YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   34 / 98

99K to 102K   out of 291.7K words

right away “hello Babe meya samu line na Very Own bayi shiga? Inason mishi magana, its high time I tell him the truth.”
“Ermm.. Ni... Nima ban sani ba fa tun d’azu nake trying.” Sede don yadda Zeezee tasan Lubiee ta gano k’arya Lubiee ke. “Babe you are hiding something from me dan Allah ki gayamun meya samu Very Own d’ina? Yayi accident ne? Is he badly injured?”
“Zeezee enough of the panicking please ba abinda yasamu Adeel nima nayi trying line nasa it aiint going through.”
“Babe please don’t lie to me on this, I can sense it ba lafiya ba dan Allah meya samu Very Own?”
“Zeezee wallahi babu abinda ya sami Adeel just that... Just that...” sekuma tayi shiru.
“Just that what? Tell me please.”
“He has find out the truth already Zeezee.”
“Truth about my wedding? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” sekuma ta fashe da kuka “Babe how? I intended on telling him everything tonight dan Allah tell me its not true, please...” ta sake rushewa da kuka.
“Please ya isa kuka is never a solution I know Adeel he’ll calm down soon enough, if he does nida kaina zan mai explaining komi please kibar kukan haka.” Har anan Zeezee kuka take, “Lubiee na fiki sanin Adeel wallahi baze ta6a sauk’owa ba, koda zeyi ma ba nan kusa ba nikam na mutu na lalace, Al’ameen be kyautamin a rayuwa ba” tana kaiwa nan ta katse wayar. Wurgi tayi da kanta bisa gado ta shiga rera kuka tana sumbatu ahaka Mama tazo ta tarar da ita ba kalan tambayan duniyan da batayi wa Zeezee ba amman Zeezee tak’i tankata. Daga k’arshe ma kawai tayi suggesting halan kukan shagwa6an barin gida Zeezee ke.

Kwana ranan Zeezee tayi tana trying layin Adeel sede sam its not going. Washegari Lubiee itama ta gwada line na Adeel bai shiga tana gama shiri tazota gidansu Zeezee inda ta sameta se kuka take Mama na a tsaye a kanta ta zuba mata ido. “Ina kwana Mama?” Lubiee ta gaisheta.
“Barka ma da kika zo Lubabatu, shin meke damun k’awar taki? Ba kalan tambayan duniyan da ban mata ba tak’i fad’amin. Tun jiya take wannan kuka ga gida ya soma cika da mutane banason a fara k’ananun magana cewa auren dole Babanta keson mata.”
“Shikenan Mama zan mata magana kije ba damuwa.”
“Yauwa please.” Mama na ficewa Lubiee taja crying Zeezee jikinta “Babe its okay please kinga kukan nan baida amfani bashi ze dawo da Adeel ba, yau zanje gidansu in samesa in person kinji?” Take Zeezee ta d’ago kai “please kije ni ko yanzu nema kije ki samesa I need him badly.”
“I will amman sekin bar kukan nan.”
“Wallahi na bari” tasa hannu ta share hawayen nata. Sosai idanunta suka kumbura sukayi water bags a k’asa.
“Toh bari naje na same san” anan Lubiee ta fice zuwa gidansu Adeel.

Mamin shi kad’ai ta tarar bayan ta gaiaheta ta tambayi ko Adeel na gida.
“Ai Auta na baya nan Lubabatu, be fad’a miki zeyi tafiya bane?”
“Tafiya Mami?!” Lubiee tayi exclaiming.
“Eh fah.”
“Amman lafiya dai ko?”
“Toh kinsan halin Auta baya son sanar dani problems nasa, nide all I know is tun jiya ko lunch yak’i fitowa yaci yau da safe kuma na gansa fuskansa duk a kumbure yana rik’e da akwati. Dana tambayesa ko lafiya kuma yacemin lafiya kawai ze wuce Florida ne yaje ya huta achan yanzu haka yana Abuja d’azu ya kirani kan sunyi landing.”
“What?! Florida ze wuce?”
“Eh wai.”
“Toh Allah sa lafiya ya kuma dawo dashi lafiya amman Mami ya gaya miki for how long he’ll be staying there?”
“A’a gaskiya nima ban tambaya ba becika son tambaya haka ba.”
“Toh numbansa nakeso zan kirashi.” Bayan Mami ta bata layin tayi godiya sannan ta fice a bakin gate ta kira layin Adeel thankfully ya d’aga “hello Adeel?”
“Lubiee?” Ya tambaya not sure.
“Eh ni, kai haka akeyi ne Adeel? Yanzu ka kyauta kenan tun jiya Zeezee ke kuka-”
_Disconnected_ taji tana dubawa taga hanging call d’in Adeel yayi kafin tace zata sake kiransa har ya cire sim d’in ya karya. Tashin hankali! Kasa komawa gidansu Zeezee tayi. Zeezee ko tun d’azu jiran Lubiee take jin shiru ta kirata da kaman Lubiee bazata d’agaba sekuma ta canza mind nata “hello Babe I’ve been waiting for you since, ina kika shiga?”

