Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
“Toh ai ba sallama akayi ba bale nasan da mutane akai na.”
“Ke Zainab! Ki kalleni ni zaki yiwa rashin kunya? Waye sa’anki anan?” Se k’ok’arin janta baya Al’ameen yake a rayuwa inda akwai abinda ya tsana shine tashin hankali. “No ka barni da ita tasamu waje ne ai, waye sa’an ki anan?”
“Aini ba rashin kunya nayi ba akan gaskiya ta nake naga nan gidan mijina ne duk shirin dayamin zanyi amman haka kawai kizo gidana ki had’a kaina da mijina? Sanin da haka ai tun farko nace bazan zauna a family house naku ba wallahi Allah ya isa na, Allah ze sak’amin. Don kun ganni k’arama kuke d’aukan alhak’i na” tasa kuka shark’af-shark’af kaman dagaske “kimin k’aninki yamin, in kinason Allah ki had’a k’anin naki da Allah ya sakeni na koma gidan ubana nima inada gatana ai, dan ina auran k’aninki bazaki tsaya kina gayamin magana son ranki ba kice mishi ya sakeni a daren yau na koma gidan Baba na inhar kun isa ‘ya‘yen halak.”
“Enough ZAINAB!!” cewar Al’ameen a tsawace cikin wani erin kakkausar muryan da ba wanda ya ta6a saninsa dashi apart from his soldiers se yau. Ba Zeezee kad’ai ba harta Hjy Sadeeyah seda ta razana. “Hjy lets leave please let her be” da k’yar ya ja Hjy waje akwatinta ta had’a tabar gidan at that instant saboda bazata iya ganin ‘yar datayi jika da ita ba tana gaya mata magana son ranta. Zama a parlour Al’ameen yayi gabad’aya ya rasa meke masa dad’i, shin meyayi wa Zeezee take punishing nasa haka? All he did was to love her. Yafi minti talatin a parlour sannan ya miqe ya nufi d’akin nasu tana miqe akan gado ko uffan bata ce mai ba. “Tashi ki zauna Zainab.” yayi ordering nata.
“In zauna kamin meh? Ka sake cin zali na?”
“Tashi ki zauna nace” yayi maganan in a serious tone da shegen tsoronta tuni ta zauna “ki gayamin mena miki kika za6i ki wulak’anta sister na haka?”
“Ma har yanzu tambayana kake mekamin? Auro ni dakayi shine laifin daka min kuma wallahi tallahi kaji rantsuwa ba kaffara inhar bakayi gaggawar saka na ba wataran akan Mamanka ze fad’a.” Tsaye yayi wajen lost of words yana kallon Zeezee, abun nata ba yarinta bane yanzu sarai tasan abinda take dagangan kawai take. Be iya yace mata komi ba ya nufi d’akinsa inda ya kwana awajen ranan ma. Da safe ya shirya yaje yasamu Hjy gabad’aya ranta ya 6aci ko kallonsa batason yi taya ze bari ‘yar yarinya ta rainasa haka? Da girmansa. Dukda nature’nsa ne hakan hak’uri dakuma juriya amman na Zainab is too much ita tsoronta befi Zeezee tasa ma k’aninta hawan jini ba tunda be ta6a so ba se akanta. Ba yadda batai dashi ba kan ya saki Zeezee koda horata zeyi, in mata ne tanada dubun da zata yimai amman yak’i bayi jin ze iya sakanta ya lalata mata future at her very tender age ace tazama bazawara dukda de har yanzu da budurcinta take amman ba kowa bane zesan da hakan bayan nan kuma yayi believeing kan wataran komin dad’ewa Zeezee zata gano kuranta ta shiryu su fara zaman lafiya shide baze gaji da farinta mata ba har se inda k’arfinsa ya k’are.
Tun lokacin wannan incident Al’ameen ya rage shiga harkan Zeezee as yanason ya bata enough space ko hakan ze taimaka mata. D’akin nasu ma gabad’aya bar mata yayi ya koma nasa inda yake kwana ya yini ciki. Ita ko wawiyar dad’i kasheta haka zata hana kanta bacci da daddare tata waya ko video call da Adeel, atimes har abinda take cewa da Adeel Al’ameen naji amman haka duk kalan kishi irin na soldiers dayake dashi zeyi hak’uri ya danne zuciyarsa. Ana sauran sati biyu ya koma Abuja ya tahowa Zeezee da sabuwar Ford Jeep nata fara k’al 2016 cikin ledarta.
Tana miqe akan gado as always da vest da nickers ya shigo d’akinta wanda baze iya tuna when last yayi hakan ba “My Princess” yayi maganan cikin sark’ak’k’iyar muryarsa. Ita kanta tayi missing sweet voice nasa “na’am” ta amsa.
