YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   62 / 98

183K to 186K   out of 291.7K words

can't bear the thought Zeezee is gone forever bazata sake dawo mishi ba, why didn't he ever appreciate her time da take nan seda ta tafi? its true indeed that we don't know the value of what we have until we loss them. Bar (gidan sai da giya) kawai ya nufa inda yaje ya bugu iya buguwa. Be tashi dawowa gida ba se quarter to 9pm. Alokacin Ruky na kallon series abinta. Se buga k'ofan Adeel ke gbam! Gbam! Gbam wane ze b'alla shi daga hinges nasa. "Ina zuwa mana Adeel ka tsaya mana ha'a! 6alla k'ofar zaka yi ne?" Bubbugawan ya cigaba dayi har seda ta bud'en. Bankad'eta yayi ya wuce inda tajiyo warin barasan dake tashi daga jikinsa.

"Adeel!" Ta kira sunansa cike da mamaki. "Me nake shirin gani? Dama kana shaye-shaye ne?" Jajayen idanunsa ya d'ago yana kallonta nan fa ta shiga tsoro, "wallahi idan baki ja bakin ki kin rufe ba zan kashe ki this instant in huta, tunda na rasa Zeezee kowa ma yana iya mutuwa."
Kum! taja bakinta tayi shiru sanin yaufa ba a cikin hankalinsa yake ba. Sid'ak sid'ak ta wuce d'akinta tasa lock kallon ma ta yafe, kwanciyarta tayi inda shima Adeel d'in a parlour bacci ya sacesa. Cikin bacci amman se name na Zeezee yake ta furtawa.
Asuban fari ya tashi da wata masifaffiyar ciwon kai, lalla6awa yayi yayi Sallah sannan ya koma ya kwanta se 9:44am ya tashi ya karya ko k'ala be had'asa da Ruky ba. Seda yazo fita take tambayarsa ina zasa.
"Ina ruwanki da inda zani? Ke kike ajiye ni ne?"
"Mallam daga tambaya? I beg free me o, just cause Zeezee tace bazata dawo gareka ba doesn't mean zaka na sauk'e min fushinka akaina, ehe!"
"Kina magana ne?" Yayi snarling at her, shiru tayi seda taji ya bud'e k'ofa tace, "baka bada kud'in cefane ba in ka dawo baka tarar da girki ba don't blame me."
"Karki girkan mschww." Yawonsa ya fice ranan instead of office, da yamma wajajen k'arfe 5:40pm ya nufi unuguwan su Zeezee one last time yaji daga bakinta bazata koma masa ba ko ze samu sukuni dan har yanzu ya kasa yarda.

Yau wai acewarsu Mama tunda an riga an sanar dasu Adeel Zeezee aiint going back to them ai shima baze sake tako k'afansa nan ba, with this thought Omar beje d'auko Zeezee daga islamiyya ba ta tako da kanta. Achan wani corner Adeel yayi parking motarsa sannan ya tako zuwa kusa da gidan su Zeezee tare da yin tsaye, tun daga nesa yake hangenta se dab data kusa shiga gida ya fito da wuri tare da sa mata kira. Chak ta tsaya jin muryan Adeel kafin tace zata bud'e k'ofa ta gudu ciki kuma har ya sha gabanta. Hannunta yaja seda ta fad'a jikinsa. Sa'an su d'aya ba mutanen dake wucewa sosai, shuresa ta shiga yi, "Adeel let me go ka sakeni meh haka?" Sake matse ta yayi a jikinsa "Zeezee please stop fighting it and just listen to my heartbeat, just listen to how much it's beating for you. Wallahi I can't do without you, hit me all you can, slap me but please karki ce bazaki dawo gida na ba. I'm truly sorry for maltreating you, I shouldn't have done that kiyi hak'uri please ki dawo I love you so much."
Kukan itama ta rushe dashi jin yadda shima yakeyi, bar kai masa bugin tayi. Tana kuka yana yi, there's no denying tasan tana son Adeel but that is still not enough reason for her to go back to him, she have to be strong for herself. Sun d'au tsawon lokaci ahaka sannan da k'yar ta samu ya saketa tare da d'ago face nata yana goge mata dangling tears nata. "I love you Zainab, I love you so much wallahi."
"What do you want Adeel?" Ta furta tana sauk'e hannayensa daga kan fuskartan.
"I want you back Zeezee, I really do."
"Why?" ta sake tambayarsa.
"Because I miss you, I miss being with my lady."
"Mami bata sanar dakai decision d'ina bane?"
"Uncle did, but ban yarda ba Zeezee, I know bazaki min haka ba cause you love me just as much as I do love you, we are meant to be Zeezee please don't say no and come back to me. In gidanki kikeso in canza miki so be it, I just want to make you happy one last time."
"You know what will make me happy once more?" Kai ya kad'a "idan kadena bothering d'ina ka fita daga harkata gabad'aya."
"Zeezee thats not possible because I love you, I can't."
"Just stick it to your head and mind that am gone forever and not coming back to you Adeel." Kai ya shiga kad'awa continuously. "Please don't say that, I really do want you back, Zeezee wallahi nayi nadaman aikata duka abubuwan da na miki, if only 'I'm sorry' can bring us back the way we use to be, give me one last chance please to prove my love to you."

