YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 98

66K to 69K   out of 291.7K words

“Ameen Baba nagode.”
“Nima nagode” har waje ta rakasa sannan ta dawo d’akinta se tsalle take ita za’a sai mata mota, fatan ta Allah yasa mercedes-benz ce, a rayuwa ba motar dake burgeta kaman benz, benz is life!

★*★*★*★
Life moved on da k’yar abubuwa suka dai-daita tsakanin Zeezee da Adeel, a rayuwa ba abinda tafiso kamar taga ita da Adeel are on good terms suna shiri. Duk wani abinda tasan ze haddiso musu da matsala tana k’ok’arin kiyayewa saboda zaman lafiyansu ya fiye mata komi a duniya.

Yau ranar ta kasance Tuesday da yamma around 4:30PM tana kwance a d’akinta ita kad’ai. Ba kowa a gidan se ita Baba ya fita su Mama kuwa sun je gidan Kaka. Baba ne ya kirata nan da nan ta d’aga “hello Baba.”
“Na’am K’anwata kina gida?”
“Eh.”
“Toh kifito bakin k’ofa yanzu.”
“Toh gani!” mayafinta taja da waya ta fice tana fita taga the most biggest suprise of her life, sabuwar mercedes benz C300 ce fa fara k’al ko ledan jiki ba’a b’are ba. “Omg!” Kawai take ta nanatawa, kuka ta soma tsabagen murna, da gudu taje tayi hugging Baba. “Baba I don’t know the right words to use in thanking you, bansan ya rayuwa na zata kasance without you ba, you mean the world to me you are my hero, I love you so much, morethan you can ever imagine.”
“Zeezee na ta girma I love you as much K’anwata ga key naki nan.” Nan ya mik’a mata, wayarta ta bud’e ta shiga snapchat ta musu selfie ita Baba da motanta tayi adding caption _priceless gift from my Amiable Dad, ILH._ daga nan tayi ta d’aukan motar hoto, saura tayi shi kad’ai saura ita dashi. Ana cikin haka su Mama suka dawo a motan Omar. A gefen motan Baba sukayi parking suka fiffito “sannu Baba” suka yi mai ya musu sannu da zuwa.

“Toh wannan mota fah? Suwa sukazo sukayi parking anan?” Mama ta tambaya.
“Bana mutane bane nawa ne Baba ya siya min” ta k’arisa gunsa tare da kwanciya ajikinsa.
“Meneh? Dawo baya ban jiki ba” Mama tayi maganan disbelievingly a yayinda Omar da Ibraheem sukayi tsaye gun dumbfounded.
“Mota na ne Baba ne ya siya min.”
“Mota! Alhj mota ka sai wa Zeezee?! Da shawaran waye? On hi Hafsah! Mota de?” Ta k’arisa gun motan tana shafawa “kuma sabuwa ko hawanta ma ba’ayi ba.”
“Sabuwa?” Omar yayi maganan yana bin motar da kallo.
“Ni kibar shafamun mota, Baba kace tabar shafa min mota.”
“In bazaku fad’i alkhairi ba keda ‘ya‘yanki seku ja bakinku kuyi shiru.”
“Alhj amman wannan wani erin rashin hankali ne?”
“Sai ma K’anwar tawa mota shine rashin hankali? Ke kin manta kalan alkhairun da marigayiya tayi min ne?”
“Ai marigayiya kace, wannan kuma ba marigayiya bace wallahi tun wuri a mai da motan nan. Wani irin rashin hankali ne haka? Ban tab’a jin inda aka saima ‘yar 16 years mota ba.”
“Yau kinji ai tunda a gidan ki akayi, kuma ba miyar da motan da za’ayi, ina key d’in mu shiga miki da motan ciki.”
“Gashi Baba” nan ta bashi key d’in, a parking lot daya gyara dan parking motansa ya mata parking nata sannan ya kai nasa garriage, Mama da yaranta de suna ganin ikon Allah yau. Kaka ta kira ta irga mata gashi fa Baba ya saiwa Zeezee mota bayan ko gama makaranta batayi ba. Suna gama wayar Kaka ta kira Baba dan mai magana aikuwa ya mata k’arya wai se Zeezee ta gama makarantar zata soma hawa.

