Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
Anan ne Mama ke sanar dashi halin da Zeezee ke ciki. Sosai masoyin hak'ik'an ya sake tausayawa Zeezee. If only there's something he could do.
Abu fa kaman wasa se worsening condition na Zeezee ke tayi, se kaman neman zarewa take ne oho, abun kaman hauka. In anji sautin muryarta toh tana kuka ne. Magana ma tabar yi, ko bayi takeji in bawai anyi timing nata bane an kaita sede tayi a jikinta, cin abinci, sallah komi nata ya tsaya kat! Abu kaman wasa-wasa har akayi sadak'an bakwai Zeezee bata san inda take ba gata nan ne kawai se yadda akayi da ita. Bayan sadak'an bakwai ne lokacin da mutane suka gama watsewa, wanda suka rage befi a k'irga ba. Se a nan ne hankalin Mama da sauran yaranta ya dawo jikinsu akayi wur-wur aka d'auko Zeezee daga gidan Mrs Mukhtar aka kaita asibiti. Bayan dogon nazari da bincike da Dr yayi ya nuna musu cewa ba abu neba na damuwa saboda hakan is normal ga duk wanda mutuwa ya ta6a sa sosai, she is psychologically and even mentally affected at her own case, but in shaa Allah bayan d'an wani lokaci she'll be back to normal. Wanda kafin nan ya zama dole a kullum ana karanta mata labarai masu dad'i masu sanya nishad'i dakuma kaita leisure places saboda yayi erasing bad memory'n dake lingering akanta na cewa ita ta kashe mahafinta. Har izuwa ga wannan lokaci kuwa koda wasa kar a mata furucin da bashida dad'i. A haka ne su Ibraheem suka dawo da ita. The next day Ibraheem da iyalansa harma da Yasmeen suka juya, inda suka ajiyeta a KD sannan suka zarce Abj. Mutuwan Baba har a yau kaman sabo yake a memory'nsu, they shall never forget about their beloved father.
*MIEMIEBEE. Team #YGC!*
Beeenovels.blogspot.com
πππππππ
πππ πππ
πβ£π
β£β£
β’Β°β’β
β’Β°β’ β’Β°β’β
β’Β°β’
Β°β’ β’Β° Β°β’ β’Β°
Β°β’Β° Β°β’Β°
*βYAR GATA CE!*πΈπ»
β’Β°β’β
β’Β°β’
Β°β’ β’Β°
Β°β’Β°
*_written by miemiebeeπ_*
*Febraury, 2017*
5β£3β£
Sabuwar rayuwa kowa kuma ya soma living, as for Mama ta shiga zaman takabarta inda take kuma kula da Zeezee, kwana ma tare suke yanzu, don kuwa har yanzu ba wani progress da aka samu game da condition nata. Mama keyi mata komi, da yamma wajajen 5:00pm kuma bayan Omar ya huta from office seya kaita waje zuwa wajen shak'atawa susha iska inda zeyita karanta mata stories. Itama Mama anytime she is less busy tana k'ok'arin karantowa Zeezee stories.
Anyi haka na kusan sati biyu da 'yan kwanaki Zeezee ta soma magana wanda da kalman 'Baba' ta bud'e bakinta. Mama ta ajiye ta kan couch a d'akinta tana shirya wardrobe nata ta tajiyo muryan Zeezee da she can't remember when last ta jisa. Da gudu ta nufi wurinta tare da riqo hannayenta sede Zeezee tayi saurin wabje su.
"Baba" ta sake nanatawa.
"Zeezee? Mama ce ba Baba ba kinji?" Bayan data k'are wa Mama kallo na kusan mintuna biyu se kuma ta miyar da kallonta kan hannunta da take gani jinin Baba ne akai.
"Baba" ta sake furtawa. Hannun nata Mama ta rufe da nata, "ba Baba anan kinji? Hannunki ne wannan."
"Kefa wacece ce? Leave me alone please, Baba! Baba!"
"Mama ce Zeezee baki gane ni ba?"
"Mama? Nasan kine? Ni Baba nakeso, ina yake?" Zuciyarta taji ya sake karyewa jin wannan kalamu daga bakin 'yarta, kamar ya Zeezee bata gane taba? How is that even possible? Danne zuciyarta tayi ta amsata;
"Baba yayi tafiya kinji?" Tayi maganan kuka na neman ku6uce mata wanda da k'yar ta samu ta had'iye.
"Ina yaje? Kice mishi ya dawo shi nakeso ba ke ba."
"Inda ya tafi ba a dawowa Zeezee, duk wanda ya tafi ya tafi kenan ba dawowa."
"Ina son in bisa nima ki kaini gunshi."
