Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
cafenin gidan?"
"Girkin da ko kinyi sekin ga daman samin d'in kikeson na miyar miki da kud'in ki yanzu? Lallai ki sake tunani yarinya."
"Ai kaima ka sake tunani wallahi dan seka miyar min da kud'i na." Shareta yayi ya zaro jeans and shirt nasa sabi yasa duk anan kallonsa take seda ya gama feffeshe turarukansa sannan tasha gabansa "Malam my money."
"Ki matsa min" yayi stating in a serious tone.
"Nak'i" ta tanka ba tsoro. Tunkud'eta yayi sede kaman gunki tana tsaye wajen "ai wallahi ba inda zanje ina nan seka biyani kud'in cefanin danayi da a baya."
"Me k'iran yarabawa kawai" yace da ita disgustedly.
"Whatever kud'i nede se ka bayar kokuwa ba inda zaka." One more hiss ya mata sannan ya irga 5k ya watsa mata se anan ta matsa mai ya fice. Kaman kullum ma yau ya nufi unguwansu Zeezee yayi parking a dai-dai tsakar unguwan inda yana iya hango almost all of the activities taking place there. Shikansa besan dalilin sa na zuwa nan kullum ba all he is adamant of is that komin jimawa zega Zeezeensa wataran saboda jikinsa na basa anan d'in Zeezee take. Ba yadda beyi da Lubiee ba ta sanar dashi inda Zeezee take amman tak'i, bataga dalili ba. 5pm na bugawa yaja motarsa yakoma gida.
5:14pm Zeezee tafito kanti don siyan kati inda take a layin shagon taji wasu maza a bayanta suna gulmanta ko dagangan suke don taji ko basu san itan bace masani se Allah.
"Ina Zeezee'n gidan Alhj Isma'eel danake maka magana akai the other day d'innan?" Cewar d'ayan.
"Eh wacce kacemin yarinya ce sosai amman auranta biyu duk sun mutun nan ko?" D'an uwan nasa ya amsa sa. Hakan yasa ya cigaba;
"Exactly!" Yayi exclaiming "aitoh bakasan meh ba, jiya Mustapha yake cemin wai ya ganta a gidan matar Uncle nasa yana sonta."
"Kai haba deh! Yanzu har akwai mutumin da zaiso zaman aure da yarinyar nan? Lallai!"
"Tayani ji deh, wai ta masa kyau."
"Kyan banza kyan maciji, ace yarinya wai ko ashirin bata kai ba da aure biyu suma wai du sun mutu, haba mana!"
"Kuma ai bakasan wani abu ba uban nata ne silan komi shiya sagaltata ta 6aci hakan."
"Toh Allah shi kyauta ya raba 'ya'yanmu da iyayen banza." Kasa rik'e kukan nata tayi kawai ta juya a guje ta fice se anan d'ayan ya saki baki yana binta da kallo "kai! ba itace Zeezeen ba?" Nan wanda ya soma kawo maganan yace, "dafa? Ai sanin tana nan na d'auko zancen don taji tasani kyau ba komai bane inba hali."
**
Tana isa gidan Mrs Mukhtar inda ya zame mata tamkar gidansu ta nufi d'akin da aka bata, ashe Mrs Mukhtar taga shigewarta ciki ga dukkan alamu kuwa ba lafiya ba don haka ta bi sahunta. Zeezee najin motsin ta tayi sauri ta shiga share hawayenta amman sede ina takasa hanasu zuba.
"Subhanallah! Kukan me kike haka Zainab?"
"Babu" ta furta a hankali covering her face.
"Ya isa toh yi hak'uri kinji? Komi meh wucewa ne wataran se labari."
"Aunty na riga na 6ata rayuwa na ashe duk mutanen da muka ga sun d'auke k'afa daga nema na 'yan unguwa ke basu tarihi na."
"Inji waye Zeezee? Karkice haka."
"Aunty yanzun nan naji da kunne na, shikenan ni haka zan qare rayuwana cikin k'unci da bak'in ciki sam ban kyauta wa kaina ba wallahi."
"Karkice haka Zeezee always have in mind that Allah na tare dake."
"Nasani Aunty amman abinda nayin ne yayi yawa, if I'll be granted one wish right now it'll be na koma gidan Ya Al'ameen I miss him so much" sekuma ta rushe da kuka. Hugging nata Mrs Mukhtar tayi tana bubbuga bayanta "Zeezee is high time ki cire Ya Al'ameen daga zuciyarki, banason kizo kizama disappointed daga baya its been morethan a year yanzu bamu sani ba ko bawan Allan ya sake aure. Ke de ki dage da addu'a in Maj-gen rabonki ne still zaki koma d'akinsa amman kidena bi a rai kinji? Inko ba haka ba Allah ze kawo miki wani na garin da ze kula dake."
