Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
“Wallahi Alhj akwai-” katse ta yayi “seki nuna ai in akwan!”
“Laaa! Bade foundation kika shafa ba?” Mama tayi maganan tana murza hannun ta don gaskata abinda idonta ke fad’i mata. Jin haka Zeezee taja baya da wuri “Baba kaga Mama tana min sharri ba?”
“Karki kulata K’anwata jeki sa hijabi yau malamin ki ze fara zuwa.”
“Yau Baba?!” Tayi exclaiming.
“Eh Zeezee zaki fara karatu.”
“O’o ni bana so suna duka.”
“Wannan bare dake kiba” haka da k’yar ta amince 4:30PM malaminta ya iso tayi karatu tak’i tayita shiririta ita wai bataso. Haka rayuwan Zeezee ya cigaba da kasancewa har ta gama primary one rigimin yau daban na gobe daban ta gagari kowa a gidan.
Washegari da safe Baba yakai Zeezee asibitin ido kasancewar complaining da take, bayan an auna idon nata aka gano tana suffering from short-sightness take gun aka auna idonta aka bata eye glasses aiko Zeezee tace ita bataso ‘yan ajinsu zasu mata dariya kasancewar wani film data kalla UGLY BETTY.
Suna dawowa gida tacire glass d’in ita bataso da k’yar Baba yayi convincing nata ta miyar, Ibraheem da Mariam zaune suka tarar a tsakar gida kasancewar yau baida lectures da safe ita kuma Mariam ta gama makaranta tana jiran admission. Gani kawai sukayi Zeezee da glass se binta suke da kallo a yayinda take watsa musu harara ganin sun kusan shiga ciki yayyun nata basuyi mata glass yayi kyau ba tasa kuka “ya haka kuma? keda waye?” Baba ya tambayeta.
“Su Ya Ibraheem basu cemin glass d’ina yayi kyau ba ni banaso” tasake sa ihu har seda Mama dake ciki tafito.
“Har kun dawo ne? Ya Zeezee da glass haka? Idon bai gani ne?” Ta tambaya, nan Baba yayi mata bayanin komai “ayya auta ta Allah baki lafiya” maimakon Zeezee tace ameen seta kuma rushewa da sabon kuka “toh ni kuma menace?”
“Bakice min yayi kyau ba ni banaso.”
“Haba! Kin ganki kuwa? Dr. kawai, Dr. Zainab.”
“Su Ya Ibraheem basu ce min yayi kyau ba.”
“Barsu, bara ku ce mata yayi kyau bane? Sam baku iya zama da k’annenku ba” Baba yayi scolding nasu, da k’yar Mariam ta iya shanye dariyan ta “yayi kyau” suka fad’a in unison.
“Aikin banza kawai mu shiga ciki K’anwata” haka koda su Omar suka dawo suma basu cemata glass nata yayi kyau ba tayita kukan banza.
~* ~* ~*
The following day as always da k’yar aka samu aka shirya Zeezee, k’iriniyarta ta yau tafi ta kowani rana sabida Baba baya gida, tun fitan sa sallan Asubah be dawo ba da alama wa’azi ya rik’e shi. Bayan an gama shiryata Mama ta feffesheta da turare sannan ta wuce gaban dressing mirror dan d’auko wa Zeezee eye glasses nata wayam! Ta duba gun da ta ajiye jiya babu ta tambayi kowa a gidan duk sukace basu gani ba, nan fa aka shiga neman glass na Zeezee ana cikin haka dai-dai 7:08AM kenan Baba ya dawo gida “hope kun gama shiri, oya kufito mu tafi.”
“Alhj ko kaga eye glasses na Zeezee?” Mama tayi tambayar tana duban cikin wardrobe nata.
“Ba gaban mirror kika ajiye jiya ba?”
“Toh gashi babu ba inda ban duba ba duk babu.”
“Kamar ya babu Hafsah? So kike kicemin glasses d’in yayi k’afa ko meh? Ni wallahi bana son carelessness yanzu ya kikeson taje makarantar?”
