo.”
“Wallahi ba k’arya ba” wasu ledan ta sake cirowa tasawa Zeezee madara da milo ciki sannan itama tayi haka anata sede nata yafi na Zeezee yawa aikuwa uwar rigima ta hau ihu “wayyayi naki yafi nawa yawa ki k’aya min.”
“Toh kiyi shiru mana sekin fallashemu ne.”
“Ni sekin k’ala min” tasake sa kuka ai kafin su hankara Mama ta diro d’akin tare da kamasu red-handed. Take Yasmeen ta b’oye ledarta a baya Zeezee kuwa se fitina take “ni ki k’ala min”
“Me za’a k’ara mikin?” Ido Yasmeen tama Zeezee nufin tayi shiru ta b’oye nata itama amman ina ita bata nan take ba, “Yasmeen ne tasha min madala kad’an nata da yawa.”
“Madara!” Exclaimed Mama, “Yasmeen ban hanaki d’iban madara kina sha ba?” Kame-kame Yasmeen ta shiga tana b’arin baki.
“Ni ki k’ala min” Zeezee tayi breaking silence d’in.
“Oya kawo madaran nan dukan ku” ba musu Yasmeen ta kai nata “kema Zeezee bani naki” kaman dagske ta nufa wajen Mama kamar kyaftawan ido tabi gefenta tasa gudu taje ta samu Baba tasha madaranta tayi nak!

Da Azahar bayan fitan Baba, kowa na zaune tsakar gida yana harkan gabansa Mama ta duba ta duba bata ga Zeezee ba haka kawai jikinta ya bata aduk inda take b’arna take “Yasmeen jeki dubo min me Zeezee take, shirun yayi yawa” da ‘toh’ ta mik’e cikin gidan kap ta duba bataga Zeezee ba chan bayan BQ ta tsince ta da irin manya-manyan dusten goge k’afan nan ta had’a ruwan kumfa tana dirje k’afanta dashi in aka tambayeta haka taga me wankin su nayi any moment ya gama wanki. “La ha ilaa!! Mama zo kiga abinda Zeezee keyi dirje k’afanta take da dutsen Sabi’u.” Daga tsakar gidan Mama tace, “wallahi Zainab ki tashi kibar wajen kamin na iso, ke ina kika ga k’afan ma bale kice zaki wani dirje, bar gun nace kokuwa inzo in miki shegen duka gashi dama Babanku bai gida.”

“Kuma wayyayi balin shake baki shweet d’ina ba tunda kin fad’awa Mama.” Zeezee tayi maganan wa Yasmeen tana barin gun, koda tazo shigewa ciki bata ce wa Mama dake ta faman kiran sunanta ko uffan ba. D’akin Mama ta nufa ta tara teddy bears nata sannan ta bud’e turaren Mama ta zazzage kan teddies d’in k’amshi har waje malam!
“Tsaya wannan ba k’amshin turare na bane?” Mama tayi maganan tare da miqewa ta nufi d’akinta. “Ai ba turare d’aya bama” cewar Mariam. Mama na tabbatar da hakan ta kama Zeezee ta mammaketa bada jimawa ba Baba ya dawo sarkin d’aure wa k’arya gindi, balbale Mama ya shiga yi bayan na ya lallashi Zeezee.

Can da yamma, bayan fitan Baba masallaci yaran kuma Islamiya Zeezee tayi parlourn Baba kawai setaji bari ta gwada cin buttons na remote yau, one-by-one ta soma bi seda ta cinyesu tas sannan ta ajiye. Ta ajiye kenan kafin ta bar gun Baba ya dawo harfa yayi d’aki wani abu yace mai ya dawo dan yadda yaga Zeezee na raba ido “Laaa’ila!” Yayi exclaiming, gudu Zeeze tasa zata bar gun ai tuni ya kamota yana bin remote na Plasma TV’nsa da kallo yace, “meh haka? Remote abinci neh da zaki kama ki cinye buttons d’in!” Lamo tayi tana kallonsa a yayinda idanunta ke cikowa da hawaye “dan bana zaneki koh?” A dai-dai nan Mama tashigo parlourn “ya haka nakejin hayaniya?”
“Kalli fah! Remote d’i TV’n ta cinye kap! Abin naki lafiya kuwa Zeezee?”
“Ahap! Ai kad’an ka gani wallahi wataran tab’arya zata d’au ta fasa TV’n nan naka dashi ba wai kai komi tayi dai-dai neba, this is just the begining Zeezee kinyi dai-dai.”

