Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
batun but he was afraid kar gabanta ya fad'i abu ya samu baby'nsu.
Bacci ne yayi awon gaba da Zeezee se Maghrib ta tashi tayi Sallah har anan tak'i kunna wayar tata shiko Al'ameen yini ranan yayi yana trying numbers nata and duk basu shiga haka ya kasa bacci ranan. Ace for a whole day beji muryan Princess tasa ba be kuma sata a ido ba ai wannan k'anin mutuwa ne. Apology messages yata tura mata wanda se a washegari da ta kunna wayar ne ta gansu still bayan ta karance su bata ji ta sauk'o ba da abinda Al'ameen ya mata. Taya zeta wasa mata da hankali haka? Idan har budurwarsa tacan ne ta ke rik'esa he could have simply told her akan wasa da hankalin daya ta mata. Wayan na a hannunta Al'ameen ya shiga kira nan ma tana gani tak'i d'agawa. Yayi mata missed calls bil adadi da text messages yana pleading nata da tayi hak'uri ta d'aga he is so sorry and damn missing her sweet voice. Seda ta gama basa wuya sannan ta d'aga wayan tare da yin shiru.
"Thanks Gee! Thank you for picking up Princess." Shiru tayi bata amsa ba, "Princess you there?" ya tambaya jin shiru.
"Ina kwana?" ta gaishesa briefly.
"Princess please kiyi hak'uri and let me explain banason inga kina fushi dani haka ko bacci na kasa yi jiya I've been thinking about you the whole night."
"Me kayimin kake bani hak'uri haka? Ni nace kamin wani abu ne? I didn't."
"Come on Princess, ni kaina nasan me laifi ne ni shiyasa nake son in baki hak'uri da ki yafe min, I'm sorry."
"Laifin me kamin Ya Al'ameen?"
"Yau ko Sweetheart babu, Oh God Princess am sorry please."
"Ni wai nace kamin laifi ne?"
"Baki fad'a ba amman ni nasan na miki, Princess bawai ina yaudarar ki bane ko wani abu, I just didn't want to tell you saboda gudun abinda ze haifar. Ba a banza 'yan office d'ina suka k'aramin 2 weeks d'incan ba, seda suka min prolonging zama na har na zuwa 3 months and I accepted it saboda I thought you were sick lokacin, yanzu kuma sun k'ara min 1 week again akai probably in 3 weeks time zan shigo in shaa Allah kiyi hak'uri please."
"All these and you didn't tell me Ya Al'ameen? Taya kakeso in yarda yanzu? I asked you at first kace min a'a se yanzu kuma kake jeromin wannan bayanan? It would have been better idan fili kafito kace min akwai wacce ke rik'e ka a chan akan wasa da hankalin da kake tayi min, I was sick yestarday, leg cramps ke damuna sosai amman na tashi ba kalan aiki da girkin da ban maka ba duk ya tashi a iska, kasan ba tahowa zakayi ba why messing with my brain and making me look like an idiot, tell me taya bazan ji haushi ba Ya Al'ameen?"
"Yaaa Salam! Princess wani irin magana kuma kike haka yau? I am sorry please."
"Thats what your actions are telling me Ya Al'ameen sau nawa kake ce min zak shigo amman har yau shiru, idan ba rik'e ka wata take ba explain the reason for all these lies."
"Princess I can't stop you from imagining and thinking of whatsoever kikeso saboda you have every single right to but ki sani wallahi I am not cheating on you, I will never cheat on you. Inada perfect wife why will I search for a better one? Its not possible. I love only you Princess and no one else and am sorry for lying to you all these times, banida enough courage da zan sanar dake ne da nayi a long time ago kiyi hak'uri please, I'm sorry and I love you so much." Kasa cewa komi tayi saboda yadda kalamunsa suke melting mata heart. Meyasa tayi judging nasa da sauri haka? Gaskiya ne Al'ameen baze ta6a cheating akanta ba amman kuma meyasa zuciyar ta takasa yarda da hakan har yanzu?
"I'm sorry also" kad'ai ta iya cewa dashi.
"You are still mad I can sense that, just know that I'll never give up har se kinyi believing d'ina I love you morethan I do love myself."
Nan ma "thank you" zallah tace dashi. Ba k'aramin damunsa I don't care short responds nata suke ba.
"Ya k'arfin jiki?"
"Alhamdulillah." Ko ya aiki tak'i tambayarsa.