"No Adeel please stop making this hard on ourselves. Idan har abinda ya kawo ka nan don kaji daga bakina final decision d'ina ne so be it, bana sonka anymore Adeel, bana buk'atarka a rayuwa na anymore, koda kai ne autan maza na yafe ka, da in koma gidanka na gommaci mutuwa na, I don't love you okay?" Kuka take sosai take wannan magana saboda how difficult it is for her to admit that bata son Adeel.
"I've once loved you but not anymore, they say first love never dies and na yarda da hakan saboda har yanzu kana da gurbi a zuciya na Adeel, na maka son da ban ta6a yima wani mahaluk'i a duniyan nan ba, na fifita ka akan iyaye na, I could die for you but not anymore, I'm hoping that one day Allah ze had'a ni da true love da ze ya burying first love da nake maka. Inhar kana sona, zaka so yimin abinda nake so by simply staying away from me" Hanky yasa ya share hawayensa sannan a hankali yace "me kikeso Zeezee? Tell me and zan miki shi saboda ina son kisan just how much I love you."
"I want you out of my life Adeel, bana son sake ganinka, I want you to forget that you've ever had Zeezee in your life and move on."
"Shikenan Zeezee, I'll try as much to get out of your life dukda nasan hakan abu ne mai wuya but tunda abinda kikeso kenan zan miki. I just want you to know that no matter how distant you are away from me, your heart is always here with me." yayi nuni da zuciyanshi. "Kuma I want you to know that I'll die loving you. Farewell Zainab, I pray Allah ya had'aki da farin cikinki kema, nikuma ya bani ikon iya jure rashin ki, I love you so much and thank you for once loving me." Mugun uncontrollable kuka ne yafi k'arfinta da irin heart melting words d'innan. Kaman kayan wanki tayi tsaye wajen tana aikin kuka, the next abinda tayi noticing is how Adeel yajata da hannu tare da shigar da ita cikin gidan nasu, before tayi comprehending wani abu taji lips nasa akan nata. Kissing nata yake hungrily yet passionately, k'in basa access tayi se hawaye kawai take tana beating against his chest da duk wani k'arfin ta. Shiko ya kasa hak'ura abubuwa da dama yayita mata har seda tayi gasping anan yayi using opportunity'n yayi owning lips nata fully, tun tana k'in basa had'in kai daga baya daya gama kashe mata jiki lik'is ta soma moving in sync with his move. Sun d'au tsawon lokaci suna abu d'aya sannan a hankali ya saketa, lasan swollen lips nata tayi tare da miyar dasu ciki tana me cigaba da kukan.
"I will forever love you Zainab" yace da ita yana kallonta. Gudu kawai tasa ta shige ciki se d'akinta ta nufa tasa lock tare da wurgi da kanta bisa gado tana kukan cire rai, hanneyenta rik'e da kanta se juyi akan gadon take. Shima Adeel tsaye yayi wajen yana tsiyayar da hawaye sannan daga bisani ya fita ya koma cikin motarsa guiwa ba k'wari. Kuka sosai ya shigayi cikin motar, ba Zeezee rayuwarsa bata da wata ma'ana again. What else does he have to live for? His advice to all mankind is to appreciate what they HAVE before life makes them appreciate what they HAD verily nothing last forever, after all the life itself is temporary.

