YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   60 / 98

177K to 180K   out of 291.7K words

Zeezee bata tunanin komi yanzu banda addinin ta, mahaifinta da kuma Ya Al'ameen nata ko tunanin Adeel da Mama ta bata labari cewa ya kawo cartons na Malt guda biyu a rasuwan Baba batayi saboda ta riga ta ciresa a ranta kwata-kwata. Ya Al'ameen ne kawai a ranta.
Islamiyya tayi joining inda kullum take cikin nik'af da dogon hijabi saboda batason ana gane mata fuska don har a yau tasan baza a rasa mutanen da zasu na kwatanta taba da wacce tayi sanadiyar mutuwan mahaifinta. A takaice de Zeezee an koma ga Allah.
Sau dayawa takan zuwa gidan Mariam ta kwaso Ramlah da Ummie suzo suyi mata weekends, ba k'aramin son babies Zeezee ke ba yanzu musamman idan ta tuna ita bazata iya haihuwa ba. Tsaf zatayi musu wanka ta shiryasu ta kaisu gidan kitso kokuwa shopping suka zo kwana ma a d'akinta suke kwana. On working days kuma tun safe zata tashi tayi shara tayi mopping ba aikin da Zeezee batayi wa Mama, har wanki atimes. Kullum cikin sambad'a mata albarka Mama take tana cewa da Babanki na nan he would have been damn proud of you.

***
Ta side na Adeel kuwa har yau ya kasa cire Zeezee daga ransa, da tunanin Zeezee yake tashi ya sake yini. Rayuwarsa da Ruky sam ba dad'i. Acikin ikon Allah Ruky ta sake samun wani cikin wanda a 5 weeks tayi 6ari komi ya 6antare, yanzu haka ma tana gida. Adeel daga ya dawo daga aiki se zaman d'aki wane amarya ko kira yaji ya jikin Ruky ma baiyi. Da yamma yau ya watsa ruwa ya shirya tsaf ya nufi unguwan su Zeezee, gaba da gidansu kad'an ya faka sannan ya fito daga motar yana dube-dube wanda shi kansa be san fa'idar yin hakan ba.
5:30pm su Zeezee suka taso daga islamiyya, cikin nik'af nata take takowa gida. Don yadda Adeel ya mugun saninta daga tafiyar ta ma yagane itan ce sede he is still doubting. Da sauri-sauri har yana neman cin tuntu6e ya tinkareta tare da yin sallama. Wani irin mumunar fad'uwa gabanta yayi jin muryan Adeel, saboda a rayuwa baza ta ta6a mancewa da muryanshi ba. Kasa d'aga kai ta kallesa tayi a yayinda hawaye ke forming rapidly a idonta.
Gefensa tabi da wuri ta wucesa sede kafin tayi nisa ya sake shan gabanta. Gefensan ta sake kuma bi wanda yanzu da sauri yayi blocking nata, d'ayan side nasa ta koma zata bi, nan ma yayi blocking nata.
"Zeezee please answer me, koda bazaki min magana ba ki amsa sallama na." Har anan takasa d'aga kai ta kallesa. "Zeezee bada wata manufa nazo miki ba, ta'aziyya nakeson miki-" katse sa tayi da wuri, "naji nagode Allah ya bada lada, excuse me." Ta fad'a a takaice.
"Zeezee please one more thing."
"Malam inba wai so kake na tara maka jama'a ba ka matsa min a gabana."
"Zeezee pl-"
"One..." ta shiga counting "two..."
"Am sorry" ya katse ta ganin how serious she is, "inhar hakan kikeso so be it but kisani Zeezee I will never rest until kinyi forgiving d'ina I want you to know that nayi regretting dukkanin abubuwan dana miki. Sharrin shaitaan ne ba komi ba wallahi, I love you morethan I can ever explain Zeezee please forgive me. Wallahi hak'k'in ki har a yau bina yake da Ruky, at first ta haihu d'an ba rai yanzu ta sake miscarrying baby'n forgive us please."
"In don wannan ka d'ibo k'afafunka all the way here kasani ni na jima da yafe muku abubuwan da kuka yimin. We are all human beings and not above making mistakes, ni kaina me laifi ce, Allah ya yafe mana gabad'aya." Tayi maganan not looking at him at all. Ba k'aramin burgesa kalamunta sukayi ba, "thank you Zeezee, thank you so much I shall never forget this. You are indeed one of a kind, Allah saka miki da mafificinsa, ameen." Ba tare da ta sake cewa dashi k'ala ba tabi gefensa ta fice. Wani irin farin ciki ya tsinci kansa ciki atleast ya sauk'e wani abin, yanzu tunanin ya zeyi ya dawo da ita gidansa yake. From yadda Zeezee ke acting yasan it'll be hard for that to happen amman karkacaccen mind nasa se tunzirasa yake kan lallai fa ya dawo da ita. Shigan Zeezee ciki kuwa bata nunawa Mama Adeel yazo wajenta ba saboda bata ga amfanin hakan ba. Uniform nata ta tu6e taje ta samu Mama a kitchen suka gama had'a dinner.

