Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
kulawa ai na gaya maka, kalli wannan shopping data shigo dashi inba saurayi ba waze bata? Ai na gaya maka wallahi in bakayi tsaye akan yarinyan nan ba seta janyo maka abin kunya” tana kaiwa nan ta basu waje “kin kyauta kenan Zeezee? Duk kalan gatan dana baki da abinda zaki sak’a min kenan? You are indirectly calling me a fool tunda har zaki iya canza result naki ki kawo min gida sannan kiyi believing zan yarda because you are taking me as a fool isn’t it? kin kyauta kenan?” Kai ta kad’a “a’a Baba kayi hak’uri.”
“Baki ganin yayyun kine da baza kiyi koyi dasu ba? Banason ina miki suratai Zeezee kidena sani, samarin dagaske kike kulawa ko? How old are you?” Fad’a sosai Baba yayi mata for the first time.
“Na tuba Baba bazan k’ara ba” bayan nan yayi mata nasiha sosai kamar dagaske ta ringa rusa mai kuka wajen tanata ta tuba bazata k’ara ba harda wai zata tattara kayakin ma ta miyar wa Ammar. Baba na barin wajen ta share hawayenta ta tattara kayakinta tayi ciki sannan ta d’au wayarta ta kira Ammar nata.
★*★*★
Ahaka har aka soma azumi, sam kaman ba da ba. Ada acika kan dining table dam da kayakin shan ruwa amman yanzu abin sam ba dad’i, Zeezee de kullum cikin k’orafi take ita fa tagaji sede Mama ta kalleta ta tab’e baki. Anyi azumi goma Baba ya siyo zannuwa irin ‘yan N5,000 d’innan masu kyau guda biyu nanma dan yayi k’arfin hali ne bayan shan ruwa ya tara iyalansa a parlour “dukanku kunsan yadda abu ya kasance min, yanzu da da ba d’aya bane ga zannuwa nan guda biyu d’aya wa Yasmeen d’aya wa Zeezee, Ibraheem Baba na nagode da komai Allah ya k’ara maka bud’i, Omar se kayi masa godiya shi ze maka kayan Sallah. Mamanku kuma ta k’ara hak’uri zuwa next week nad’an samu abu zan sai mata zanin itama.”
“Ba komai Baba” cewar Ibraheem bayan Omar yamai godiya.
“A’a nikuma sekace yarinya kabari kawai ansan babu ai karka damu addu’armu de Allah yayi maka bud’i.”
“Ameen Hafsah ta nagode.” Yasmeen ce ta numfasa tace, “ayyi Baba aini ko baka sai min kayan Sallan bama tunda duk kowa yasan halin da ake ciki yanzu.”
“Aw bakiso? Sena had’a da naki ai, meh kayan sallah d’aya zeyi wa mutum? Ai wannan abin kunya nema Lubiee taji anmin kayan Sallah set d’aya-”
“Ke jahilar inace?!” Ibraheem yayi interrupting nata angrily.
“Haa’a! Ni namaka magana ne? Ai baka min kayan Sallah ba bale kasamu bakin magana.”
“Ya isa haka Zeezee!” Baba ya tsawata mata juyawa kowa yayi yana kallon Baba yau shike ma Zeezee masifa a idon kowa! “Bakida hankali neh? Ma yayan naki kike gayawa magana? Ko bakisan dabadon taimakonsa ba da kin jima da dawowa nan Havardth da karatu, maza basa hak’uri.”
“Toh Baba ni na mai magana ne, wallahi Allah ze saqa min bayan talauci ga kuma masifa da rashin kwanciyan hankali” ta k’are maganan tana kuka “ko waya an kasa canza min tun jss3” zaninta dana Yasmeen ta had’a tabar gun a guje kowa se kallonta yake daga bisani suka maido da kallonsu kan Baba suna basa kallon ‘its all your fault’ kai ya girgiza “Allah shirya Zeezee toh.”
“Ameen” Mama tace “inta shiryuwan ce, Yasmeen muje mu had’a miyan suhoor d’in.”***
Kuka Zeezee ta tayi a d’akinta ita an had’a ta da kayan Sallah d’aya, Baba daya rage shi kad’ai a parlour se jin sautin kukanta yake. A sanyaye ya mik’e yayi knocking a k’ofar kamar wacce bazata bud’e ba ta tashi ta bud’e ranta a dak’ule. Bayan sun zauna kan kujera Baba ya shiga mata nasiha saboda shi kansa abin Zeezee ya soma basa mamaki, yarinyar da nasiha ba shiganta yake ba ko a kwalan rigarta ita zannuwan Sallah take so ba suratai ba seda Baba ya gama zuba tace, “nagode Allah k’ara bud’i.”
