YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   52 / 98

153K to 156K   out of 291.7K words

tashin hankali ya bi bayanta aman ta cigaba dayi a yayinda Zeezee ta tsaya tana kallonsu daga inda ta tsaya.
"Sannu Babe sannu kinji? How are you feeling?" Yayi maganan yana ja mata kujeran dining ta zauna har anan kallonsu Zeezee ke tasan sarai shigan ciki ne da Ruky cause exactly haka Fateeman Ya Ibraheem take time da take da ciki itama.
"Baby am feeling nauseatic."
"Sannu kinji tashi muje asibiti."
"No need" ta amsa a takaice.
"Why?" Ya tambaya a take. "You are sick."
"I think am pregnant saboda nayi missing period d'ina this month." Dum! Zuciyar Zeezee ya buga Allah sarki ita, daba don abinda Adeel ya mata ba da yanzu itama da 'yarta kokuwa d'anta yana ibe mata kewa, ace shekaranta d'aya da watanni aka da aure amman ko 6ari bata ta6a yiba se wacce dududu 3 months ne da aurenta har ta samu ciki, amman Allah ze saqa mata.

"Pregnant!" Yayi exclaiming "are you serious Babe?!" Gabad'aya ya kid'ime don dad'i tsugunawa yayi ya shiga kissing nata anan Zeezee ta yasar da towel d'in ta ruga a guje izuwa site nata ta baje kan gado ta shiga rusa kuka. A ba cikin ma ya ta qare da wulak'anci bale yanzu da Ruky ke d'auke da juna biyu? Tabbas tasan nata ya qare. Haka ta cigaba da kuka har seda ta jiyo qaran bud'uwa da ruhuwan gate tabbacin su Adeel sunfita asibiti kenan. Anan ta sake rushewa da wani kukan.
It didnt took them long suka dawo da wuri ta miqe ta shiga leqensu ta window sede wani tattalin dataga Adeel nayiwa Ruky wato tafiyan ma bazata yiba d'agata yayi chak har ciki nan fa kumburarrun idanunta suka shiga zubda sabon hawaye tana cikin yin kukan wayanta yahau ringing ko bata duba ba tasan Adeel ne ba tare da ta duba screen din ba tayi answering "gani ina zuwa" ta furta tare da katse wayar. Nan da nan ta wanke fuskarta ta fice, zube a parlour ta samesu se faman sannu Adeel keyiwa Ruky wanda take ta shagwaba.
"Ga Zeezee'n nan toh me kikeso?"
"Custard nakeso."
"Kinji Zeezee had'a mata custard me kyau anan yi sauri, our baby is craving" gabad'aya Zeezee ma hankalinta ba a gun yake ba tayi zurfi cikin tunani "dake fa nake Malama! Ko baqin ciki kike mana don mun samu qaruwa? So kike kowa ya zauna kaman ki ba cigaba?"
"A'a Allah raba lafiya Ruky" ta fad'a tana danne hawayenta.
"Ameen nagode kiyi sauri please." Nuni da kitchen d'in Adeel yayi mata nufin tayi sauri nan ta miqe in less than 15mins ta kawo wa Ruky Custard nata ta miqe zata tafi kenan Ruky tayi sauri taja Adeel ta rad'a masa abu a kunne.
"Tsaya Zeezee" chak ta tsaya "massage Ruky's legs for her suna mata tsami."
"Nikuma?" Ta tambaya suprisingly.
"Baki san mata masu ciki hakan na faruwa dasu bane? Koda shike ko 6ari baki ta6a ba bale ki sani."
"Naji ban ta6a yin kida 6ari ba amman suma ai se in cikin yayi girma ne. Amman nata ko 6ullo kai yayi ne?"
"Ja chan gefe da Allah! Ke mema kika sani game da mata masu d'auke da juna biyu? Ko 6ari baki ta6a ba don haka kimin shirru kiyi abinda na saki." Kai zallah ta kad'a sannan ta qarisa nan Ruky ta aza mata santala-santalan k'afafunta bisa cinyarta. D'ago kai Zeezee tayi ta kalleta sannan ta shiga massaging mata dagangan Ruky tasa ihu. "Arghhh!"
Nan Adeel dake gefensu yana latsan waya ya juyo "ya haka Zeezee?"
"Baby kace tamin a hankali."
"Da da k'arfi take miki? Kefa banison mugunta kina jina ko? Ba yadda za'ayi ke kin kasa d'aukan ciki wacce ta d'auka kuma kina yi mata mugunta tell her sorry."
"Ad-" ta gwada explaining kanta.
"I said tell her sorry!" ya katse ta angrily.
"Kiyi haquri" ta fad'a tears na forming a idonta seda Ruky ta soma gyangyad'i Adeel ya yarda Zeezee takoma site nata achan ta cigaba da kukan abin tausayi.