Zeezee kam na can a d’akinta tana ta kan applying makeup tana gamawa taci farar gown nata sukayi anko da motanta sannan taje ta cigaba da d’aukan selfie da motar tata. Ranan snapchat seda yayi kuka haka instagram ma. Lubiee couldn’t believe it dataga ansai wa Zeezee mota haka Adeel ma, shi shege girlfriend nasa na hawan C300 shikuma E350 4matic. Washegari Mariam tazo kallon motan *_‘YAR GATAN BABA_*

Cikin sati biyu Baba ya sa wani yaronsa ya koya wa Zeezee mota, tinting glasses d’in tayi da darkest colour, hakan kuwa ba k’aramin karb’an motan yayi ba dake farar mota ce. Kullum ba aikinta se wanke motanta, ko kad’an batason abinda ze tab’a mata shi. Yau da La’asr ta d’au wanka ta feffeshe da turare sannan ta d’au key’n motarta ta fice a waje taci karo da Mama “aikin kenan a penta fuksa a fita yawon banza sa’o’inki suna karatun jamb da waec ke kullum cikin fita unguwa koda shike ba laifinki bane na Baban naki ne tunda ya d’au mota ya baki.”
“Haters are gonna die.”
“Me kika ce?”
“Nace Allah barmin Maman Zeezee, gidansu Lubiee zani.”
“Zancen kenan kullum gidansu Lubiee. Seta gaji dake ai, ke bazaki zauna ki fara karatu ba ko?”
“Wai Mama ce miki akayi yanzu ana karatun waec ne? Answer kawai ake suburbud’a wa mutane.”
“Da kyau.”
“Eh man ku naku lokacin da ba’a baku ba flat F9 kuke fitowa dashi ba bayan karatun da kuke, nide in Baba ya tambayi ina nake kice mai na tafi gidansu Lubiee, ko akwai abinda kikeso?”
“Kan Uwarki nakeso ‘yar banza kawai.”
“Hohoho Maman Zeezee Allah barmin ke kiga ci gabana a duniya.”
“Mschww!” taja tsaki ta fice. K’arisawa gun motarta tayi ta hau gogewa akan wankewan da tayi d’azu. Tana cikinyi Omar ya fito ya k’are mata kallo sannan yace, “ke bud’emin gate.”
“Hehe! Su Ya Omar jiya ba yau bane fa. Levels don change yanzu, ni me sabuwan mota pil bance a bud’en gate ba sekai da seda wani bature ya hau ya baka zakace na bud’e maka?”
“Me kika ce?” yayi snarling at her.
“Babu nace barin gama gogewan na bud’e maka.”
“Da yafi maki kam” nan da nan ta gama ta bud’e mai yana fita itama ta fice. Music nata ta k’ure tana kad’a kai tana driving ana tab’a rawan dab, hankalinta a ruwan sanyi. Gidansu Adeel nata ta wuce, bayan ta samu gu tayi parking ta kirasa “hello My Very Own.”
“Sweetest Love.”
“Kana gida ne?”
“Yup wani abu ne?”
“Nop just kafito bakin gate.”
“Okay right away!” nan yayi hanging. Wayoyinsa ya tattara sannan yayi glancing kansa a mirror ya fice, yana fita bakin gate yaga Zeezeensa tsaye gefen motarta da sunglasses maqale a fuskanta tana mai wani mayen murmushi, murmushin shima ya mayar mata sannan ya k’arisa gun sukayi hugging as always kamar yadda suka saba sekace ba ‘ya‘yan musulmai ba. Bayan yayi releasing nata yayi pecking nata a kumatu “you are looking super sexy Barbie.”
“I know right Very Own toh ya kake?”
“Lafiya, you didn’t tell me you were coming” yayi maganan yana wasa da siraran yatsunta.
“I thought I might suprise My Very Own.”
“Best suprise ever!” ya sake pecking nata “so zamu shiga ciki ko we are going somehwere?”
“Going somewhere just the two of us.”
“I love you Babe.”
“I love you much more My Very Own” ta mik’a itama tayi pecking nasa a cheeks “lets go, hurry I’ll be the one to drive.”
“No way my Queen, allow your King to drive you.” Shi da kansa ya bud’e mata motan ta shiga sannan ya rufe ya zagaya ya tada motan suka fice zuwa Hysaan beverages ya siya musu roasted chicken da drinks daga nan suka wuce can bayan gari inda ba mutane yayi parking. Suna cin kazan su suna hira har suka gama se kusan to 6pm Zeezee ta isa gida.