“Alhj ji yadda kake magana kaman da gan-gan nayi misplacing ni wallahi am certain agaban mirror na ajiye.”
“Seki d’auka ai in achan d’in kika ajiye.” Bin Zeezeen dake zaune kan gado Mama tayi da kallo tace, “Ke ina kika kai glasses nakin?”
“Aww yanzu kuma sharri zakiyi mata? Kuma ban hanaki ce mata ‘Ke’ ba?”
“Ai tasan me nake nufi ina kika kai glasses d’in?”
“Ni ban d’auka ba, Baba kaga Mama koh?”
“Barta K’anwata zo abinki.”
“Ai tun jiya take cewa batason glass d’in ba tantama ita ta d’auka ta b’oye.”
“Kede kice kinason mata sharri kawai K’anwata ke kika d’auka?”
“A’a” ta kad’a kai.
“Tsakanin ki da wa?” Baba ya tambayeta, Shiruu Zeezee bata ce komai ba “Zeezee ke kika b’oye wai?”
“Dagaske bani bane Baba.”
“Za kiyi wa Baba k’arya?” Kai ta kad’a “to gayamun ina glasses nakin yake?” Baki ta turo “ni banaso.”
“Bakiji me Dr. yace bane Zeezee? Idon ki na ciwo only if kina sawa idon zasu gyaru ko kinaso ki tsufa ba ido?”
“O’o”
“Good then you must wear your glasses temporarily kinji? Yi hak’uri kije ki d’auko min.” Zatayi magana Baba yayi saurin katse ta “shhh! And je ki d’auko min” haka ba yadda ta iya tabi Mama da dirty look sannan ta fice babban parlour inda ta b’oye glasses d’in in between cushion na 3 seater tasa hannu ta zaro ta kaiwa Baba yasa mata da kansa sannan suka fice se kumbure-kumbure take a motan haka har suka isa school.
AT SCHOOL...
Kap ‘yan ajin su Zeezee se binta suke da kallo ganinta da sukayi da eye glasses wanda ba k’aramin ci mata rai yake ba, ji take kamar ta cire glasses d’in ta b’oye.
Ana fita break Zeezee ta tarke yarinya a lungu tayi mata dukan tsiya itama de ta bugu sede ba kamar yadda ta daki yarinyan ba agarin haka ta samu cizo babba a hannunta. Suna cikin damben Allah ya kawo teacher wucewa nan da nan ya rabasu akayi dasu admin block, tsawata musu sosai headmaster yayi sannan ya kira iyayensu sam Baba yak’i yarda da aka cemai wai Zeezee tayi fad’a a school ashe de ba k’arya ba Mama kemai ba last time data ce masa Zeezee tana fad’a a school. Hak’uri sosai Baba da parent na d’ayan yarinyan suka tayi ta bawa headmaster d’in in bahaka ba yace sam se an basu punishment na picking after every school day for the whole week. Bayan an samu an shawo kan komi Baba yayi godiya yaja hannun Zeezee suka fice “haba K’anwata wani irin hali ne haka na fad’a school? Bafa haka takwararki take ba.”
“Toh Baba kasan me tamin ne?”
“Koda me ta miki be kamata ki tuhumeta da dambe ba, kai k’aranta zakiyi wa form teacher’nku.”
“Kai k’ara Baba ai se ‘yan class namu sumin dariya ni ta sake kallo na wallahi dukanta zanyi.”
“Aww bazakiji maganan Baba ba kenan? Inda kuma yanzu kin ji mata babban ciwo ko kin fasa mata kai fah?” Shiru tayi batace komi ba har suka isa gida, isarsu ta fito ita kad’anta Baba na binta da jakanta da lunch pack suna shiga ciki sukayi karo da Mama tana kwashe kayan shanya kan igiya sannu da zuwa ta musu data lura da yadda Zeezee ke cinno k’aramin bakinta tagano da akwai matsala. “Mekuma ya faru yau? Alhj ko kunyi fad’a ne?” Kan wanda bazeyi magana ba yace;
“Ke yanzu da zaran na fad’a miki meya faru seki hau cewa ai dama na gaya maka” Baba na maganan Mama kuwa na bin Zeezee da kallo nan ta hango babban shatin cizon dake hannun damanta.
