YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   38 / 98

111K to 114K   out of 291.7K words

k’are breakfast ta bar mai wajen. Tsaraban su Mama ta tattara ta fito “toh ni na fita sauran kace ban tambayeka izini ba.” Bece mata komi ba ta fice achan gida ta rabawa su Omar tsarabansu, sosai Baba yaji dad’i se albarka yake ta sa mata haka Mama ma. Bayan ya kira Maj-Gen. Ya tambayesa izini kan ze iya miyar wa Zeezee da motanta, Maj-Gen yace ba damuwa Baba yad’au key’n motar ta ya bata bayan nasihan dayayi ta mata. Ita de Zeezee dad’i kasheta.

Suna zaune a d’akinta ita da Mama, Mama ta tambayeta “mijinki fah? Me kika kawo masa?”
“Da har da shine a tsaraban Mama?”
“Kaji ‘ya! Kar kisa na zageki Allah, ya biya miki kud’in Hajj gabad’aya amman kice baki kawo masa komi ba? Haba Zainab mesa kike hakane? Wannan rashin hakali dame yayi kama?”
“Nikam gaskiya hankalina beban haka ba.”
“Toh kina jina ba? Kina komawa gida ki d’au agogo da darduman da kikace zaki bawa Ya Ibraheem ki bawa Maj-Gen kinji ko bakiji ba?”
“Naji” tayi murmuring.
“Bayan nan zan d’au d’aya daga jallabiyan Babanku ki had’a duka ki kai masa sannan kuma ki basa hak’uri, ke ashe rashin hankalin kin har ya kaiga haka? Toh Allah shiryeki Zainab don nabar zaginki da yi maki baki yanzu saboda bashida fa’ida addu’a kad’ai zan miki Allah ya shiryeki.”
“Ameen ,harda jallabiyan Baba? Wallahi masu tsada ne kuma wa Baba na siyo wa.” Bige bakinta tayi “ungo naki nan da masu tsadan.”

****
Tuni Zeezee ta tura driver’nta gida. Gidansu Lubiee ta wuce da motarta sannan lastly gidan Mariam daga chan se gidanta. A parlour ta tsinci Al’ameen data shigo sannu da zuwa yayi mata sannan ta amsa sama-sama ta wuce ciki. After a while ta fito da tsaraban dole da Mama tace seta basa, a gefensa ta ajiye “gashi wai inji Mama na baka.”
“Name fah?”
“Tsaraba daga Makkah.”
“Mama ne tace kibani?”
“Eh ko baka so ne?”
“D’auki abinki My Princess karki damu nasan bawani kikayi niyyan kawowa ba, tattara kinji?”
“Aww wai bakaso? Aikuwa tafi nono fari wallahi daman agogon Ya Ibraheem ne kayan kuma na Baba, karka kar6an.” Binta yayi da kallo seda ta 6ace sannan ya kad’a kai yacigaba da kallon sports nasa.

*© MIEMIEBEE Team #‘YGC!*
www.beeeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*

*January, 2017*
3⃣6⃣
_Just to let you know👌🏿 Masu karatu wai shin kun d’au ni kaina dad’i rashin kunyan da Zeezee keyima Al’ameen d’inmu yakemin neh? Kusani Mahak’urci Mawadaci, kuma me hak’uri shi kan dafa dutse yasha romo. Ita kuma Zeezee acewarku haka zan barta ne taci bulus bayan dukkanin aikin haramun datake aikatawa? Ofcourse no dole zata gir6e abinda ta shuk’a wataran. Duk wanda yayi ba dai-dai ba dole zega consequences so nomore bina private ana cemin abinda Zeezee keyiwa Al’ameen yayi yawa I know right what am doing ™YGC!💞_
_Ahh! Almost forgotten this page is honoured to *D Queen, Humairah,* and *Ummi Ayshatu* #OneLove💞_



Few days later yar Maj-Gen. wato Hajiya Sadeeyah ta mai waya kan zata zo nan Bauchi bikin ‘yar k’awarta zata kuma sauk’a a gidansa. Bayan sun k’are wayan yaje ya samu Zeezee mik’e kan gado tana chatting da Adeel tunda ba halin yin waya Maj-Gen. na gida. “My Princess” banza dashi tayi se a karo na biyu ta amsa “menayi kuma yanzu?”
“Haba Princess give me a break mana ni bansan mena miki ba kullum kike cikin 6atamin rai, in wani abun na miki lemmi know sena gyara ko ke marital life namu na miki dad’i? Kullum babu jituwa a tsakanin mu? Its hightime ki gyara ko ba haka ba?”
“In gyara? Me zan gyara? Kai babba bakace zaka daidaita komi ba seni zaka wani cemin na gyara.”
“Me zanyi toh Princess? Duk yadda nasan zanbi dan daidaita tsakaninmu nayi kink’i bada had’in kai.”
“Lallai kuwa, ka kama ka barni da outdated mota kam ai dole kace kabi anyway you know how, ni kaga ba dogon surutu nakeson yi ba, uban nawa in Allah ya sake hore mai ze canza min motar.”
“So kike a canza miki mota Princess?”
“Eh mana waye bayison sabon abu?”
“Shine kad’ai dalilin dayasa kike duk abubuwan da kike, akan mota ne kad’ai?”
“Kafa dena cewa kad’an nan Malam Soja tunda ka kasa canza min.”

