Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
ta samu ta had'iye kukan sannan tayi womaning up tace "ka shigo ciki Ya Al'ameen bari inyi wa Mama magana."
"Okay tana cike ne?" Ya tambaya yana bata full concentration nasa cike da dignity.
"Eh bismillah." Bayan ta yabi yana wasa da Ramlah dake ta faman shafa sajen fuskarsa tana cewa irin na Daddy na. A parlour tace ya zauna ita kuma tayo d'akinta inda ta d'au gyale ta yafa, har anan kaman jela Ummie keta binta. Kitchen ta nufa tare da d'auko masa ruwa da 5 alive ta kawo har gabansa ta ajiye. "Ai da kin bari Zainab."
"A'a Ya Al'ameen koban tambaya ba nasan daga tafiya kake" tayi maganan tana tsiyayar masa da juice d'in a cup.
"Toh nagode."
"Bari inyi wa Mama magana." Tana miqewa Ummie ma ta shiga bin bayanta, "Ummie bazaki bar Aunty Zainab ba kizo mu gaisa?"
"Ai Uncle Soldier kabal Ummie nima haka take min wataran kaman bata sanni ba nima sena shareta kawai, kaima ka shareta, ni kad'ai ma na isheka wasa." Kai kawai Zeezee ta kad'a sannan ta shiga ciki ta sanar da Mama dake fitowa daga bayi bayan tayi wanka.
"Allah sarki Maj-Gen. kice mai gani nan zuwa, kun gaisa ne ke?"
"A'a yanzu zanje mu gaisa."
"Yauwa jeki nima gani fitowa."
Back in the parlour ta tarar dashi da Ramlah se game take bugawa a wayansa tana zaune bisa cinyansa. Daga can nesa adjacent to him ta zauna tare da zaunar da Ummie a gefenta.
"Ina yini Ya Al'ameen?"
"Lafiya Zainab" ya d'ago kai yana kallonta. "Mun yini lafiya?"
"Lafiya k'alau ya gajiyan hanya da kuma aiki?"
"Alhamdulillah, ya mukaji da hak'uri Baba lokaci yayi."
"Alhamdulillah Baba Lokaci yayi."
"Toh Allah ya jik'anshi ya gafar ta mishi ya kuma kai rahma kabarinsa, our prayers are with him."
"Ameen ameen nagode Ya Al'ameen."
"What for? Sannun mu da hak'uri ko? Tun tuni nakeson shigowa wallahi but Allah be nufa ba, an kai mu Maiduguri saboda state of emergency shiyasa kuka jini shiru aiki yamin yawa. Da akayi rasuwan kuma I called you but bana samun ki, Mama tace bakida lafiya."
"Ayyah ba komai Ya Al'ameen ko yanzu da kazo ai bakayi latti ba, zuwan shine babba ai, da rasuwan nima banji dad'i bakam shiyasa."
"Ayya ya jikin toh yanzu?"
"Alhamdulillah da sauk'i sosai."
"Toh Masha All-" be gama maganan ba Mama tayi sallama tare da shigowa nan ya shiga neman sauk'owa daga kan kujerar don bata girma inda tayi saurin hanasa.
Gaisawa sukayi sosai inda yayi mata ta'aziyya itama yake kuma bata hak'uri na jinkirta zuwa ta'aziyyan da yayin, su Hajiya Mama duk suna gaishesu. Bayan gaisuwa yayi wa Baba addu'a sosai, seda Zeezee ta zubda k'walla se gani take kaman jiya-jiya Baba ya rasu.
"Mungode sosai Maj-Gen. Allah shi biya."
"Ameen Mama" d'ayan wayansa ya d'aga ya kira men nasan kan su shigo da drinks d'in. Carton na malts da other canned drinks ne har guda biyar ya kawo musu, sosai Mama tayi appreciating tayi kuma masa godiya haka Zeezee ma.
"Toh ni zan tafi Mama dawowa na kenan daga tafiya zuwa jibi haka nakega zan koma."
"Toh, toh a huta gajiya Maj-Gen mungode fa sosai ina zuwa." Nan ta koma ciki. Tun tun d'azu kallonsa Zeezee take ko kyafta ido bata iyawa tana ganin ze juya seta kawar da kanta haka ma yanzu, kallon Ummie dake zaune akan cinyarta yayi sannan yana murmushi yace "anya kuwa wannan ba 'yar Aunty Zainab bace Ramlah?" Murmushin dole ta k'irk'iro sannan
tace, "ba 'yata bace Ya Al'ameen."
"Kai ban yarda ba dan kin dace ki zama Maminta kyanku d'aya."
"Kai Ya Al'ameen 'yar sister na ne Mariam, dukansu biyu da Ramlah."
"Ayyah toh Allah ya raya mana su, ina namu toh?"
