Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
ya sawaqa wallahi." Dai-dai nan isowar friend inta kenan, "ahh! Ruky Mama ya ana bidiri ke kina anan?"
"Kibari kawai Mamx, Adeel ne wai ya dawo gida."
"Meaning?" Ta tambaya tana tauna chewing gum.
"Meaning na koma gida."
"Dalili?" Ta sake tanbaya.
"Nayi locking gida kafin na fito kuma ba key a gunsa."
"Yo! Bashida gidan friends da zasa kafin nan ne? Nifa banison tak'ura a rayuwa wallahi shiyasa bazan iya zaman aure ba, shikenan mutum bashida 'yancin kansa se abinda wani ya fad'a, mschw!"
"Kibari kawai Mamx kuma fa be ta6a dawowa gida war haka ba."
"Ke kinsan meh?" Kai Ruky ta kad'a "ki sharesa kawai, kibari se Maghrib ki koma gida by then an gama duk abinda za'ayi anan."
"Ke bakisan Adeel da surutu bane wallahi."
"Ce mai zakiyi key'n motarki ta 6ace da k'yar kika samu."
"Amman fa kin kawo point wallahi, hakan za'ayi." Hi five sukayi sannan suka koma ciki suka cigaba da karya kwankwaso.
Adeel har ya gaji da kiran Ruky Mama, gashi har tak'ara 15mins kan 20'n daya bata amman bata dawo ba, wannan raini dame yayi kama? Cikin motansa ya koma yayi zaman jirarta. Se chan 7:45pm ya hango wutan motarta yana nan zaune a motar har yanzu. A nitse ta fito ta bud'e gate d'in sannan ta k'arisa gun motar nasa tayi knocking bisa window, ko d'aga kai ya kalleta beyi ba, yin hakan sau biyu yasa ta koma motar ta tashiga, tana cikin kunnawa Adeel yasa kai ya shige gidan sannan ya jirata tayi locking kwad'o ta iso ta bud'e musu entrance door. Seda ta shiga yabi bayanta, a parlour ya tarar da ita "sa'an wasanki ne niko?" Yayi snarling at her.
"Kaman ya sa'an wasa na kuma Adeel?" Binsa takeyi a hankali gudun ya hanata kud'in kashewa.
"Bansani ba, minti nawa na baki kuma mintuna nawa kika k'ara akai?"
"Toh ka tsaya mana ka saurari dalili na. Key'n mota na ne ya 6ata a gidan bikin da k'yar na samu."
"Da kin ganni sanye da pampers ne sekice min haka and expect me to believe you. wallahi Ruky ki sani ba tsoronki nakeji ba just because ina d'aga miki k'afa ina ganin bakida lafiya doesn't mean I can't beat you up, wallahi kinji na rantse idan kika sake taka waje bada izini na ba Allah ya isa na as your husband na kanki, idan kuma bakisan ma'anan hakan ba try it keda mahaliccinki." Yana kaiwa nan ya fice zuwa d'aki inda ya hau tunanin Zeezee.
Doguwar tsuka ta bisa dashi, "wallahi k'aryanka ne" sekuma ta kad'a kai "ya zanyi yanzu don Allah? Gobe dinner I can't miss it for the world, shi wannan Adeel yanada problem wallahi, mazajen kowa na barinsu suyi yawo amman banda shi mschw wallahi sa'an ka d'aya kafini gaskiya anan dana zaune kan cikinka." D'ayan d'akin ta nufa ta canza kayan jikinta zuwa a light and simple one sannan ta fito ta nufa kitchen. Spaghetti me rai da lafiya ta dafa tare da had'a mai mango juice sanin its his favorite. A dining ta jera sannan ta koma d'akin data fito ta feffeshe jikinta da turare tare da sake seducing shirin dake jikinta. D'akin nasa ta nufa inda ta tarar da shi miqe bisa gado ya zura wa ceiling ido, ko bata tambaya ba tasan tunanin Zeezee yake, ita tun tana kishi ma har ya zame mata jiki, Zeezeen ma ta dawo ita batada case as long as zena bata kud'i ze kuma barta tana fita unguwa ba matsala. Kan gadon ta k'arisa tare da hayewa ta end d'in da yake ta zauna.