Yana murmushi yace, “toh ai baki ta6a cemin na canza miki mota ba Princess.”
“Komi ne sena gaya maka? Hankali bayi gayawa mutum whats right ne?”
“Yana yi Princess toh am sorry it never blinked into my mind, za’a canza miki mota inhar shi kikeso anything for My Princess.”
“Wani iri zaka sai min toh?” Tayi maganan finally tana murmushi.
“Duk kalan wanda Princess take so za’a sai mata.”
“Dagaske Ya Al’ameen?”
“Sosai ma Princess, wani iri kikeso?”
“Kalan Ford Jeep naka 2016 d’innan nakeso.”
“Irin nawa?!” Yayi exclaiming.
“Me wani kake zaro ido ba zaka iya sai min bane? Kokuwa kaima kana sahun mazajen da suke cewa matansu basu hawa mota iri d’aya da nasu?”
“Ko d’aya Princes naga kaman wancan ya miki girma da yawa ba gara irin simple cars haka ba, inaga jeep nan ya mik’i kato kona miji ma ya ake ganinsa ciki? But inhar jeep d’in kikeso why not try out prado ko LR-3?”
“Banaso in bazaka saimin kalan naka ba shikenan dama haka kake ba abinda ka ta6a min tunda ka auroni, agida ban ta6a neman abu gun Baba na rasa ba Allah ze sak’a min ai” se ta 6arke da kuka tana Allah zeyi mata sakayya. Kallon yarintan ta kawai Al’ameen yake yana murmushi, “toh ya isa haka Ford Jeep kikeso?” Kai tayi saurin gyad’awa tana hawayen har yanzu. “Toh stop crying zan sai miki.”
“Dagaske Ya Al’ameen? Irin nakan nan fa nakeso amman fararta banason bak’ar mota.”
“Ko pink kikeso za’a sai miki stop crying I don’t want you to think bana miki komai, I’ll use the last kobo I have to make you happy.”
“Yeyy!! Nagode toh se zuwa yaushe toh zaka siyamin d’in?”
“Nan bada jimawa ba Princess, I want a favor from you also kinji?”
“Ahap ai dama nasani ba tsakani da Allah kace zaka sai min motar ba, nasani zakace yau sena baka hak’k’in kane toh inhar haka ne ka riqe motar taka tunda kai bakada tausayi ‘yar ni d’innan zaka ce zaka sa a gaba seka k’wato abinda yana iya kaini lahira.”

“Ohh Zainab! Ashe haka masu sunan naku suke? Ki kwantar da hankalinki in hak’k’i na ne na jima da yafe miki sabida banason tsinuwan mala’iku akanki se rananda kika yarda tukuna, yanzu that aside gobe Hajiya Sadeeyah tace zata zo nan Bauchi bikin ‘yar friend nata.”
“Wata Hajiya Sadeeyah tukun? Sis naka babba?”
“Eh ita kuma na mata masauk’i anan-”
“Anan?” Tayi saurin katsesa “haba kaikuwa, mesa baka barta ta sauk’a a hotel ba.”
“Haba Princess wani irin magana kike? She is my blood sister fa, ke yanzu zakiso ace in Yasmeen namu zatazo Bauchi takama hotel ne?” Kai ta kad’a da nufin a’a “toh nima ai kinga be kamata nabar Hajiya Sadeeyah bako?”
“Eh be kamata ba kam amman kaga ai in Yasmeem ce zata sauk’a anan ba girkin da zan mata komi ita zata na yiwa kanta amman incase of Hjy Sadeeyah kuma kaga fa dole sena hura wuta kuma ni ban iya ba wallahi ba abinda na iya girkawa aside from indomie da chips se dama-dama suyan kaza.”
“Duk ba matsala neba wannan Princess abinda nakeso dake shine kawai ki ajiye wannan rashin kunya da yawon na kwana biyu har seta tafi kinji?”
“Haba! Haba! Daddy kayi adalci mana, shikenan don ita se a tauyemin hak’k’i? Rashin kunya kuma in zakamin abinda nakeso ka sakeni ba wanda ze ji kanmu.”
“Its a favor am asking yi hak’uri kinji? Ko bakiya son Ford Jeep naki ne?”
“Inaso amman de-” hannunsa ya aza bisa lips nata;
“Yi hak’uri just this once.” hannun nasa ta cire;
“Naji Allah sa kar wani abin ya taso toh don gaskiya da sakel.”
“Nagode kinji Princess? I love you so much.”
“Naji toh, excuse me.” Be sake ceda ita komi ba ya yai finding way nasa out.