"Allah be kawo ba tukuna" ta amsa tana forcing out a smile.
"Toh Allah kawo rayayyu masu albarka."
"Ameen ameen."
"Ya mai gidan naki da kowa?"
"Alhamdulillah" kaman da tayi mai k'arya tace yana lafiya seta ga kuma ba amfani. "Na dawo gida ai yanzu." Sam be fahimci me take nufi da ta dawo gida ba yanzu, "baza a iya rabaki da gida ba Zainab, kin dawo yima Mama weekends kenan."
"A'a" ta kad'a kai "actually mun rabu dashi tun kafin rasuwan Baba ma." Ido ya kwararo waje da kyau yana sauraronta amman Adeel be kyauta mata ba, shi bayi ma tunanin kalan rashin kyautatawan da tayi masa, rashin kyautatawan da Adeel yayi wa Zeezee ne ke damunsa (see true love.)
"Subhanallah!" Sam beji dad'in hakan ba, she's of too tender age ace aurenta biyu duk babu no wonder ashe yaga tad'an zube not as before. "Allah rufa mana asiri toh."
"Ameen nagode." Tayi forcing out a smile "ya Madam kuma? From all seeing tana kula mana da kai."
"Haha" yad'an murmusa "toh gamu nan de, har yanzu ban sake..." sekuma yayi shiru da kaman yace mata yana shirye-shiryen sake aure se kuma ya fasa. Dukda be k'arisa zancen nasa ba Zeezee ta gane be sake aure ba yake nufi. Only this thought is driving her crazy.
*MIEMIEBEE. Team #YGC!π*
Beeenovels.blogspot.com
ππππππ
πππ πππ
πβ£π
β£β£
β’Β°β’β
β’Β°β’ β’Β°β’β
β’Β°β’
Β°β’ β’Β° Β°β’ β’Β°
Β°β’Β° Β°β’Β°
*βYAR GATA CE!*πΈπ»
β’Β°β’β
β’Β°β’
Β°β’ β’Β°
Β°β’Β°
*_written by miemiebeeπ_*
*Febraury, 2017*
5β£9β£
Toh kode ya fad'a mata ne? Shawara ya tsaya yi, dai-dai lokacin da ya yanke hukuncin gaya mata gaskia batun auren da ze sake yi a dai-dai lokacin ne Mama ke fitowa daga d'aki da alama ta koma tasa kaya ne. "Ahh barka baka tafi ba, ai na sha ma koka riga ka wuce."
"A'a Mama ina jiran fitowanki ne toh ni zan wuce." Yayi maganan yana miqewa da Ramlah a hannunsa.
"Ke kuwa Ramlah haka akeyiwa bak'o ne? Seki d'ale jikinsa haka." Cewar Mama da mamaki.
"A'a Mama bar jikar takin nan zan zo in d'auke ta ta kwana min ma."
"Dagaske Uncle Soldier?" Tayi maganan with zealous flavor.
"Ji wani suna wai Uncle Soldier" Mama tayi maganan tana dariya. Raka Al'ameen duka sukayi seda yayi dagaske Ramlah ta yarda ta sauk'a. 5k ya bata inda Mama tayi godiya sannan taja hannun Ramlah dake ta faman yiwa Al'ameen ba-bye shiko se biye mata yake, dana Ummie sukayi ciki.
"Toh Zainab zan wuce."
"Toh Ya Al'ameen ka huta gajiya mun gode."
"Ba komai" har an bud'e mai k'ofan mota ya kusan shiga Zeezee ta kirasa a nitse. A hankali ya juyo yana kallonta wani k'war jini taga ya sake mata all she wants is HIM.
Shiru tayi kuma ta kasa magana se kallonsa take "Zainab?" ya kira sunanta.
"Na'am." Ta amsa a hankali idonta a k'asa.
"Lafiya koh?" Takawa tayi seda ta matso d'an kusa dashi kad'an sannan ta soma da cewa;
"Ya Al'ameen don Allah kayi hak'uri ka yafemin rashin hankalin da nayi ta maka lokacin da nake gidanka, I want you to know that I've regretted every single thing I've done to you. Alhak'inka ba k'aramin bina yayi ba, please forgive me Ya Al'ameen am truly sorry." Totally speechless ya tsaya yana kallon Zeezee dama tana da hankali ta kuma iya tsara magana haka? this is where she is wrong saboda tun rananda ya sake ta ya yafe mata komi. Tausayi sosai Zeezee ta basa, he never wished for her life to turn out this way. Me take nufi da alhak'insa ya riga binta? Is that the reason why suka rabu da mijinta? Maltreating nata yayi tayi shine har ta zube ta rage haske haka? (Wai anan ma don be ganta time da ta fito sabo-sabo ba daga gidan Adeel.)
