YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   25 / 98

72K to 75K   out of 291.7K words

_I’m sorry Sweetest Love for going wild mad at you yestarday, I hope you can find it somewhere in your precious heart to forgive me am sorry. ILY_ D’an murmushi ta saki sannan ta bud’e pack d’in, sabuwar rose gold iphone 7pro taga aciki kafin ta tambayesa nawaye ne yace, “naki ne Babe, I’m sorry accept my apologies.”
“Omg! Very Own! You’re the most sweetest thing that has ever happened to me thank you so much.”
“Your sim is ready, I love you.”
“I love you too” tayi hugging nasa. Bayan ta kunna wayan yace;
“Akwai wani d’an party’n da clique d’ina sukayi organising a Yankari I want you to be there” yayi maganan yana shafa hannunta.
“Har Yankari Very Own?”
“Nan da Yankarin ne har?” Yayi maganan a bit angry.
“I’m sorry please don’t be mad ba wai ina nufin bazan je bane, I mean kaga yanzu fa 4:30pm har yaushe zamuje Yankari in koma gida? Baba ya hanani staying late at night.”
“Shikenan ke baki kai ki kula da kanki ba? Such a Daddy’s girl.”
“Bawai haka bane Very Own understand mana.”
“Da fitowa fili kikayi kikace you don’t love me it would have been better.”
“Omg! Adeel” ta kama hannunsa da nata bibbiyu, “please kabar fad’in haka wallahi I love you morethan so much.”
“If you really do then do this for me Babe, be there I really want you to be there.”

“Very Own-” katse ta yayi;
“Zakije yes or no? Stop wasting my time.” Shiru tayi totally speechless “I guess the answer is no” yana kaiwa nan ya bud’e motar ya fice not minding ya rufe mata k’ofan. Bayansa tabi ta shiga k’wala mai kira amman kota kanta beyi ba. “Adeel please don’t go ka tsaya please...” yana kaiwa gun motansa ya shiga ya fice. Hawaye ta soma yi a wajen unstoppingly da k’yar ta k’arisa gun motarta ta share hawayenta sannan ta d’ago wayan ta shiga kiransa sede har 5 missed calls be d’auka ba. Hankalinta sam baya jikinta ta shiga driving, ikon Allah kad’ai ya kaita gida.
Tana isa tayi wulli da kanta kan gado ta cigaba da rusa kukan seda tayi me isarta ta mik’e ta watsa ruwa ta sake gwada layin Adeel har 2 missed calls be d’aga ba, texting nasa tayi _Very Own you don’t have to be mad anymore, your happiness means the world to me text me your location I’ll be there. ILY_

**
Yana a d’akinsa yana kan shirin zuwa Yankari message na Zeezee ya shigo, da kaman baze d’aga ba sekuma ya bud’e bayan ya gama karantawa ya murmusa sannan ya kirata take ta d’aga “hello Very Own I’m sorry dan Allah kayi hak’uri it won’t happen again.”
“Thats my lady I love you.” Sanyi sosai taji a ranta “I love you more so where will I meet you up?”
“Zanzo in d’aukeki.”
“Toh I’ll be waiting.”
“Aha and also kinsan how you’ll dress koh? Party-like”
“Yes Baby.”
“Yauwa Babe sena zo” yana kaiwa nan ya katse. Da sauri-sauri ya gama shiri itama haka. Crazy pencil jeans trousers nata tasha da wani top dake nan kaman vest saman sa had’e yake da sark’a dogo me fad’i black colour. Mininal makeup tayi applying tasa assesories nata sannan ta b’urma babban hijabi kai ta fito that was by 5:20pm kenan. “Ina kuma zakije?” Mama ta tambayeta.
“Kati zan siyo anan shago.”
“Toh Allah sa” batayi ta kanta ba ta fice a dai-dai wani shagon dake bakin corner ta tsaya ta kira Adeel in less than five (5) minutes ya k’ariso. Ba tare da b’ata lokaci ba ta shige ciki sede Ya Wakeel me shago yaga shigewarta cikin motar. Pecking nata yayi a kumatu sannan yace, “ya da hijabi kuma Babe?”
“Don’t worry” hijabin nata ta kwaye ta wurga back seat “thats my babe you are looking super sexy.”
“Thank you.” Motan ya ja suka hau tafiya ayayinda take d’aura kanta. Sun d’au tsawon lokaci kad’an suka isa Yankari inda duk sauran party rockers d’in suke.
“Mu fita koh?” Hannunsa ta rik’e “Very Own promise me I’ll be safe with you ba abinda ze sameni please” tayi pleading. Tausayi ta basa, hannun nasa ya cire daga nata sannan ya kwantar da ita ajikinsa “don’t worry Babe, you are safe with me nothing will happen to you. ”
“I trust you and love you.”
“I love you too lets go then.”

