Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
shiga neman Al'ameen daman wayan na gefensa shima tun sanar dashi da Zeezee tayi ta shiga labor yau ko office ya kasa shiga se tunanin wani halin take ciki yanzu yake. "Halo Mama ina yini?"
"Lafiya Al'ameen ya kake?"
"Lafiya Mama ya Zainab ta sauqa?"
"Har yanzu fa Maj-Gen ba yadda ba'ayi da ita ba tayi pushing tak'i wai se kana wajen zata yi ni bansan ya zamuyi ba, ba kalan rok'an ta da banyi ba tayi hak'uri tak'i wai akira ka kazo."
"Oh God! Ya zamuyi yanzu? Ga pilot na Private jet d'inmu yayi tafiya, Mama please ki rok'eta nasan zata ji maganan ki she is in so much pain."
"Maj-Gen. ba yadda banyi da ita ba tak'i jina bari na had'aku a wayan muga." Nan da nan takaiwa Zeezee wayan tasa a speaker. "Princess?" Ya kirata cike da tashin hankali.
"Ya Al'ameen" ta fad'a cike da azaba da wahala.
"Princess calm down and breathe kinji calm down am here."
"Ya Al'ameen I need you I can't do this without you please come."
"Am here Princess am here for you, Khaleefah is also here fo you ke kad'ai zaki iya kawo mana Princess namu into live and I trust you. I love you so much."
"I love you also."
"Good breathe along with me, in... out. In... out" sunyi hakan kusan sau biyar sannan yace, "thats My Princess now is time to push."
"No Ya Al'ameen bazan iya ba."
"Zaki iya Princess I trust you remember kin cemin you'll never break down my trust, haka ne?"
"Haka ne."
"Good so I trust you I know you can do this. In the count of three se kiyi pushing kinji? Kinji?"
"Uhum."
"One... two... three push." Pushing d'in tayi da iya k'arfin ta amman ko 6ullo kai baby beyi ba. Jin ihun Maminsa tun daga waje yasa Khaleefah 6arkewa da kuka daman tun d'azu se turancin where is my Mammy and Granny yake yiwa Baaba kasancewar ba jin turancin take ba se ce mai take eh takalmin ka yayi kyau d'an kyakkyawa. Kansa ya rik'e yana toshe kunnuwansa "Mammy!" Ya kira ya na kuka nan ta fito dashi harabar asibitin tana jijik'a shi.
*MIEMIEBEE. Team YGC!🎀 ZAIMEEN flames🔥🔥🔥*
Beeenovels.blogspot.com 👄
[3/29, 21:24] +234 810 030 0159: 🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*March, 2017*
8⃣0⃣
Back inside mutuwa ne kawai Zeezee batayi ba har airtime na Mama ya k'are ta kasa wani push d'in shima Al'ameen sau biyu katin sa na k'arewa yana sake loda new pin. Da k'yar ya samu Zeezee ta sake wani push d'in anan Dr Sammy Tayi exclaiming "the baby's head is finally showing we need three more push, you are doing good Zeezee."
"Thats My Princess kinga saura just three pushes one for Mama, one for Khaleefah and one for me ko? Muje na Mama toh."
"Ya Al'ameen ji nake like zan mutu ku bani fresh air please." Bayan fifitan da akayi mata aka samu ta sake wani push d'in. Sun mugun shan wahala sannan aka samu tayi remaining two pushes d'in. Suul Dr Sammy ta jawo baby "wow its a girl!" Wani ajiyan zuciya Zeezee ta sauk'e wearing the most expensive smile. "You did it Princess!" cewar Al'ameen sounding delighted.
"I wouldn't have done it without you Sweetheart, I love you so much" sannan ta dawo da kallonta kan Mama "thanks for not giving up on me Mama I love you so much also."
"We love you more" cewar Mama "so Maj-Gen. Bari a kintsa little Princess taka za ayi maka sending picture'nta."
"Toh Mama thank you, take care okay Princess I love you." Ji yake ina ma yana tare dasu suma yaga little Princess nasa finally.
"I love you more" Cewar Zeezee, daga nan Mama ta katse wayan. Baby'n aka wanke aka kawo wa Zeezee ita nannad'e cikin pink showel. Se tace tunda tasan kanta bata ta6a ganin kyakkyawar hallita ba kaman wannan little angel dake hannunta ba, gashin kanta ya sauk'o har kan goshinta seda ya had'e da gashin girarta. K'ara ta saki kad'an se kuma tayi shiru tana nonnok'e kanta cikin showel d'in which is damn cute. Bin every move nata Zeezee ke da kallo, "she is soo cute Mama."