****
A washegari Hjy Sadeeyah ta iso, a tare Zeezee da Al’ameen sukaje suka d’aukota daga airport. Se admiring nasu take, a rayuwa batada burin da yafi taga her only brother da matarsa, hakan yasa takeson Zeezee sosai. Tin a mota se yaba Zeezee take har suka iso gida. Bayan Zeezee takai mata akwatinta d’aki ta zarce ta had’a kan dining sekace ita tayi girkin. Bada jimawa Hjy Sadeeyah tafito suka ci lunch sannan Zeezee ta tattara wajen instead tayi wanke-wanke seta jibge kayan gu d’aya kawai abinta ta dawo ciki.
Ganin Al’ameen nacan parlour da sis nasa suna hira tasa lock a d’akinsu ta hau skyping Adeel.
“Very Own.”
“Yes Sweetest love howayou?”
“Am good and you?”
“Also, is it my eyes or kin k’ara weight ne?”
“K’iba? Well maybe.” tayi maganan tana checking kanta.
“Am jealous that soldier is finally making my woman happy tunda har take k’ara weight.”
“Oh common Very Own please don’t say that kaima kasan no one will make me happy than you will.”
“Hakane?”
“Yes Baby, ya Florida?”
“As it always is, party here party there.”
“Very Own nasan kana chan kanata shafa jikin sluts d’incan ko?”
“Toh kema ba kina chan ba kinayi da mijinki ba?”
“Wallahi thats not true ko ta6ani ban bari yayi.”
“LOL am kidding you ni naki ne ke kad’ai kinji?”
“Yauwa Very Own.”
“So har yanzu be sake kinba?”
“Am still working on it, mutumin ne bansan dame zanyi describing nasa ba, komin me nayi masa baya gani yace ze d’au mataki akai he keeps on ignoring me.”
“Meaning baze iya sakin kiba kenan bale mu kasance together?” Yayi maganan haushi yana building a voice nasa.
“No Very Own calm down ba haka bane, I will never rest until ya sakeni you have my solemn words.”
“Alright Babe I trust you amman fa kiyi a hankali banason naji shima ya ta6amin lafiyarki as Baba did kinsan soldiers d’innan.”
“Don’t worry wannan I don’t think ze iya d’aga hannu ya ta6ani.” Jin motsin mutum tayi sauri tace mai “am cutting off he is here.” Da sauri ta katse sede daga yadda take raba ido ana iya gano batada gaskiya.

“Princess me kike haka?”
“Mekaga? Babu ofcourse.”
“I thought I heard you on the phone with someone.”
“Toh shikenan yanzu ko waya ban isa inayi ba? Classmate d’ina ne ya kiran ko shima zaka hanani waya dashi ne?”
“Are you sure?”
“Yoh jimin mutum kanason kaji da wa nayi waya? Da sauarayi na Adeel ne, nifa tak’ura ne banso duk ladabin danayi wa Hjy Sadeeyah baka gani ba kanason 6atamin rai shikenan ka rik’e motarka na rik’e ladabi na aikin banza kawai” tana kaiwa nan ta bar masa d’akin. Binta kawai yayi da kallo.

****
Washegari da safe Zeezee ta tashi sid’ak-sid’ak tayi wanka ta shirya tsaf ko karyawa batai ba wai seta isa gidan su Lubiee tukunnah. Motarta ta ja ta fice yawon banzan data saba.

9:20am Al’ameen ya tashi yayi wanka ya shirya, d’akin Zeezee ya wuce kasancewar ranan a nasa ya kwana, dabe ganta ciki ba se yayi tunanin ko tana kitchen ne sede da yafito ya dudduba Zeezee was nowhere to be found. This is serious! Yaushe ta fitan?

