Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
fara kawowa gida ko?” Kafin ta hankara ya kwad’a mata mari a fuska, ihu tasa wajen tana kuka ahaka ya jawota ciki “ke ba wai ‘yar iska ba, zaki gane kuran ki agidan nan” belt ya zare ya hau dukanta seda yamata lik’is sannan yace, “nan gaba ko kwatancen gidanku bazaki wa ‘yan iskan yaran ba balle suce zasu zo d’aukanki.” Da k’yar ta mik’e zata nufi d’aki tana kuka ya dakatar da ita “where do you think you are going? Haka da kayan Baba zezo ya sameki yasan abinda kikeyi.”
“Ya dan Allah ka rufa min asiri wallahi na tuba bazan sake ba.”
“Karki b’ata miyan bakinki kina ban hak’uri saboda ba jinki zanba.”
“Wayyo Allah na! dan Allah kayi hak’uri wallahi na tuba bazan k’ara ba.” Ba kalan had’a shi da Allan da batai ba yak’i hak’ura. Ana cikin haka Mama ta dawo nan ya irga mata komi sam bata sha mamaki ba, saboda tasan wannan ne dalilin dayasa tace bazata gidan Kaka ba kenan, not long enough Baba ya dawo shima Ibraheem ya irga mai komi sosai yasha mamaki da har baison believeling abinda Zeezee tayi. Kuka tahau musu a wajen tana rantsuwa akan k’arya ita sam wallahi ba saurayinta bane classmate nata ne.
“Inhar classmate nakin ne meya zo yi?” Mama ta tambayeta, shi Ibraheem dan haushi ma barin gun yayi.
“Amsan list na materials da ze siya mana na physics practicals.”
“Shi ne kikayi wannan shigan?”
“Toh ba nayi wanka bane zan d’au hoto yacemin gashi yazo na fito.”
“Kai! Yarinyan nan k’arya take wallahi, saurayinta ne, inada tabbacin kina sane da zuwansa yasa kika k’i bin yayyun naki gidan Kaka.”
“A’a wallahi ba haka bane, Baba Allah ba k’arya nake ba, ba saurayi na bane.”
“Na yarda dake K’anwata ba saurayi sekin gama secondary ba?”
“Eh Baba.”
“Aww ka yarda da k’aryan data sharara ma d’in kenan? Humm wallahi Alhj ka cigaba da take gaskiya, ka kuma guji ranan da yarinyan nan zata ma abin kunya” tana kaiwa nan ta fice itama. “Zeezee kifad’an gaskiya shin dagaske saurayi ne yazo gunki?”
“Wallahi a’a Baba ai bazan ma k’arya ba.”
“Shikenan jeki huta yi hak’uri kinji? Zanma Ibraheem magana.”
“Bashi kad’ai ba har Mama d’azu ta d’ibe min kayakina wai za’a kai gidan Kaka.”
“Karki damu gobe Omar ze rakaki shago na ki d’au turame biyar masu kyau abinki.”
“Toh Baba nagode.”***
Haka nan Baba ya cigaba da d’aure wa Zeezee gindi agidan komi tayi koda kuwa yasan ba dai-dai bane bayi tsawata mata ga kuma yadda yake spending money lavishly akanta, bada jimawa ba akayi auren Yasmeen, ansha budiri sosai barin ma Zeezee dake nan wane amarya itama dan yadda tasha gayu. Bayan biki aka kai amarya Yasmeen Kaduna.
_Wednesday morning 11:30AM_
Kowani d’alibi na a class yana d’aukan lesson banda Zeezee da Ammar da suka keb’e a wani empty class suna hira. Ana cikin haka wani teacher yazo wucewa ya kamasu. Ai kuwa Zeezee ta tsure tarasa nayi dan inhar aka kira Baba aka sanar dashi nata ya k’are. “What are you two doing here while classes are taking place?” Ya tambayesu both in an angry tone. Kame-kame suka shigayi both of them har teacher’n ya zagayo ya shiga class d’in “oya follow me to my office now!” Zeezee najin haka tayi ma Ammar ido se kawai ta yanki jiki ta fad’i k’asa ta soma wani irin mahaukacin tari da wani d’an banzan nishi wane ana cirewa kafiri rai, ganin haka Ammar da teacher’n sukayi kanta “whats happening to her?” Yayi saurin tambaya.