“Uhn Ummi ce ta kirani wallahi I had to go back home.”
“Oh ayyah kinsamu kinje gidansu Adeel d’in?”
“Uhm-”
“Please don’t lie to me, komin d’acinta ki gayamin wani yanayi kika tsinci Adeel please.”
“Zeezee I’m terribly sorry, I went Adeel bai gida yana Abj as we speak now daga can ze wuce Florida for a break regarding what happened.”
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! No! No! No please!!!” jefar da wayan nata tayi ta ruga aguje zuwa bayi tasa lock. Bajewa tayi k’asan toilet d’in tana kuka wane don shi aka turota. Hakan ta cigaba dayi seda hawayenta ya kusa k’arewa. “Adeel why do you have to leave me please, why? You know right I can’t leave without you please come back it doesn’t have to be this way.” Seda tayi calming kanta ta fito ta d’au wayar several missed calls na Lubiee ta tarar nan ta kirata back “thanks Gee!” Lubiee tayi exclaiming.
“Lubiee kimin sending digits na Adeel if kinada please.”
“Wallahi bani dashi sabo wanda Mamin shi taban ma yabar shiga maybe ya karya koya kashe wayan. Yanzu ba lokacin damuwa da Adeel bane it might follow afterwards kinsan fa jibi za’a fara wedding events naki inhar kikayi ruining su Sumayya sun samu abin magana akai kenan. Please ba don ni ba don Allah ki manta Adeel for now kinji? Kiyi hak’uri.”
“Thank you sekinzo gobe” nan tayi hanging. Haka koda Mama ta kawo mata maganinta yau tasha ba tare da sunyi long drama ba takoma gado ta kwanta. Mama de harta gaji da tambayan Zeezee whats her problem.
A washegari Yasmeen, Fateemah da mazajensu suka hallaro.

_PROGRAMS OF EVENT Starts..._
Da Tea party suka fara, event ya had’u iya had’uwa sede Zeezee sam ba walwala tatattare da ita su Lubiee kad’ai sukayi enjoying party’n through out the event tunanin Adeel Zeezee ke. The following day akayi English dinner Zeezee and Al’ameen nailed it a wajen ba’a cewa komi se wanda yagani, naira yayi kuka. Bayan english dinner akayi Kamu se sword crossing wanda yafi dukannin events d’in so far had’ewa. The next day which is Friday aka d’aura auren MAJ-GEN. MUHAMMAD AL’AMEEN SHETTIMA da ZAINAB ISMA’EEL YUSOUF akan sadaki naira dubu d’ari biyu.

Zeezee najin an d’aura aurenta da Al’ameen ta rikice musu a gida ranan. Kuka tayita yi wane zata cire ranta. Ita abubuwan ma sun taru sunyi mata yawa. Na farko ba wanda takeso zata aura ba, na biyu ga barin gidan da zatayi and above all rashin Adeel nata. Su Mariam sun bata hak’uri har sun gaji, haka Lubiee, Fateemah da Mama ma. Wani kukan ma seda dangin Ango sukazo d’aukan Amaryarsu. Zanin Mama ta kama k’ememe tak’i sakewa se rusa kuka take tana sumbatu tana ita ta fasa auren. Ba yadda basuyi ba a fito da Zeezee sun kasa daga k’arshe Baba aka kira tana ganinsa ta ruga aguje ta nufi kansa tare da tattara jamfansa a hannu tana kukan cire rai tana basa hak’uri dan Allah ya barta ta cigaba da zama a gida ta tuba bazata sakeyin wani rashin hankali ba. Seda Zeezee tasa idon Baba yayi ja saboda yadda take kuka sosai har se ji yake kaman yasa Al’ameen ya saketa a fasa auran amman hakan bame yuwuwa bane.
“Yi hak’uri Zeezee, everything will turn out perfect kibi su Ayshah kinji? Muma zamu taho daga baya, muna tare ai Hafsah zoki jata.”
“Baba dan Allah kayi hak’uri Mama please karku fitar dani daga gidan nan.” Haka da k’yar aka fitar da ita aka sata mota zuwa gidanta, su Lubiee se hak’uri suke bata. Not long enough aka hau shirin dinner, makeup na ranan shine beyi kyau ba saboda yadda fuskan Zeezee ya kumbura bayan nan kuma tak’i ajiye fuskan nata se kuka take. 8:30pm suka wuce Zaranda Hotel inda za’ayi program d’in. Ai ganin hotel d’in kawai ta sake tunawa da Very Own nata. Suna zaune da Al’ameen a motar ta shiga rusa mai kuka, beso mata magana ba saboda yasan theres no point doing so and koda hak’uri ya bata ma sake worsening situation d’in zeyi dan haka kawai ya zuba mata ido se aikin kukan take. Dai-dai driver yayi parking Al’ameen juya ya kalleta “My Princess all shall be well kinji? Stop crying haka, our families awaits us.” Wani wutan tsanansa ne ke ruruwa a zuciyarta ko kallonsa batayi ba, da k’yar su Lubiee suka fito da ita daga motar. Tabari ya rik’e hannunta ma tak’i haka through out the event tak’iyin murmushi bale dariya se tissue take sawa a idonta tana tare hawaye.