Washegari exactly time da Adeel yaga Zeezee jiya yau ma ya shirya yana jiranta. 5:35pm sega tanan, da wuri yaje ya sameta yana mata sallama sede ko sauraronsa batayi ba, binta yake tayi har seda ta kusan isa gida sannann yasha gabanta.


*MIEMIEBEE👄. Team #YGC!🎀*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
Page 54
*FEBRUARY, 2017*




"Zeezee please kiyi hak'uri ki saurareni, slap me, insult the hell out of me, hit me anywhere you want and how but please don't shut me out. Wallahi Zeezee tun rananda na sake ki na shiga wani gaggarimin yanayi, give your very own one last chance please I beg of you, its all I ask."
"One last chance?" Ta d'ago kai tana kallonsa ta nik'af nata finally cike da mamaki. "One last chance so you can maltreat me again? One last chance so ka sake duka na? force me into bed? make me do yours and wife's laundry? cook for you? sweep-" katse ta yayi da wuri "no, no please-" ya fad'a wane zeyi kuka.
"Then why? Saboda kana nunamin Ruky ta fini k'ima da daraja a idonka?"
"No Zeezee enough of that please, I want you back because I love you and miss everything about you, your smile, fragrance, body, hair, everything about you. I miss it."
"I should have guess, ko ka manta am of no use to you tunda bazan iya haihuwa ba yanzu."
"I don't f*cking care Zeezee, all I want is you."
"You should have thought about that earlier kafin ka dakeni ka kuma buga min saki biyu."
"Zeezee please! Cut it out. Meh kikeson in miki kigane cewa I've regretted every single action of mine back then? In Ruky kikeson in saka I'll at this instant because I don't love her, ke nakeso Zeezee please pity your very own."
"What I want? What I want is for you to f*cking stay away from me Adeel plus you are nomore my very own, you never were. Bana k'aunar ka anymore Adeel ka riga ka fitamin a rai na, bana sonka. You came to me jiya da sunan tuba na kake nema and I did forgave you don't make me change my mind please."
"Zee-"
"I said go away!" Ta katse sa a tsawace.
"No Zeezee please listen to me, lets solve this out, Zeezee haka kikeson ki k'arisa rayuwarki as bazawara? Bana son ganinki haka, you are worth than this."
"Am I? Baka son ganina a haka ka buga min saki biyu? Mschww! am running out of patience just go away and never come back I don't ever need you in my life again."
"No, that's not true, you can't forget me this soon-"
"I can't?" Ta tambayesa "I was never in love with you Adeel, ko a da inma ba sonka nake ba. I came to realise that I was just afraid of you, a monster. Ya Al'ameen is the one I love and not you."
"That's not true Zeezee you still love me I know that please come back."
"Never."
"Haka kikeso ki cigaba da zama?"
"Koda hakan zan cigaba da zama meya maka zafi? Besides am going back to my truest love Ya Al'ameen."

