YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   72 / 98

213K to 216K   out of 291.7K words

wulla mata "gashi, se munyi yawa toh, I love you make sure you take care of yourself kinji? You are free to go anywhere you want na baki izini saidai don't stay late at night, okay?" Yana kaiwa nan ya sauk'e hannunta dake cikin nasa a hankali sannan ya juya, be kaiga fara tafiya ba Zeezee da hawaye ya cike dam a idonta ta kama hannunsa tare da juyo dashi.

Lips nasu kawai tayi crashing akan na juna ta shiga kissing nasa with all that she got not minding a sh*t. Hannayenta ta zagaye a wuyansa, kissing him the more a yayinda shi kuma a hankali ya zagaye hannayensa a tiny waist nata tare da bending height nasa kad'an giving her more access. Moving in sync with each of her move yake, he didn't make any move rather following nata kawai yake. Sun d'au tsawon lokaci a haka sannan a hankali Zeezee ta sake shi tare da hugging nasa gam-gam wane za'a k'watan mata shi. "I love you more My Husband, you are the most sweetest thing that has ever happened to me. Allah ya kare min kai ya kaika ya kuma sake dawo min da kai lafiya, safe and sound. Allah ya raba ka da dukkan wani sharri da masu sharri, may you live long and prosper, your Wife and also your Princess loves you way much." Hugging nata back yayi yana me sake jin sonta na shigansa, "ameen My Princess thank you so much." A hankali ta raba hug d'in sede har yanzu bata sake kallon cikin idonsa ba, ita kanta bata d'au zata iya kissing nasa as how she did ba, atleast kissing him was worth it, his lips are sweeter than that of Adeel's. "You should go kar kayi missing flight naka" tana fad'in haka ta juya mishi baya da wuri don bata son yaga kalan hawayen da takeyi, shima he can't take her crying anymore kuma yasan muddin ya cigaba da tsayuwa anan kukan ze cigaba da sata, "I love you Princess" yayi whispering mata sannan ya fice.

Wani kukan ma se da taji an tada engine na motan Al'ameen. Bajewa tayi kan gado tana kuka sosai wane zata cire ranta, never once have she ever imagined that she'll love Al'ameen like this. Sam ta kasa dena kukan, drawer'n gefenta tasa hannu ta zaro wedding album nasu nan ta bud'e ta shiga viewing tana me sake wani sabon kukan, a haka ne har bacci 6arawo ya saceta. Se kusan after 2pm ta tashi tayi alwala tayi Sallah ta kuma ci abinci. Wayarta ta d'aga don kiran Al'ameen inda ta tarar da two missed calls nasa, take tayi calling back wanda shima se a karo na biyu ya d'aga kasancewar bai kusa.
"My Princess" ya fad'a cike da k'auna.
"Na'am My Soldier" se kawai memory'n how tayi kissing nasa ya soma dancing a kanta, kissing him was the best feeling ever.
"Nad'au kinyi fushi dani ne ai."
"Ai baka laifi bale nayi fushi da kai Sweetheart, how was your trip?"
"Alhamdulillah kin bar kukan yanzu ko?"
"Nabari but I'm missing you already."
"I know and me either, kinci abinci?"
"Eh kai fah?"
"Also, meh kikeyi yanzu?"
"Babu, yanzu na idar da Sallah."
"Princess se pass 2 kikeyin Sallah, why?"
"Ba dagangan bane I slept over shiyasa bazan sake wasa da Sallah ba."
"Yauwa Princess, I'll be heading to a meeting yanzu, take care okay? I love you."
"I love you more." Kiss ta mai blowing a wayan "muahh." Yana murmushi sosai yace, "thank you" tare da katsewa. Through out a gida Zeezee ta yini, waya da Lubiee kawai suka tayi kafin ta kwanta around 10pm ta gwada layin Al'ameen inda ta mai har two missed calls be d'aga ba kasancewar kansa yayi zafi da aiki. Taso jin muryansa kafin ta kwanta amman hakan be yuwu ba don haka ta mai sending message as follows,
_My Handsome Soldier, just called to check up on you before going to bed, my bed is empty without you. Your Princess miss you badly, take care I love you._ takai 10mins rik'e da wayan tana jiran reply nasa amman shiru don haka kawai ta kashe wuta ta kwanta.
Ba Al'ameen ya sake sa wayansa a ido ba se 12am dayazo kwanciya missed calls nata da text mssg ya tarar, har ya shiga dialing numbanta amma ganin pass 12 na dare kawai ya katse yace ze bari se gobe kar yayi interfering wa baccinta. Da Asubah bim ake sanar dashi zasu koma Abuja, tafiya ba shiri gabad'aya ya mantar dashi da kiran Zeezee daya keson yi, itako batayi zuciya ba dukda rashin calling nata back da Al'ameen beyi ba ta sake yi mai wasu two missed calls d'in yau da safe had'e da good morning text message. Aiki ne sosai ya rik'e Al'ameen se a daren ranan ya samu time na kansa, baccin bala'i yake ji amman yasan he needs to hear from his Princess ya take. Kiranta yayi har kusan 3 missed calls amman tak'i d'auka by now tayi zuciya itama.