"Baby" ta kirasa cikin wata tantiriyar murya. Ko kallonta ma beyi ba bale yasan tanayi. "Haba! Baby am sorry don Allah." Nan ma banza da ita yayi.
"Baby yanzu bazaka d'ago ido ka kalleni bama? I said am sorry dagaske key'n mota na ne ya 6ata kaima kasan bazan shanya ka haka kawai a bakin gate ba ai ko? Yi hak'uri kaji I'm sorry."
Se anan ya juyo yana kallonta, sake bank'aro mai da k'irjinta tayi "tashi muje kaci abinci dinner is ready."
"Kije kici bana jin yunwa" yayi maganan yana kawar da kallonsa daga gareta cause he is not in the mood, tunanin ya ze dawo da Zeezee ne ke gabansa.
"Babe kaci lunch ne da zakace baka jin yunwa? Yi hak'uri muje I'll be the one to feed you." Haka tayita lalla6asa seda ya tashin, bayan tayi serving nasa tace zatayi feeding nasa sam yak'i shiwai shi zeci da kansa. Zama tayi gefensa se daddad'un kalamu masu sanya sanyi a zuciya take tayi mai, chan da lokacin bacci yayi ta sake d'aukan wani wankan tasa wasu arnan sleeping dress nata gata daman ba kad'an ba. Shisshige mai ta rigayi daren ranan seda tayi turning nasa on. A ranan ba k'aramin pleasure ta bawa Adeel ba. Da Asuba ta tashesa sukayi wanka sukayi sallah and in the morning ta had'a mai breakfast tare da shiryasa for office. Suna cikin karyawan ta kirasa a hankali yet romantically "Baby." Kaman baze amsa ba yace, "meh?"
"Baby baka hak'ura ba har yanzu?" Yi yayi kaman be jita ba. "Na fa san kana jina, me kakeso in sake maka domin ka hak'ura? Am sorry kaji?"
"Naji ya wuce."
"Meaning kayi hak'urin?" Nodding kai yayi mata "thank you Baby I love you." Nan ma kai ya mata nodding "toh Baby kaja baya da Allah ya isan kenan daga kaina?"
"That's it" yayi exclaiming "ai dama nasan ba tsakani da Allah bane kike duka wannan abubuwan nan da kikeyi."
"Allah tsakani da Allah ne please kaja baya da Allah ya isan yi hak'uri, bazan sake fita ba seda izinin ka amman incase of state of emergencies kaga ya zama dole, da Allah ya isanka a kaina kuma kaga ai da akwai matsala." Shiru yayi se cin abincinsa yake "Baby ba zaka ce ka yafe ba? Me kakeso for lunch yau?" Kai ya d'ago yana kallonta kaman bazeyi magana ba chan yace, "naji naja baya da batun Allah ya isan, you are free."
"Yeyy! Thank you" nan da nan ta taimaka masa yagama breakfast, sa6anin kullum yau har gun mota ta rakasa "Baby zan samu 5k please?"
"Again!" Yayi maganan yana tadda engine d'in motar. "Ke wai ATM machine kika maida nine ko meh? Kullum cikin tambayan kud'i naga ko shi ATM machine d'inma wani sa'in cewa yake ba kud'i."
"Haba mana don Allah bikin k'awata fa ake shikenan se ana yimata manni ni se in tsaya ina kallonsu? Yi hak'uri please."
"Ruky banida kud'i kiyi hak'uri yau, dubu nawa na kashe miki tunda muka shiga month d'innan?"
"Ni ba dogon surutu na buk'ata ba, zaka bani ne kokuwa a'a?"
"Kema kin amsa da kanki ai."
"Yama kyau wallahi" tana kaiwa nan tabar mai wajen "sekace ATM machine kullum bani wannan bani wancan, bazan bada ba."