*~ *~ *~``
Haka deh Allah ya cigaba da raya Zeezee har suka samu sukayi jamb nasu ta fito da 205 points. Ita kanta bata zata zataci ya kai haka ba saboda bawani karatun kirkin datayi as always tana kan waya da Adeel nata. Dama Baba yayi promising nata kan intaci fiye da 200 points ze sai mata duk abinda takeso, iphone 7s tace takeso aranan aka sai mata shi, haka tayita cika ‘yan instagram da snapchat da pictures na iphone 7s nata. Ana cikin haka bikin Ibraheem da Fateemah ya taso, preparation suke sosai ‘cause this is the first time Baba da Mama suke aurar da d’an su na miji. Not long enough aka soma wedding events, Zeezee de kam har ta kusa fin amarya shan kyau dan kuwa har Abj ta tura akayi mata gowns nata. Makeup artist da tama amarya makeup kuwa ita tayi mata nata.

Se palli take da rawan kai. A ranan dinner ta d’au mutane cikin motar tama tak’i ba yadda Mama batayi da ita ba amman tak’i, agun dinner kuwa table nata ita da Lubiee, Adeel, Uthman (boyfrined na Lubiee) seda friends nasu guda biyu ta tanadar musu suka zauna. Angama komi aka kai amarya Abuja. Zeezee dad’i kasheta yanzu ba Ya Ibraheem d’an shisshigi, cin duniyarta zatayi da tsinke hankalinta kwance. Wannan kenan!

Tunda Ibraheem yabar gidan iskancin Zeezee ya k’aru, daman ba wani tsoron Ya Omar take ba, hakan yasa ta sake raina Mama kota mata magana se in ta gadama tayi, cikin sa’a suka soma waec nasu har suka gama saura neco suyi goodbye da secondary school. D’an hutun dake tsakanin waec and neco Zeezee ta had’a akwatinta zata Abuja gun Ya Ibraheem simply because taje taga kalan zaman da suke da matarsa badan wani abu ba. Ta jirgi Baba ya biya mata, 1pm suka yi landing. Ibraheem da Fateemah duka sukaje d’aukota daga airport bayan angama hugging da gaisuwa suka dawo gida. Baki Zeezee ta sake data ga mansion na Ibraheem ashe de magabata basuyi k’arya ba irin wannan gida! Mschww ita da tasan Ibraheem zexo yayi kud’i haka data had’a Aunt na Lubiee da Ibraheem akan wanan Fateeman, haka kawai Zeezee ta tsaneta.