"No Zeezee please don't, karki tafi ki barni I beg you please. Kimin komi amman karki koma gidan Maj- Gen."
"Give me one reason not to. Gidanshi zan koma I've made up my mind." Tana kaiwa nan tabi gefensa zata fice da sauri ya rik'o hijabin ta stopping her. Chak ta tsaya, kuka kawai taji ya fara kaman d'an yaro wanda itama tuni ya karya mata zuciya ta soma kukan.
"Zeezee please" yayi pleading in a crying tone. "Please don't leave me" ya k'arisa maganan yana sauk'a akan guiwowinsa a idanun jami'un da ke wucewa. "I beg you please karki koma gun Ya Al'ameen come back to me and let me prove my love to you one last chance, please Zeezee don't refuse my offer." Kuka ne sosai yaci k'arfinta yadda words na Adeel ke getting to her. Tanayi yana yi, "let me go, ka sakeni" kad'ai ta iya furta mai. Kai yake kad'awa still in the kneeling position. "Zeezee please." Fincike hijabin nata tayi ta ruga ciki a guje tana kuka sosai. As always Mama na kitchen taga wucewan Zeezee da gudu yau unlike always da zata tsaya tayi mata sannu. Barin duk abinda takeyi tayi taje ta samu Zeezee dake baje akan gado tana kuka me tsuma zuciya.
"Subhanallah!" Tayi exclaiming. "Ya da kuka haka? Meya faru?" Tayi maganan hannunta manne akan bayan Zeezee data kasa koda d'ago kai har yanzu.
"Zeezee? Yi hak'uri ki amsa ni kinji? Meya faru?" Da k'yar ta iya tsagaita kukan tace, "babu."
"Kamar ya babu kuma? Kina nufin haka kawai yau kika d'auro niyyan dawo min gida da kuka?" Kanta ta d'ago finally tare da share rolling tears nata. "Babu an yi mana wa'azi ne me ratsa jiki a islamiyya akan mutuwa se kawai na tuna da Baba."
"Allah sarki, in shaa Allah Babanku is in a better place kinji? Mu cigaba da yimai addu'a yi hak'uri kukan ya isa haka Mamana."
"In shaa Allah Mama thank you."
"Tashi ki tu6e uniform d'in toh." Da nod da tayi wa Mama, Mama ta fice. Duk yadda tayi don kawar da tunanin Adeel daga k'wak'walwarta ta kasa, haka ta kwana ranan da tunaninsa.
Washegari kuwa ko zancen zuwa islamiyya Zeezee batayi wa Mama ba, pass 3pm Mama ta shigota d'akinta, miqe kan gado ta tarar da ita tayi dunk'um tana tunani.
"Bade tunanin Baba kike ba yau ma?Zeezee shin wai sekin haifar wa kanki ciwon zuciya sannan zaki huta? Da rasuwan Babanku sati nawa but kin kasa ki daidaita rayuwarki, haba mana! Mutuwa da zafi amman ya zama dole ki hak'ura."
Tasowa tayi ta zauna "nifa ba tunanin Baba nake ba, ai kince in dena kuma ina iya k'ok'ari na ganin na ragen."
"Toh me kike zaune yi haka tun d'azu? Tun da kika gama ayyukan ki ban sake jin motsinki ba."

"Babu." Ta amsa blankly.
"Toh islamiyyan fa? Babu ne yau?"
"Akwai Bazan jeba ne" ((dalili kuwa shine bata son yau ma su sake had'uwa da Adeel she is simply avoiding him.)
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya" tayi faking smile.
"A'a ban san ki da haka bafa, gayamin mene"
"Allah babu Mama, bana jin dad'in jiki na ne."
"Kinsa tunani a gaba ba dole ba, bale ma I don't trust this silly excuse, gayamin gaskian zancen meya hanaki zuwa islamiya yau? Keda baki ta6a fashi.l
"Mama babu."
"Zainab!"
"Na'am" ta amsa.
"Tell me, mene?"
"Mama..." sekuma tayi shiru. Isowa kusa da ita Mama tayi ta zauna a gefenta tare da rik'o hannunta "gayamin kinji? Am here for you."
"Mama its Adeel" ta fad'a hawaye na forming rapidly a idanunta.
"Subhanallah! What about him?"
"Mama shekaran jiya yazo har nan bakin gate on my way back home daga islamiyya na ganshi..." nan ta kwashe labarin komi tabawa Mama bata ragar da komi ba.
Ajiyar zuciya Mama ta sauk'e "ikon Allah! Ke yanzu me zuciyar ki ke raya miki?"
"Mama I don't know I've had enough of his torture, I don't need some more."
"Bakiya sonshi yanzu?" Kai ta gyad'a a hankali.
"Are you sure?" Sekuma ta kad'a kai da nufin a'a. "Mama its hard for me to admit that bana son Adeel saboda he was my first love, I loved him with all that I've got."
"I know Zeezee you must not repeat it again. Kina ganin ke ya tuba, tuban gaske?"
"He did Mama saboda he even knelt down in front of me, but it still isn't enough compared to abubuwan dayamin da nake gidansa, Mama ban ta6a fad'a miki bane but har forcing d'ina in to bed Adeel nayi, sometimes ma he'll be drunk and then sleep with me forcefully" ta k'are maganan cikin kuka sosai. Hugging nata sosai Mama tayi cike da tausayi. "Its okay Sweetheart baza ki komawa Adeel ba unless you want to kinji? Kibar kukan haka." Kai tayi nodding "thank you Mama."
"Always dear, share hawayenki ki shirya islamiyya idan aka tashi zan sa Omar yaje ya d'auko ki kinga ta hakan Adeel baze iya sake tsayar dake ba."
"Are you sure Mama?"
"I'm definitely am."