Hakanan tun daga ranan Adeel yake bawa Ruky extra ordinary kulawa, ciki sekace dashi aka fara a duniya kuma shine na qarshe. Kusan a kullum se sun fita shopping wa unborn nasu. A rana se Zeezee tayi girki kusan kala uku zuwa hud'u duk Ruky tace bataso tamkar baiwa haka Zeezee ta zame a gidan se ramewa take tana duhu. Yauma kaman kullum Adeel ya kirata bayan taje ta tarar da Ruky kwance bisa cinyan Adeel.
"Baby kikace me kikeso?"
"Miyan gauta." Ta ansa a kasalance.
"Kinji miyan gauta takeso, na siyo d'azu seki d'auka a fride ki mata da tuwon semolina ko?"
"Eh" ta gyad'a kai.
"Oya Zeezee tashi."
"Adeel mene kuma miyan gauta? Bansan shiba ban kuma iya ba ta za6i wani abin na daban."
"Shi baby'nmu yakeson ciki don haka shi zaki girka mata."
"Da ban iya bafa?"
"Seki koya a daren yau ko da yunwa kikeson Baby machine d'ina ta kwana?"
"Allah huci zuciyarka" tana kaiwa nan ta miqe ta ciro gautan daga fridge sannan ta nufi site nata, tunanin ya za'ayi ta girka ta shigayi chan idean ta kira Mama ya fad'o mata nan da nan tayi grabbing phone nata ta yi calling Mama.
"Hello Zeezee?"
"Na'am Mama ina yini?"
"Lafiya ya kike?"
"Lafiya qalau ya Baba?"
"Shima qalau."
"Toh Madallah Mama dama nace ko kinsan ya ake miyan gauta?"
"Miyan gauta kuma Zeezee? Meya kaiki?"
"Ermmm kawai inason cine. "
"A'a ke tuwon ma yaushe kike ci, gayamun gaskiya."
"Mama Adeel ne keson na girka wa matarsa kinsan tana d'auke da juna biyu."
"Tohhh kece cookursu kenan? Ko yarinyan tanada hankali ne?"
"Eh Mama-"
"A'a gayamun gaskiya" ta katse ta. Ai kasa magana tayi se hawaye da kuka kawai seda tayi tasamu tayi shiru sannan Mama ta tambayeta meke faruwa. Bata 6oye mata komi ba ta labarta mata komi. Sosai Mama taji tausayin 'yarta ina ma ace zata iya cirota daga cikin wannan hali da take ciki.
"Kina jina ba Zeezee? Bazaki girka ba ai don ya sameki a sadaqa doesn't mean a talauci ko wahala ya tsintoki da ze maidaki baiwa haka. Oh God! Duk fa kece Zeezee kikace ke bazaki ji maganan kowa ba se na wannan d'an iskan da besan darajarki ba, ga irinta ai yanzu."
"Mama wallahi I deeply regret every single action of mine back then ban ta6a sanin za6in iyaye is the best ba kuma iyaye nada haqqi akan 'ya'yansu haka ba se yanzu ku gafirceni Mama."
"Nikam na yafe miki Zainab Baban nakine har yanzu na gagara karkato da hankalinsa."
"Karki gaji dani don Allah Mama, daga Allah seke nakeda."
"Kin ta6a jin inda uwa ta gaji da 'ya'yanta ne? Kome kika min ina sonki Zainab saboda ni kad'ai nasan zafin haihuwarki."
"I love you so much Mama❤" ta fad'a tana kuka sosai.
"Kibar kukan haka kuma bazaki dafawa kowata shegiya ba abinci in bayi son ta kwana da yunwa ya je ya sai mata abincin mana."
"Mama dole na na girka mata shine kwanciyan hankali na."
"Kamar ya Zeezee?"
"Mama inbar girka ba duka na zeyi wallahi."
"Duka fa kikace? Wa iyya zubillah! Zana de? Abin nasa gaskiya ya soma wuce gona da iri Zeezee I cant take it anymore haifanki fa nayi ba akan bola na tsince kiba wallahi na gaji sede yin hakan ya zama sanadiyar rabuwana da Babanki amman gobe gobe zanzo gidan naku in d'aukeki kimin kwatance."
"A'a Mama please karkiyi haka, banason abinda ze shiga tsakaninki da Baba da hakan ya faru gomma ace har qarshen rayuwa na haka da Adeel zan qare yata galla min azaba, ba laifinki bane after all nine nan na jefa kaina cikin wannan yanayi da kaina don haka kibar damuwa kuma ai Allah baya d'aurawa bawansa jarabawan da baze iya d'auka ba."
"Hakane Zeezee amm-"
"Toh kinga Mama zan cigaba da haqura surely one day Allah ze yayemin wannan bala'i nide yanzu kawai ki bani ingredients da procedure karki damu."
"No way bazan bayar ba."
"Please Mama in babaka ba ze dakeni wallahi" don dukan kad'ai data ambata yasa Mama ta gayamata yadda ake yi. Godiya sosai tayi sannan ta shiga hura wuta, tana gamawa takai mata.