***
Loud music ke tashi wajen, gabad’aya ba wuta se turning club lights, maqale jikinta tayi ana Adeel duk tsoro takeji seyanzu takeji dama ta sani da bata biyosa ba, what if abu ya sameta yanzu? VIP table ya kaisu suka zauna sam tak’i sakesa, abinci akayi serving nasu taci tak’i gudun kar ansa abin bugarwa aciki taci ta bugu.
“Babe aiint you hungry?” Kai kawai ta kad’a masa “you don’t trust me?”
“I do, inda banyi trusting naka ba zan biyo ka nan ne?”
“Toh why won’t you eat?”
“Am not hungry” ta k’irk’iro murmushi.

_7:12PM_
Zeezee ta warware sosai har tayi new friends wasu ‘yan iska first class wajen, se rawa suke suna goga jikinsu dana maza. Wayanta dake pocket nata ne ya soma ringing tana kai dubanta taga Amiable Dad dum! Zuciyarta ta buga hannun Adeel taja zuwa waje “Very Own Baba na kira na me zanyi please?” Tayi stating all confused, wayar ya amsa a zatonta ma picking zeyi tayi saurin fad’in “no please karka d’aga.” Gani kawai tayi ya kashe wayan gabad’aya.
“Adeel Baba na ne fa yake kira, how could you?”
“Babe kin cika tsoro, let them be you are safe with me.”
“Kabani waya na!” Tayi maganan a tsawace, kallonta ya tsaya yi ransa na tafasa. Wayar ya wurga mata “mani kike d’agawa murya? Gashi kiyi duk abinda kikeso, bullshit kawai!” yana kaiwa nan yabar mata gun. Hawaye ta shiga yi ga wayan a hannunta ta kira Baba ta kasa gashi bata taho da motar taba bale ta koma gida, Adeel is her only way back home. Ita yanzu ba Baba ba bakuma Adeel ba, bazata iya yin 2-0 ba. Waje ta nema ta zauna tasha kukanta har seda ta godewa Allah sannan ta share hawayenta ta gyara makeup nata ta koma ciki in the midst of some bitches ta samu Adeel zaune se hira suke suna dariya. Wani irin wawan kishi taji ya rufeta tsam amman she can’t blame him ita ta jawo komi.

A nitse ta k’arisa wajen, koda ya ganta beyi ta kanta ba, gabansa ta nufa, “Adeel I’m sorry” tayi maganan a hankali, yi yayi kaman be ganta ba, “I said am sorry please” hannunsa ya mik’a mata sannan ta jasa zuwa wurin da akwai privacy. “Adeel am sorry please” sekuma ta rushe da kuka, kallonta ya tsaya yi daga bisani yayi hugging nata “Babe if you’ll do as I say bazamu na fad’a ba, kidena crossing d’ina.” Hugging nasa back tayi “I wont ever please kadena kula wancan hoes d’in.”
“If you’ll give me all of yourself and listen to me I won’t.”
“I’m all yours Adeel just promise me bazakamin abinda ze tab’amin pride (budurci) d’ina ba.”
“Never Babe, your pride belongs to me but only if mukayi aure so stop worrying yourself on that kinji?” Kai tayi nodding “I love you.” Hawayenta ya share mata suka koma ciki suka cigaba da partying.