Ba tare da ta sake cewa uffan ba ta shirya tsaf ta wuce islamiyya. Sede yau ma kaman jiya, bayan Omar ya d'aukota daga islamiya suka tarar da maroon Genesis G80'n Adeel parked gaba da gidansu kad'an.
""Ya Omar gashi chan." Tayi stating ba nitsuwa a tattare da ita.
"Waye Zeezee?"
"Adeel, gashi chan don Allah do something." Tana idar da maganan sega Adeel yana fitowa daga motarsa, ita se yau ma ta lura da bak'in da Adeel yayi.
"Go inside Omar" ya buk'aceta. Da sauri ta bud'e motan ta fita nan Adeel ya shiga k'walla mata kira sam tayi kaman ba ita yake kira ba, tana kaiwa ciki tasa lock. Juyawan da Adeel zeyi yaga Omar, although besan saba amman jikinsa na basa wan Zeezee ne.
Hannu Adeel ya miqa masa sukayi sallama sannan Omar ya tambayesa purpose of being here inshi.
"I know ba lallai bane ka sanni, I'm Adeel Zeezee's husband-"
"Ex husband" Omar yayi correcting nashi. Baki na 6ari yace, "yes ex husband, Yaya please bikon Zeezee nake sonyi, ku yafemin ku dawo min da ita, I love her."
"Kasan kana sonta shine ka wulak'an tata ka buga mata saki bama d'aya ba har biyu? Please Mallam pack your wahala and go bamu buk'atanka."
"Yaya please karka min haka, idan ita Zeezee yarinya tamin haka, kai babba be kamata kamin haka ba kaima. Wallahi sharrin shaitaan ne I never meant to divorce Zeezee believe me."
"Bazaka tafi ta ruwan sanyi bane sena sa an maka koran akuya?"
"Yaya please..." ya sake pleading. Ganin Omar na neman tara masa jama'a yasa kawai ya tafi badon yana so.

Adeel be fasa zuwa gidansu Zeezee a kullum ba, infact he decided to make it a hobby. A kullum kuwa idan yazo da Omar suke had'uwa dan kuwa Zeezee a mota Omar ke barinta shi ya fito ya zazzage wa Adeel buhu-buhun rashin mutunci amman ba hakan zaisa gobe yak'i zuwa ba. Akan Zeezee ya ajiye pride nasa a gefe, inhar ze sameta he is ready to loss everything like everything. Kusan sati biyu Adeel ya jera yana zuwa gidansu Zeezee kaman maye. Ruky Mama sede ta kallesa saboda ko maganan arziki bayi had'asu don Adeel ya fita harkarta gabad'aya. In sunyi magana toh Ruky money monger tazo kar6an kud'i ne, wanda da yak'i da ya so dole ya bata kokuwa ta b'oye key'n motarsa. Yau ma kaman kullum yajesa gidan su Zeezee, bayan Omar ya korasa ya dawo gida rai a dak'ule only to find the gate locked harda kwad'o. Danqaree! Ya furta a ransa sannan ya shiga bubbuga k'ofan yana me sauk'e haushinsa akai. "Ruky! Rukayya! Ina wannan bayerabiyar ta shiga? Mschww!" Ganin fa bata gida yasa ya zaro wayansa daga aljihu a fusace ya shiga nemanta. Several missed calls yayi mata wanda ciki ba wanda ta d'aga as tasa wayar a silent se bidirin biki suke sha.

*^GIDAN BIKI^*
Wak'an girgiza k'wank'waso ke tashi wane ze har6a zuciyan mutum. Ruky da friends nata ne ke tsaye se rawa sukeyi, chan wata friend nata ta buk'aceta da sanin time, anan ne Ruky ta zira hannu tare da zaro wayanta nan taci karo da 28 missed calls from Baby. Tsuka taja sannan ta sanar da k'awarta ta.
"Toh ni nasan zaka dawo da wuri ne? Ina kullum se bayan Maghrib kake dawowa, mschww!" Fita tayi zuwa less crowded area ta shiga Calling nasa back wanda tuni ya d'aga kasancewar wayan na a hannunsa yana tsaye bakin gate d'in wane me maula.
"Ke mahaukaciyar ina ce? Gidan naki ne da zaki kama ki rufeni a waje?"
"Abeg Mallam free me oo, kai kanka ka fad'a ka ta6a dawowa gida at this time ne? Base bayan Maghrib kake dawowa ba?"
"Aww! Ma abinda zaki ce kenan saboda bakida tarbiyya koh?"
"Ai gaskiya ne."
"Da izinin uban wa kika fita? Na baki izini ne?"
"Kaman ya kabani izini, baka gida izinin wa kakeso in tambaya?"
"Aww kuma bakisan ki kirani ki sanar dani a waya ba wato."
"Banida kati" ta amsa a takaice.
"Yanzu da bakinki kika kirani ai."
"K'awata ce ta samin."
"Whatever come back home this instant kizo ki bud'e min gidana."
"Gidan biki fa nake."
"Allah yasa gidan mutuwa kike ki dawo Ruky bana wasa dake."
"Gaskia nikam da sakel wallahi."
"Zan sa6a miki kina jina? Wallahi na baki 20 minutes." Ding yayi hanging. Doguwar tsuka taja wane zata cire bakinta. "Allah

60 / 98