"When your time comes zaki bisa kema kinji? In kaiki bayi kiyi alwala kiyi sallah?"
"Sallah? Meshi kuma? Ni Baba nakeso." Sosai Mama tasake shan mamaki. Me hakan ke nufi? Zeezee ta mance da kowa da komai kenan? Omar ta kira ta gwada tambayan Zeezee waye shi inda ta nuna musu bata san shi bama at all shima. Cike da tashin hankali Mama ta kira Dr tayi mai bayanin komi, "calm down Ma'am I think she must have lost her memories-" katse sa tayi saurin yi da "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Dr memories fa kace? Kana nufin bata san kowa ba kenan yanzu?"
"Yes but fatan mu Allah yasa temporarily ne ba permanent ba."
"Innalillahi! Yanzu in kuma permanent d'in ne fa?"
"I'm sorry but it'll take morethan a year kafin ta sake ganeku but inhar temporary ne within months zata tuna komi. You can only make this possible by staying close to her always, karki ta6a barinta ita kad'ai. Kuma never give up from making her happy, duk abinda takeso kina yimata kina tuna mata da ko ke wacece, in shaa Allah as time passes by she'll get back her memory."
"Toh Dr data ce ko Sallah bata sani bafa?"
"Komi ai yanzu ta mance dashi, her memory is as fresh as that of a baby."
"Ya Salam!" Ta furta a hankali.
"Ku cigaba da sata a addu'a in shaa Allah she'll be back to normal."
"I pray so Dr, thank you."
"In 3 weeks time call me back muga in har akwai improvement."
"I'll Dr thank you."
"You're welcome." Kai zallah ta kad'awa Omar daya saurari wayan da sukayin. "In shaa Allah zata warke Mama don't give up hope." Ya fad'a soothingly.
"I pray so Omar, dududu da rasuwan mahaifinku sati nawa ne wannan masifa ze sake afka mana."
"Subhanallah! Mama kisani Allah baya d'aura wa bawansa musibar da baze iya d'aukawa, muyi tawakalli kawai."
"In shaa Allah Omar thanks for the reminder." Nodding kai kawai ya mata sannan a tare suka dawo da kallonsu kan Zeezee dake ta faman kallon hannunta.
"Zeezee?" Mama ta kirata soothingly amman ko d'aga kai ta kalleta Zeezee batayi ba se a karo na uku. "Zaki ci abinci Mama na?" Kallon Mama kawai take totally lost.
"Abinci, zaki ci? Kina jin yunwa?" Har anan kallonta Zeezee kawai take. Suratai ba wanda Mama batayi ba wanda ciki ba wanda Zeezee ta amsa. Kuka ta soma without knowing how, "Omar tabar maganan kuma again.
Ina zan sa kaina?" Hugging nata Omar yayi yana tapping bayanta. "Shhh! Have faith zata samu sauk'i bi izinillah." Da k'yar ya samu ya fito da Mama daga d'akin yaje ya tsuguna gaban Zeezee dake ta kallonsa shima, se gani take kaman ta sansa. Badon komi ba kuma illa don kaman da Omar da sauran yaran suke ne da Baba, dama chan Zeezee ce kad'ai me kamannin Mama. Hannunta ta aza a hankali akan fuskarsa tana shafawa a hankali. "Baba?" Ta kirashi.
Kai ya kad'a mata yana murmushi, "Suna na Omar am your big brother ba Baba bane, Omar suna na."
"Omar? Toh ina Baba?"
"Yayi tafiya, mesa kika k'i yi wa Mama magana?"
"Wace Mama?"
"Farar matar data fita yanzu."
"Ni ban santa ba."
"Ni kin sanni? Kin gane ni?"
"Ba kai bane Baba?"
"I'm Omar, Ya Omar remember me?"
"No kaine Baba, ashe ba jinin ka anan" ta nuna mai hannunta. "Babu" ya fad'a yana mata murmushi, "hannunki ne ba komai kinji?"
"Naji Baba." Kaman ya sake ce mata shifa ba Baba bane sekuma yaga ba amfani.
"Zaki ci abinci?" Kallonsa ta tsaya yi nufin bata fahimta ba. "Yunwa" yayi pointing cikinsa "zakici abinci?" Yayi tambayan yana immitating da body movement. Kai ta gyad'a masa nufin yes.
"Toh bari inyi ma Mama magana ta kawo miki." Da wuri ta kama hannunsa ta rik'e "ni o'o kai nakeso."
"Ga Mama zata sa miki." Kafad'a ta buga "yi hak'uri Baba ni kai nakeso."
"Toh naji sakeni ina zuwa."
"Zaka sake tafiya ka barni?"