_9:21PM Gidansu Zeezee_
Dawowan Baba gida kenan wannan shine fitansa na tara tun d’azu yake neman Zeezee. Duk inda yasan tana zuwa yaje ba Zeezee ba labarinta, har report yakai wa police hankalinsa ya matuk’ar tashi sosai, bashi kad’ai ba har Mama da Omar.
“Ina K’anwata ta shiga? Ina aka kaimin K’anwata? Ba halinta bane staying late at night, duk laifin kine Hafsah be kamata kibarta ta fita shagon ba, tunda Omar na gida mesa baki aikesa ya siya mata katin ba?”
“Kamar ya laifi na Alhj? Kasan de Zeezee ba magana na takeji ba koda nace mata kada tafitan eventually se tayi.”
“Toh baga irinta ba yanzu yarinya ta b’ata, wallahi duk abinda ya sami K’anwata kisani kece sanadi mschw!” Yana kaiwa nan yaja motansa ya sake fita for the 10th time yana zagaya unguwa yana tambayan mutane ko sunga Zeezee. Sede duk inda ya tambaya se suce mai sun ganta ne lokacinda take dawowa daga school. At last ya wuce shagon Ya Wakeel daya raina, aikuwa Ya Wakeel yace tabbas ya ganta tana shigan wani Mercedes-benz bak’a dawani saurayi ciki.
“Zeezeen! Kaga tana shiga cikin motan wani?!” Baba yayi maganan disbelievingly.
“Tabbas! Na ganta da idanu na Alhj.” kai Baba ya shiga kad’awa.
“Wallahi k’arya ne ban yarda Zeezee na zatayi wannan abu ba kai de kawai kace kana son yi mata sharri ne shikenan in bahaka ‘yar 16 years zakace tabi d’a na miji? To zuwa ina?! Wallahi k’arya ne ba kalan tarbiyyan dana bata ba kenan.”
“Shikenan Alhj amman nide kam naga Zeezee tana shiga motan wani.” Ko k’arisa sauraronsa Baba beyi ba yaja mota ya koma gida a fusace still not believing any of Ya Wakeel’s words sede his words kept on dancing in his head. “Ya Alhj? Any good news?” Banza da Mama yayi ya wuce d’aki, sam brain nasa yakasa comprehending abinda Ya Wakeel ya fad’a mai, what if its true? Kai yayi saurin kad’awa “noo it can’t be possible, sharri ne.”
“Sharri mawa Alhj?” Mama dake zaune a gefensa ta tambaya. “Dan Allah ka gayamun.”
“Hafsah wallahi sharri ne, Zeezee bata bi wani namiji ba sharri ne.” Zumbur Mama ta miqe tare da dafe k’irji, “Zeezee tabi wani na miji? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un nawa yak’are nashiga uku!”

For the 1000th time Baba ya sake gwada line na Zeezee switched off.
“Hafsah kin yarda Zeezee zatabi wani d’a na mijin waje? Kin yarda?”
“Alhj ba batun na yarda koko a’a bane fatan mu Allah yasa yadda ya d’auketa ya dawo mana da ita lafiya ba tare da yamata wani abun ba dan Ya Wakeel babban mutum ne bazeyi wa Zeezee sharri ba.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, mena ma Zeezee a rayuwa da zatayimin haka Hafsah? Yarinyan nan bata tab’a neman abu tarasa a k’ark’ashina ba, koda banida hali zan kwatanta, mesa zatayimin haka? Mesa zata nemi tozartani cikin jama’a?”
“Alhj yanzu duk ba wannan ba addu’a zamuyi Allah sa ta dawo gida lafiya. Dalilin dukannin wannan abubuwa kuwa shine ILLAN GATA daman ni seda na gaya, sam tarbiyyan daka d’aura Zeezee akai gurb’arcacciya ne kaima kasani amman kak’i saurarona, ba abinda nafi guje mana kamar rana irin ta yau yanzu inhar wani abin b’atanci ya samu Zeezee ya zamuyi? Ina zamu sa kanmu acikin jama’a? Bama wannan ba in ta kamu da ciwon zamani kaman Aids fah? Wayyo Allah ka rufa mana siri ka dawo mana da Zeezee safe and sound.” wayarta ta ja ta sake gwada layin Ummien Lubiee kan ko Zeezee ta biya chan, sede har yanzu amsar d’aya ce bata zoba, Allah sa a sameta. Lubiee kanta couldn’t believe it dataji Zeezee bata dawo gida ba har yanzu, where could she be?