****
"Zeezee! Ki bud'e k'ofar mana sekin sa min hawan jini ne tukuna?" Har anan se sautin kukan Zeezee kawai takeji. "Zeezee please upon up."
"Mama am sorry please go away I need to be alone, kiyi hak'uri don Allah."
"Zeezee bazan iya barinki haka ba ki tashi ki bud'emin ko sena yi kuka tukuna."
"No Mama I beg of you dan Allah kiyi hak'urri ki tafi." Ta k'are maganan tana jan hanci. K'in tafiya Mama tayi har seda Zeezee ta taso ta bud'e mata don dolenta. Fad'awa jikin Mama tayi tana kuka me tsuma zuciya. A sannu a sannu Mama ta k'arisa da ita cikin d'akin tare da zaunar da ita bisa kan gado.
"I'm here for you, I've gotchu." Kuka tayita yi Mama na bata hak'uri tana soothing nata. Se chan ta tsagaita kukan. "Can you tell me what happened?" Kai zallah take kad'awa nufin no, "remember am here for you kinji? Tell me meya faru? Keda Mallamin islamiyyan ku ne?" Kai kawai ta kad'a mata. "Then who?"
"Adeel Mama."
"Again? Meya faru kuma? Kina son ki koma mishi ne?"
"Mama he left just now, Adeel ya tuba kuma yana son in koma mishi he kept on crying like a baby yana gayamin how much he wants me back. Yadda yake kuka nima ya sani Mama."
"Shhh! all shall be well kinji? Bar kukan haka."
"Mama I love Adeel also."
"I know Zeezee kiyi hak'uri ki danne zuciyarki ki koma mishi nasan yayi nadama tunda abinda zuciyarki keso kenan."
"I can't Mama, d'akin Ya Al'ameen nakeso-" katse ta Mama tayi "Zeezee bamu san ko Al'ameen ya sake aure ba or not we don't even know either Mamanshi zata bari ki koma masa."
"I still don't care Mama shi nakeso gareshi kuma zan koma."
"Allah sa hakan yafi alkhairi toh."
"Ameen Mama nagode."
"Ki huta kinji? Kukan ya isa."




*MIEMIEBEE. Team #YGC!🎀*
Beeenovels.blogspot.com

🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*

*Febraury, 2017*
5⃣6⃣

_For all the love and support you've shown to my special soul AUNTY SIS, for all the hardships you've been through and still didn't give up on her, AUNTY SIS wants to show her deepest appreciation to y'all. This page is yours members of THE TEAM._


Tun daga ranan da Adeel yaji daga bakin Zeezee da kuma kunnuwansa kan ta tafi bazata sake dawo masa ba, he can't ever have her back ya miyar da life nasa useless. Ba aikinsa sede kullum yaje bar and get himself drunk, aikin office ma ya yanke zuwa ba kuma wai ya tura musu notice bane, Mami tayi surutu har ta gaji. Sa'an sa d'aya, Boss nashi was once a friend to his Dad if not da tuni yayi firing nashi.
Ruky kam kullum cikin habaici da zaginsa take musamman ma idan ta tuna da about 2weeks kenan yanzu ya yanke mata weekly allowances nata. Sam ba jituwa a tsakaninsu kullum cikin tashin hankali sekace Tom and Jerry. Adeel bema aza Ruky aka ba ko zaginsa take sede ya saurareta ya kad'a kai saboda rashin Zeezee kad'ai ya ishesa damuwa, da haka fa Adeel ya soma neman mata amman bawai fasik'anci yake dasu ba sede yayi dating nasu suci mai kud'i ahaka har suka dace da wata 'yan mata wanda a birthday'n wata cousin nasa suka had'u da ita, abu kaman wasa-wasa Adeel idan ya fita tun safe se kusan goman dare ko sha d'aya ya dawo as kullum yana cikin partying. Office daya koma ma ba kullum yake zuwa ba, sosai staying late nashi ya soma damun Ruky, she can't remember when last ma abu ya shiga tsakaninta da Adeel, she needs her husband atleast. Yau ma as always se 10:56pm Adeel ya bugo Genesis nasa ya dawo gida, alokacin Ruky na tsaye a parlour tana jiransa tana sanye ne da free size rigan bancinta riga da wando. Yana bud'e k'ofan sega tanan tsaye, tsuka yaja sannan ya maida k'ofan ya rufe.