"Naji Aunty, amman ni bazan sake welcoming wani na miji a rayuwa na ba" Zeezee tayi maganan tana d'agowa daga jikin Mrs Mukhtar "nagode Aunty barin kar6eki girkin."
"A'a no kibari zan gama da kaina ki huta abinki kinji?"
"Toh nagode" nan Mrs Mukhtar ta fice nan Zeezee ta koma aikinta na kullum wato tunanin masoyinta na haqiqa Ya Al'ameen . If only tasan ina zata samesa da taje ta samesan ta fayyace mai abinda ke ranta takuma nemi gafarsa. She don't care koda fad'a mai tana sonsa ze rage mata self esteem and dignity saboda she loves him so much ba wanda takeson ta kasance dashi kaman Al'ameen bayan iyayenta. Tunanin Adeel kuwa koda wasa batayi roqon Allah tayita yi Allah ya yaye mata son da take mai gabad'aya saboda Adeel bashida wani amfani a rayuwarta yanzu koda shine autan maza ta yafe shi.
****
Sanin koda ya (Adeel) wuce gida yanzu, Ruky bata dafa abinci dashi ba saboda zatace tayi lunch bazata yi dinner ba yasa ya wuce gidan Maminsa kawai. Achan tayi serving nasa dinner suna cikin ci ta lura da yadda Adeel is lost in his thoughts. Gyaran murya tayi still be motsa ba.
"Auta?" Tayi patting shoulder nasa. Ad'an razane ya d'ago kai daga kan plate nasa yana kallonta.
"Yes Mami."
"Meke damunka Auta? Tunanin me kake? Meke damunka?"
"Babu" yayi mata k'arya.
"Kamar ya babu? Kai da matarka ne?" Kai zallah ya kad'a mata.
"Toh dawa?"
"Mami I miss Zeezee, I want her back."
*MIEMIEBEE. Team #YGC!*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*Febraury, 2017*
5⃣0⃣
_Yo! Assalamu Alaikum Beautiful ones, I know I've been keeping you guys in such a suspence and for that MIEMIEBEE is sorry. To those who think they know me, well I don't think you know know me if you don't know that *Aunty Sis* and *Lubabatu Maitafseer* are my buddies😻. You guys are just simply amazing, my life is a blast with you two. Know that I love you so much and that may ALLAH SWT guide us together and may we continue to prosper. I'm indebted to you two. This page is in you honors. #TheThree❤#youKnowWhatIMean😂🤳🏻_
"Tooohh" Ta saki baki cike da mamaki. "Auta kasan da haka ka buga mata saki biyu lokaci guda?"
"Mami wallahi sharrin shaitaan ne, I didn't mean it wallahi ina son Zeezee."
"Ruky fa?"
"Mschww!"Yaja k'aramar tsuka "ina miki maganan mutane kina kawomin na beyerabiyar can."
"Oh! Da Alama gida ba lafiya kenan, toh kaje kayo bikon Zeezeen mana."
"Bansan ina take ba naje gidansu bata nan da alama Dad nata be yafe mata ba har yanzu, bansan ina zan sameta ba her line is not going through."
"Tooh kuma... ka tambayi Lubiee mana." Tayi suggesting.
"She will not tell me tana ganin naci amanar best friend nata she'll never tell me."
"Ko na kirata ne?"
"Zaki 6ata lokacinki ne I know Lubiee batayin abu se in tayi niyyah."
"Toh Auta ka cireta daga ranka kawai ka rungumi k'addara."
"I can't Mami I love her." Ya fad'a a tsawace.
"Kai don Allah free me bafa ni nace ka sake taba, kunje kun samu misunderstanding da matarka zakazo kana sauqe min fushinka."
"Everywhere is just hell!" ya buga plate nasa kan table d'in "na tafi." Ko seda safe bata mai ba tana kallonsa har ya fice. Getting to 9 ya isa gida bayan yayi parking yafito instead ya zarce site nasa da Ruky seya nufi na Zeezee wanda tun tafiyar ta ko tako varendar be ta6ayi ba se yau, gun yayi k'ura putuk! Key'n k'ofar dake had'e da car key nasa yasa sannan ya juya ya bud'e tare da sa kai. K'ura ne da cobwebs ya mamaye ko ina. Yana tafiya guiwa ba k'arfi ya samu ya qarasa har cikin d'akinta. Wardrobe nata ya bud'e yaga wayam! Ba abinda tabari komi ta kwashe Allah sarki Zeezee ya furta a ransa.