Itama a ciki se gunguni take tana zaginsa "wallahi ba abincin ranan da zan girka da kai aikin banza kawai." Tuna tasan inda yake ajiye wasu kud'ad'ensa yasa ta saki murmushi sannan ta nufi d'akin. Cikin pocket na wani suit nasa tasa hannnu ta zaro d'imbin kud'ad'de, dubu goma ta zara ta miyar da sauran sannan nan da nan ta shirya gidan biki abinta, dinner'n da se dare za'a soma amman dan neman yawo tun yanzu zata ita.
*MIEMIEBEE. Team #YGC!🎀*
Beeenovels.blogspot.com
Page 55
February, 2017
Yau ne kawai Adeel be jesa gidansu Zeezee ba, instead yaje sa gida gun Maminsa. Bayan sun k'are cin lunch take tambayarsa ya rayuwa. Kai zallah ya kad'a mata.
"Wai kai da Ruky ne har yanzu?"
"Mami in kinayi wa Allah ki dena d'auko min zancen Bayerabiyar chan anytime we are together."
"Toh Allah baka hak'uri meke damunka?"
"Zeezee, I want her back, for the past two weeks ina zuwa gidansu amman brother'nta yak'i hak'ura ya barni inyo bikonta."
"Itan ta yarda zata dawo ma ne?"
"Bata yarda ba but I know she'll eventually."
"Uhm Auta nida zaka ji nawa da hak'ura da ita kawai-"
"I can't" yayi saurin katse ta. "I love her way much, I can't sacrifice her love to anyone."
"Toh me kakeso ayi?"
"Kuje da Uncle kumin bikonta."
"Wannan abin kunya har ina? Despite yadda ka wulak'anta yarinyan nan."
"Kema haka zakice wato? Wai akwai wanda baya making mistake ne a duniyan nan? I miss Daddy wallahi nasan da yana nan in an eye blink yamin abinda nakeso, kar kujen zan cigaba da trying luck d'ina har sena samu na shawo kanta da family'nta."
"Me yayi zafi kake magana haka Auta? Sanin kanka ne ina sonka sosai-"
"Shine bazaki iya zuwa kiyi ma Mom na Zeezee magana ba?" Ya katse ta. "Ina love anan?"
"Abinda kakeso kenan?" Gira ya d'age mata. "Toh shikenan Allah shi kaimu gobe zanyi ma Baffan naka magana."
"Yauwa ko kefa Mami? Thank you kinji?"
"Ba komai amman Allah ka dena min magana gatsau-gatsau haka, uwarka ce nifa ko dan bani dukan ka ne?"
"LOL duka fa kikace Mami? Wuce nan ai yanzu." Yi tayi kaman zata maresa take ya miqe daga kan kujeran tare da jan baya, "toh ni zan koma gida se goben."
"Toh Allah kaimu ka gaishe da Ruky."
"Ki kirata ku gaisa ni bazan gaisheta ba."
"Heh! Su Auta manya" yana murmushi ya fice se bayan Maghrib ya dawo gida a lokacin Ruky na gida tana shirye shiryen fita dinner.
"Har ka dawo ne?" Tayi maganan tana jawo k'ofan d'akinta.
"A'a ina hanya ne" ya amsata ba tare da ya kalleta ba.
"Toh ni na tafi" bece mata k'ala ba taja motarta ta fice. Chan getting to 10 Adeel ya shiga d'akinsa tare da d'auko suit dayake saving kud'ad'ensa. Zaro su duka yayi ya irga sede a maimakon yaga 100k se 90k yake gani, sau uku yake irgawa amman ba gomansa. Danqaree! Aiko ba 6era suke dashi ba bale ace su suka cinye goman, kuma he is adamant be zare ko d'ari ba daga cikin d'arin how comes?
"Ruky! Ruky sata ta fara min? Kut! Allah dawo dake gida wallahi zaki yaba wa aya zak'inta." Bacci yakeji amman yak'iyi yana jiran dawowan Ruky. Se pass 11 ta dawo gida all exhausted so kawai take ta kwanta. Tana stepping foot nata a parlour Adeel ya jefa mata tambaya, "ina kud'i na? B'arauniya."
