Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
"Ehemm ina jinki."
"Mama I called Mama Babba..." duk yadda sukayi da Mama Babba ta gayawa Mama tana kuka sosai. Kwantar da kanta Mama tayi a jikinta tana bubbuga bayanta "shhh its okay kinji? Kede ki cigaba da addu'a kawai Allah ya kawo miki miji na gari ba lallai se Ya Al'ameen ba."
"Mama but ni shi nakeso, banason kowa se shi."
"Toh Zeezee ya zakiyi? Wata ta riga ta rigaki dole ki rungumi k'addara kiyi hak'uri."
"Mama banjin zan iya hak'ura da kalan soyayyan da nakeyi wa Ya Al'ameen, this feeling has never happened to me. Gani nake as if idan ban sake kasancewa matarshi ba ina iya rasa raina gabad'aya." Da sauri Mama ta d'agota daga jikinta, "kinada hankali kuwa? Banason sake jin maganan nan daga bakinki kina jina ko?"
"Mama all I want is to be with him and make him happy, I love him so much."
"I know shiyasa nace ki dage da addu'a, idan you and Ya Al'ameen are destined to be together once again you two shall remarry have faith okay?"
"Okay Mama thank you."
"Tashi kiyi alwala kiyi sallah na riga na had'a lunch."
"Toh Mama thank you." Mama na ficewa ta nufi bayi tayi alwala ta idar da sallanta. Hanky'n Al'ameen daya bata jiya wanda ta adana sa ta ciro tare da kaiwa kan hancinta tana shunshuna daddad'an turarensa me sanya mata kwanciyar hankali. Kaman jiya yau ma ta yini tana tunanin Al'ameen. Da daddare kamin ta kwanta ta kira Hjy Sadeeyah inda ta gaisheta, bayan gaisuwa Hjy Sadeeyah tayi mata ta'aziyya sannan Zeezee ta nemi gafararta itama sosai. Tun Hjy Sadeeyah batayi niyyan yafe mata ba amman jin yadda Zeezee tad'an bata highlights kad'an daga kalan rayuwar auren da tayi living with Adeel yasa tuni ta yafewa Zeezee takuma tausaya mata sosai inda tayi mata addu'a kan Allah ya kawo mata miji na gari daze kula da ita. Zeezee na son sanar da Hjy Sadeeyah akan tayi mata hanya ta dawo da ita wa Ya Al'ameen koda kuwa as his second wife ne zata dawo, she don't care tanaso muddin she'll be able to show him love and comfort amman ta kasa gaya matan saboda batada courage haka tana ji sukayi sallama. Kuka kuma ta d'auro daga nan har bacci 6arawo ya sace ta inda tayita mafarke-mafarken Al'ameen. Washegari da safe bayan ta gama chores nata ta lalimo wayan Mama ma yau ta kofi numban Ya Al'ameen. So take ta kirasa taji idan still yana gari amman ta gagara seya kusan shiga seta katse. At long last ta samu ta kira san.
"Hello" ya fad'a a lokacin da yayi picking. Muryansa da bata iya ignoring ne ke neman wullata dreamland wanda tayi sauri ta amsa da "Ina kwana Ya Al'ameen?"
Yana jin muryar ya gane nata ne, "Zainab."
"Na'am Ya Al'ameen ina kwana?"
"Lafiya kin tashi lafiya?"
"Lafiya ya gajiya kuma?"
"Alhamdulillah."
"Uhn nace kana gari ne ko har ka tafi?"
"Ina nan se gobe zan tafi yau zan kammala abinda ya kawoni in shaa Allah."
"Toh Allah ya taimaka, ko me ya kawo kan amma?" So take taji ko ze iya fad'a mata da bakinsa aure ze sakeyi. Shiru yayi na d'an wani lokaci sannan ya amsata finally, "Allah ya sake azurta ni ne Zainab, I'll be getting married in some couple of months." Hannu tasa a face nata inda tajiyo hawaye sosai nata kan zuba, rawa muryanta ke tace "Allah sarki, Allah baku zaman lafiya toh ya kuma tabbatar da alkhairi. Whoever she is, she should know that she is lucky to be blessed with an affectionate and patient husband as you, Allah bata ikon farinta maka." Besan me ba amman seyaji dama be sanar da ita ba, ko be tambaya ba yasan kuka Zeezee ke don jin yadda muryarta ke rawa sosai. Amman kuma why is she crying? Does she wants him back? So take ta dawo mishi ne komeh? But anya? Ai Zeezee never loved him. Ignoring this thought ya amsa addu'o'in da tayi mai da "ameen Zainab thank you kema Allah had'aki da wanda zaki so ya kuma soki." A ranta tace that person is you.