"Ai ban ta6a tafiya na barki ba Zeezee" ganin kalamunsa na neman dak'ula mata lisafi yace, "tashi toh muje" haka tana rik'e da kayansa suka k'arisa kitchen yasa mata abincin, tabari Mama tayi feeding nata ma bataso, sam in taga Mama se tayi as if bata magana. Bayan ta gama cin abincin yace da ita "sauran Sallah ko?"
"Me ma Sallan nanne?"
"Kin manta Sallah Zeezee?"
"Eh Baba mesa baka cemin K'anwata yanzu?" Allah sarki seya tuna da Baba, murmushin dole ya k'irk'iro sannan yace, "toh K'anwata sauran Sallah ba?"
"Baka fad'amin ba meh shi Sallan ba ai."
"Sallan da yazama wajibi akan kowani musulmi da zaran ya mallaki hankalinsa, wanda ake yinsa 5 times daily, Subh, Zuhr, Asr, Maghrib-"
"And Isha!" tayi saurin katse sa.
"Excellent" dad'i sosai yaji ganin memory loss nata beyi affecting educational stuffs nata ba. "Kin tuna shi?"
"Eh Baba na tuna."
"Good tashi toh kije kiyi alwala." Nan ma tace batasan me alwala ba seda yayi ta mata kwatance sannan ta soma tunawa, yana alwala tanayi har suka idar sannan yayi mata shimfid'a tare da d'auko mata hijabi.
"Raka'ah nawa zanyi toh Baba?"
"Yanzu kinga tunda kika fara rashin lafiyarki baki samu dama kinyi Sallah ko sau d'aya ba, Sallah kuwa idan ba mutuwa ba ba'a yimai uzuri so yanzu zakiyi La'asr raka'a hud'u-hud'u sau biyu, haka zaki cigaba dayi duk Sallan da zakiyi sekina yinsu bibbiyu zuwa nawani tsawon lokaci, innallaha gafurur raheem."
"Toh Baba" ta fad'a ba musu. Yana zaune agun har ta idar. Da Maghrib ya shirya zasa Masjid nan ta tukuikuiye mai kaya ita karya fita ya barta, ya kaita gun Mama kuma tak'i.
"Toh kinga idan baki bari na kaiki gun Mama ba zan tafi bazan sake dawowa ba."
"A'a Baba please karka ce haka nayi al'kawari bazan sake sa6awa umarnin kaba."
"Good girl tashi muje wajen Mama toh, ba abinda zata miki actually tana sonki ma sosai, bakiga kuna kama ba?"
"Kama a ina?" Ta tambaya. Tuna halan ma fa yanzu batasan kamanninta ba yasa yace, "bari idan na dawo daga Masjid yanzu tashi in kaiki gun Mama."
"Baba kace bazata min komi bako?"
"Eh K'anwata tashi muje." A nitse ya kaita gun Mama tare da umurtanta da tayi alwala tayi Sallah.
Tana idar da Sallan Mama ta juya ta kalleta "har kin idar Mamana?" Shiru tayi not ready to talk. Danne zuciyarta tayi tace _"kin ta6a jin inda uwa tak'i 'ya'yanta ne? Kisani Zainab kome kikayi min ina sonki saboda ni kad'ai nasan zafin haihuwarki."_ Take Zeezee ta juya tana yima Mama wani irin kallo as if though trying to remember something. Toh aina nasan wannan matar? Ta tambayi kanta.
Dawowan Omar yaje ya d'auko family album nasu tare da ajiyewa gaban Zeezee dake mak'e a jikinsa. Picture'nta da Mama su kad'ai ya zaro ya miqa mata "wace wannan?" Ya tambayeta yana nuna mata kanta. Kai ta kad'a alaman bata san wace ba, "wannan fa?" Ya nuna kan Mama. Kai ta d'ago tana kallon Mama sannan tace, "itace Matar da kake kira da Mama ko?"
"Exactly" hannu ya miqa kan dressing mirror tare da d'ago k'aramar mirror ya bata don kallon face nata "laaa! Wannan ba itace na hoton nan ba Baba?"
"Kinga kuna kama ko? Toh ai kece wannan d'in."
"Kana nufin nice a hoton nan da kuma madubin?" Kallon kanta ta sakeyi a mirror'n sannan back to the picture, tafa tabbatar itance but how comes? "Taya muke kama da ita toh?"