"How's my Little Princess?"
"She's fine." So yake ya sata surutu amman se basar dashi take, da a da ne cewa zatayi ba Princess bace Soldier ne, he miss her being herself.
"school fah?"
"Muna tests ma."
"Wow really? Not so fast, Allah ya taimaka ya bada sa'a I love you."
"Ameen thank you zanyi karatu se anjima."
"Toh Princess, I love you."
"Aha bye" tana kaiwa nan ta katse wayar.
Daren ranan Al'ameen ya kasa bacci se tunanin Zeezee yake besan ya zeyi ba ya gyara tsakaninsu yasan koda ze had'a sama da k'asa 'yan office nasa baza su barsa ya koma gida ba. Haka nan tun daga ranan idan ba wai Al'ameen neba ya kira Zeezee ita bata d'aukan waya ta kirasa. She is damn missing him har wani rashin lafiya rashin sa ke sata but she can't help it ta kasa gane dalilin da zesa yayi ta mata k'arerayin da ya mata, meya miyar da ita? Doll baby? koda tace zatayi believing abinda ya fad'a mata seta kasa. Sunyi haka na two more weeks Al'ameen da k'yar ya samu ya kar6a break bayan k'aryan daya musu na cewa matarsa batada lafiya nan ma one week break kad'ai ya samu da k'yar. Sam be sanar da Zeezee ba yanason suprising nata. A ranan da ze taho da safe ya kirata dan su gaisa. Seda call d'in ya kusa yankewa ta d'aga "hello Ya Al'ameen?"
"Na'am My Princess ina kwana?"
"Ina kwana Ya Al'ameen?"
"Lafiya ya kike? Ya Little Princess d'ina?"
"We are all good."
"Leg cramps sun dena?"
"Da sauk'i yau."
"I miss you Princess, I miss your crazy talks, your smile I miss everything, I promise to make it up to you."
"Uhm ya aiki?"
"Na gaji da shi I want to come back to my Princesses."
"Ina d'an aiki kad'an will call you up later." Zaune take a d'aki tana buga candy crush amman take cewa tana aiki.
"Princess haka kike avoiding d'ina yanzu?"
"Ba avoiding naka bane inason in k'are aikin da naken ne, ga baby se kicking yake gabad'aya ya dameni."
"Awcch! Sorry Princess, just some months to go finally zamuyi meeting Little Princess namu."
"Allah ya kaimu."
"Ameen Habibtee."
"So sena kira ka anjiman."
"I love you so much."
"I know se anjima" tana kaiwa nan ta katse.
Cikin d'an k'ank'anin lokaci hadari ya had'e a garin Abuja gashi dai-dai time na flight na Al'ameen kenan noway jirgi ze iya tashi. Driver'nsa dake Abuja yayi wa magana akan ya taho zasu tafi by land. Driver ya rasa why Al'ameen is so desperate haka, mostly rananda wheather bashida kyau yana fasa tafiyan amman wannan karan ba yadda beyi da Al'ameen ba yak'i jinsa. Haka suka d'au hanya wajajen k'arfe hud'u su Al'ameen suka shigo su garin Bauchi.
*****4:30pm Zeezee na zaune a parlour ta baza agwalu6a a gabanta se sha take da book akan cinyarta tana karatu ta jiyo rurin wayarta. Ganin Al'ameen taji kaman ma kar ta d'aga har yanzu bata hushe ba ita, sanda ya kusan tsinkewa tayi picking up "hello Ya Al'ameen?" Jin different voice from na Al'ameen ya sata cikin duhu.
"Please ina magana da matar me wayan nan ne?" Ba k'aramin rud'ani ba question na mutumin ya jefata.
"E... eh itace matarsa ce."
"Toh Madam please ki kwantar da hankalinki ki taho Teaching Hospital yanzu."
"Teaching hospital?" Ta zabura tana zaro ido a yayinda cikinta yake mugun d'aukan ruwa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Teaching hospital? Meya same sa please? Teaching hospital na wani gari?" Take ta shiga zubda hawaye.
"Na nan garin Bauchi."
"Bauchi? Ba a Abuja yake ba? Bawan Allah anya kuwa ka gane da wayan wa kake magana? Ya Al'ameen miji na fa a Abuja yake ba a Bauchi ba."