Hawayenta ta share sannan tace, "kana gida ko?"
"Eh ina gida Zainab wani abu neh?"
"Lunch nakeso na kawo maka."
"No please you don't have to karki gajar da kanki zansa asiyomin."
"No please I insist Ya Al'ameen don't reject my offer please."
"Zainab seriously I don't want to be a burden to you."
"Shikenan toh" tayi maganan sounding sad and defeated.
"But in kinga its okay with you, ba komai nine da godiya."
"Thank you Ya Al'ameen."
"It is I who should be thankful."
"Sena shigo toh."
"Ki taho min da Ramlah."
"Ramlah zata islamiyya by then" ta amsa da murmushi kad'an a fuskarta wane yana gabanta.
"Ayyah to ki gaishemin ita."
"Yauwa se anjima" jira tayi yayi hanging sannan ta sauk'e wayar ta ajiye a gefe. Tunanin me zata girka masa ta shiga yi amman kwata-kwata she can't think of anything. Haushin kanta taji for not paying attention before to know what dish was her husband's favorite. Zama tayi ta shiga tunani sosai wani abinci yafi son siya adan? miyan ganye da tuon shinkafa yafi siya da kuma rice and stew. Sanin bata iya yin miyan ba yasa ta yanke hukuncin yi mai rice and stew.
In less than 3 hours Zeezee ta gama had'a basmati rice and stew nata daya sha kaji dakuma co-slow nata a gefe together with kidney sauce. Cikin had'ad'd'un food warmers na Mama da ake sawa Baba abinci aciki ta zuba mishi abincin, tana d'ago flask d'in kawai ta tuna da Baba. Zama tayi a kitchen din tayi mai addu'a da dama harda 'yar k'wallarta sannan ta tofe ta juye abincin ciki ta shirya komi cikin wata fancy basket sannan ta ajiye kan counter ta nufi d'akinta don yin wanka ganin sha biyu ya wuce.
Tana cikin wankan ne Mama ta dawo daga islamiyya inda ta nufi kitchen dan shan ruwa, achan ta tarar da basket da Zeezee ta had'an. Bata ta6a ba ta wuce d'akin Zeezee anan ta tarar da ita tana wanka. Zama tayi ta jira fitowarta inda take tambayarta "waya kawo basket dake kitchen?"
"Ba kawowa akayi ba Mama."
"Ba kawowa ba? Ban fahimta ba."
"Ni na girka naki dana Ya Omar nakan dining table."
"Wancan kuma fa?" Tayi maganan tana pointing direction na kitchen.
"Na... na..." sekuma tayi shiru.
"Ki gayan mana na waye?"
"Na Ya Al'ameen ne."
"Oh ni Hafsah! Yanzu girki kikayi ma bawan Allan da bakisan ko yana gari ba kokuwa a'a?"
"Mama I called him and asked yace min se gobe ze tafi."
"Toh me had'in ki da kai masa abinci? Se ya fassaraki tukun ko?"
"Mama fassaranin nake so yayi saboda yasan I love him ko ze tausaya min ya dawo dani koda as his second wife ne ni ban damu ba."
"Oh! Toh nikam babu bakina acikin wannan abu."
"Eh naji amman please kice Allah bani sa'a kinji Mama?" Shiru Mama tayi danko Zeezee bata isheta da kallo ba. "Please..." ta sake pleading.
"Naji Allah baki sa'a."
"Ameen Mama thank you."
"Ze aiko masu gadinsa ne su zo su kar6o koya?"
"Ni zan kai masa."
"Oh! Zainab!"
"Please Mama karki min baki kince Allah bani sa'a ya isa kinji please." One more look Mama tayi mata sannan ta miqe tare da ficewa.
Nan da nan Zeezee ta shafa mai tasa kaya tayi Sallah sannan tayi applying light makeup wanda ya mugun amsarta ba kad'an ba. Material gown na tiger design red and brown tasa tare da yafa red gyale a kanta ta nannad'e a wuyanta. Shoe and bag nata ma red tasa, tana cikin aikin feffesa turare wayarta ya shiga ruri. Ganin Ya Al'ameen na flashing akai tayi sauri ta d'aga "hello Ya Al'ameen?"