*™ MrAndMrsMuhammadAl’ameen.*💑

*© MIEMIEBEE Team #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*

*January, 2017*
3⃣3⃣
_Hummm! I can smell my birthday tomorrow☺😋_

_This page is in honour of *Zaynab Anka, Ummee, Feedy G Muh’d, Kabo Daughter, Mom Nu’aym, Umm Aneesah, Maryam,* and *Maryam Wasagu* #OneLove❤_


Ana gama event su Zeezee suka dawo gida gabad’aya kowa ya watse a gidan daga ita se Al’ameen se soliders kota ina suna gadi. Driver na parking ta bud’o k’ofa ta fita gaban entrance door ta tsaya tana jiran Al’ameen ya bud’e mata k’ofa har anan bata bar kuka ba wanda hakan ba mugun damun Al’ameen yake ba. Har tambayan kansa ya somayi anya kuwa Zeezee na sonsa? Da guards nasa biye dashi ya k’arisa ya bud’e mata k’ofan kai kawai tasa se a d’akinta ta tsaya ta baje kan gado tana me cigaba da rusa kuka. Bayan Al’ameen ya bud’e kazan amarchi yasa mata a plate da farm fresh a cup ya nufi d’akin nasu, sallama yayi ganin batada niyyan amsawa yasa kai ciki kawai. A kan side drawer ya ajiye “Princess?” Ya kirata a hankali cikin sark’ak’k’iyar muryansa. “Princess kukan ya isa kinji? Yi hak’uri” hannunsa ya d’aga a hankali ya aza kan bayanta, jikinta ta ja da wuri tare da d’ago kanta tana mai wani mugun kallo. “Don’t touch me Al’ameen don’t! Bak’in cikin daka jefani kad’ai ya isheni ba seka k’ara min da wani ba. Ka rabani da iyayena and above all ka rabani da saurayi na Adeel kasa yayi nesa dani kasani bazan ta6a yafe maka ba Al’ameen. Ka cuceni I wish I’ve never met you.” ta k’are maganan hawaye na bin k’uncinta.

“Zainab what are you talking about? Weren’t you the one that agreed to thsi wedding in the first place? Dama ba sona kike ba kika bari akayi auren?” Ya tambayeta suprisingly.
“Nayi ne saboda in farintawa Baba rai amman badon wai ina sonka ba, ban ta6a sonka ba kuma bazan ta6a sonka ba. I hate everything about you, your skin and that sweet irritating voice of yours Adeel nakeso I want you to stick that to your head and please excuse me just looking at you disgusts me.” Ta k’are maganan tare da watsa mai harara.
Mamaki ne sosai ya cika Al’ameen da har ya zama lost of words amman be damu ba saboda gani yake har yanzu yarinya ce batasan ciwon kanta ba eventually al’amura zasu daidaita tsakanin su, he believe. Murmushi me sake k’ayatasa ya saki “naji toh My Zainab amman tashi kiyi having dinner seki kwanta kinji?”
“I am not yours and ba ruwanka da abinda zanyi tunda ba zaman ka nake ba, kuma ka tattara kajinka kayi waje dasu banaso bazan ciba.” Tana kaiwa nan ta mik’e tare da jan akwatinta ta ciro night gown nata ta nufi bathroom. Kai kawai Al’ameen ya kad’a ya wuce d’akinsa shima ya watsa ruwa, koda yafito be koma d’akin nasu ba atunaninsa bari ya bata space. A parlour ya zauna yaci ragowar kajin. To twelve (12) ya lek’a d’akin nata yana sanye da ¾ wandon soldiers zalla, hakan ya sake fiddo da how muscular and built up his body is making him worth more looking. Kwance tana bacci ya tarar da ita tana sanye da wani pink sleeping dress me hannun spaghetti da ¾ wando. Kajin data ce bazata cin bama ta cinye tas harda fasa k’ashi. Murmushi me sake k’ayatasa ya saki sannan ya k’arisa d’akin tare da gyara mata kwanciya yaja comforter ya rufeta sannan ya kashe musu wutan d’akin ya hauro suka kwanta. Sam beyi niyyan mata wani abu ba a daren ranan saboda yasan koda had’a sama da k’asa zeyi ba basa had’in kai Zeezee zatayi ba she needs some space.