Side drawers yashiga ja yana dubawa kozega wani abinta amman duk ba komai, kominta ta tattara. A na qarshen ne yaci karo da wedding albums nasu guda biyu ciki ba wanda Zeezee ta tafi dasu nufin bata sake buk'atansa a rayuwarta kenan. Wani heart break ya sake ji. Bakin gadon yad'an kakka6e sa'annan ya zauna ya shiga viewing lovely photos d'in. Even though a ranan hankalinta baya jikinta tana tunanin gida, hakan be hana photos nasun yin kyau ba. Kalla ya rigayi har seda ya jiyo k'walla. Gabad'aya yaji ya tsani kansa yanzu meyasa ya hanke hukunci ba tare da yin dogon bincike da nazari ba? Addini beyi qarya ba dayace kafin a yanke hukunci ya zamanto anyi dogon bincike ga irinsa ai yanzu. Missing d'inta bil adadin ya shiga yi har don haka ya kakka6e gadon ya gyara ya kwanta gun yana rungume da photo album d'in ahaka har ya samu yayi bacci, Ruky kuwa koda tajisa shiru setayi zaton ko yana parlour ko sauran d'akunan don haka tana gama kallon series nata tayi kwanciyarta itama.
*^*^*^
Haka rayuwa on both sides ta cigaba da kasancewa ba dad'i. A kullum Adeel da tunanin Zeezee yake tashi ya kuma yini, Ruky abinda taga daman yi shi take Adeel be isa ya mata magana ba har wani shakka-shakkanta ma yake yanzu. On Zeezee's side kuwa tama bar fita waje yanzu kwata-kwata koda kuwa don siyan kati ne ta gommaci ta aika almajirai saboda abinda 'yan unguawa keyi mata sede bata fita waje ba shikenan sun shiga habaici suna zaginta kenan, abinda yafi cimata rai shine harda zagin Baba ma da suke.
Shi kansa Baba basu barsa ba, basuyi a gaban idonsa amman a bayan idonsa dandalin hira da zaginsa suke bud'ewa. Yau kamar kullum Baba da Omar sukaje masallaci an idar da Sallah ana zaune ana tasbih wasu maza daga bayansu Baba wanda basu gane Baban bane zaune a gabansu suka bud'e dandalin hira suna zagin Zeezee suna aibanta Baba, kalamu ba dad'in ji duk anan Baba na jinsu se k'ona da rad'ad'i zuciyarsa keyi masa. Omar na sallame nafilarsa ya hau bayin Allan da masifa da k'yar aka samu aka sasantasu if not cewa yayi seya musu duka danko yafisu k'arfi ko kodaga mere look. Dama kullum ana gayawa Baba abubuwan da 'yan unguwa ke cewa akanshi be ta6a ji da kansa ba se yau, jikinsa ne yayi sanyi a lokaci guda da k'yar suka samu suka k'arisa gida da Omar as tafiya kad'an yayi se sun tsaya ya huta. Sun shiga gida Baba ya wuce d'akin Mama ko tanka Mama dake musu sannu da zuwa beyi ba, miqewa yayi bisa gado yana riqe da zuciyarsa dake masa ciwo sosai.
"Omar lafiya? Meya sami Baban naku? Ko kunyi fad'a ne?"
"A'a Mama kede go and calm him down kar ciwonsa ya tashi."
"Gayamin meya faru Omar?"
Be b'oyewa Mama komi ba ya fad'i mata abinda ya faru. Cike da tashin hankali Mama ta shiga d'akinsu inda ta tarar da Baba kwance akan gado sede meh? Baya motsi wani irin rikicaccen ihu ta saki sannan ta biyosa da "inna-lillahi-wa-inna-ilaihi-raji'un. Alhj!" Da gudu ta nufi kan gadon tana tapping nasa sede at all baya responding. Omar ta shiga kira seda ya fito a rikice jin yadda take ihu "Omar Babanku, don Allah kayi wani abu." Shima Omar d'in gabad'aya ya rikice ya nufi kansu yana kiran Baba sede baya amsawa. Bayan nan ga kuma yadda heart nasa ke beating a hankali. Seda sukayi dagaske suka samu suka d'aga Baba ba tare da 6ata lokaci ba sukayi dashi asibiti inda aka wuce dashi emergency ward.