"A hanyarsu na tahowa Bauchi yau ko ince bayan shigowansu Bauchi a bayan gari armed robbers suka yi attacking nasa da driver'nsa. Shi mijin naki sun har6esa-"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fad'a tare da katse sa, "Ya Al'ameen!" Tasa wani irin d'ankaren ihu na bakin gate na iya jiyota. Kawai ji tayi jini na bin k'afafunta tsabagen kalan tashin hankali da tsan-tsan masifan data tsinci kanta a ciki. Se k'aran fad'uwan abu kukeji a k'asa rigijib! "Hello? Hello?" Mutumin ketayi amman ba response kasancewar sumewan da Zeezee tayi. Sakamakon ihun da tayi yasa Sadeeq shigowa don tabbatar da ko lafiya knocking ya tayi bisa k'ofan jin ba response kawai ya fad'a ciki nan ya samu Zeezee cikin pool of blood a sume. Da gudu yayi kanta tsoron ta6ata ma yake ganin he is running out of time yasa kawai ya cinci6eta se Teaching Hospital achan aka shiga bata taimakon gaggawa don stopping bleeding d'in before yayi affecting baby'n nata. Kafin nan kuma Sadeeq ya kira layin Al'ameen inda yata ringing ba a d'aga ba. Mota ya shiga ya wuce gidansu Zeezee inda yake sanar da Mama halin da ake ciki. Nan da nan tasa hijabinta suka fice kwata-kwata basuda labarin halin da Al'ameen yake ciki.
_30 more minutes..._
K'ofan d'akin da Zeezee ke ciki ne ya bud'u revealing a Dr da sauri Mama tayo kansa. "Dr how is she?"
"Calm down Ma'am she is fine ki kwantar da hankalinki."
"Alhamdulillah! Baby'n nata fah?"
"Both the Mother and child are fine, mun samu munyi stopping bleeding d'in before it went any far yanzu ma zaki iya shiga ganinta."
"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Thank you Dr Allah ya biyaku."
"Ameen excuse me please." Bata kai da shiga cikin d'akin ba Sadiq ya iso gun yana gudu yana hak'i. "Hajiya! Hajiya" Chak ta tsaya tare da kewayowa.
"Sadeeq lafiya?" Kai zallah yake kad'a mata "Hajiya I just received a call."
*MIEMIEBEE. Team #YGC!🎀*
*ZAIMEEN flames🔥🔥🔥*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*March, 2017*
7⃣2⃣
"Call daga wa kenan?"
"Daga colleague d'ina regarding Boss."
"Boss? Wani Boss kenan?"
"Your in-law mijin Madam."
"Kana nufin Ya Al'ameen? Meya samesa?" Tayi maganan cikin tsan-tsan tashin hankali.
"Hajiya Boss is in a very critical condition, yanzu na gano dalilin dayasa Madam ta sume, a hanyan dawowansa yau daga Abuja 6arayi suka taresu suka gudu da motanshi suka kuma har6esa kusa da heart nashi Driver'nsa kuma suka mai d'ankaren duka yanzu duk haka suna nan a Teaching Hospital a emergency ward."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, what?! Da wanne zanji yanzu? An shiga da Ya Al'ameen d'in OR ne?"
"Eh Hajiya."
"Innalillahi! Ka samu dama ka gansa kai?"
"Yes Hajiya he is in a very critical condition he is bleeding through everywhere."
"Subhanallah! Allah ya bashi lafiya Allah ya fito dashi yasa ayi a sa'a bari na leqa Zeezee mu koma chan d'in." Nan da nan ta shiga d'akin Zeezee inda ta tarar da ita se aikin kuka take. A gefenta ta zauna tare da had'a musu hannayensu. "Sannu Mama na sannu, ya jikin?" Kai zallah Zeezee ta gyad'a mata "Mama ina Ya Al'ameen? Please tell me its not true tell me ba a har6esa ba, and also my baby please tell me banyi miscarrying baby na ba. I can't afford to lose my family" tayi maganan cikin kuka sosai.
"Zeezee ki kwantar da hankalin ki please kinga kema ba lafiya kike dashi ba, baby'n ki na nan lafiya ba abinda ya samesa."
"That's not true Mama kawai kina fad'a min ne."
"Am not lying to you Zainab ki ta6a cikinki kiji your baby is fit." A hankali ta aza hannunta kan cikinta cike da fargaba, feeling bomb d'in yasa taji d'an sanyi a ranta "Ya Al'ameen fah? Please kar ki gaya min ya mutu Mama." Kuka take sosai, hugging nata Mama tayi "shhh! Its okay please anyi OR dashi in shaa Allah he is going to make it muyi mishi addu'a kawai."