Facetime Video call ya shiga mata wanda shima se kusan a karo na uku ta d'aga, nan ma k'eyarta ta juya mishi wai baze kalli face nata ba tunda yake shareta haka.
"Haba Princess turn mana."
"O'o" tace still backing him, "missed calls nawa na maka se yanzu kaga daman kira na, kasan yadda hankali na ya tashi kuwa?"
"Princess am sorry give your Soldier a chance to explain kinji?" Nanma kafad'a ta buga "please Princess I want to see that beautiful face" yayi maganan tamkar zeyi kuka jin haka ta juyo da wuri, anan ya samu daman kallonta shima, fuskarta na d'auke da light makeup "wow! You are looking spectacular, I'm missing you Princess."
"Nasan nice kawai ke missing naka, kaida tunda ka tafi sau d'aya ka kirani."
"Princess kema kinsan I won't do that on purpose." Explaining komi dallah dallah yayi mata wanda ta fahimce sa sosai itama ta kuma basa hak'uri game da saurin fushin da tayi. Lovey-dovey hira suka ta sha seda taga Al'ameen na gyan-gyad'i sannan ta barsa ya kwanta. Kaman yadda ta saba tun tafiyarsa, yau ma ta d'auko shirt nasa ta sak'ala a hancinta tana shaqan daddad'an turaren jikinsa har tayi bacci.

Haka kuma rayuwarsu ta cigaba da kasancewa anytime Al'ameen is less busy ze kira Zeezee ko yayi mata video call suyita hira, a kullum dad'a son juna suke barin ma Zeezee da take ganin bazata iya rayuwa idan ba Al'ameen ba. Idan ta gaji da zaman gida se ta leqa gida chan gun Mama kokuwa gidansu Lubiee, last weekend ta d'auko su Ramlah suka taya ta yin weekends.
Yau ne cur two weeks da Al'ameen yace zeyi ya cika, tun jiya Zeezee ta kasa samun sukuni she can't wait for today, da safe yau ta kirasa bayan su gaisa sun gama gaya ma juna how much they miss each other take tunasar dashi batun yau fa yace ze dawo. Anzo gurin yace a ransa domin yasan dawowansa wannan satin ma baze yuwu ba balle wai yau, shine kaman babba yanzu manya biyu zuwa ukun da suke gabansa duk an sauk'e musu aiki shi ke komi, its damn hectic.
"Hello Sweetheart kayi shiru fah."
"Princess." Daga yadda ya kira sunanta ta gane he can't make it.
"Princess I'm so sorry." Kuka kawai yaji tasa ta cikin wayar, "Ya Salam! Princess please cut it out, kukan me kuma kike? Ya isa please, I'm sorry I can't make it this week kiyi hak'uri kinji? Aiki ne yamin yawa."
"Its okay" kad'ai tace masa sounding disappointed sarai yasan its not okay kawai ta fad'a ne.
"I know its not kiyi hak'uri kinji? I miss you also."
"Shikenan."
"Princess you are still mad, I can sense it."
"Am not" ta k'arya tasa.
"Tell me you love me if you are not toh." Shiru tayi danko she is really mad d'in, ta gama sa rai yau ze dawo kuma yace aiki ya rik'e shi? Bata so haka ba. Hak'uri yata bata da k'yar ya samu ta hak'ura suka ta6a hira kad'an sannan yayi excusing kansa. Mama Babba ta kira suka gaisa sannan Hjy Sadeeyah.