“Kizo I have a suprise for you.”
“Takardan saki na ne? Inhar bashi bane save it banaso.”
“Yi hak’uri ki fito kinji? Seda ta gama 6ata mai lokaci sannan ta mik’e “muje” tayi maganan tana mai dirty look.
“Toh kisa hijabi mana Princess kinfa san yadda gidan yake da maza kullum.”
“Toh ni nace kana kawo sune? Ai laifinka ne ga guards sannan ga ‘yan maula ni gaskiya zafi ake banajin zan iya sa hijabi.” Da kansa ya nufi wardrobe nata ya ciro hijabk ya miqa mata “yi hak’uri kisa sa” kaman bazata amsa ba sekuma ta kar6a tasa tabi bayansa suna fita kawai taga sabuwar mota na mata sallama ita kanta bazata iya descriing how motan ya birgeta ba amman dan ta k’untata mai ta dake “se yau motan ya iso? Ina key’n?” Mamaki sosai tabasa wato ko d’an godiyan da take d’anyi adan ma babu shi yanzu. “Gashi” ya miqa mata “My Princess ko motan be miki bane?”
“Me kaga?”
“Your face didn’t show and bakiyi godiya ba.”
“Daman don nayima godiya ka siyo? Ashe ba tsakani da Allah bane anyways kayi kok’ari” tana kaiwa nan takoma ciki Lubiee takira tayita mata hauka kan Maj-Gen ya sai mata Ford Jeep 2016. Lubiee de tun tana yiwa Zeezee wa’azi bataji har ya zammana yanzu kawai sede tajita ta kad’a kai saboda Zeezee batajin magana kona k’alilan.
*© MIEMIEBEE ™YGC!*
www.beeenovels.blpgspot.com
👄👄👄👄
[1/20, 9:01 PM]
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣7⃣
_Assalamu Alaikum, literally I don’t even know where to start from my family, to friends, to fans, supporters, readers and to everyone who missed either my book or me, know that I missed you guys as much and am so sorry for keeping you people in such a non ending but now ended suspense and also that I can't reply back to each and everyone of you that cared and stopped by to ask for me privately, or on the blog or in groups or even tried calling me. The messages are over Alhamdulillah I have such awesome people that care for me, nagode sosai for your maxi support, care and love I love y'all oceans and galaxies❤❤. With your prayers, Allah ya dawo dani safe and sound se muyi firing on da *™YGC*💞_
_2 days later..._
Ba inda Zeezee bata taka ba da sabuwar motarta a garin Bauchi tana bawa mutane assignment. Duk mutan arziki sun taya ta murna barin ma Baba da Mama they can’t ask for a better son-in-law than Al’ameen. They are sure ko bayan ransu ze cigaba da kula da Zeezee, nasiha again Baba yata mata amman haka baiwar Allahn nan ta ajiye mai abinsa a wajen da tazo tafiya.
_Afternoon hours..._
Kasancewar Al’ameen be ta6a jimawa haka a gari ba se wannan karan yasa mutanensa da suke Bauchi duk suka soma hallaro gidan nasa suna zuwa yimai gaisuwa. Duk yadda yayi dan kada su san yana gari abin ya gagara babban mutum kamanshi se a hankali. Suna zaune da mutanen nasa a parlour yayi excusing kansa ya shiga d’akin Zeezee alokacin ma waya da Adeel take wanda da sauri ta katse ganin Al’ameen. Kai kawai ya kad’a yace da ita, “Zainab white rice nakeson ki dafa wa bak’in danayi sekiyi slicing carrots akai dakuma peas da za’a sa akai kinji?”
“Kut! Nice zanma duka wannan aikin? Wallahi k’arya ne ni banida lafiya.” tayi maganan cike da rashin kunya.
“Ki dafa white rice shine bakida lafiya Zainab? Bance fa zakiyi stew ba, na riga nasa an siyo stew shinkafan kawai zaki dafa thats all.”
“Yo dama kace nayi stew’n mana in bakayi asaran kayan miya ba kuma ma wai su abokan naka basuda mata ne kokuwa iskanci da son sa mutum aiki ne ke hanasu zama a gidansu suci abinci se sunzo gidan mutane? Allah wadai d’in mutane kaman su wallahi mschww.”
“Ya isa haka toh wuce kije ki dafa kiyi sauri.”
“Kuma wallahi in shinkafan be dahu yadda kakeso ba don’t blame me bani nace ka kawo bak’i ba aikin banza.” Mayafinta ta taje ta fice mai, in less than one hour shinakfan ya dahu yadda Al’ameen ya buk’ata sede ruwa yaso yi mata yawa kad’an amman de tayi k’ok’ari. Ita bama haka taso ba, taso ace shinkafan yayi fate-fate yadda ko a mafarki baze sake sata dafa mai abu ba.