"Kamar ya kuma kud'inka? Ka bani ajiya ne? Kuma ka dena cemin b'arauniya."
"Na k'ara b'arauniya kawai! Zan k'arisa gun in goga wannan bakin naki a k'asa wallahi, ina kika kaimin 10k d'ina?"
"Ni ban d'auka ba" ta fad'a tana cire goggoron dake kanta. "Se kinji na jaki sannan zakiyi magana? Ina yake? Ko sena gayawa Babanki kin fara min d'auke-d'auke tukun?"
"Toh ai laifinka ne, I asked you nicely kak'i bani ba dole nayi following other alternative ba."
"Ohh is that so? Nasan maganinki wallahi bake ba allowances daga nan zuwa next two months. Wani irin rayuwa ne wannan? Zeezee dako k'wandala bayi had'a ni da ita, she never once stole from me. What kind of a woman are you? Mark me, kinyi na farko kinyi na k'arshe kenan wallahi." Baki ta murgud'a mai "kada ka bayar d'in" ta fad'a a lokacin da ya shige d'akinsa. "Barka na d'an rage wasu canjin anan."
_Washegari. Gidan Lt Alhj Isma'eel Yusouf._
Zaune Mama da Omar suke a tsakar gida inda suka jiyo sallaman babban mutum daga waje. Sauri Mama tayi ta koma ciki sannan Omar ya amsa, bak'in fuska ya tarar sede kallo d'aya yayi wa Mami yagano mahaifiyar Adeel ce, yana kan wannan nazari ne yaga Adeel biye a bayanta. Welcoming nasu yayi suka wuce parlour suka zazzauna bayan gaisuwa suka yimai ta'aziyya sannan suka fayyace mai purpose na zuwansu inda Mami ta buk'aci Omar daya kaita gun Mama tana son yimata magana. Se kallace-kallace Adeel ke ko zega Zeezee not knowing bata gida taje ta gidan Adda Mariam. Ba musu Omar ya kaita gun Mama sannan ya dawo ya samu Adeel da Baffansa. Hak'uri suka yita bawa Omar inda Baffan Adeel ke sake jaddada masa batun nadaman da Adeel yayi and how bad he wants Zeezee back, achan ciki ma abinda Mami keyi kenan. At last Mama da Omar suka ce musu hakan ba damuwa bane zasuyi wa Zeezee magana idan har ta amince she wants to go back so be it, if not kuma they can't force her. Godiya sosai Mami sukayi sannan Omar yayi musu rakiya kasancewar Mama bata gama zaman takabarta ba har yanzun.
Ko cikakken minti d'aya da tafiyansu Adeel beyi ba Zeezee ta dawo, bayan tayi parking motarta ta fito ta k'arisa ciki tare da yima su Mama sannu inda sukeyi mata sannu da zuwa.
"Suwa suka zo Mama? Naga wani mota yabar gidan nan just now." Kallon Omar Mama tayi sannan back to Zeezee "zoki zauna kinji." Ba gardama ta zaunan, "Adeel, Mom and Uncle nasa ne sukazo Zeezee."
"Me suka zo yi?"
"Sunzo bikon ki" nan Mama ta zana mata yadda komi ya faru "so mu duk abinda kikeso shi zamuyi miki, in har kinga zaki iya komawa Adeel fine if not kuma a yanzu Omar na kiran Uncle nasan ya sanar dashi." Shiru tayi a yayinda hawaye ke forming rapidly a idonta. "Ko kina neman time to think?" Kai ta kad'a "Mama I don't need to think bana buk'atan Adeel a rayuwa na again, I've had enough."
"I know Sweetheart amman still zan baki daga nan zuwa gobe kiyi making up mind naki kinji? Tashi kije you are free."
"Nagode Mama, nagode Ya Omar Adda Mariam tace in gaishe daku."