*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com

PAGE 25

*December, 2016*



Line na Zeezee tayi dialing sede switched off yake ta cemata don haka ta kira na Adeel kusan 4 missed calls tamai be d’aga ba.

_Party hall, Yankari._
Rawa su Zeezee ke tasha, gabad’aya filin an bata ita da Adeel se cashewa suke daman gwana ce when it comes to dancing, a jikinta ba inda Adeel be ta6a ba. Ko sallan Maghrib basuyi ba to talk more of Ishaa, bayan sun gama cashewa sun yi taking dance floor, aka hau applauding nasu. Hannunsa taja suka koma gefe suka zauna bayan tasha ruwa ta d’aga wayansa dake kan table dan duban time. To her suprise taga 10:02PM “o my Gee! Na shiga uku! Very Own k’arfe 10:02 banyi sallah ba, nashiga uku Baba must have gone crazy looking for me, wayyo Allah na mutu!” Tayi maganan kamar wacce zatayi kuka all confused.
“Calm down Babe we’ll go and pray now soon zamu tafi.”
“Very Own dan Allah mutafi yanzu na shiga uku me zan fad’awa Baba? Please do something.” Hannunta ya kama ya had’a da nasa “calm down okay? You are not going home at this night saboda nasan Baba will be very furious at you kibari se gobe.”
“What?!” Tayi maganan unblievably “har gobe? Kana nufin yau ba a gidan Babana zan kwana ba? Please karka min haka ba haka mukayi dakai ba Adeel save me please, wallahi Baba ze kasheni.”
“I told you to stop crossing me, don’t you trust me? Kika koma gida a daren yau sun saki gaba sun rik’a miki questions kenan ina kikaje, if you’re not lucky har dukanki zasu iya yi amman kika bari gobe da safe kika koma seki tinkaresu da kuka kice wani ne ya d’aukeki jiya ya gudu dake, addu’a kika tayi Allah ya dawo dake.”
“How is that even possible Adeel? My parents are not dumb dan Allah ka kaini gida I can’t sleep outside my Dad’s house.”
“In kinga nabar nan toh safiya tayi ne, ke mesa ba’a gayamiki magana kiji ne wai? Tun da muka zo nan acikin friends d’ina kinga wanda girlfriend nasa ke basa matsala ne inba niba? Cut it out okay? This is bullsh*t!” Key’n motarsa ya zaro ya wurga mata “gashi seki tafin ai tunda ke ba’a tab’a gaya miki magana kiji mschw!” Yayi hitting table d’in so hard da hannunsa.