"Masha Allah, Allah ya raya mana ita."
"Ameen Mama." D'aukanta Mama tayi a hoto ta wayan Zeezee tayi ma Al'ameen sending ta whatsapp take yayi updating nata ya kira su.
"Princess little Princess is damn beautiful." Ya fara fad'a. Mama dake jinsu kasancewar a speaker phone suke wayan tace, "saboda wannan karan ta d'auko kamannin both parents nata shiyasa tayi kyau dayawa, tubarkallah." Murmushi Zeezee ta saki "nima tun d'azu kallonta nake na kasa gane dawa take kama nasan wannan hanci na ne a fuskanta."
"Lips nata kuma da eye brows irin nawa ne." Cewar Al'ameen yana me jin dad'i.
"Yess shape na face nata kam nawa ne her eyes kuma..." Zeezee bata k'arisa maganan ba baby'n ta bud'e idonta "irin na Maj-Gen!" Shouted Mama.
"Yeyy! Ta d'au lips d'ina, eyes amd eyebrows nose na Princess ne kawai."
"Inji wa? Harda shape na fuska. Ai inade ba kamanninka duka ta d'auko ba kuma ma yawan gashin kan goshintan nan irin nawa ne."
"Amman kamanni na yafi yawa ai."
"Naji toh, wani suna kasa wa Lil Princess tamu?"
"Sunan Mama Babba AMEENAH da al-kunyan AFREEN."
"Masha Allah, Allah ya raya mana surika ta akan addinin muslinci ya albarkaci rayuwarta."
"Ameen" su uku suka fad'a in unison.
"Toh Sweetheart se mun sake waya zan shiga wanka yanzu."
"Toh Princess take care okay? Mun gode Mama."
"Ba komai Maj-Gen." Anan Mama ta katse wayan ta amshe Afreen daga hannun Zeezee, Zeezee ta shiga bayi bada jimawa ba Baaba da Khaleefah suka shigo, wajen Mama ya nufa da gudu "Granny where is Mammy?"
"Mammy ta shiga wanka."
"Who ish this toy Granny?"
"She is not a toy Mijina, wannan Little Princess taku ce your baby sister."
"My sister?"
"Yes your Sister Mammy ta haihu, wannan ne Princess da tasa cikinta yayi k'ato."
"Ohhhh! Ches cute."
"Yes she is."
"Sunanta Plincess?"
"Afreen Da da ya nad'a mata sunanta Afreen." Ai kawai yasa musu kuka dalili kuwa wai sunan Afreen yafi nasa dad'i shi baze yarda ba.
***
Kusan da Maghrib aka sallami su Zeezee. Son Afreen Zeezee ke sosai, yarinyar abar so ce kodan kyanta gata bata kuka like Khaleefah tun da aka haifeta har izuwa yanzu bata sha nono ba ruwa kawai tasha se bayan isha Zeezee ta sa mata mama a hankali ta kama, kad'an tasha ta sake. In three days time Al'ameen ya iso dad'i kashe Zeezee yau mafarkinta ya zamo gaskiya. Gashi ta haifi yara har biyu mace da miji sauran su koma Washington kawai yanzu dream nata yayi coming true.
Suna wane sunan d'an fari haka wannan ma mutane suka cika, abubuwan da Al'ameen yayi a bikin sunan Khaleefah haka sak yayi ana Afreen Zeezee da 'yarta sun sha kyautuka sosai abin ba'a cewa komi. Zeezee na nan fit sekace ba wacce ta dire yara biyu ba. Ko da aka yi suna Al'ameen be koma Abuja ba hakan yasa Mama ta k'ara mata kwanaki hud'u kawai ta koma gida, Al'ameen keyi wa Afreen wanka da kansa atimes kuma Zeezee shide Khaleefah ya kasa gane feeling da yake yi wa Afreen atimes ya ji yana sonta atimes kuma yaji ya tsaneta yata kuka wai se an mayar da ita asibiti inda suka d'aukota sam wai Zeezee bata sonshi se Afreen, d'an banzan kishi ne dashi. Idan iskancin sa ya tashi kuwa yace shima seya sha nono musamman idan yaga Zeezee na breastfeeding Afreen, ba k'aramin drama suke sha ba. Akwai rananda Al'ameen ya kama Khaleefah na toshewa Afreen hanci don mugunta kawai, kad'an ya rage Zeezee bata mai duka ba ranan.