“That was how I found her also Sir, I think she’s athmatic.” Ammar yayi stating yana k’ok’arin d’ago ta daga k’asa. “Is that the reason why you two are here alone?”
“Yyes Sir, I was passing by and then saw her unconcious that was why I rushed in.”
“Hurry lets take her to the sick bay” haka ya kinkimi Zeezee zuwa bay aka kwantar da ita har a yanzu bata bar tarin munafircin ba “is she asthmatic?” Nurse d’in tayi saurin tambaya “yes” Ammar ya bada amsa. Inhaler sabuwa ta b’allo ta bata, zugi biyu Zeezee tayi ta soma daidaita numfashinta kaman dagaske, bayan d’an hutawan da tayi a bay ta koma class. Su Lubiee se tambayarta suke ko lafiya nan ta labarta masu komi sukayi ta dariya.
_Closing hours_
Yau Baba da kansa yazo d’aukan Zeezee, dai-dai ta shiga mota kenan teacher’n d’azun ya fito ganin Baba da prado jeep ya nufi motan nasu ya gaishesa, zuciyan Zeezee se harb’awa yake Allah sa karya cewa Baba ya kamata dana miji su kad’ai a class, kawai seji tayi yana cewa Baba akai ta asibiti d’azu asthman ta ya tashi.
Suprisingly Baba ya tambaya dama Zeezee nada asthma ne? Bayan ya sallami teacher’n da N5,000 ya tafi. “K’anwata kinada asthma ne dama?”
“Wallahi Baba kawai yau ina zaune naji nishi na nawani sama-sama, chest d’ina na tightning nayita attishawa kuma amman da sauk’i yanzu.”
“Kaman ya da sauk’i? Bari mu wuce asibiti Dr. Zakir ya duba ki, sannu ko?” Anzo gurin Zeezee tace a ranta. “Baba cikina na min ciwo inason using bathroom mubari ko gobe muje, wayyo!”
“Toh Allah kaimu goben sannu ko, amman ko inhaler ne asai miki ai ko?”
“Eh Baba” pharmacy suka wuce ya sai mata inhaler sannan sukayi gida. Haka kullum Zeezee ke raina wa Baba hankali tak’i yarda aje asibiti daga k’arshe kiran Dr. Zakir akayi aka irga masa symptoms na k’aryan da Zeezee keyi nan ya tabbatar musu da eh asthman ne, magunguna yayi texting wa Baba aka sai mata. Itade Mama kallonsu kawai take sabida tasan k’arya Zeezee ke. Tun daga ranan Zeezee ta samu sara ba aikin da take agidan in Baaba batazo ba sede in Mama tayi shara da kanta danko fakewa Zeezee ke tace asthman ta ze tashi idan tayi shara Baba ko ya d’aure mata gindi as always.
_Few days later..._
Kwanan Baaba uku batazo ba kasancewar batada lafiya, through out Mama ke shara Zeezee sede ta mata sannu da aiki. “Zeezee!” Mama ta kirata kan su wuce su share mata d’aki dan kuwa rabon d’akin Zeezee da shara tun da Baaba tabar zuwa, “shiga mu share miki d’akin mak’aryaciya kawai. Kalli wai wannan d’akin budurwa ko kan gadonki baki iya gyarawa ba maza kakkab’e ki gyara” tana tura baki ta jajja ending d’in ta tuttusa “gashi na gama.”
“Ahakan ne kin gyara? Kifa sani ‘ya mace ce ke kuma dole wataran zakiyi aure kina gani ai ba Yasmeen ba Mariam yanzu next kece.”
“Ai zan koya in na gama secondary school.”
“Mschww!” Hannu tasa ta d’aga katifan ma gabad’aya dan share k’ark’ashin gadon. Ai kawai sega maguna k’ark’ashin gadon Zeezee tamkar pharmacy, maguna barkace.