*^*^*^
Haka Zeezee ta cigaba da azabartuwa a gidan, na yau daban na gobe daban. A haka har cikin Ruky ya samu 5 months yasoma nunawa, nan fa iskanci da iyayi ya qaru. Bata zama a gidan seda vest yadda cikin ze sake nunowa gashi seta bari Zeezee na aiki seta zo tana ture-turen tsiya kokuwa ta soma fitowa da ledan gashi kokuwa tsire wanda she is sure Zeezee ta manta rabonta data d'ana nama a baki.

Yau ma as always Zeezee na cikin mopping parlour da wuraren 6:15pm na yamma Adeel da Ruky suka dawo daga kasuwa anje anyi shopping kayan baby kan ba gobe. A parlour suka dire kayakin ko sannu da aiki ba wanda yayiwa Zeezee cikinsu itako Allah-Allah take tagama ta fita. Bada jimawa ba Adeel yace ze fita, "ina zakaje Baby?" Ruky ta tambaya tana ninke kayakin baby'n nata.
"Zan anso abu ne I'll be right back."
"Toh shikenan kadawo ka sameni a site na Zeezee zanje na tayata hira."
"Is that necessary Babe? Ba gomma kin kwanta kin huta ba."
"Dont worry seka dawo, Baby and I love you so much."
"I love you both too" nan ya bata light peck sannan ya fice. Timing nasa tayi seda ta bari ya kusa dawowa sannan ta nufi site na Zeezee tayi sallama kaman dagaske. Nan ta shigo ta gaisheta and ba yabo ba fallasa Zeezee ta amsata "dama nace barinzo na gaisheki ina d'an zagaya cikin gida kinsan abinki da me juna biyu seda strolling in ba haka ba k'afafun se su kumbura."
"Hakane Allah raba lafiya" kadai Zeezee tace mata anan suka jiyo k'aran bud'uwan gate se shigowan motan Adeel seda Ruky ta tabbata yafito kuma sunyi dashi idan ya dawo yazo ya sameta anan, seta zaro wani jan bakin dake nan kaman jini ta goggoga a gefen bakinta tare da zare ribbon nata ta barbaza gashinta kan fuskarta alaman tasha wuya d'innan. Kafin Zeezee ta tambayeta yada haka har ta sauqa k'asa tare da wulla wa Zeezee wani d'an k'aramin wuqa da mamaki Zeezee ta cafke wuqan without knowing how, danko still takasa comprehending me Ruky ke shirin yi haka.
"Ruky lafiya dai ko? Wuqan name kuma?" Anan ne Adeel ke shigowa nan Ruky data goga rope k'asan idonta ta shiga ihu na sosai tana sumbatu "don Allah kiyi hak'uri Zeezee karki kasheni ki kashemin abinda ke ciki wayyo Adeel! Please come back zata kasheni." Dumbfounded Zeezee ta tsaya wajen tama kasa magana as Ruky bata isheta da kallo ba.