Yana juyawa yaci karo da Hjy Sadeeyah, “little bro ina kwana?”
“Ina kwana Hjy har kin tashi ne?”
“Eh kasan zuwa anjima zan fita” tayi maganan tana bin kitchen d’in da kallo, gani tayi wanke-wanke kota ina kuda suna bi. “Maj-Gen!” Tayi exclaiming.
“Me wannan nake gani haka? Karka gayamin wanke-wanken jiya ne?”
“Erm..” Ya shiga kame-kame.
“I knew it all along, ko me kakeyi a kitchen d’in kuma yanzu? Ina fatan bawai wankewa zakayi bako?”
“Oh common Hjy! Nazo d’aukan abu ne.”
“D’aukan abu ko neman matarka? Karka damu naga ficewarta d’azu.” Hannunsa ta rik’o “zo nan” a parlour suka zauna “what is going on a gidanka Maj-Gen?”
“Seriously babu Hjy itama Zainab d’in biki suke dashi shiyasa tafita yau.”
“And you expect me to believe that? Yau ma ni kake yiwa k’arya Little Bro?”
“Ba haka bane Hjy please lets drop this topic.”
“What is going? Wahala Zainab take baka shine baka sanr dani ko Mama ba? Meye amfanin family toh?”
“Gosh! Hjy enough please ba haka bane.”
“Toh yaneh? Gashi nan its written all over your face da akwai matsala, nikuma ba haka nasanka ba, abu bai ta6a damunka inba wai yakai maqora ba. Waye ne? Zainab ce?”
“Hjy I don’t know either I just can’t get her. Inason Zainab you know that.”
“I know Little Bro fiye da tsammaninka so meke faruwa?”
“Tunda aka d’aura mana aure ta canza gabad’aya, she is not the Zainab I use to know, narasa dalilin dayasa take hakan bayan ban ta6a tauye nata hak’k’inta ba, duk wani abinda takeso shi nake mata na kaita Hajj yanzu haka tace tanason na sai mata irin Ford Jeep d’ina I agree zan saya mata but I don’t get anything good from her tun abun bayi damuna ya soma. Hjy akwai wani abinda nake lacking ne as a man? Ko kuwa akwai abinda mazaje keyima matansu ne don su sosu wanda ni bansani ba baniyi mata? Let me know please.” Ya k’are maganan abin tausayi.

“Is okay kaji? Ba abinda ka rasa as a man Maj-Gen sabida haka kuma ‘yar yarinya bazata tsaya tana baka wahala ba. Adalilin me? Allah dawo da ita gida I’ll confront her myself wannan ai bayi bane.”
“No please don’t let her be time heals, eventually zata gano kuskuren yin hakan wataran please karki mata magana kinji?”
“Kamar ya kar na mata magana Al’ameen? Yarinyan da ina iya yin jika da ita ne zakace kar na mata magana bayan tanayin ba dai-dai ba? Wallahi k’arya ne. Tasan ina nan zata kama ta fita ba tare da ta tanarda min breakfast ba? Haka akeyi?”
“Nasan tayi laifi am apologising on ber behalf kiyu hak’uri please but karki mata magana kinji Big Sis?”
“Al’ameen...”
“Please for me.”
“Toh shikenan but promise me kai zaka mata.”
“I do, zan mata in shaa Allah nagode.”
“Gaskiya amman inhar bata shiryu ta shiga hankalinta ba dole a raba auren nan don ina raye bazan bari wata tasawa Brother na hawan jini ba, I can’t take it.”
“Is okay ki shiga kiyi wanka bari na aika a siyo mana breakfast.”

****
Ba Zeezee ce ta dawo gida ba se bayan Maghrib a dai-dai bakin k’ofa ta kasa kunnenta sanadin jin muryan dake tashi a parlour da tayi.
“Allah ka barni da ita senayi mata magana wannan rashin hankali har ina? Ace yarinya ta fita tun safe har yanzu bata dawo ba kuma bawai ta tambayeka izini ba?” cewar Hjy Sadeeyah a fad’ace.
“Hjy I said enough let her be please.”
“Shegiya munafuka irin kune koda kunje Makkah baku ganin Ka’abah ina ruwanki da inda naje dakuma lokacin dawowa na gida mschww.” Zeezee tayi maganan a fusace a kuma cike da rashin kunya sannan ta bud’e k’ofar, tsaye ta tarar dasu. Ba tare da tace da ko d’ayansu uffan ba ta wuce ta nufi d’akinta binta kawai Hjy Sadeeyah tayi da kallo.
“Ahakan kake cewa kar na mata magana? Matsa min tunda kai dama haka Allah ya yika da shegen hak’uri, anason mutum me hak’uri amman ba irin naka ba.” Bin gefensa tayi yana binta a baya suka shiga d’akin Zeezee alokacin harta rage kayan jikinta ta ragar da vest da short zallah, koda taga Hjy Sadeeyah batayi niyan rufe jikinta ba wayar hannunta ta cigaba da latsawa.

“In shi mijin naki ya saba ganinki haka don ni aikuma seki rufe jikin naki ko ya?”

38 / 98