“Hohoho dambe ma tayi yau a school kenan, no wonder ka fita d’auko ta yau da wuri halan ma har headmaster’s office aka kaita ko? Ko sunsa sunanta a black list?”
“Ke da Allah bakin ya isa haka ba sunanta da aka sa a balck list.”
“Me za’a fasa dama mutuwa ko hisabi? Mena gaya maka kwanaki? Ai wallahi kad’an ka gani wataran seta fasa ma wata kai a school a kaiku duka police station anan ne zakuyi hankali.”
“Toh ya isa da Allah muguwa kawai abinda dama kika iya kenan baki wa mutane instead kijata kiyi mata nasiha kina cewa har station se an kaita to tare zakuje kiji in gaya miki.”
“Ai ba nasihar da zan mata kanku akeji tunda cikin sauran ‘ya‘ya na k’waya hud’u ba wanda aka tab’a kawo min k’ararsa yana fad’a a school dan anyi akan Zeezee se meh? Kai ka lalata mata tarbiyyarta saboda haka ba abinda zance mata kai d’in daka b’ata seka gyara” tana kaiwa nan ta gama sauk’e kayakin daga igiya tayi ficewarta.
_Wednesday afternoon, 2:35PM_
Chess of drawer’n Mama wanda ake adana mata socks nata ta fito dasu, sanye take da black english wear kanta a tsefe an kamasa sakwa-sakwa. A dai-dai tsakar gida ta ajiye sannan ta d’ago new pair of socks tasa ta tattara teddy bears nata ta jerasu kan table da bulala rik’e hannunta wai tana musu lesson. Mama na gama cin abinci tafito kai plate kitchen ta tarar da Zeezee da socks tana yawo tsakar gida “haba! Zeezee wani irin sabon salon iskanci ne wannan? An tab’a sa farin socks a gida ne? Bana school bane?”
“Ni ki banni ai ba naki bane nawa ne.”
“Oya maza cire socks d’in ki mayar”
“O’o” ta fad’a stubbornly, idanun Mama na sauk’a kan drawern ta da Zeezee tayi wurgi dashi tsakar gidan ta fusata, kanta tanufa ta nad’a mata na jaki ta kuma sata ta miyar da drawer’n ciki, kuka Zeezee tayi tayi har seda Baba yadawo as always ya bata gaskiya ya yita balbale Mama yana ikirarin ze soma jan Allah ya isa next time ta sake tab’a masa Zeezee’nsa.
★★★★★
Days, months and even years passed by Zeezee nada eleven (11) years yanzu tana matakin Jss 1 a LYS still, yarinya a kullum dad’a kyau take ga tsawo masha Allah bata da wani kauri ‘yar slim to fashion take. Yasmeen kuwa nada seventeen (17) years last year ta gama makaranta tana jiran admission a ATBU into physics education. Omar kuwa is twenty and half (20½) years old an zama saurayi se rawan kai yana ATBU shima studying computer engineering. Mariam kam ma preparation na bikinta ake she is twenty-two (22) years old, last year tayi graduating daga ATBU in microbiology, bikin ta bayan babban sallah in Allah ya yarda. Ibraheem yaya babba kuwa is now twenty-four (24) years old, two (2) years back yayi graduating from ATBU in Petrochemical engineering (course d’in manya!) Saurayi son kowa k’in wanda ya rasa yayi service nasa yanzu haka ya fara aiki a NNPC, kud’i yake samu sosai har ya sai motarsa k’irar Honda Anaconda new model.