*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com

PAGE 23

*December, 2016*




A guest room ta sauka, bayan ta watsa ruwa ta fito tana bin gidan da kallo, a kitchen ta tarar da Fateemah tana had’a lunch “sannu Aunty Fatee” tayi maganan cike da gatsine.
“Yauwa Zeezee har kin fito ne?”
“Eh ina Ya Ibraheem?”
“Yanzun ya fita ya koma office.”
“Ohh gidan Yaya na yayi kyau ba laifi.”
“Ko? Toh mungode” A zuciyarta tace _ya gode ko kun gode? Sekace tare kuka gina gidan, over sabi._
“Chab! Amman kam Aunty Fatee kin k’ara k’iba abincin gidan Yayana na aiki.”
“LOL koh? Kije ki d’anyi kallo kafin na gama had’a lunch d’in” chan k’asa-k’asa Zeezee tace, “da yafi maki kam dan ba assisting naki girkin zanba hutu na zoyi ehe!”
“Na’am kikace meh?”
“A’a babu nace sannu da aiki ni zan d’an zagaya ta cikin gidan, naga kaman akwai garden.”
“Eh akwai bismillah.” D’akin data sauk’a ta koma ta d’au wayarta sannan ta wuce garden d’in se videon kanta take tana posting a snapchat haka ta tayi har seda Fateemah ta kirata kan lunch is ready. Cikin nutsuwa suka gama cin abincin agun Zeezee tabar plate nata, Fateemah da kanta ta tattara tayi wanke-wanke. Kallo kad’an Zeezee ta tab’a ta koma d’aki ta hau waya da Adeel nata. Se 5pm da Ibraheem ya dawo tafito ta mai sannu da zuwa nan sukayi proper gaisuwa ya mutan gida da komi da komi. “Kinbar rashin kunya kokuwa har yansu halin naki na nan?”
“Ni daman ina rashin kunya ne?”
“Allah sa toh, bazaki ci abinci bane ke?” Yayi maganan yana zama kan kujerar dining da Fateemah taja mai.
“Munci da Aunty Fatee d’azu.”
“Oh okay” nan Fateemah tayi serving nasa tare da zama gefensa tahau feeding nasa. Baki Zeezee ta sake wangalau tana kallon ikon Allah. Yi tayi kamar tana kalllon TV amman hasali hankalinta akan su yake bayan ya gama cin abincin ya rik’o hannun Fateemah “zamu shiga ciki Zeezee feel at home.”
“ko baka fad’a ba ai” tace tana bin interwined hands nasu da kallo suna b’acewa ta tafe hannunta “oh! iskanci a idona yau, kome zasuyi acikin d’akin kuma se Allah hehehe! Su Ya Ibraheem manya” kallo ta tayi chan da kallon ya isheta ta hau chatting. 6:30pm Ibraheem yafito sanye da jallabiya “lokacin Sallah yayi seki tashi.”
“Toh ni banayi.”
“Ya miki kyau ni na tafi masallaci.”
“Allah kare toh” yana fita ta mik’e zunbur ta nufi d’akin da taga sun shiga d’azu. Fateemah ta tarar da hand drier a rik’e a hannunta tana d’aure da towel both a jikinta da kuma kanta. Wani shegen kallo Zeezee ta bita dashi ina irin nasan me kukayin nan. “Uh Aunty Fatee ashe d’akinku na shigo na zata nawa ne.”
“A’a naki na k’arshen corrider by your left hand.”
“Aihoo amman wanke kanki kikayi ko?”
“Eh” ta amsa a takaice.
“Ohh amman meyasa? Naga sabon kitso ne akanki.”
“Ermm... Eh normally idan nayi wanka haka nake sena wanke kan.” tayi maganan tana neman ignoring topic d’in.
“Wow wierd! Ga kuma ko ina tsaf a d’akin illa kan gado sekace anyi dambe akai.”
“Zeezee kije kiyi sallah kinji? Nima yanzu zanyi.”
“Nikam bana Sallah bazan taya ki gyaran gadon kafin Ya yadawo.” Ganin ta nufi gadon Fateemah tayi saurin shan gabanta “a’a bari karki damu ai hutu kika zoyi ba aiki ba zan gyara da kaina nagode.”
“Allah Aunty Fatee kibari na gyara miki.”
“A’a Zeezee kibari nagode” haka suka tayi seda Zeezee ta wahalar da ita ta hak’uran tare da ficewa “‘yar is.. ai da kin bari na gyaran naga me kike b’oyewa, ai wallahi sena hanaku sukuni keda Ya” tayi maganan tana mik’ewa kan gadonta.