"Zainab..." ya kira sunanta finally cike da tausayi.
"Ya Al'ameen I know its hard for you to believe me but wallahi na tuba please forgive me ko I can be free nima."
"Zainab" ya sake kiran sunanta this time more slow.
"You can't forgive?" Hannu tasa ta share rolling tears nata, "I've asked too much huh? nasan abubuwan da na maka are unforgettably unforgivable ina me sake baka hak'uri Ya Al'ameen. Even though bazaka yafemin ba just know that I'm deeply sorry for the fact that I disrespected you as my husband, I can't ever be in peace har se in ka yafemin, thank you listening to me anyway." Tana kaiwa nan ta juya cikin kuka zata koma ciki. Da sauri ya rik'o hannunta restraining her, kasa juyawa ta kallesa tayi saboda yadda kuka yaci k'arfinta wanda ba mugun d'agawa Al'ameen hankali yake ba.
"Zainab" ya sake kiran sunanta a hankali. "Turn around kinji?" Sam ta kasa juyawan "turn around and look at me." Da k'yar ya samu ta juyan da water bags a idanunta.
"Look at me" ya buk'ace ta. Kai zallah take kad'a masa. "Look up kinji?" Instead ta kalle san se kallon hannunsa daya rik'e nata take. Da ya gano hakan se yayi sauri ya saketa "I'm sorry" ya fad'a calmly. Nan ma kai ta kad'a mai nufin its nothing.
"Zainab I'm sorry kinji? I'm sorry for what you've gone through. Ni na jima da yafe miki a very long time ago regarding dukkannin abubuwan da kikayi min fid duniya wal akhira, kinji?"
"Are you sure Ya Al'ameen?" Ta d'ago kai tana kallonsa a yayinda hawaye ke ambaliya akan kumatunta. "Ka yafemin duk abubuwan da na maka? All of it?"
"All of it Zainab." Hawayen jin dad'i ne kuma suka shiga tsiyaya daga idanunta. "Thank you, thank you Ya Al'ameen finally my mind can be at ease." Hannu ya mik'a a aljihunsa ya fito da hanky tare da mannawa akan cheeks nata yana share mata rolling tears natan a hankali. Duk anan binsa da kallo kawai take a yayinda wutan sonsa ke sake ruruwa a zuciyarta. She don't think akwai wanda ze iya gane mata just how much she loves Al'ameen. Seda ya gama share mata hawayen sannan ya d'aga hannunta ya sa mata hanky'n a ciki tare da kullewa da other hand nasa. "Don't cry again kinji? "Kai tamai nodding tana forcing out a smile. "Thank you Ya Al'ameen."
"Always welcomed Zainab, koma ciki kinji?" Be shiga mota ba se da yaga shigewar Zeezee ciki.
Zeezee na k'arisawa ciki ta ruga d'akinta a guje tare da wurga kanta bisa gado ta shiga rusa kuka. Hanky'n daya batan ta rungume tsam-tsam a daidai wajen zuciyarta tana kuka sosai. Tana cikin wannan kuka Mama da jikokinta suka shigo, tana ganinsu ta juya musu baya tana me cigaba da kukan.
"Granny mesa Aunty Zeezee ke kuka?" Cewar Ramlah.
"Ungo Ramlah rik'e hannun Ummie kuje kuyi wasa a parlour banda duka, ina zuwa."
"Toh Aunty Zeezee fah? Mesa take kuka?"
"Kuje ina zuwa." A hankali ta fito dasu Ramlah sannan ta koma ciki ta samu Zeezee.
"Zeezee kuma kukan meh haka kike a idon su Ramlah?" Banza da ita Zeezee.
"Keda Ya Al'ameen ne?"
"Mama I love him and I want to go back to him." Tayi maganan in between tears.
"Toh Zeezee kika sani ko ya sake wani auren?"
"Mama be sake ba he told me himself."
"Zeezee kin manta da labarin Maman shi da sister'n shi ne?" Ita Zeezee gabad'aya ma ta manta da rashin hankalin da tayi musu se yanzu da Mama tayi maganan su.
"Mama I'll call them each and ask for their forgivenesses I love Ya Al'ameen."
"Zeezee kina ganin yin hakan ba komai?"
"Mama bana son wata ta rigani auran Ya Al'ameen I can't take it."
"Toh nikam bansan me zance ba a irin wannan al'amari sekace Ya Al'ameen d'inne autan maza."
"Just pray for me Mama, its all I ask."
"Toh Zeezee."
"Thank you."