Haka kuma rayuwarsu ta cigaba da kasancewa, what a family they are now kullum Zeezee na cikin kamawa Afreen gashinta into different and stunning styles saboda aljanun gashi ne da Afreen sekace ba yarinya ba. Cikin runfan Allah yara suke ta girma a yayinda soyayya tsakanin iyayensu ke sake dad'uwa a kullum.
_3 years later..._
Da gudu Afreen dake 3years old yanzu ta fito daga d'akin Khaleefah tana sanye ne da penal 4 uniform nata na school da alama yanzu suka taso daga. Kanta an kama mata into two ponytails, shima Khaleefah da gudun ya fito yana paparota. He is now 5 years 4 months old yaro ya zama saurayi sanye yake da wandon uniform na school nasu shima da singlet hannunsa d'aure dawani blue agogon ben 10 na roba. Kitchen Afreen ta fad'a tana kiran "Mammy Mammy!" Da gudu ta k'arisa tana 6uya Bayan Zeezee. Khaleefah na k'arisowa ya wuce direct zeje ya fincikota wai, da sauri Zeezee taja sa baya "what is wrong with you Khaleefah? Get your senses together, ban hanaka biyo Afreen kitchen ba?"
"Kullum ni kita scolding d'ina Mammy, kinsan me tamin ne?"
"Zan saka kneeling k'ark'ashin rana fah! Manners!"
"I'm sorry, book d'ina fa ta d'auka tana drawing ABCD wai nata ne."
"Afreen Princess give him back his book."
"No! Ba naci bane its mine!"
"Its mine keda kike Nursery 1, ita da zaran taga 1 akai kawai setace nata ne, nima ba primary 1 nake ba, give it back."
"No I won't its mine."
"Princess let me have a look at the book." Cewar Zeezee calmly.
"O'o nawa ne."
"I know lemmi have a look."
"O'o zaki bashi."
"Bazan bashi ba in gani." Da k'yar Zeezee ta iya ta amshe book d'in "Princess wannan ai na Khaleefah ne."
Zaune tayi akan tiles tana shure k'afafunta tana kuka "nawa ne ga one akai."
"Tsaya kiga, kinga ke sunan ki daga letter 'A' ya fara nashi kuma daga 'I' now tell me the Princess with brains what letter is here?"
"Number I." Ta fad'a confidently. Dariya Khaleefah yasa "jita wai number I dolo kawai, letter 'I'"
"Mammy kinji yana shemin dolo ba." Hannu ta d'aga ta zage shi. "Laaa a kunnen Da da Afreen na zagi."
"Zagi" Exclaimed Zeezee "ban hana zagi ba Princess?"
"I didn't insult him."
"Yes you did, she did Mammy."
"Toh kaima meya kaika ce mata dolo? Ban hanaka ba?"
"Kin hana" ya fad'a yana kallon k'asa "ni bani book d'ina in koma d'aki na." Miqa mai littafin Zeezee tayi "oya hold your sister's hand kuje ka cire mata kayanta kasa mata leggings da crossed neck vest nata all in blue, na aiki nanny'n ku kasuwa. Kai kuma kasa shorts naka da shirt."
Ni bazan cire mata ba rashin kunya ne da ita. Kuma ni banason shorts full length trouser zan sa."
"Khaleefah! Manners!"
"Am sorry amman kice karta min rashin kunya."
"Princess banda rashin kunya kinji? Khaleefah is your big bro."
"He ish not." Tayi maganan tana zuba mai harara.
"Kingani ba Mammy?"
"He is Sweetheart bisa ya cire miki uniform naki se kuzo muci abinci zamu fita shopping kunsan next week zamu je Washington ko?"
"Yeyy! We are going to fly!!!" Afreen tasa ihu.
'Yar k'auye kawai me acikin flying d'in?" Cewar Khaleefah yana wani basarwa.
"Ba laifinka bane ai saboda bana maka malu kake wannan iyayin gobe zan kaika barbing salon a kwashe wannan gashin duka."
"No please Mama I'm sorry bana son malu."
"Then behave yourself."
"I will Afreen lets go."
"Mammy kishe mishi yashe min Plincess."
"Call her a Princess Khaleefah."
"Why shall I Mammy? Neither you nor Da da is a King or a Queen taya ta zama Princess?"
"Mammy tell him to call me a Plincess."
"Call her a Princess Khaleefah!"
"No Mammy."
"Aje ayi maka malu?"
"Alright, alright Afreen Princess muje in cire miki uniform naki, shikenan?"
"Yeyy! I am a Plincess."
"Yes you are Sweetheart" pecking nata tayi a forehead sannan wa Khaleefah ai kuwa shi babban yaro yasa hannu ya share "ni banason kiss d'innan kinayi wa Afreen zallah."