12:50am Zeezee ta farka gabad’aya takasa gane meke damunta, tunda tasan kanta bata ta6a jin abinda takeji ba yau, juye-juye tahau yi kan gadon duk anan Al’ameen bacci yake peacefully besan meke faruwa ba. “Wayyo Allah na! Mama me kika samin a maganin d’azu?” Sauk’a tayi daga kan gadon tana me cigaba da juye-juyen a k’asa wani irin sha’awa kawai take jiyowa ita kad’anta ta rasa dalili. K’ara ta saki sosai seda Al’ameen ya tashi ganinta kawai yayi se juye-juye take. A hanzarce ya nufi kanta tare da sa hannunsa akan bare back nata kasancewar sleeping dress natan show me your back ne, “My Princess are you okay? Meke damunki?” Da wuri taja jikinta don d’an ta6a tan da yayi ba k’aramin affecting nata yayi ba kawai jin wasu electric sparks suna bin jikinta ta tayi a yayinda degree na sha’awan nata ya sake k’aruwa.
“Wayyo Allah zan mutu Mama kin kasheni dan Allah karka sake ta6ani I can’t take it.”
“Mama kuma? Me ta miki?”
“Dan Allah kabarni in kanayi wa Allah karka sake ta6ani muryanka ma dad’a min abinda nakeji yake in kanayi wa Allah ka tashi ka fita kokuma kasa kaya.” So take ta miqe amman takasa se juyi take wajen, tuni Al’ameen yagano meke faruwa. “Tashi toh muje mu kwanta.”
“Wai ana dole ne? Wayyo Allah na! Dan Allah ka tashi kabarmin kaina, Mama kin kasheni yau! Nashiga uku!!” Murmushi kawai Al’ameen ke ba yadda beyi da ita ba ta tashi suje su kwanta tak’i haka ya koma ya kwanta yana kallonta. Juyi Zeezee ta cigaba dayi agun ganin abin bana sauk’i bane taja pillow ta danne kanta har anan bata barjin abinda takeji ba. Ga sauk’i nan kawai taje ta samu Al’ameen amman batajin zata iya basa kanta tayima Adeel alk’awarin budurcinta. Haka tayita wahalar da kanta a daren ranan da k’yar d’in k’yar takoma normal ta haura gado ta kwanta.

Da Asubah ya tashi yayi alwala sannan ya zauna gefen sleeping Zeezee yana k’arewa kyakkyawan fuskanta kallo then back to d’an mitsitsin bakinta me uban tsiwa. Kallonta kad’ai na sanya masa farin ciki baze iya kwatanta yadda yakeson Zeezee ba. “Zainab” yayi whispering name nata. “Zainab tashi muyi Sallah kinji? Zainab!” yayi tapping nata. A hankali ta bud’e idanunta tare da kallonsa sekuma ta juya mai baya. “Tashi muyi Sallah ko inyi nawa ni kad’ai?”
“Ban sani ba” ta amsa a takaice ganin batada niyyan tashi ya miqe ya hau yin Sallansa. Seda ya kusa idarwa ta tashi itama tayi alwala. Koda ta idar bata gaishesa ba ta koma gadon ta cigaba da bacci. Al’ameen kuwa na gama Azkhar nasa ya fita waje ya samu men nasa ya hau training nasu har safiya be koma bacci ba.

Amarya kuwa se 10am ta tashi, bayi ta fad’a tayi wanka tana zaune gaban mirror da towel zallah a jikinta tana shafa mai Al’ameen ya shigo ganin batada kaya yad’an tsaya gun tare da clearing throat nasa ko zata gyara. Aiko maras kunyan yi tayi kaman bata jisa ba ta cigaba da wangale santala-santalan cinyoyinta tana shafa mai. Cikin d’akin ya k’arisa tare da zama bakin gado yana kallonta a yayinda wutan so da sha’awanta ke running a veins and atteries nasa. Tana gama shafa man ta d’au inner wears nata tasa sannan kayanta ko kunyansa bataji. “good morning My Princess tunda bazaki gaisheni ba” yayi speaking up finally. Ko kallon direction nasa batayi ba tafice izuwa kitchen tana tunanin dame

34 / 98