"Innalillahi! Kisa!" Exclaimed Adeel alokacin dayake tsaye tsakiyar parlour'n. "Meke faruwa? Me nake shirin gani haka?" Da gudu Ruky ta miqe ta fad'a jikinsa tana wani irin kuka fuskarta ya d'ago yaga duk alaman jini "metayi miki? Me kika mata nace!" Ya daka wa Zeezee tsawa wanda sanadin haka Ruky ta sake lumewa jikinsa don yadda ta firgita inaga wacce akayima tsawan Har anan Zeezee ta kasa magana sema kallon wuqan dake hannun tan take hawaye na forming rapidly a idonta sbin taysayi. "Dake nake magana kashe min mata kikesonyi saboda ke kin kasa d'aukan abinda ke jikinta? Jahilar ina ce ke? Iyye?!" Cikin sautin kuka Ruky ta soma magana, "wallahi ni zamana ya qare a gidan nan ka za6i niko ita kawai a banza bazan zauna tazo ta kasheni ba cikin dare tunda gashi da rana ma ta kasa hak'ura."
"Kaman ya na za6a Babe? Mezan da wacce bata haihuwa?"
"Ni wallahi ka za6a kafin nan zan koma gidan Babana" wani haushin Zeezeen da banda raba ido tana hawaye ba abinda take har yanzu yake a fusace ya nufi inda take tare da damqo ta da wuyan hijabinta, mari lafiyayye ya zuba mata a kumatu nan fa Ruky tahau murmusawa finally plan nata has worked out seta raba auren su a yau. Kumatun nata ta riqe da d'ayan hannunta hawaye nabin k'uncinta.

"Bakida hankali ne? Dake nake magana!" Adeel yayi maganan yana jijjiga Zeezeen da har anan ta kasa cewa komi, banda kukan da take theres nothing more.
"Bazaki amsani ba?" Y sake kifa mata wani. Belt nasa ya zare a gun ya shiga nad'a mata na jaki se kuka take ba sauti. Duk anan kallonsu munafukar take tana jin dad'i seda taga Adeel na neman illata Zeezee sannan kaman dagaske ta shiga tajasa baya. Se huci yake "matsa min Ruky sena fara kaita lahira kafin nan ta kaiki, muguwa azzalima kawai." Jina-jina yayi wa Zeezee. Hawaye kawai take har anan ta kasa cewa komi, nishinta ma ba fita yake sosai ba gakuma jinin dake yoyo ta hancinta dakuma baki. Kaca-kaca Adeel yayi mata.

"Maza tashi kibarmin gidana annamimiya me kisan kai kawai tashi kibar min gida na sawwaqe miki, na sakeki saki d'aya, biyu ki tashi ki fita nace! banason sake ganin fuskarki koda a mafarkine. Kuma kikayi wasa har kotu sena kaiki kowa yasan me kisan kai ce ke. Na rasa ya iyayenki suka girmar dake, banda rashin hankali ga mugun hali again" Tana kuka sosai ta furta Alhamdulillah a ranta dukda de bata san ina zata jeba a daren nan amman tasan koma ina ne ze fiye mata gidan Adeel. Miqewa takesonyi amman don yadda jikinta yayi tsami ta kasa "bazaki tashi bane sena gama hallakaki komeh?"
"Baby please let her be she have had enough mu tafi site namu zata tafi ai ka riga ka sawwaqe mata" tayi maganan wane tana tausayawa Zeezee but deep inside ba wanda yakaita murnan wannan saki. Da k'yar ta samu taja Adeel suka fice nan ma se hak'uri yake bata tabari ya goge mata ciwon nata ma taqi sanin na qarya ne karta tozarta kanta.