Washegari Mama da Yasmeen suna aikin kayan bud’a baki Zeezee na a d’aki as always tana chatting, dawowan Ibraheem ya taho da fruits bayan ya dire a kitchen yayi musu sannu da aiki sannan ya tambayi ina Zeezee.
“Tana d’aki as always” Yasmeen tabada amsa.
“Ita bazata fito tayi aikin bane?”
“Ai na gwada yi mata magana tak’i, Mama tasa baki kuma wai a’a abartan.”
“Mama hakan da kikeyin fa ba taimakan ‘yar nan kike ba, wace ita da zata ce bazata yi aiki ba?”
“Toh Ibraheem kana ganin laifi na ne? Katab’a jin nama Zeezee magana tajini? Sede in kai da kake dukanta, nikam ba haka iyayena suka girmar dani ba, bazan iya dukanta haka ba kullum. Ta cigaba da halin nata surely someday zatayi regretting” ba tare da ya sake cewa komi ba yafice se d’akin Zeezee knocking yake gbam! Gbam! Gbam! “Waye haka b’allan k’ofan za’ayi?” tayi maganar tana b’oye wayarta cikin pillow case.
“Bud’e k’ofan nace maras kunya kawai bud’e!” jin muryan Ibraheem ta mik’e aguje ta bud’e k’ofar sannan ta soma rik’e cikinta “maza wuce kitchen, wace ke ana aikin bud’a baki kina kwance a d’aki?”
“Ya cikina ne yake ciwo wayyo Allah!”
“Sekisha magani ai wuce kitchen nace.”
“Ya ai ina azumi kuma period d’ina ne yakeson zuwa wallahi bazan iya mik’ewa dakyau ba.”
“Ni zaki raina wa hankali? Ko bakisan nasan date naki bane wuce nace kona miki d’an banzan duka kan azumin naki.” Ganin ya kamata, ta mik’e da kyau.
“Ni shikenan kullum mutum baida hutu agidan nan ni wallahi na gaji ga bak’in talauci gakuma uban-” ai bata k’are maganan ba ya bige k’aramin bakin nata tare da fisgota a tsakar gida ya yasar da ita. Tuni ta soma kuka “maza wuce kitchen kije ki karb’i Mama, Mama fito daga kitchen d’in cinta za’a zo ayi ne? Ki mik’e wallahi kona zaneki” yayi maganan yana cire belt nasa, ganin haka ta mik’e tayi kitchen d’in. Da kansa ya fito da Mama daga kitchen d’in sannan ya tsaya kansu yasa Yasmeen tabata aiki in batayi ba kuma ya mauje ta. Haka tana kumbure-kumbure ta shiga yi bayan ta gama yamata nuni da ledan fruits d’in kan tashiga gyara water melon da paw-paw d’in, “ni wallahi nagaji ai ba engine ce niba ita Yasmeen me zatayi?”
“Magana kike?” Ya mata sending wani dirty look, miyau ta had’iye ta d’au ledan ta wanke fruits d’in sannan ta shiga yimusu gyaran walaqanci. Bada jimawa ba Ibraheem ya fita, ko cikakken two minutes ba’ayi ba Baba ya dawo nan Zeezee ta soma kukan munafirci “yada kuka kuma K’anwata?”
“Ya Ibraheem ne wai sena gyara wannan duka kuma cikina ciyo yakemin.”
“Ita Yasmeen ina take?”
“Tana d’aki.”
“Yasmeen! Yasmeen!”
“Na’am” ta amsa tare da fitowa “sannu da zuwa Baba.”
“Yauwa sannu zoki karb’i Zeezee kinji batada lafiya.”
“Baba wallahi k’arya take lafiyanta lau.”
“Baba wall-” tuna tana azumi ta gyara zancen nata, “dagaske ba k’arya bane Baba wayyo Allah na.”
“Yi ki karb’eta Mama na Yasmeen yi hak’uri.”
“Wallahi kinci darajan Baba ne maras kunya kawai” gwalo Zeezee tamata sannan ta mik’e ta nufi d’akinta ta cigaba da chatting from where she stopped.
Shigan Baba d’aki Mama ta mai sannu da zuwa sannan tace, “wallahi Alhj ka rage biyewa Zeezee, nad’au kayi hankali bayan ‘yan abubuwan datayi days back amman ashe ba haka bane.”