Sati uku Zeezee ta kwashe bata sa Al'ameen nata a ido ba in bade Video call sukayi ba, she miss him so much. A ranan daya kamata ya shigon ma be samu dama ba, kuka Zeezee tayita mar da suke Video call bayan daya sanar da ita cewa he can't make it ranan. Ba irin hak'urin da be bata ba amman tak'i hak'ura haka tayi mai fushi bata sake kiransa ba.
Hakan ba k'aramin damun Al'ameen yake ba, squeezing time nasa yayi sosai ya samu ya zak'ulo hutun sati d'aya zuwa biyu haka wanda yak'i sanar da Zeezee yana son suprising nata. Ko ya kirata yanzu bata zagewa tayi mai hira as before shiko bai gajiya da bata hak'uri, se daya k'ara three more days akan actual date daya kamata ya dawo sannan ya samu ya kammala abubuwan da yake gabansa. Zuwan bazata yayi mata ko kad'an be nuna mata a yau ze shigo gari ba.

Tun tashiwar Zeezee yau tayi wanka ta gama ayyukanta ta kwanta a parlour tana kallo, chan da kallon ya isheta tayi tunanin zuwa gidansu Lubiee. Tsaf ta shirya ta fice, da misalin k'arfe uku Al'ameen ya shigo gari, 3:30pm dot ya masa a gida, ciki Saje ya shiga masa da akwatinsa. Ganin ba motan Zeezee Al'ameen ya tambayi me gadi inda yake sanar dashi just now ta fita gidan k'awarta Lubiee amman tace she won't take long. Kai yamai nodding sannan ya shigo ciki inda ya tarar da ko ina tsaf ba dotti ga kuma k'amshin turaren wuta, kayan jikinsa ya rage ya watsa ruwa ya fito parlour yayi zamansa. Around 4:30pm Zeezee ta dawo gida inda tayi parking daga waje-wajen parking lot shikuma driver can cikin garriage yakai motan Al'ameen hakan yasa Zeezee bata gani ba. All exhausted ta bud'e k'ofa ta shiga ta sake miyarwa, mutumin data gani zaune akan kujera a gabanta ne ya mugun bata mamaki tare da jefata cikin wani irin farin ciki.
"Ya Al'ameen! My Soldier!" Tayi exclaiming sunansa unbelievably. Miqewa yayi a nitse yana sanye da vest da free sized black sports trousers. Hannunsa ya bud'e mata "My Princess" ya kirata cikin zazzak'ar muryansa. Yasar da handbag natan tayi ta ruga a guje taje tayi hugging nasa.

*MIEMIEBEE. Team #YGC!πŸŽ€*
Beeenovels.blogspot.com
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€ πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
πŸŽ€β£πŸŽ€
❣❣
β€’Β°β€’β˜…β€’Β°β€’ β€’Β°β€’β˜…β€’Β°β€’
Β°β€’ β€’Β° Β°β€’ β€’Β°
Β°β€’Β° Β°β€’Β°
*β€˜YAR GATA CE!*πŸ‘ΈπŸ»
β€’Β°β€’β˜…β€’Β°β€’
Β°β€’ β€’Β°
Β°β€’Β°
*_written by miemiebeeπŸ‘„_*

*March, 2017*
6⃣5⃣

_Here's to third page of dedication My Special Star ⭐ AUNTY SIS, my love for you is like tears from the sky thanks for everything._

Washegari bayan sallan Azahar Lovebirds d'in suna zaune a parlour suna shak'atawa. Zeezee ta kwantar da kanta bisa cinyan Al'ameen suna kallon sports. Chan ta juyo tana kallonsa, "Princess wani abu ne?" Ya tambayeta.
"Ya Al'ameen dagaske yanzu this week zaka koma?"
"Princess haven't we talked about this? Kiyi hak'uri nima fa ba son tafiyan nan nake ba."
"Toh ka fasa mana."
"Its not possible they need me."
"And I need you also."
"Princess am here for you ain't I?"
"For the time being ba, wai ma aurenka suke ne da zamu na sharing time naka. Ni wallahi banaso, you are mine alone."
"Princess who says am not yours? Am yours alone Kiyi hak'uri kinji? I won't take long zan dawo."
"Bawani nasan ka tafi sena sake ganinka ne" tana kaiwa nan ta fice zuwa d'akinsu. Kuka ta shiga yi a rayuwa bata son abinda ze nisantar da ita daga Al'ameen nata. Tana cikin rera kukan taji hannunsa akan bayanta, ignoring nasa tayi sema dad'a k'arfin kukan nata da tayi.