Zeezee kuwa seda tayi dagaske sannan ta samu ta miqe da k'yar ko wanke fuskarta batayi ba tashiga had'a akwatunanta tana kuka na haqiqa. gabad'aya jikinta ya tashi yayi pink. Nan da nan ta shirya kayakinta kap ba abinda ta bari har anan kuma bata bar kukan da take ba, tambayan kanta ina zata je take. Ma wacce erin rayuwa ta jefa kanta at her tender age ace auranta har biyu duk sun mutu? Wani irin bala'i ne haka? A yau da zata tarar da watan da take neman bijire wa iyayenta data zauna ta bata labarinta don rayuwar ta rayuwa ce dake cike da abin koyo da darusa. Bijire wa umarnin iyaye ba abu bane nayi, tabbas ba wanda zeji labarinta yakuma ce still ze bijirewa umarnin iyayensa. A yau ace ga mahaukaci Baba ze miqa ta gashi as sadaqa wallahi bazata k'i ba ta koyi lesson a rayuwarta daman we are learn from our mistakes. Allah rufa mana asiri Ameen.

*MIEMIEBEE. Team #YGC!*
beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
Page 48
FEBRUARY , 2017




Jikinta ba k'wari yana mata ciwo sosai tasamu da k'yar taja luggages nata ta fita dasu tasa a booth. Hamdala ta saki ganin da mai a ciki, ba tare da b'ata lokaci ba tayi shoving kanta cikin motar ta kunna, koda su Adeel suka jiyo qaran motarta basuyi ta kanta ba. Gate na recognising motarta ya bud'u mata ta fice sede kash bata iya tuk'in dare ba bayan nan kuma bata san ina zata dosa ba gidansu Lubiee ne? Gaskiya ba fasali koda Baba baze barta ta kwana mai a gida ba theres no place like home ya kamata iyayenta ne su soma sanin wani hali take ciki, bazata sake tafka sakarcin da tayi da a baya ba, don haka gidan zata wuce sede bata da courage. Parking tayi gaba da layin gidansu kad'an ta shiga rusa kuka sosai, tissue tajawo tare da kunna wutar motar nata ta shiga share jinin dake fuskanta inda Adeel yayi mata jina-jina sede don zafi ta kasa gogewa don haka ta yasar ta kunna motar ta shiga tuqi. Unguwansu dutsan tanshi ta nufa cikin ikon Allah tana driving a hankali har ta isa gida alokacin ana neman wuraren 7:12pm gari be gama yin duhu shar ba. Sam ta kasa fitowa daga motan da k'yar tayi gathering courage ta shiga ciki tana rik'e da medium sized akwatinta. Mama ta tarar a tsakar gida tana zaune bisa sallaya da alama yanzu take idar da Sallah. "Assalamu Alaikum" Zeezee tayi sallamar tsoro na building acikin muryarta.
"Wa'alaikumus salam" Mama ta amsa cike da zumud'i jin muryan Zeezee. To her suprise ta ganta riqe da akwati kobata tambaya ba tasan korota Adeel yayi ga kuma yadda fuskanta yake duk jini tagun bakinta.
"Subhanallahi!" Tayi maganan tana dosan gaban Zeezee, kuka kawai Zeezee tasa tare da fad'awa jikin Mama tana kuka me tsuma zuciya, hugging nata Mama tayi tana bubbuga bayanta.
"Ya isa kiyi haquri bar kukan."
"Mama ya sakeni kafin nan seda yamin d'ankaren duka."
"Kiyi haquri Zeezee in shaa Allahu kin rabu dashi kenan har abada wuyarki ya k'are ya isa kukan." Janta Mama tayi suka zauna kan darduma, "gayamin meya faru." Tana kuka tana bawa Mama labarin k'azafin da Ruky Mama tayi mata da kuma yadda Adeel na zuwa ba tare da ya bata chance tayi explaining kanta ba ya rufeta da duka. Sosai Mama ta tausayawa 'yarta. Suna zaune a wajen Mama na ta kan bata haquri

52 / 98