“Laaa’ila! Meh wannan? Drugs kike siyarwa?”
“Nikam ki sauk’e min katifa na zan share d’akin da kaina.”
“Ai dama nasani ba asthman da kike da, kuma wallahi a kunnen Babanku, ‘yar banza kawai kullum kisa ayita siyan maki magani masu tsada baki sha?”
“Ina sha mana wannan fa ba maganin asthman bane na zazzab’in dana tab’a yi ne.”
“Allah yasa na haukan da kika tab’ayi ne.”
“Toh ki kawo tsinstiyan zan share amman karki gayawa Baba please Mama.”
“Mschww!” yasar da tsintsiyan tayi ta fice, Zeezee da kanta ta shiga share d’akinta tana cikinyi Baba ya dawo ya tarar da ita “ya da haka? Mesa zakiyi shara bayan bakida lafiya, Hafsah! Ban hanaki sa yarinyan nan shara ba.”
“A’a Baba ba ita ta sani ba kuma ma ai sharan kad’an ne karka damu I can manage, sannu da zuwa.”
“Are you sure baze dameki ba? Kinsan fa bakida lafiya.”
“Eh karka damu Baba.”
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 19
*December, 2016*
Washegari bayan Ibraheem ya sauk’e Zeezee a school ta tuna da mantuwan TD assignment nata datayi a gida, ga teacher’n mugu ne baya sauraron excuses. Form teacher’nsu tanema tamai magana ya had’ata da Baba a waya tamai explaining komi. Suna cikin yin second period nasu Ibraheem yashigo class nasu bayan excusing kansa da yayi. Sanye yake da T shirt me long sleeve arms da not too tight pencil trousers, yayi matuk’ar yin kyau ai tuni ‘yan matan class nasu Zeezee sukayi falling masa cikin k’asaita kamar yadda ya saba gudanar da ayyukansa ya k’arisa cikin class d’in suka gaisa da malamin sannan ya bawa Zeezee drawing natan yayi ficewarsa. Ai ana fita break ‘yan matan class nasu Zeezee da wanda suke mata magana da wanda basu matan sukayi layi a seat nata “wai meh haka? Ku matsamin mana ko bakuga an fita break bane?” Zeezee tayi stating angrily.
“Zeezee don’t tell me that Hottie is your brother?!” Matan class nasun sukayi exclaiming almost at thesame time.
“Ba brother na bane naku ne ai aikin banza, matsa mun nikam.”
“Please ki tsaya muyi magana” cewar Lieemarh “wallahi yayi min nikam omg! His skin!”
“Skin ja kaman tsuliyan birin? Lallai kam matsa min mana ku!”
“Dan Allah meh IG handle nasa Zeezee?” Mjay ta tambaya.
“Wai tsaya son Ya Ibraheem dukkanin kun nan kuke wai?” Tayi pointing nasu da yatsa.
“Eh ni wallahi yamin.” said Hajara. Dariyan rainin hankali Zeezee ta saki “Lubiee kinaji wai Ya Ibraheem suke so, wai lallai kam kun tashi a aiki excuse me now, will you?” Nan suka matsa mata suna fad’in “kije ki dawo ma tona.” Ta kai da bakin k’ofa kenan mortal enemy’nta a class d’in wata Sumayya wanda Babanta ke mugun ji da kud’i har mota ya sai mata. Ko kad’an bata wa mutane magana dan haka basu shiri da Zeezee dan itama ‘yar iskan kanta ce. “Zeezee we need to talk please” tace da Zeezee.
“Sumayya ko? Aww! Dama kina wa mutane magana? LOL toh I aiint got your time matsa min.”
“Please Zeezee lets keep our differences aside wallahi ko me kikeso zan miki just listen to me.”
“You have two minutes to do so.”
“Its about the guy that came earlier waye shi?”
“Wanne? Be precise please kina b’ata min time” Zeezee tayi maganan as if bata gane Ibraheem, Sumayya ke nufi ba.
“The tall, fair and good looking one daya kawo miki TD drawing naki.”
“Aww you mean my handsome brother, what about him?”