"Toh muna amsawa" Mama ta amsa, nan Zeezee ta fice. D'akinta ta nufa tare da bajewa kan gado inda ta fad'a kogin tunani, gabad'aya she is lost bata san me zatayi ba. Lubiee her only adviser ta kira bayan gaisuwa take sanrar da ita halin da take ciki.
"Haba Babe! Yanzu har sekin tambayen shawara regarding wannan matter? I thought you've had enough, me zaki sakeyi da Adeel? Although nasan abu me kyau ne a sasanta amman what Adeel did you is unforgettable, kodan yadda kika nuna kinfi sonsa fiye da parents naki kad'ai ya isa ace baze ta6a wulak'anta ki ba, but he did it anyway."
"Yes Lubiee nima ba son in koma masa nake ba."
"But you still love him don't you?"
"I will be lying if to say no kema kinsan he was my first love."
"I know Babe, but please karki koma masa in shaa Allahu Allah ze kawo miki wanda ya fisa kinji? Have faith in faith."
"Yes Babe thank you."
"Always barin gudu muna da exams gobe."
"Toh success" anan ta katse. Wahsegari da Asubah bayan sallah Mama tashigo ta d'akin Zeezee, bayan sun gaisa take tambayar ta have she made up her mind.
"Mama ku kirasu ku ce musu suyi hak'uri don ni bazan sake komawa Adeel ba."
"Are you sure this is what your heart wants?"
"Yes Mama."
"Amman Zeezee ai Adeel ya tuba naga, kuma ke haka kikeso kiyita zama, mahaifiyarki na zaman zawarci kema haka?"
"Mama please don't talk like that, I believe one day Ya Al'ameen ze dawo min."
"Hmm idan beyi aure ba kenan."
"Ko da matansa uku ne inhar he is willing ya cikata dani in zama ta hud'u I'll accept his marriage Mama because I love him so much."
"Zeezee bana son kizo kiyi 2-0."
"Mama please..."
"Shikenan zan yima Omar magana ya sanar dasu final decision naki ko?" Kai ta gyad'a "good" cewar Mama. "Amman Zeezee just because you're holding on to the feeling that Ya Al'ameen ze sake dawo miki hakan baze sa kina shutting bak'in da suke zuwa miki ba, banason k'arama dake jikin ki ya saba da zaman haka, d'akinki shine k'ima da darajar ki kinji?"
"Naji Mama."
"Wanda keda nistuwa ya fara zuwa ta wajen yayanki Omar semu basa dama muga iya gudun ruwansa in ya dace a had'aku walillahil hamd ke bakison ki koma d'akinki ne?"
"Ina so Mama."
"Yauwa 'yar albarka tashi ki koma bacci."
"No ban gama azkhar ina ba tukun. "
"Toh se zuwa safen."
A yau d'in bayan sallan Azahar Omar ya kira Baffan Adeel inda ya sanar dashi final decision da Zeezee ta yanke tare da basu hak'uri. Sosai Baffa ya fahimce shi ya kuma mai godiya sannan yayi hanging wayar. Mami ya soma kira ya sanar da ita, rasa yadda zata fara breaking wagga news wa Adeel tayi inda ta buk'aci Baffa da yayi hak'uri shi ya fad'a ma shi Adeel d'in. Adeel na zaune a office wayarsa ya shiga ruri ganin 'Uncle A' yayi saurin picking.
"Hello Uncle?"
"Na'am Adeel kana ina ne?"
"Office." Ya amsa.
"Toh ba dan komi na kiraka ba illa don in jaddada maka outcome da muka samu, kasani kowani musulmi da k'addararsa a rayuwa kuma idan Allah ya aza wa mutum so ake ya danne zuciyarsa yayi accepting ya kuma dage da addu'a Allah fito mai da alkhairi daga hakan kana jina?" Jikinsa ne yayi sanyi matuk'a, "Uncle just tell me tace she isn't coming back huh?"
"Eh Adeel kayi hak'uri, we can't force her."
"Shikenan nagode." Nan ya katse wayar, jakansa kawai ya d'aga ya fice. He