"A ina suka har6esa Mama?"
"Zainab-"
"Please answer me I need to know."
"Zai-"
"Mama please I beg you" ta k'ara rushewa da kuka.
"A kusa da heart nasa ne Zainab."
"Innalillahi! Mama I killed my Husband, na kashe Ya Al'ameen."
"Kaman ya kin kashe sa Zeezee? Armed robbers su har6esa kice ke kika kashe sa."
"Mama its all my fault, about 3 weeks now kullum ina cikin fushi dashi I failed to believe him daya cemin he wasn't cheating on me, I killed him also." Sake hugging nata Mama tayi "shhh! Ya Al'ameen be mutu ba kuma in shaa Allahu baze mutu ba kinji? Mu mushi addu'a kawai."
"I can't afford to lose him Mama."
"You won't in shaa Allah Zeezee, ina zuwa bari inje in duba shi."
"Zan biki."
"Kaman ya zaki bini Zeezee? Kema bakiga gado aka baki ba."
"I don't care about myself Ya Al'ameen is all I care about."
"No Zainab ba inda zakije kina nan so kike kije kiga condition da yake ciki abu ya samu lafiyan abinda ke cikin ki?"
"Mama please karki hanani ganin Ya Al'ameen please."
"Zainab-"
"Please Mama." Hannu Mama tasa ta share mata hawayen nata sannan a nitse ta mik'ar da ita suka shiga takawa har suka isa izuwa ward d'in. Sadeeq na ganinsu ya miqe tare da basu waje don su zauna, "Sadeeq ina Ya Al'ameen?" Zeezee ta tambaya in a cracky voice. K'ofan d'akin kawai ya nuna musu "basu fito ba har yanzu?" Asked Mama.
"Eh har yanzu."
"Sadeeq how bad is his condition? Please karka min k'arya." Zeezee ta tambaya.
"Critically bad, acikin jini suka wuce dashi he seemed so lifeless." Kwanciya kawai Zeezee tayi jikin Mama tana kuka sosai da k'yar suka zauna har anan Zeezee ta kasa barin kukan da take yi. Hajiya Babba ne ta kira Mama inda take tambayarta ya jikin Al'ameen nata, ana ruwa a KD bazeyi ta shigo ba please a kula mata da yaronta.
"In shaa Allah Mama Babba kibar kukan haka please addu'ar mu kawai yake buk'ata."
"Nagode Maman Zeezee Allah yabar zumunci."
"Ameen ki gaida Hjy Sadeeyah."
"In shaa Allah zataji, nima ki gaishemin Zeezee da jiki please ta kuma kwantar da hankalinta kar abu ya samu lafiyan d'an nata."
"In shaa Allah zan gaya mata sannu."
"Yauwa sannu se anjima."
Few minutes more k'ofan d'akin da Al'ameen ke ciki ya bud'u. Kusan a tare suka dosa gun duk tashin hankali bayyane a fuskokinsu karara. "Dr how is he?" sukayi maganan dukansu uku in unisons.
"Kune family'nshi?"
"Eh" Mama ta amsa.
"Am his wife and this is my mother" Zeezee tayi explaining "so tell me how is my husband doing inside there please, karku cemin ya mutu don Allah."
"Zainab calm down please" cewar Mama.
"Kuyi hak'uri amman bazan 6oye muku wannan lamari ba. Mijinki is in a very critical condition rai a hannun Allah yake, mude munyi abinda ya kamata bullet a cardiac walls ba abu ne ba na wasa. Mun samu mun cire bullet d'in amman har yanzu pulse nasa is not responding ya tsaya gu d'aya baya picking."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Suka ambata a tare. Rushewa cikin wani irin kuka me tsuma zuciya Zeezee tayi tana sumbatu tana ta kashe mijinta a yayinda Mama ke calming nata down. "Kuyi hak'uri kuyi mishi addu'a wala Allah ko zuwa nan da gobe pulse nasa yana iya dawowa idan be dawo ba kuma... I'm sorry."
"No! No! No! Please this can't be true it can't be. Ya Al'ameen can't die don Allah Dr do something baku iya aikinku bane da zaka cemin sorry? Kana nufin mutuwa zeyi kenan?