"Zainab nace ba sekin fito ba I'll send Saje yazo ya kar6a abincin kinji? " Shi Al'ameen besan zuwanta da biyu bane, k'arya ta had'a mai tace ta riga ta fito saboda zata wuce gidan friend nata daga nan.
"Oh, toh shikenan sekin iso." Nan ya katse. Tana gama abinda zatayi tayi sallama da Mama sannan ta fice. Tun rabuwanta da Al'ameen bata sake taka corner'n gidan nasu ba se yau, ji take ina ma ace ya dawo da ita d'akinta ne. Tana k'arisawa gaban gidan tayi parking a waje sannan ta fito da basket d'in ta danna bell. Within seconds guard yazo ya bud'e tare da yi mata sannu da zuwa. Basket d'in yaso amsa amman ta hanasa, sebin gidan take da kallo a yayinda take sake missing gidanta sosai. A parlour ta tarar da Al'ameen yana sanye da farar vest revealing his muscular body da kuma sky blue wandon jamfa. Tana shigowa ya miqe tare da yi mata sannu da zuwa, se kallonsa take ta kasa dena staring. "kuma su Saje suna kallonki basu kar6eki ba?" Kai tayi shaking da wuri;
"No ni na hanasu, its no big deal" ta amsa tare da ajiye basket d'in kan centre table.
"Toh Zainab thank you kinji? Ya Mama."
"Lafiyanta k'alau" ta amsa still a tsaye tana wasa da bakin gyalenta. So yake yace mata ta zauna amman kuma ganin how awkward it'll sound yayi shiru. "Toh ni zan koma."
"Toh Zainab thank you" d'aya daga cikin throw pillows dake kan kujeran da ya tashi akai ne ya d'aga tare da d'ago kud'in dayasa cikin wata envelope.
"Zainab" ya kirata alokacin da har ta juya ta soma tafiya. Chak ta tsaya tare da amsawa "na'am?"
*MIEMIEBEE. Team #YGC!π*
Beeenovels.blogspot.com
ππππππ
πππ πππ
πβ£π
β£β£
β’Β°β’β
β’Β°β’ β’Β°β’β
β’Β°β’
Β°β’ β’Β° Β°β’ β’Β°
Β°β’Β° Β°β’Β°
*βYAR GATA CE!*πΈπ»
β’Β°β’β
β’Β°β’
Β°β’ β’Β°
Β°β’Β°
*_written by miemiebeeπ_*
*March, 2017*
6β£0β£
Takawa yayi har izuwa gabanta sannan ya miqa mata envelope d'in. K'in amsa tayi instead seta tsaya tana kallonsa bewildering. "Amsa Zainab naki ne."
"Nawa kuma?"
"Don't reject my offer also amsa kinji." Kai tayi saurin kad'awa "no Ya Al'ameen thank you ni don Allah na kawo maka."
"I know ni kuma as kyautatawa nake son na baki, amsa kinji?"
"No tha-" bata k'arasa maganan ba ya d'aga hannunta ganin haka tayi saurin kulle tafin hannun nata. "Yi hak'uri ki kar6a kinji?" Kai kawai take kad'a mai, "in kira Mama ince na baki kyauta kin k'i kar6a?" Nan ma kan ta sake kad'awa. "Toh bud'e ki kar6a kinji?" Seda yayi dagaske sannan ya samu ta bud'e hannun yasa mata envelope d'in tare da kullewa. "Thank you kinji?" Me yake shirin gani? Kuka Zeezee ta rushe dashi a wajen.
"Oh God! Zainab did I say something wrong? I take it back" Kai kawai take kad'a mai ta kuma kasa dena kukan. "I'm sorry Zainab please kibar kukan, in kud'in ne bakiya so I'll take it back but please stop crying" yayi maganan har yanzu yana rik'e da hannunta. Ba kalan surutun da Al'ameen beyi ba gabad'aya Zeezee ta tayar mishi da hankali gashi duk maganan da yayi mata sede ta kad'a mai kai. At long last tayi magana tace, "ba kai bane Ya Al'ameen." D'an relief yaji "toh wayene?" Ya tambayeta sede Shiru ba response. "Tell me kinji? Is this about your Ex?"
"No."
"Then waye?"