“Nothing really you mean he is your brother?” Ta tambaya kinda shocked.
“Ban kai na zama sister’sa bane kome kike wani zaro idanun nan naki waje haka.”
“No ba haka bane, abin ne yazo min da sauk’i I don’t need to suffer.”
“Like I don’t get you kuma kina b’ata min lokaci.”
“My apologies, dama bawani abu bane digits nasa nake buk’ata.” Dariya Zeezee da Lubiee sukasa harda tafewa, “you mean digits na Ya Ibraheem?”
“Owww what a lovely name eh na Ya Ibraheem d’in.”
“Lallai ko kinyi kad’an na baki digits nasa, dana baki gomma na bawa su Salmah.”
“Please Zeezee lets talk business ki fad’an ko meh kikeso zan baki inhar zaki bani digits nasa in return.”
“Like money?” Tayi maganar tana lasan lips nata.
“Eh wallahi ko nawa kikeso.”
“Interesting Lubiee deal ya taso, kibari yanzu zanje shop in na dawo we’ll discuss it.”
“Okay am grateful Ameenah lets go” tace da k’awarta suka fice.
*~ *~
Zeezee na dawowa daga shop ta tara ‘yan class nasu da sukayi falling wa Ibraheem gu d’aya sannan tayi clearing throat nata ta soma da cewa, “so all of you here have fallen for my handsome brother kuma kunason digits nasa ko? Cikin ku takwas (8) d’innan mutum d’aya zan baiwa.”
“Zeezee ni please” cewar, Ashnur da Xarah.
“Ai ba daganan take ba girls, sayar maku da digits nasan zanyi.”
“Ki fad’i ko nawa ne am ready to pay” Sumayya tayi stating arrogantly.
“Good I like that, so out of the eleven digits each number contains, kowani digit d’aya N500 altogether making five thousand five hundred (N5,500) kenan who will pay?” Ai kap suka d’aga hannu dake duk ‘ya‘yan masu kud’i ne ‘yan k’arya kuma. Ganin haka Zeezee ta k’ara deal d’in zuwa one thousand (1,000) nan ma kusan duka sun d’aga hannu haka tayita raina musu wayo har suka iso two thousand inda Sumayya kad’ai ta d’aga hannu.
“Tam Sumayya kece winner ke zan bawa number’n Ya Ibraheem that is after I get to see my tewnty-two (22) thousand.”
“Toh ai kinsan bada kud’i dayawa nake zuwa school ba but trust me gobe zan kawo miki kiban contact d’in.”
“Uh-uh Babe, I don’t play that game, pay before service kina bani kud’i na ina baki digits nasa” haka Sumayya ta hak’ura a washegari ta taho da 22k pil cikin envelope ta danka wa Zeezee ita gata shegiya ‘yar gidan minister nan Zeezee ta bata number’n Ibraheem not minding the consequences.
_Da La’asr._
Baba na zaune a parlour da friends nasa suna hira, Zeezee ta shigo bako sallama bale gaisuwa ko sannu, wajen Baba ta nufa direct ta tsaya akansa “ya akayi K’anwata, lafiya?” Kai ta kad’a nufin a’a.
“Toh baki gaishe da friends d’ina ba.”
“Ina wuninku Uncles?”
“Lafiya Zeezeen Baba” suka amsa in unison almost about 5 of them.
“Yauwa to meneh neh?”
“Baba pad d’ina ya k’are kabani kud’i na sai sabo.” Kunya sosai Baba yaji tamkar ya nitse k’asa, dama seda Mama ta gaya masa yayi a hankali wataran se Zeezee tamai abin kunya amman yak’i jinta ya mata kunnen shegu. Ga irinta ai yau!
Bending nata yayi dab da kunnenta yace, “haba K’anwata bazaki jira se friends nawan sun tafi ba tukun?”
“Toh ai zanyi staining kaya na.” wani abin kunyan again! Cike da mamaki friends nasan suke kallon Zeezee “excuse me please” cewar Baba tare da jan hannun Zeezee izuwa d’akin Mama.