"Bari kiga" ya amsa ta. Allah sarki hotonsa da Baba ya ciro ya ajiye mata, "su waye wannan?" Kallon pic d'in take bewildering, ga wanda de take ce mai Baba nan amman kuma k'wak'walwarta na soma ce mata babba na hoton ne asalin Baban nata. Wani irin sara da juyi kanta ya shiga yi mata wanda da wuri Mama ta kar6e album d'in gudun kar ya haifar mata da something bad. Rufe idonta da tayi kawai se bacci, sallan isha da k'yar Omar yasata a gaba tayi ta sake komawa baccin. Da wai sam ita a d'akinsa zata kwana seda yayi dagaske ta yarda zata kwana da Mama.
Banda mafarke-mafarken Mama data yitayi ba abinda ta tsinana a baccin, se raya mata mind nata ke tasan Mama.
Haka a hankali a hankali Omar ke flashing wa Zeezee da old memories nata back har tazo ta gane ba shine babanta ba, toh ina Babanta yaje? Ta fannin Mama kuwa, ta soma sakewa da Mama ganin how free they are da Omar, a kullum idan suna zaune da Mama ba abinda take banda flashing mata back memories nata cikin ikon Allah Zeezee ta soma tuna Mama da sauran 'yan uwanta anan ta gane Omar ma ashe yayanta ne. Duk hakan yafaru ne within 3 weeks da Dr ya fad'a.
Yau tana zaune a parlour ita kad'ai chan Mama ta shigo d'aukan ruwa, binta da kallo Zeezee tayi seda tazo gab da fita ta furta "Mama" a hankali. Wani dad'i sosai Mama taji wanda ta kasa 6oyewa seda ta zubda k'walla.
"Mama, kece?" Ta tambaya Tana kallon cikin idanunta.
"Nice Mama na, Mama ce Zeezee" da gudu Zeezee ta miqe taje tayi hugging Mama tana kuka sosai, itama haka Maman.
"I love you Mama, I love you so much."
"Ya Allah thanks for bringing back my daughter for me, I love you more sweetheart."
"Ina Ya Ibraheem, Mariam, Omar and Yasmeen?"
"Duk suna nan kina son musu magana?"
"Eh Mama amman kafin nan ina Baba?"
"Kin manta inda Baba yaje Zeezee?"
"Wai yayi tafiya inji Ya Omar amman k'arya ne ko?" Kai Mama ta gyad'a mata a hankali.
"Tell me ina yake toh?" Chan k'asa-k'asa tace;
"kin manta Baba lokaci yayi?"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Take idanunta suka sake kad'awa, "Mama yanzu Baba ya tafi ban nemi tubansa ba kenan? Baze sake dawowa ba?"
"Zeezee Baba ya yafe miki" hak
kalamun da Baba yace ta fad'awa Zeezee Mama ta sake nanata mata su "kinji? Ya yafe miki for a very long time now."
"Mama ba k'arya kike min bako?" Ta tambaya tana hawaye.
"Taya zan miki k'arya Zeezee? Babanki ya yafe miki komi, he asked me to tell you in person and that he misses being with you."
"Nima na yafe masa Mama, I miss him so much" tasa kuka. "Shhh!" Mama tayi hugging nata "he is in a better place in shaa Allah." Kuka Zeezee ta shiga yi sosai, da k'yar Mama ta samu ta sata tayi shiru sannan tayi waya ta had'ata da Ibraheem. Sosai Ibraheem yaji dad'in having his little sister back. Tubansa Zeezee ta nema inda ya nuna mata ya yafe mata for a very long time now, haka Mariam and Yasmeen ma.
Getting to 4 Omar ya dawo from work, tun a bakin k'ofa Zeezee ke jiransa. Tana ganinsa ta mai oyoyo shima tare da neman tubansa, he can't ask for more his little sister is back. Dr, Mama ta kira ta sanar dashi this great news.
"Semu godewa Allah gashi within three weeks d'in tayi getting back memories nata, am so happy for you people."
"Thank you Dr, thank you so much."
"Allah k'ara mana lafiya gabad'aya."
"Ameen" ta amsa "se anjima mun gode."
"Yauwa sannu" yayi hanging.
***
Tun daga ranan Zeezee ta sake maida hankalinta kan ibadan ta sosai, a day never goes by ba tare da tayi tunanin Babanta ba ta zubar da hawaye, kullum kuwa cikin yimai addu'a ita da Mama suke. 2 weeks after samun sauk'in ta akayi rabiyar gado inda magada suka samu d'imbin arzikin mahaifinsu. Dukansu sunyi amfani da kud'in sunyi aikin lada dashi inda suke baran Allah ya kai ladan kabarin mahaifinsu. Banda Zeezee data yi amfani da rabin kud'in gadon nata gabad'aya don tallafawa addinin musulunci zallah. Saura takai masallatai da gidan maryu saura gidan television da radio na yad'a muslinci da sunnan annabi. Inda tayi baran Allah da ya kai ladan duka kabarin mahaifinta.