Banda kuka ba abinda Mama keyi a corridor'n d'akin da lokitoci da Baba ke ciki suna aikin ceto ransa. Omar ne ke k'ok'arin calming nata don shima hankalinsa gabad'aya a tashe yake fatansu kar Baba ya tafi ya barsu don tun ba yau ba Mama take lura da yadda Baba kebin abin Zeezee a rai. Ya yafe mata komi ya wuce yaqi, ga irinta nan ai yanzu. Me za'ayi da gata a rayuwa? Dama-dama ma ace gatan da hankali ke d'aukawa ake bayarwa yaro ba erin wanda Baba ya riga bawa Zeezee ba.
****
"Zainab! Zainab!" Kirar Mrs Muktar ga Zeezee wanda tuni ta gudu izuwa bayi ta 6uya a zatonta ma tayi bak'o ne shine Mrs Mukhtar ke kirarta dan kuwa ta rantse bazata sake kula wani na miji ba face Ya Al'ameen nata wanda she is sure shima yanzu ya riga yayi aure ya mata nisa.
"Zeezee! Ina kike ne?" Mrs Mukhtar tasake kiranta a yayinda tashin hankali ke building a voice nata.
"Zeezee!" A yanzu kam ta shigota d'akin.
"Na'am" Zeezee ta amsa tare da fitowa daga bayin, tashin hankali ne kwance karara a fuskar Mrs Mukhtar wanda tun kafin ta fayyace wa Zeezee komi, tayi saurin tambaya "Aunty lafiya?" Kai zallah Mrs Mukhtar ke kad'a mata "Zeezee Babanki."
"Baba!" Tayi exclaiming "meya samu Baba Aunty? Please tell me."
"Ya sake samun heart failure Zeezee yanzu haka yana asibiti su Mama sun kaisa."
"Innalillahi-" kasa qarisa salatin tayi se kuka wane lalacaccen famfo.
"Zeezee ba kuka bane abinyi, ki sanya hijabin ki mu fice, yi hak'uri in shaa Allahu ze samu sauk'i."
Hakanan through out the drive Zeezee ke ta kuka. Suna isa asibitin suka nufi inda su Mama dasu Mariam suke already se kuka suke. Da gudu Zeezee ta nufi inda Mama ke, sede kafin ta k'arisa Mariam tayi mata katanga stopping her.
"Kin halaka Baba, Maman ma bazaki barta ba?" Tayi maganan idanunta na tsiyayar da hawaye sosai. Cikin kuka da tsan-tsan tashin hankali Zeezee ta soma da cewa; "Adda Mariam don Allah kiyi hak'uri and let me hug her I beg you please."
"No way ki koma daga inda kika fito, tunda aka haifeki you've been nothing but badluck to us Zainab, wallahi idan abu ya samu Baba kisani I won't ever forgive you."
"Adda Mariam ya isa please yanzu ba lokacin yin tashin hankali bane" cewar Omar a yayinda Zeezee tasake rushewa da kuka tana kiran sunan Mama amman itama Maman yau ta kanta take bata iya tacewa Zeezee komi ba. Mariam ta bari Zeezee ta zauna kusa dasu ma tak'i. Tana kuka Mrs Mukhtar tajata zuwa wani benchi dake chan gefe ta zaunar da ita tana lalashinta amman se kaman sake tunzirata Mrs Mukhtar ke.
Not long enough Dr ya fito inda ya kira Mama zallah ya buk'aceta data bisa office nasa. Tana kuka tabi bayansa inda ya bud'e k'ofar ta samu tashiga tare da jan kujera ta zauna tana shessheqa.
Tissue ya miqa mata tare da sanar da ita "please calm down mijinki na cikin critical condition bazan 6oye miki ba."
"Subhanallah!" Ta furta tana kuka sosai "Dr is he going to make it?"
"Agaskiya bazan 6oye miki ba, chances na rayuwansa is not upto 30% kunsan condition nasa be kamata ba kuna barinsa yana tunani haka. His heart is all damaged yaci ace zuciyar ma ta buga yabar aiki amman Allah be k'addara hakan ba. Ku sashi a addu'a bamu san me Allah ke ciki ba."
"Dr dan Allah ba abinda zaku iya masa? He can't die don Allah ka taimakeni da 'ya'yana." Ta k'are maganan cikin kuka sosai.
"I'm sorry Ma'am but we've done all we can sauran mun bar wa Allah kuyi hak'uri. Kuna iya shiga ganinsa amman please Karki kuyi abinda ze tayar mai da hankali Allah basa lafiya."
"Amin Dr" ta amsa tana share hawayenta.
***
Mama ya jikin Baban? Mariam tayi saurin tambaya. Kai zallah Mama ke kad'a musu, nan fa hankalin yaran ya sake tashi binta kawai sukeyi a yayinda take heading