"Princess why are you punishing me like this? Yanzu da gan-gan kike wannan kukan ko sanin banaso." Banza dashi tayi se kukan take. Zagayowa yayi ta gaban ta da wuri ta gwada juyawa wanda tuni Al'ameen ya rik'o face nata. A hankali ya d'agata tare da zaunar da ita, "I'm sorry kinji? Nasan kina hak'uri but ki k'ara, its never my wish to leave you all by yourself." Hawayenta ya share mata da hannunsa, hugging nasa kawai tayi "not a tear again please Princess." Da k'yar ta danne kukan sannan ta d'ago daga jikinsa tana kallonsa. Kallo d'aya ya mata ya gano tana buk'atar mijinta ne, shikuwa duk abinda take so shi zeyi mata. Ba k'aramin dad'i Zeezee ta jiyo ba ganin yau bata nemi Al'ameen ba amman ya biya mata buk'atar ta.

***
Da La'asr bayan sun idar da Sallah Zeezee taje ta samu Al'ameen dake miqe kan gado ta kwanta a gefensa, "Sweetheart?"
"Yes Princess."
"Am bored mu d'an fita please, tunda kazo ba inda muka je."
"Ina kikeson muje?"
"Ko ina ni ka kaini." Matso da ita jikinsa yayi "bari zuwa 5 haka yanzu mu d'an huta kinji?" Kai ta gyad'a mai a hankali sannan ta aza kanta bisa k'irjinsa "I love you Ya Al'ameen, you are My Everything."
"As you are to me also Princess lets get some nap." Daga nan duk sukayi shiru inda a hankali bacci yayi gaba dasu. 5:20pm Al'ameen ya tashi, a hankali ya raba jikin Zeezee daga nasa sannan ya fad'a bathroom yayi wanka ya shirya sannan itama ya tada ita. Cikin k'ank'anin lokaci duk suka shirya sunzo fita Zeezee ta kalli Al'ameen a marainace.

"What is it Princess?"
"My Soldier kullum ne bodyguards nakan nan se sun raka ka duk inda zaka?"
"Why? What is it?"
"I want us to go out just the two of us, be the one to drive us."
"Is that what you want?"
"Yes Sweetheart."
"Toh chill, your wish is my absolute command. Ahmad and co, ku koma posts naku I'll be the one to drive today."
"With all due respect Sir we are being assigned to guard you anywhere you go." Ahmad yayi explaining.
"And my wife says no, she wants me to drive her today, any question?"
"No Sir" cewar Sadeeq a tare sukayi saluting nasa suka ja baya. Dad'i sosai Zeezee taji ganin yadda da zaran tacewa Al'ameen ga abinda take so yake kwatanta yi mata.
"I love you Sweetheart" ta fad'a tare da pecking nasa a cheeks nasa, murmushi ya mata sannan da kansa ya bud'e mata motar ta shiga "thank you My Soldier."
"You're most welcome Princess."
Su biyu abinsu suka fita yau ya kaita shopping daga chan suka wuce Ice Cream shop ya saya mata sannan suka dawo gida.

A daren ranan da Al'ameen ze koma Abj Zeezee ta shirya masa akwatinsa tsaf sede komi sime-sime takeyi, don bata son ya tafi ji take as if tayi faking rashin lafiya yace ya fasa tafiyan. Daren ranan Al'ameen keta shisshigewa Zeezee itako se basar dashi take ta na nuna mai bata so badan komi ba kuwa don yasan she is not happy ze tafi ya barta gobe ne. Shiko yasan halinta sarai bayan tafiyansa tana iya kiransa ma tace koda ze tafi be bata hak'k'inta ba yasa yak'i hak'ura yata binta har seda yayi turning nata on daman yasan she can't ignore him. Sosai ya gamsar da ita daren ranan making he forget all of her problems.

Da Asubah yau tare ma sukayi wankan sannan sukayi Sallah, Zeezee bata koma bacci ba kasancewar flight na Al'ameen 8am ne. Chores nata ta gama ta yi musu breakfast sannan taje ta tada Al'ameen yayi wanka. Kallonta yake tayi tun da suka idar da Sallah yau take ta faman had'a mishi rai. She couldn't hold her tears back anymore a lokacin da Saje yazo ya fita da akwatin Al'ameen. Juyawa tayi da suri zata wuce d'aki inda ya rik'e hannunta restraining her. "Princess in duk wani tafiya na zakina kuka haka ya kikeson ina ji a jikina? Gani nake like ni ke saki kukan." Ya fad'a cikin zazzak'ar muryansa a hankali.
"Ba kai bane Ya Al'ameen just go."
"I can't leave you

72 / 98