“Kamar ya Hafsah? Yarinyan nan she is not used to rayuwan da take living yanzu koshi ya isheta damuwa be kamata muna d’aura mata da namu akai ba.”
“To mud’in mun saba da wahalan ne? Ai kowa hak’uri yake.”
“Toh ai ku manya ne ita kuma yarinya ce, kuyi mata uzuri mana please! ko waya na kasa canza mata abarta hakan nan.”
“Yayi kyau, Allah kyauta amman de don’t come and cry to me when the head has been cut off already.”
I MISS MY OLD ACTIVE BLOG READERS😵😵
*© MIEMIEEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 18
*December, 2016*
On the 20th of Ramadhan Zeezee ta tashi ba azumi, dad’i kasheta tun on 15th take jiran date nata daman, se aukin son shan azumi da kuma k’in yin ramako. Ko wannan karan ana weeks to Ramadhan Mama tasa Ibraheem tsaye kanta sannan ta biya azumin nata. Da safe around 10:30AM ta tashi, wani irin sanyi ake wane a Moscow, Malam bahaushe yace jifa yazo dai-dai da zama. Dama bason wankan take ba jin wannan sanyi ta kwaskware jikinta ta canza inner wears tasa sabon kaya sannan ta fito a parlour taci karo da Mama ta gaisheta.
“Se yanzu kika ga daman tashin?”
“Eh sanyi ake shiyasa.”
“Yayi kyau kinga Baaba harta gama aikinta ta tafi, in kin gama breakfast nakin seki wanke plates da duk abinda kikayi amfani dashi sannan ki share kitchen ki sake mopping.”
“Wai duka aikin nan ni zanyi? Ita Baaban nan sekace aljana wai harta gama aiki mschw ni wallahi dama canza me aiki akayi.”
“Nide na gaya miki ga Ya Ibraheem na gida, in kinason kanki sekiyi abinda na saki kona basa izini ya zane min ke k’azama kawai, dubi k’wansa a idonki amman de bakiyi wanka ba ko?”
“Nayi mana” tayi maganan tana sa k’ark’ashin skirt nata tana ciro k’wansan.
“K’arya kike bakiyi ba nasan ki ai.”
“Toh a wannan uban sanyin mutum ya hau wankan safe sekace meh zuwa office, se can anjima zan yi” tana kaiwa nan ta zarce kitchen tashiga had’a indomie abinda ta iya.
*~ *~
Da Azahar bayan sanyi ya ragu rana yayi taking over Zeezee tayi wanka tasa ¾ leggings nata da vest ganin Ibraheem bai gida, bayan tagama had’a lunch nata nanma indomie ta d’au tabarma ta baje tsakar gida da kanta a bud’e tana cin abincinta bad’an kunya taje d’aki taci. Tafe side-by-side Mama da Baba suke tana mai rakiya, tana ganin Zeezee tahau surutu “haba Zainab! Meh hakan? Ke bakida kunya ne ko sekin gaya wa duniya yau baki yin azumi ne? Maza wuce d’akinki da Allah sakariya kawai.”
“A’a Hafsah me kuma yayi zafi haka da zagi? Me aciki dan yarinya nacin abinci a tsakar gidan Babanta?”
“Aww ma tambaya kake? What if ko friends nasu Omar suka shigo fah? Zeyi fasali ne?”
“A’a gaskiya banason irin wannan tak’uri wallahi, kibarta kurum! ci abincinki Zeezee.”
“Da kyau daman ka saba ai” bata k’arisa mai rakiyan ba ta dawo ciki. Bayan fitan Baba bada jimawa ba Ibraheem da friends nasa about 4 of them suka shigo gatsau! Kasancewar shine a gaba yana ganinta yamata ido kan tayi sauri ta fice aiko data gano haka ta juya mai kai ta cigaba da cin abincinta. Yace da friends nasan su juya kuma kunya yakeji haka suka zo wucewa suna kallon Zeezee ko ajikinta ba kayan arziki ne sanye da ita ba, bama wannan ba ace agaban friends na yayanta tana cin abinci a azumi. Bayan da tagama tayi dukkan aikin da Mama tasata da cuwa-cuwa kamar yadda ta saba. Koda aka soma aikin bud’a baki yau tak’i sa hannu acewarta ai ba azumi take dashi ba, saboda haka ba aikin da zatayi shide Ibraheem jira yake Baba ya fita yayi mata d’ankaren duka.