"Adeel!" Ta kirasa in a serious tone.
"Lafiya?" Ya amsa in an I dont care tone.
"Daga ina kake?"
"Daga k'aniyan ki nake, mschw! Ina ruwanki da inda naje? Wake ajiye wani tsakani na dake?"
"Ba abinda na tambaya ba kenan daga ina kake nace?"
"So kike kiji? Daga french party'n friend d'ina, aikin banza kawai!"
"Party? Ko kunya baka ji ba? Da aurenka kake zuwa party?"
"Kunya? Sata nayi? Da da muke zuwa taren ba auren Zeezee a kaina ne?"
"Zeezee kace nikuwa Ruky Mama ce, ita taga zata iya nide wallahi ba'a gidana ba, ba yadda za'ayi ka fita chan kana partying nikuma ka barni da yima gadi, wai bama wannan ba rabonka da kabani hak'k'i na since when?"
"LOL. Ai seki fito fili kice Adeel I need you bawai ki tsaya kina bin long process ba."
"Wait, wait tsaya Mallam karka kuskura wallahi koda wasa, kace zaka soma kula matan wajen nan don wallahi bazan yarda ba."
"Zeezee ma ta hak'ura bale ke d'in banza, kin gadama kada kiyi mschw!" Yana kaiwa nan ya nufi d'akinsa.
"Adeel baka sanni bane wallahi baka san Ruky Mama ba" tace da kanta, "idan Zeezee ta barka kasani Ruky baza ta barka ba, mu zuba mu gani." Rai a dak'ule ta wuce d'akinta. Washegari Ruky ta kira wata friend nata party rocker akan tayo mata bincike either dagaske Adeel nada girlfriend a waje or not.
"I've got this Babe karki damu."
"Yauwa Ammatas thank you." Ahaka sukayi sallama. Tun safe as always yauma ya shirya ya fita, da yamma friend na Ruky tayi calling nata back inda take jaddada mata cewa yes its true Adeel is currently dating wata Babe sunanta Nusaiba amman da Nusee ake kirarta.
"Babe are you serious please?" Ruky tayi maganan cike da k'in yarda.
"Wallahi, ko jiya ma sunje wani French Party da ita." Nan Ruky ta sake gaskata zancen saboda Adeel da bakinsa jiya ya gaya mata daga French party yake.
"Thank you Ammatas, aikin ki yayi kyau."
"Take it easy Babe na sanki."
"Wani irin easy? Barni dashi."

Da goshin Maghrib Adeel ya dawo gida yau unlike yadda ya saba, Ruky na kallonsa ya wuce d'akinsa seda ta tabbata ya shiga bayi ta bi bayansa, jin alaman gudun ruwa ta tabbata wanka yake, hakan yasa ta k'arisa ciki ta d'au wayarsa, unluckily ta samu yasa lock na pattern. Dabara ce ta fad'o mata ta lak'uta vaseline kad'an ta shafa kan screen d'in yadda da zaran ya zana pattern d'in design d'in ze fito. Fita tayi da sauri jin ya kashe tap d'in. Anan ta la6e bakin k'ofa tana kallonsa. Kaya yasa me kyau ya feffeshe jikinsa da turare, duk anan kallonsa take seda taga ya d'aga wayansa ya bud'e sannan ta fad'a d'akin da sauri stopping him from what he is about doing.

"Lafiya? Zaki fad'o min d'aki ba sallama?"
"Baby wallahi tsaka! Tsaka a parlour."
"Mschww! Shine me?"
"Baby please ka kashe wallahi bana son abin ko kad'an."
"Ni dake waya yi kalan zefi wani iya kashe tsaka? Abeg fita min daga d'aki." Isowa tayi har gabansa a maraice "Baby please kayi hak'uri ka kashe min, Allah banason abin" Kallonta ya tsaya yi yana nazari nan ta samu daman amshe wayan nasa a nitse "please Baby."
"Yana ina?" Ya tambayeta yana mata mugun kallo.
"A parlour Baby."
"Muje."
"Kayi hak'uri kaje kai d'aya wallahi

62 / 98