"Toh kibar kukan haka ya isa."***
Kwana zaune Zeezee tayi a daren ranan tana tunanin ya zata 6ullowa Al'ameen da wannan lamari, shi kam tasan mutum ne me sauk'in kai, problem d'in da za'a samu daga gun Mom nasa ne da sistersa Sadiya. Washegari Zeezee ta saci idon Mama ta d'au wayarta ta shiga contacts inda ta k'wak'ulo numban Mama Babba dana Hjy Sadeeyah ta zuba a wayarta. D'akinta ta koma inda seta soma dialing numban Mama Babba sekuma ta katse, tayi hakan kusan sau hud'u ana biyar ne tabari ya shiga inda tayi mata one missed call amman bata d'aga ba kasancewar bata kusa. Se a karo na biyu ta d'aga tare da yin sallama nan itama Zeezee ta amsa tare da gaisheta.
"Ina kwana Mama?"
"Lafiya k'alau" ta amsa ba fara'a sosai kasancewar bata gane wake maganan ba.
"Zainab ce Mama."
"Toh Zainab, Zainab wacce kenan 'yata?"
"Zainab ex wife na Ya Al'ameen."
"Aww Zeezee?"
"Eh Mama."
"Kina nan ashe, sannun toh Zeezee."
"Ina nan Mama."
"Ya hak'uri kuma? Baba lokaci yazo yayi, Allah ya jik'anshi da rahama ya cigaba da baku ikon juriya."
"Ameen ameen Mama nagode. Mama don Allah kiyi hak'uri regarding abinda nayi maki da Hjy Sadeeyah back then, I was young and stupid ku gafirceni don Allah na tuba bazan k'ara ba."
"Masha Allah, Zainab naji dad'i da har kika gano kuranki kika gyara sannan kuma kika nemeni musamman don jin yafiya na, I want you to know a matsayinki na 'yata na yafe miki kinji?"
"Alhamdulillah Mama, jazakillahu khairan. Naji dad'i sosai thank you so much Mama."
"Ba komai Zeezee ya mamanki?"
"Lafiyarta k'alau tana gaishe ki ma."
"Toh ina amsawa, ya mai gidan naki kuma?" Shiru Zeezee tayi tama kasa amsata "hello Zeezee?"
"Na'am Mama?"
"Ba ki jina ne? Nace yamai gidan naki?"
"Mama ina gida ne yanzu, auren nawa ya jima da mutuwa tun kafin Baba ya rasu. Wallahi hak'k'in Ya Al'ameen, da naku dana su Mama da Baba shi ya rink'a bina tabbas nayi nadaman duk wani abinda na aikata, rashin kyautatawa Ya Al'ameen dana rink'ayi shi na tarar a gidan Adeel, I hated myself for going against umarnin Baba and disrespecting you guys all, ina me sake baku hak'uri."
"Allah sarki Zeezee, we all learn from our mistakes ina fatan de bazaki sake tafka wannan mistake ba saboda shi mu'mini ba a sokinshi a rami biyu."
"In shaa Allahu Mama nagode."
"Ba komai, ina miki fatan Allah kawo miji na gari." Da k'yar ta iya cewa "ameen" a zatonta ma ko Mama Babba zata ce mata zata dawo da ita gidan Ya Al'ameen ne, amman ashe ba haka abin yake ba.
"Jiya ma Ya Al'ameen yazo nan har gida yayi mana ta'aziyyah."
"Ayyah Allah ya bada lada, yazo Bauchi duban abu ne kinsan ya kusa aure shima zamu aura masa wata 'yar uwarsa anan Kaduna." Dum! Zeezee taji zuciyarta ta buga sosai, she couldn't hold back the tears anymore, zuba kawai suka soma shikenan abinda take gudu ya riga ya faru, wata ta riga ta sa'an Ya Al'ameen. Just how bad ta cuci kanta a rayuwa? Da k'yar ta iya cewa "ayyah, Allah shi basu zaman lafiya."
"Ameen" Mama Babba ta amsa.
"Toh Mama se next time nagode ki gaishe dasu Aysha."
"Yauwa ki gaishe da Mamanki zasu ji" anan ta katse. Kuka me sauti sosai Zeezee ta rushe dashi a d'akin.
Bata bar kukanba har seda bacci 6arawo ya saceta. Koda Mama ta dawo daga islamiyyar safenta ta tarar da ita tana bacci bata kawo tunanin komi a ranta ba taja mata k'ofar. Se chan da Azahar tazo tada ita Sallah inda anan tayi noticing yadda idanun Zeezee suka kumbura.
"Lafiya da kumburarrun idanuwa haka Zeezee?" Kai zallah ta gyad'a tana k'ok'arin shiga bayi.
"A'a dawo nan, dawo ki zauna."
"Mama babu zanyi alwala ne."
"Nace ki dawo" bata sake gardama ba tazo ta zauna a gefenta.
"Kuka kikayi koba haka ba?" Batayi k'arya ba ta gyad'a kai.
"Dalili?"
"Mama..." sekuma tayi shiru.