A food warmer ta juye ta basshi a kitchen d’in sannan ta nufi parlour inda yake zaune da mutanen nasa ta bisu da dirty look sannan tace, “Daddy kaje ga abincin bak’in naka yayi.” Da mamaki friends nasan suka juyo suna kallonta taya zata kira mijinta da Daddy? Ignoring this thought suka gaisheta kusan a tare dukansu tunda ita tak’i gaishesu. “Ba gaisuwarku nake buk’ata ba ni, inda hali daga yau karku sake zuwa gidana tunda kwad’ayin abinci ke kawo ku.” Tana kaiwa nan tayi d’akinta binta da kallo duka sukayi wide in shock sannan back to Al’ameen “kuyi hak’uri dan Allah, kuyi mata uzuri yarinya ce har yanzu.”
“Bakomai Maj-Gen Allah rufa mana asiri” cewar d’aya daga cikinsu. Haka dan kansa yaje ya d’auko wa bak’in nasa abinci sukaci bayan tafiyansu ya tara plates yakai kitchen. Banda kuda dake yawo suna bin wanke-wanke tun na shekaran jiya ba abinda ke gudana a kitchen d’in. Beso ba amman dan dolensa ya nufi d’akinta be sameta ciki ba kasancewar tana wanka zaman jiranta yayi. Kaman me haihuwa seda tayi spending numerous minutes ta fito da towel nata iyaka tsakiyan cinyarta.
“Haka kawai ba sallama seka na fad’omin d’aki inda kuma ba komi a jikina na fito fah?”
“Am sorry, in kin gama shiri kije ki rage wanke-wanken kuma its hightime ko sau d’aya ne kibi gidan nan da shara Zainab, ko ke zama cikin dottin na miki dad’i sede kiyita tsaftace jikinki amman banda na muhalli.”
“Look at who’s talking dan Allah” tayi maganan tana tafe hannu “bakason ganin gidanka da dotti fine and good kana iya saka na right now ka auro wacce zatayi maka wannan bauta. Kafa sani niba boyi-boyi bace bazaka na kawomin so called friends naka suna taramin wanke-wanke ba and expect me to be washing the dishes for you, uh-uh baka da wannan gatan Daddy.”
“Zainab mesa kike haka ne? Baki tsoron tsinuwan mala’ikun Allah ne ke? In ni ina barinki sufa bazasu barki ba.”
“Ai tsoronsun yasa nake tambayar takarda na saboda in samu wanda zan na mai bauta wanda nake so ba kai ba.”
“Naji bakiya sona but you can’t change the fact that am your husband koba haka ba? Kije kiyi wanke-wanken nace” yayi maganan this time a bit tensed.
“Bazan yiba inma zan wanke se wanda nida kai mukaci abinci akai ba wanda wad’ancan bak’in naka suka ci abinci akai ba in kanason ana maka wanke-wanke kana iya kawo me aiki.”
“Naji zan kawo me aikin amman yanzu kije ki wanke na kitchen d’in in shaa Allah zan d’auko miki me aiki.”
“Ma kanka de ba mani ba yanzu excuse me zan sa kaya.” Be sake cemata komi ba ya fice. Nan da nan tagama shiri tafito kitchen kenan taji an danna door bell tana dubawa taga Mama salati kawai tahau yi har anan Al’ameen na zaune a kan sofa be motsa ba. “Ki bud’e k’ofan mana Zainab waye ne? ”
“Mama ce nawa ya k’are!” tayi maganan hankali a tashe. Murmushi me sake k’ayatasa ya saki seda dimples nasa suka lotse sosai sannan ya kad’a kai ya kawar da kansa daga kallonta. “Aww ma dariya kake min ko? Mugu kawai, mutum babba amman wai da dimples mschw” Da k’yar ta bud’e k’ofan atare ita da Al’ameen suka yima Mama sannu da zuwa. Drink da snacks ta kawo tayi serving Mama dashi.
“Ai na d’au ma ko ka koma Abujan ne Maj-Gen.” Maa tayi maganan tana cin kad’an daga cikin cin-cin dake gabanta.
“A’a wallahi se next week in shaa Allah.”
“Toh Allah ya kaimu, bazan gaji da maka godiya bafa naga sabuwar motar da ka sai wa Zeezee Allah k’ara bud’i mungode sosai.”
“Ba komai Mama an zamo d’aya ai yanzu, barin shiga ciki toh.”
“Nazo na koreka ko? Kayi zamanka de zamu shiga ni da ita.”
“A’a please kuyi zamanku anan” yana kaiwa nan ya fice. “Ke kin mai godiya kuwa daya sai miki motan?”
“Nayi mana Mama nayi sosai ma.”