Koda Mama tagansu bata ce komi ba se kallonsu kawai take, “haba Zeezee! Meh amfanin hakan? Bakiga inada bak’i bane?”
“Ya meya faru haka?” Mama tayi speaking up finally.
“Muna zaune da friends d’ina taje wai na bata kud’i ta sai pad.”
“Ahap! Ban fad’a maka ba dama ka guji rana kamar ta yau? Tunda Allah yayi ina raye duk lokacin da take buk’atan abubuwa haka tazo ta sameni tamin magana sam kace kai ba haka ba, duk abinda take buk’ata ta sameka ta maka magana, kad’an ka gani ai wataran cewa zatayi kasa mata inde Zeezee ne expect more wallahi.”
“Toh ya isa haka! Ni nake gama wallahi bakinki yake kama mu, kullum sede bakiyi magana ba se abin ta faru, dan Allah daga yau inkin san bazaki fad’i alkhairi ba kija bakinki kiyi shiru.”
“Kanku akeji kai da ‘yar naka da bata da kunya.” Kuka Zeezee tasa wai Mama tace mata batada kunya da k’yar Baba ya samu tayi shiru “amman kema karki sake tambaya na stuffs haka in public kinji?”
“Koda zanyi staining kaya na?”
“A’a ni bance haka ba what I mean is nan gaba in na cikin mutane ki kirani gefe kinji?”
“Toh naji.”
“Yauwa K’anwata Allah miki albarka” yayi maganan tare da zaro 5k daga wallet nasa, “ungo toh in cenji ya rage ki d’auka na baki.”
“Toh nagode” tana kaiwa nan ta fice.
“Hmm kaide inba kuka Zeezee ta saka da hawaye ba bazaka tab’a yin hankali ka soma ganin laifinta ba.”
“Kanka akeji” yana kaiwa nan ya bar mata d’akin.
_8:45PM_
Ibraheem na mik’e kan gadon d’akinsa yasa earpiece a kunne yana d’anjin beats, kira daga new number ya katse mai waqansa bayan daya duba yaga fa besan lamban ba seya k’i d’agawa se a karo na biyu “Halo” Sumayya tace cikin wata karuwar murya sekace ba ‘yar 16 years ba.
“Yes Hello” yayi speaking finally.
“Uhm Ibraheem ne please?”
“Yes shine.”
“Ohh thanks Gee! Am Sumayya by the way, I know baka gane wacece ba ko nace bakasan wacece bama thats why I need to introduce myself.” Har anan sauraronta kawai Ibraheem yake totally specheelss, bayan data gama bayanin kantan yaji ma ashe yarinya ce sa’ar k’anwarsa na chan baya-baya.
“So little baby dake a ina kika samu digits d’ina?” ya tambayeta finally.
“It doesn’t matter ni kawai kabani dama na fad’a maka meke tattarre dani.” Murmusawa yayi ya sake mik’ewa kan gadon “meke tattare da ke ‘yar yarinya?”
“Right from the moment my eyes decended akan breathtaking face and body naka heart d’ina yayi skyrocketing, I don’t know how to explain it to you but the truth is I’ve fallen for you and I love you.”
“Woah! You’ve got such confidence, kafin nan answer me aina kika samu digits d’ina Zeezee ce ta baki?”
“A’a ba ita bace.”
“Don’t lie to me kikayi hakan you’ll just ruin yourself and make me hate you.”
“Yes itace, but it does-” bata kaida idda maganan ba yayi hanging wayan tare da mik’ewa a fusace yaja belt nasa dake rataye jikin wardrobe yabar d’akin sena Zeezee gbam! gbam! gbam! Yayi knocking tana cikin irgen kud’ad’d’enta tace, “ina zuwa” da sauri ta miyar tasa cikin pillow case nata sannan ta mik’e ta bud’e k’ofan. “Ya lafiya?” Idanunta na kaiga belt dake nannad’e a hannunsa ta shiga b’ari kafin tayi wani k’wararren motsi ya bankad’eta tare da sa kai cikin d’akin “wayyo Allah Baba na wallahi ze kasheni!” tasa ihu, kota kanta beyi ba yayi locking k’ofan d’akin.
“What