*ZEEZEE...*
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 13
_I’ve recieved your message *Khadija Shehu Musa* and I want to thank you in person for the love and support, ILY too💕 this page is dedicated to YOU #OneLove_
_*A/N*_
_Assalamu Alaikum everyone, I usually don’t say a thing on matters like this but I think its high time I do now, ku sani your negative comments will never stop me from continuing with what I’ve started. Na farko dana fara rubutun nan ba wacce na cukume mata kwalar riga ko bakin zani nace dole seta karanta min littafi in kinga bazaki iya karantawa ba fine quit it there are thousand of books out there sekije ki karantasu amman kam BAZAN TAB’A TSARIN RUBUTA NA BA saboda tun farko dana fara bada idea'n wata na fara ba dan haka dan ke ko ita bazan canza tsarin labarina ba wacce taga bata k'aruwa dashi walillahil hamd seta bar karantawa. Duk me hankalin da ya zauna yasan akwai babban darasi cikin wannan littafin saboda dole ILLAN GATA ze biyo baya, ku baku tsaya kunga k'arshen littafi naba kuna judging d’ina, phew!😅. Masu cewa wai zagin Mama da Zeezee takeyi is too much inku baku tab'a ji ko gani ba toni nagani da idanu na inda 'ya ke zagin uwa infact abinda ke faruwa mostly kenan a rayumar ta yau and dole agyara kokuwa muna tare da babban hatsari. Ni ba anyhow nake rubutu ba duk books d'ina akwai life lessons ciki kamar yadda wannan ma darusan suna nan fitowa one-by-one wanda already wasu masu tunanin har sun fara gano hakan. I just want to tell y'all masu cewa littafi na baida direction su sani cewa reading is not by force kamar yanda ban saki karantawa ba seki bari dan kanki tunda yana b'ata miki rai ba dole a duniya. Fans dina masu sona kuma thanks y'all for the support, I LOVE YOU ALL, INA TARE DA KU!_
***********
Tsaye take a tsakiyan d’akinta tana sanye da blue vest meh crossed arms seda ¾ black leggings, kanta kitson shade biyu ne wanda ta kama k’arshen da ribbon jaa da alama neman abu take bata gani ba danko gabad’aya d’akin nata upside down yake, d’aki ne me kyan gaske komi cikinsa combination na dark and light pink ne ba’a cewa komai sede masha Allah, dogon tsuka taja sannan ta d’au laptop nata ta fice daga d’akin a fusace tana k’walla wa Baaba meh aikinsu kira “Baaba! Baaba! Baaba!”
“Na’am” dattijuwar ta amsa tare da katse sharan da take.
“Ina kika kaimin USB na?”
“Meh kuma USB Zeezee ban tab’a kominki ba, d’akin naki kawai na share.”
“Bawanin nan kullum sede baki shiga min d’aki ba se na rasa abuna ni wallahi bana so kije ki d’au min USB na kawai” ana cikin haka Mama ta shigo parlour’n “ya haka Zeezee mawa kike d’agawa murya haka?”
“Ma Baaba haka kawai kullum tayita canza min position na abubuwa na ni banaso abanza ta b’atar min da USB yanzu.”
“Bakida hankali ne? Baaban kike cewa haka? Batayi jika dake bane?”
“Wannan kuma ku ya dama nide kar a sake tab’a min abu na, ina wayana in kira Baba ya sai min sabo” ta k’are maganan dai-dai ta shiga d’akinta ta musu banging k’ofar. Binta Mama tayi da kallo sannan ta kad’a kai “yi hak’uri Baaba kinsan halin Zeezee addu’a kawai zamuyi mata.”
“Ba komai Maman Zeezee ai yarinya ce.”
“Kuma daga yau karki sake share mata d’akin, tunda da kin share se tace abinta ya b’ata.”
“Maman Zeezee beyi zafi haka ba.”
“A’a Baaba karki sake ni na fad’a miki.”
_Back in Zeezee’s room..._
“Hello Baba?” Tayi maganan a shagwabance.
“K’anwata ya haka? Meya sameki?”
“Baaba ce” tayi stating almost like crying.
“Me tayi miki kuma?”
“Ta b’atar min da USB na.”