“Wani irin magana kike haka Hafsah, kamar ya zakice mata tayi dai-dai? Remote fa ta ci.”
“Da take kira na da suna na kota zagen kota min b’arna me kake cewa? Yarinya ace abarta koba haka ba? kaima seka barta yanzu yarinya ce, Auta ta taho muje kici abinci” da gudu Zeezee tayi gun Mama ta d’aga ta.
“Wallahi kin kyauta ke kuma wai bakinki razor ba ki sake cimin remote kigani mschww!”
“Ramin mugunta tauna shi gajere!” Mama tayi stating tare da baro parlourn.

~* ~* ~*
Monday morning as always and usual Zeezee tayi ta daru da k’yar aka samu aka shiryata school seda taga Lubiee hankalinta ya kwanta.
Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa Zeezee, rikicin yau daban na gobe daban ga wani masifaffen rashin kunyan da take tashi dashi kuwa ba wanda ya isa ya tab’ata a gidan, ka tab’ata ma jikin ka ze ma bayani. Ba yadda Mama batai da Baba asa Zeezee a islamiya ba sam yak’i wai seta k’ara girma. Ana cikin haka bikin ‘yar Aunty SDY ya iso duk events da akayi Mama tasamu hallara, sauran kai amarya Kano da za’ayi da kuma yin dinner da ya rage, cikin sauk’in kai ta tambayi Baba izini ya kuma bata.
Kayakin Mama ne baje kan gado se had’a akwatin ta take tana cikin yin hakan Zeezee ta shigo d’akin delibrately matching Mama’s ironed clothes da motan ta.

“Sabon iskanci nekuma haka Zeezee kina ji kina taka min kaya matsa min!”
“Toh ba na miki honk ba” ta murgud’a baki.
“Dake da honk d’in uwaku.”
“Kema-”
“Wallahi kika kuskura kika zageni dukan ki zanyi a d’akin nan” Mama tayi saurin katse ta. “Ni thank god ma gobe zanyi tafiya in huta wallahi.”
“Nima shena biki.”
“Ai da inyi tafiya dake gwara na fasa tafiyan” ba tare da Zeezee ta tanka Mama ba taja motan ta tayi d’akin Baba kukan munafirci ta soma tana mishi bayanin abinda ya faru ba tare da b’ata lokaci ba ya mik’e suka dawo d’akin Mama aiko tana ganinsa jikinta ya bata Zeezee ce takai k’ararta. “Wallahi Ahj inma batun inbawa Zeezee hak’uri kazo yi is better ka koma dan ba bata zanba yau abin nata is getting out of hand.”
“Kinsan kinyi laifi kenan, anyways ba abinda ya kawoni ba kenan ki had’awa Zeezee kayakin ta itama da ita zakiyi tafiyan.” Zumbur Mama ta mik’e tsaye tana zaro ido, “da wa zanyi tafiyan? Wallahi baran je ko ina da wannan maras kunyan ba.”
“Kin de jini” ya fad’a authoritatively.
“Wallahi bazan yi tafiya da yarainyan da bata jin magana naba, kalan taje tabani kunya a idanun jama’a, ace yarinya sede bata ga abu gun yara ba tace itama se an siya mata kuma da kake wani cewa zata bini makarantar ta kuma fa? Kai zaka je mata?”

“Ba yau Thursday ba, Friday ne kawai bazata jeba ai, Sunday kun dawo Monday ta wuce school koba haka ba?”
“Wallahi ba haka ba, ba inda zanje da wannan yarinyan ehe!”
“Ni shena biki Hafsah!” Zeezee tayi maganar cike da tsiwa da fitsara.
“Nifa na gaya miki Hafsah.”
“Wallahi da inje da ita gwara na fasa tafiyan ai dama anyi me yawan, dinner ne daman kawai ya rage se in fasa zuwa.”
“Eh sede ki fasan amman muddin zaki sekinje da Zeezee.”
“Eh nafasan...” Bayan ficewar Baba, Mama ta d’au wayarta takira Aunty SDY tayi making up excuses kan bazata samu zuwa ba dan ta gwammaci missing bikin da tai tafiya da Zeezee.

★★★
Haka Allah

11 / 98