“Toh ki rik’e mijinki hannu bibbiyu Zeezee aljannarki a tafin k’afafunsa yake ba a nawa ba yanzu duk lokacinda ya nemi had’a kwanciya dake karki hanasa sannan duk abinda kika san bayaso ki kiyaye wanda yakeso kuma kina mishi kina jina ko?”
“Eh Mama inayi sosai nagode.” Hira kad’an suka ta6a can Mama tace zata kai plate nata kitchen nan Zeezee ta dage atapir ita zata kai mata sanin kitchen natan bamai ganuwa bane. “Kibari mana meh haka? Bak’uwa ce ni?”
“A’a amman kibari zan kai da kaina.”
“Matsa min da Allah kaman dagaske.” ta tureta ta shiga kitchen d’in, baki kawai ta sake wide in shock tama kasa believing abinda idanunta ke gane mata. “Ke! Me wannan? Kitchen d’in mahaukaciya komeh?”
“Mama wallahi nad’anyi rashin lafiya ne kwana biyu shiyasa wanke-wanken ya taru.”
“K’arya zakiyi min? Ba two days back bane Maj-Gen ya sai miki motan kika rik’a fita yawo anyhow shine zaki cemin bakida lafiya iyyeh?” Mari lafiyayye Mama takai mata a baya. “Rashin hankalin da kikeyi agidan naki kenan ko wanke-wanke bakiyi?” K’walla na cika a idonta ta kad’a kai “wallahi a’a da Allah karki gayawa Baba wallahi ze kasheni.”
“Me ze hanani gaya mishi? Ke bazaki ta6a shiga hankalinki bako? Wannan wanke-wanke tun na yaushe?”
“Mama wallahi be jima ba kuma yau ma nakeda niyyan wankesu, MP ne ya sani gaba shiyasa.”
“Na yaushene nace? Bazaki amsa bane? Kuma wallahi kimin k’arya kiga inban kira Maj-Gen. ba na tambayesa, na yaushe ne nace?!”
“Wallahi na shekaranjiya ne.”
“Innalillahi! tun shekaran jiya? Yanzu na shekaran jiyan ne be jima ba? Ma’ana har na sati kina tarawa kenan ko?”
“Wallahi a’a Mama wannan d’inma sharrin shed’an ne” Ajiye cup d’in Mama tayi ta jawo hannun Zeezee sannan ta shiga kai mata mari kota ina, ihu Zeezee ta shiga rusawa har seda Al’ameen ya fito da mamaki yayi sauri ya k’wato Zeezee yana bawa Mama hak’uri.
Kama shirt nasa Zeezee tayi gagam tana b’oye jikinta a bayansa. “Ni zakiyi wa abin kunya iyye? Kalan tarbiyyan dana baki kenan, tunda kike kin ta6a ganin wanke-wanke ya kwana a gida na dake zaki bar har na shekaran jiya? Maj-Gen in kanayi wa Allah dan Allah ka fita kabarni da wannan maras kunyan.”
“A’a Mama dan Allah kiyi hak’uri duk beyi zafi haka ba ita kanta tanada niyyan wanke dishes d’in yau.”
“Aww ai dama nasan kai kake d’aure mata gindi, haba Maj-Gen. kai da ya kamata ka gyara mata zama se kuma ka zuba mata ido tana rashin hankali iya son ranta gaskiya am very disappointed in you. Wannan abu dame yayi kama?”
“Kiyi hak’uri Mama.”
“Ka gayamin bayan wannan wani rashin hankali kuma take again?” Shirt nasa Zeezee ta shiga tukiukuyawa tana mai nufin kar ya tozarta ta.
“Babu wannan ne kad’ai kuma shima zata gyara ko Zainab?” Tana riqe da shirt nasan ta gyad’a kai “eh eh wallahi.”
“Zan samo mata me aiki ma tana taimaka mata tunda gidan yayi girma da yawa.”
“Me aiki?” exclaimed Mama. “Wallahi bame aikin da zaka nemo ma wannan ‘yar, shara da mopping d’inne shine se an nemo mata me aiki? Da wanke wanken da befi a k’irga ba? Inhar kana k’aunan Allah kaja baya da wannan zance, ban yarda ba. Koda wasa karka d’aukan mata me aiki, kajini ko?”
“Naji Mama amman-”
“Don Allah nace Maj-Gen kai wai bakasan halin Zeezee bane? ka fara mata da haka by the time kuka zo kuka haifafa fah? Ya gidan naku ze kasance tunda yanzu da take ‘yar amaryarta ma baka barinta tayi aiki.”
“Toh Mama za’ayi kaman yadda kikace kiyi hak’uri.”
“Yauwa yanzu inason kabani waje kuma kabarni da ita kad’ai.”