Kuka ta shiga rusawa wajen if only ta iya driving late at night da ta tafin, da tasan da haka da bata biyosa bama in the first place. Taya iyayenta suna raye bawai aure ko tafiya tayi ba zata kwana a waje? Ita yanzu bama wannan ba what if shed’an ya rinjayi Adeel yayi mata wani abin da daddare fah? K’ara volume na kukan nata tayi amman ko ta kanta Adeel beyi ba, hasali wayarsa ma yake ta latsawa seda tayi me isarta sannan ta share hawayen nata. _Adeel is my only hope, dole nayi kamar yadda yakeso kokuwa nice da asara_ tayi tunanin haka a ranta. Key’n motar ta ajiye masa kan table d’in, adalilin haka ya d’ago kai yana kallonta “kin fasa tafiyan ne?” Kai kawai ta gyad’a mai.
“Why?”
“Because I trust you Very Own.”
“Then why did you cross me?”
“Because I was afraid Very Own ban tab’a kwana a waje ba se yau tsoro nakeji” miqewa yayi ya jawota jikinsa “I’m with you, you are safe kinji?” Kai ta gyad’a a hankali seda hankalinta yad’an kwanta ya saketa suka fice zuwa wani hotel not too far from Yankari. D’aki ya musu booking seperately anan suka biya sallolinsu sannan suka ci abinci. Sam hankalin Zeezee yakasa kwanciya ta kunna wayarta ma tsoro take gudun kar Baba ya kirata ya shiga.
Kafin Adeel ya kwanta ya nufi d’akinta dan dubata, “hope ba abinda kike buk’ata ko?” Kai kawai ta kad’a mai. “Don’t worry kinji? I’ve got you, gobe first thing in the morning zan kaiki gida, I love you” yayi pecking nata a forehead.
“I love you too” ta fad’a a hankali nan ya ja mata k’ofan ya rufe. Yana juyawa sega friend nasa Anaconda da wasu mata guda biyu ta each side nasa “ya Adeel? Don’t tell me you are sleeping alone?”
“I am” yabasa amsa a takaice.
“Babe nakan fah meya sameta ko kunyi fad’a ne?”
“Nahh bata sallah ne” yayi mai k’arya.
“Ohh I see kona baka d’aya daga cikin nawa ne?”
“No thanks seda safe” yana kaiwa nan ya fice zuwa d’akinsa.
Kwana zaune Zeezee tayi gabad’aya takasa bacci tsantsan tashin hankali, tunanin ya iyayenta za suyi da ita gobe kawai take. Achan gida ma haka ne Mama duk ta kasa bacci as tana tunanin wani hali Zeezee ke ciki, kwana Mama tayi tana Sallah Allah dawo mata da Zeezee gida safe and sound. Abin ya bata mamaki yadda hankalin Baba ya kwanta lokaci guda gashi koda ta tambayesa any news seya ce mata babu.

_5:56AM_
Adeel yayi knocking bisa door na Zeezee, ba tare d a b’ata lokaci ba ta bud’e “morning Sunshine.” Yayi greeting nata.
“Morning Very Own.” tace sama-sama.
“Owww don’t tell me you didn’t sleep yestarnight.” Yayi maganan hannunsa k’ark’ashin fuskarta, kai ta kad’a tare da sauk’e hannun nasa.
“I couldn’t force myself into sleeping shiyasa.”
“So lets have breakfast?”
“No Adeel dan Allah ka kaini gida kaji please kayi hak’uri bawai ina crossing naka bane kawai inason inje gida ne” tayi asking pleadingly.
“Okay Babe lets go.”

45 minutes drive yakaisu corner’n gidansu Zeezee. Tun anan tahau kakkarwa hannunta Adeel ya riqo “all is well kinji karki damu, ba abinda Baba ze miki you are his girl just tell him someone tried ro run away with you.”
“I’ll try.”
“Duk abinda akwai call me up kinji? Thanks for yestarday, I love you” yayi pecking kumatunta. “I love you too” tafad’a da k’yar sannan ta bud’e k’ofan ta fice seda ta shiga gida Adeel yaja mota ya tafi shima. A dai-dai bakin k’ofan ta tsaya takasa going any further. Wani erin mumunar harb’awa zuciyarta ke, tafi minti uku tsaye wajen sannan daga bisani tayi _womaning_ up ta k’arisa ciki. A dai-dai lokacin Mama da Baba suke shirin fitowa da alama don cigaba da nemanta ne, tana ganinsu ta wani mugun razana.
“Zeezee!” Mama da Baba sukayi exclaiming in unison. Kakkarwan take har yanzu

25 / 98