"Ya Al'ameen I want you back, I want to go back to you, I want to be your wife once more." Ta furta tana kallon k'asa. Hannunsa dake rik'e da nata ya sake a hankali cike da mamakin jin wannan kalamu daga bakin Zeezee. Da sauri ta d'ago kan ta tana kallonsa. "I know am wrong to say this, you'll be getting married in some couple of months but I can't keep it in again. I love you Ya Al'ameen, I love you so much that I can't afford to lose you for the second time, koda as your second wife ne bring me back, I just want to make you happy one last time." Tunda ta fara maganan kallonta Al'ameen ke as yadda take kallonsa itama tana hawaye. He never expected to hear all of these words from Zeezee. Since when ta fara sonshi? Why him and not Adeel yanzu? Meya faru tsakaninsu da bata maganansa yanzu? Wani irin cutarwa yayi mata har yasa bata sonsa haka yanzu?
"Zainab..." ya kirata a nitse.
"Please don't say no Ya Al'ameen, in kana ganin Mama ko Hjy Sadeeyah bazasu yarda ka dawo dani bane thats not true. I've called them both and have asked for their forgivenesses kuma sun yafe min. I just want to be with you and make you happy, I want to prove to you just how much I love you Ya Al'ameen. I can wait, koda it'll take me eternity ne muddin ka amince zaka dawo dani d'akina, please don't say no. I'm sorry if my words have offended you but I just need you to know how I feel about you." Ta k'are maganan cikin kuka sosai wanda ta mugun bawa Al'ameen tausayi. Just what hell did she went through a rayuwar ta da Adeel? Ji yake kaman yaje ya 6a66alla Adeel into pieces for hurting Zeezee like this. Jin yayi shiru har yanzu tace, "I should go, thank you for listening to me." Hannunta ya rik'e immediately tana juyawan, chak ta tsaya kanta na pointing downwards. Hannu yasa a aljihunsa ya zaro hanky sannan ya d'ago face nata ya shiga share mata rolling tears nata affectionately. "Don't cry again kinji?" Da k'yar ta iya nodding masa kai saboda wasu sabin hawayen da takejin suna shirin 6allo mata. Hanky'n kawai ta kar6a ta juya ta fice a guje se gun motarta inda ta zauna tayita shar6an kuka, gidansu Lubiee da take son zuwa ma bata jin zata iya zuwa yanzu. Seda ta tsagaita kukan nata sannan taja motarta ta koma gida inda har ta isa d'akinta Mama bata ganta ba.
***
Abincin da ta kawo mishi ya d'iba kad'an a plate amman ko kad'an ya kasa ci saboda tunanin Zeezee zallah da yakeyi. Duk irin aromatic taste da abincin nata yayi masa ya kasa yaci kamar yadda yakamata don tunaninta dayake tayi. He knows exactly what she must be going through, saboda he went through it before shima. Baze iya zama yana ganinta tana shan wahala haka ba knowing there's something he can do. Tausayinta yake sosai but inhar Mama tace she ain't letting him ya dawo da Zeezee dole ta hak'ura kaman yadda shima ya hak'ura ya cireta daga ransa lokacinda ta auri Adeel. Even though har yanzu yana son Zeezee, but not as before ko a yanzun ma ze dawo da ita ne saboda abinda take so ne not because he loves her as he does before. Yanzu bama wannan ba, Mama Babba zata yarda ne ayiwa 'yar uwarta Murja kishiya? Ji yayi tunaninsa gabad'aya ya dak'ule mai dan dole ya fita ya shiga training men nasa in order to let go off tunanin nata. Kamar yadda take son miyar da tunanin Al'ameen hobby, haka yau ma ta yini ta kuma kwana da tunaninsa. Koda Mama ta tambayeta ya suka k'are da shi ce mata tayi babu ta kai mai abincin ne yabata kyautan d'imbin kud'ad'd'en data nuna mata d'azu.
Washegari Al'ameen ya shirya ze koma Kaduna, half of him is telling him ya sanar da Zeezee while half of him na ce masa ya basar. Har ya shiga mota sun d'au hanya se kuma yaga be kyauta mata ba don haka yayi asking driver'nshi da yayi parking sannan ya kirata. Kaman me jiran call nasa kafin ya shiga ringing ta d'aga tare da yin sallama.
"Wa'alai kumus salam Zainab."
"Ina kwana Ya Al'ameen?"
"Lafiya ya gajiyan ki na jiya?"
"Ba gajiya."
"Kaman kinsan rice and stew is my fav, thank you kinji? Ashe Zainab namun is such a great cook."
"Kai Ya Al'ameen banda zugi."
"Seriously fa ga ragowan nan nayi heating kafin mu isa KD zan tsaya inci."
"Aww har kun d'au hanya ne?"
"Eh nace bari na