Washegari ranar ta kasance Saturday ba aiki, tun 9am su Ibraheem suka tashi banda Zeezee dake ta sharb’an bacci. Shi da Fateemansa suka had’a breakfast suka karya sannan suka ajiyewa Zeezee nata se 12noon ta tashi tayi wanka ta shirya sannan ta fito. A parlour ta tarar dasu suna hira suna kallo Fateemah ta kwanta jikin Ibraheem comfortably sekace ‘yar baby. Seda Zeezee ta k’are musu kallo sannan tayi gyaran murya nan Fateemah tahau k’ok’arin d’agowa daga jikin Ibraheem, ganin haka shikuma yak’i saketa “toh in bazaku gyara ba ina kwananku.”
“Baby ka sakeni please” Fateemah tayi maganan can k’asa-k’asa.
“Ko gaisuwan ma bazaku amsa bane Lovey-Dovey?”
“Kin fara koh? Baki bar halin nan naki na rashin kunya ba ashe.”
“Hali zanen dutse, kuma ai naga akan gaskiya na nake, inba neman ku b’atani ba taya kunji motsi na bazaku d’an gyara ba?”
“Yi hak’uri Zeezee ga can breakfast naki a dining.” Fateemah tayi stating shamely.
“Apologies accepted, me kika girka?”
“Chips ne da omalet.”
“Nikam banason chips indomie nakeso.”
“Ga kitchen ai seki shiga ki dafa ko ita Fateeman kikeso ta girka miki?”
“Aiko tanason girkamin d’in ma ba barin ta zakayi ba yadda kawani damk’eta ajikin ka sekace za’a sace maka ita, you may carry on na wuce kitchen.” Anan ta fice kai kawai Ibraheem ya kad’a Fateemah na murmushi tace, “Zeezeenmu se a hankali.”
“Ai nakega kafin ta gama hutun nata seta bugu zatayi hankali, tad’an manta ni ne two days”
“No Baby banda duka please.”

****
Bayan Sallan Azahar Fateemah ta shiga had’a lunch, Ibraheem na dawowa yaga Zeezee zaune a parlour tana kallo while Fateemah nacan tana aiki. “Ke bazaki je ki taya Aunty’n ki aiki bane?”
“Ya aiki nazo yi ko hutu? Danfa Mama na tak’ura mun agida yasa nazo nan dan na d’an huta, nan d’in ma kace wai sena taya Aunty Fatee aiki? Da bani nan wake taya ta?”
“Karkiga fa dan kinzo hutu ki zata wai bazan iya dukanki ba tam! is better kiyi minding tongue naki.”
“Toh Ya amman nazo hutu kuma sekace senayi aiki.”
“Sekinyi tashi kije ki sameta.”
“Ni wallahi-” ganin ya nufi kanta ta mik’e a 360 se kitchen d’in tana cunno baki tana gun-guni “lafiya dai ko Zeezee?”
“Wani irin lafiya wannan mijinkin wai sede nazo na tayaki aiki sekace ba hutu nazo yiba.”
“LOL toh karki damu jeki cigaba da kallon ki yanzu ma zan gama.”
“Yauwa toh ki fad’a mishi yaji karya daken.”
“Baby! Aww sorry Ya Ibraheem!” ta kirasa.
“A’a ni koda Baby’n ma kika kirasa ba matsala nide in baze daken ba shikenan.”
“Yes Sweetheart” yayi magana yana k’arisowa kitchen d’in “me kike tsaye achan bance kiyi assiting Fateemah ba?”
“A’a Baby kabarta please kaga ba dad’i hutu tazo let her be. Ai aikin ma ba yawa yanzu zan gama.”
“Wai ance miki anayiwa Zeezee abinda takeso ne? Ko washing dishes ne kibata.”
“Seriously Babe let her be na gama komi jekiyi kallonki Zeezee.” Gwalo Zeezee tama Ibraheem tazo wucewa ya danna mata rank’washi akai “Allah ya-”
“Me kika ce?” tana murza wajen tace;
“Nace Allah saka maka da alkhairi” ta gyara zancen nata. Ita de Fateema dariya kawai take sha’anin Ibraheem da Zeezee se kallo.

★*★*★*★
Haka fa Zeezee ta cigaba da moran hutun ta gidan Ibraheem, ba aikinda take komi Fateemah keyi koda Ibraheem yace tayi se Fateemah tace a’a tabari zatayi da kanta. In garin Allah ya waye Zeezee sede tayi wanka tayita d’aukan hoto, chatting, waya da Adeel da kuma kallo. Sekuma ta bari Ibraheem da Fateemah sunyi d’aki seta ruga aguje ta shiga ciki ba notice ta hau ihu wai taga kyankyeso ko b’era. Gabad’aya ta hana Fateemah sukuni dan ita Fateemah ta rage kalan love da take bawa mijinta amman dukda haka Zeezee bata gani bale tad’an rage mata wani abun.

7:48AM Fateemah da Ibraheem suna tsaye gaban dressing mirror tana mai bottling shirt, tana gamawa ta d’aura masa

23 / 98