“Shine abin damuwan? Bari yanzu zan aika Omar ya siyo miki kinji?”
“Toh yaje yanzu.”
“Angama K’anwata shikenan?”
“Eh shikenan nagode” tayi hanging. Data connection ta bud’e ta hau whatsapp, group nasu na LYS STARS ta shiga tana glimpsing chats d’in data gama taje kan contact na Lubiee tayi mata sending;
_‘Yan mata kinsan yau kika ce zakizo koh? I will be waiting for you_.
Kafin ta sauk’a Lubiee ta hau tayi replying nata back;
_Ina tuni Babe, Ya Salman nake jira by 3 in shaa Allah zan iso akwai gist fah, Ahmed yace yana son Lailan Jss 1B se nazo deh!_ Zeezee na gama karantawa tayi replying nata;
_Sekin iso I can’t wait_ nan ta kashe datan ta had’a wayarta chargy ta baro d’akin.
*
~* ~* ~*
“Ya haka kana tsaki kai kad’ai?” Ibraheem dake sake da headphone akansa amman ba komi yakeji ba ya jefa wa d’an uwansa Omar tambaya.
“Mschw! Wannan Baba da Zeezee mana wai inbar duk abinda nake inje in siyo mata USB tayi misplacing nata.”
“Shine abin tsakin? Sekace sabon abu, yaci ace ka saba ai yanzu”
“Ai dole kace haka saboda kaga kai babba ne yanzu ana isolating naka a matters haka wallahi yarinyan nan b’ab’b’ala ta zan mschww!”
“Wai ina Ya Omar ne beje ya siyo min USB’n bane? Inafa so inyi amfani dashi” Zeezee tayi maganan tana shiga d’akinsu Omar.
“Ke ban hanaki yawo cikin gidan nan da vest da ¾ leggings ba? Ce miki akayi gidan arna ne? Maza wuce kije kisa kaya” Ibraheem yayi scolding nata.
“Haaa’a! Jimin mutum, nikam ka barni sekace wani Babana ka tsaya kana wani gaya min abinda zanyi bale ma ni ban maka magana ba kowa yayi harkan gabansa, Ya Omar USB na” ta miqa hannu nufin ya sa mata.
“Ni kike gayawa magana?” Ibraheem yayi maganar a fusace tare da mik’ewa, ganin haka tasa gudu amman ina taku d’aya yayi ya cafko hannunta “wayyo Allah Baba na kayi hak’uri, wallahi bada kai nake ba dan Allah karka tab’ani na tuba.” rank’washi me d’ankaren zafi ya danna mata akai “waye sa’anki anan?” Tana kuka tace, “wallahi babu duk kun girmen kayi hak’uri dan Allah.”
“Shegiya me kan kwa-kwa kawai ki sake min rashin kunya kiga abinda zan miki” ya turata seda ta fad’i, harara ta watsa masa ganin bai ganinta “mugu kawai” ta fad’i chan k’asa k’asa yadda ita kad’ai taji me ta fad’an, miqewa tayi a wahalance ta takai bakin k’ofa tace, “mugu kawai da wani farin fuska kaman k’osai Allah ze sak’a min kai kuma Omar kaje ka siyomin USB na” tana kaiwa nan tasa gudu binta Ibraheem yayi a guje se bayan Mama taje ta lab’e, “meh haka? Sakeni nikam! Kije kiyi rashin kunya kizo kina b’uya min a baya, sakeni!”
“Wallahi Mama yarinyan nan ta kiyaye ni.” Ibraheem yayi maganan yana nunata da yatsa.
“Ai kazo ka d’auke ta ka mata duk abinda kaga ya dace shegen rashin kunya ne da ita.” Jin haka Zeezee ta sake dandame jikinta a na Mama tana ihu dan kanta Mama tabawa Ibraheem hak’uri ya fice, “wallahi Zeezee ki sake kibar halin nan naki kin mai da manyan yayyun ki tamkar kece babba bakijin tsoron idonsu?”
“Nikam da Allah! kullum sede kita