"Ai sena aske gashin nan zaka shiga hankalinka." Be sake cewa komi ba ya shiga jan hannun Afreen "banda duka ko fad'a Khaleefah duk wanda yayi fad'a baza a je Washington da shi ba." Seda suka 6ace daga kallonta ta hanzarta ta k'arisa lunch ta yi setting table, gashi Al'ameen ze shigo gobe she is damn busy.
Bayan sun ci abinci sun kuma wani wankan suka fice Jifatu shopping mall. 100k each Al'ameen yama Zeezee sending akan tayi musu siyayyan kaya, duk abinda yaran suka ce suna so shi take siya musu tunda Baban su ya bada kud'in. Sunyi shopping kaman ba gobe sunzo fita kenan se k'iriniya Khaleefah da Afreen suke kaman yadda suka saba, basu mintuna biyu gu d'aya basu yi fad'a ba.
Khaleefah na rik'e da stickers daya sa Zeezee ta siya masa zeje ya manna a d'akinsa Afreen ta sa hannu ta wabce tasa wani d'ankaren gudu tsantsi ne ya kwashe ta gab da ta kusa fita daga exit d'in, ta kusa fad'i kenan wani mutum ya tare ta daba don haka ba data sha k'asa. Gaban Zeezee ya mununar fad'i a rayuwa batason abinda ze ta6a mata lafiyan Afreen ko Khaleefah. Khaleefah ko dariya yake haushi ma yaji da aka tarota yaso ta fad'i ta buga bakinta nan gaba bazata sake guduwa da abinda ba nata ba.
"Afreen!!!" Zeezee Tasa ihu. "Alhamdulillah!" Ta fad'a sounding relieved, da sauri ta k'arisa wajen tare da jan hannunta "bawan Allah thank y-" bata kai ga k'arisa maganan ba mutumin ya d'ago kansa, fuskan data gani ne ya mugun jijjigata.
"Adeel?!" Ta furta with ultimate suprise and disbelief. Shima kallonta yake ya ma kasa cewa koda uffan. Da ba don ya ma Zeezee sani na sosai ba da seyace wata ce me kama da ita saboda wani haske na musamman data k'ara da kuma k'iba, a takaice tafi da yin kyau. "Zeezee, kece?" Ya fad'a shima disbelievingly.
"Laaaa!" Afreen tayi covering bakinta da hannu "Khaleefah a stranger just called Mammy Zeezee, ba Da da ya hana ba?"
"Ke da Allah kima mutane shiru and give me back my stickers"
"Its mine."
"Give it back." Ganin suna neman fara wani sabon fad'a Zeezee tayi seizing stickers d'in "oya kubi driver ku wuce mota."
"But Mammy its mine."
"Do as I ask Khaleefah to the car."
"Mammy my stickers." Cewar Afreen.
"Se munje gida, to the car now."
Mammy why are you talking tona stranger? Da da ya hana."
"He is not a stranger Honey sunan shi Uncle Adeel."
"Da da ya san shi?"
"Kibi Khaleefah ku wuce mota we'll discuss it later okay? I love you both." Hannun Afreen Khaleefah ya rik'e suka fice. "I should get going also Adeel, thanks for saving my daughter from tripping." Har yanzu Zeezee bata ishe sa da kallo ba a gaskia yayi babban rashi a rayuwan shi na rasa Zeezee gadhi nan ita har yara biyu. allah ya azurta ta dashi, kyawawa sasu wane yaran larabawa. Gaskiya ne Allah ba azzalumin bwansa bane, duk yadda yaso destroying wa Zeezee mahaifatrta Allah be yarda da hakan ba tunda she was innocent gashi nan shi yanzu yana neman shekara tara (9) da aure ko rabin yaro baida, a rayuwa koda wasa kar mutum ya yarda ya d'au alhak'in wani. Seda tazo gab da fita bakinsa ya iya bud'uwa.
"Zeezee ko gaisawa ai sai muyi... please." Kaman bazata tsaya ba se kuma ta tsaya, "ina yini?" ta gaishesa briefly.
"Thousands of days, how have you been great I guess."
"Alhamdulillah ya kake da kuma Ruky?"
"Lafiya, were those two your-" katse sa tayi with a "yes. Yarana ne babban Khaleefah, k'aramar Afreen."
"Masha Allah time heals, Allah ya raya mana su."
"Amin, nagode ya naka yaran?" Kai ya kad'a mata "sorry?" Ta tambayesa bewildering.
"Allah be kawo rayayye ba har yanzu Zeezee, sau uku kenan tana haifa ba