★*★*★*★
Life moved on, abubuwa da dama sun gudana ciki harda samun bud’i kad’an kad’an da Baba ya soma samu, abu fa kamar wasa arziki se dawowa yake fiye dana da, kowa se murna yake a gidan suna cigaba da addu’a suna kuma yiwa Allah godiya babu kamar Mama data d’au yanzu wai Baba yayi hankali, kodan abubuwan da suka faru a baya yaci ace Baba ya koyi darasi yanzu ya dena biyewa Zeezee. Ashe de kam abu na cikin duhu ne! Sabuwar ipad da waya k’irar iphone 6s ya sai wa Zeezee, ba ita kad’ai ba har Yasmeen sannan a babban sallah yayi ma kowa d’inki kala bakwai-bakwai Zeezee kam kala goma akayi mata wayyo ita dad’i kasheta. 2 weeks back sukayi resuming school tana Ss 2 kenan yanzu with fifteen (15) years old. Ana takan zama budurwa se pallin tsiya, sede fa har yanzu hankalinta na akan Ammar bawani paying attention d’in kirkin da take a school.
Bayan Sallah da sati d’aya Mariam ta sake haihuwa tasamu ‘yarta Hafsah takwaran Mama anyi hidiman suna lau, Allah shi raya Mama.
*~ *~ Saturday morning.
Zeezee as well as her other siblings duk suna gida, Omar ma recently ya gama service ya shiga neman aiki.
Knocking Mama tayi bisa k’ofan d’akin Zeezee sannan ta shiga da sauri-sauri ta b’oye wayarta ta soma faking bacci.
“Wai bacci kike? Tashi zaku gidan Kaka yau (Maman Babansu) kafin nan tashi mu zab’i kad’an daga cikin kayakin ki zaku d’an bawa yaran da suke zama da ita kunce, Yasmeen harta bada nata set biyar saura ke.” Zumbur Zeezee ta mik’e zaune, “meneh? Bada kuncen kaya? Ni wallahi bazan bada komi ba shikenan abi asawa mutum ido kan kayakinsa gaskiya a’a.”
“Kamar ya a’a Zeezee? Ke bakisan aikin lada bane, in Allah ya hore maka se ai ka taimaki na k’asa da kai ke kanki bakisan yawan adadin kayakinki ba, ko wanda Babanku ya d’inka miki recently bayan Sallah ma kd’ai sun isheki amman kice bazaki bada kuncen kaya ba? Maza tashi ki zab’a min guda biyar nace karki bari raina ya b’aci.”
“Ni wallahi banaso” tayi stating tana shure k’afafunta kan gadon.
“Zan kira Ibraheem fah!” Jin haka ta mik’e ta bud’e wardrobe natan, wasu kod’ad’d’un kayakinta guda uku tun tana Jss3 tafito dasu ta ajiye kan gadon “gasu nan ai sunyi ko?”
“Tsumman goge tiles nace kibada ko kayan sawa?” Bankad’eta Mama tayi ta ciro wasu sabin kayakinta biyu sannan ta had’a da wanda suka d’an sha ruwa kad’an guda uku. Ihu Zeezee ta k’urma tashiga k’wala wa Baba kira, unfortunately bayi gida haka tayita kukanta har ta godewa Allah. Tana ganin Yasmeen nata shiri ita ko wankan ma batai ba, seda sukazo tafiya Ibraheem ya tambayeta, “kefa bazaki bane?”
“Bazan jeba me ze kaini gidan Kaka ana zaman lafiya, ace ma mutuwa tayi mana amman tana k’alau sena hau zuwa gidanta adafa wa mutane tuwo a kuma sasu cin dole kuje Allah ya kare.”
“Mu tafi Yasmeen bar fitsararriyar nan anan.” Maman data d’au duka yaran suka fita tana fitowa daga d’aki itama tayi shirinta zata fita kawai taga Zeezee “ya haka? Baki bisu bane ke?”
“Meh ruwanki toh? Kin kama kin kyautar min da kayaki na” nan ta mik’e tazo shiga Mama ta d’aka mata dundi a baya “shegiya fitsararriya kawai”
“Wallahi Baba ya dawo sena gaya mai kince min shegiya” tayi stating in a crying tone, kota kanta Mama batai ba ta fice. Wayarta dake cikin pillow case ne ya soma ruri, tana dubawa taga Ammar hesitantly ta d’aga, “halo Sweetheart.”
“Yes Pretty are you free?”
“Yes I am wani abu ne?”
“Ki shirya zanzo in d’auke ki we are going somewhere.”
“Zaka zo kuma Handsome? Ko ka manta inada brothers ne?”
“Holy sh*t suna gida kuma ko?”
“Actually no duk sun fita am home alone but they can come back at any moment.”
“Kawai de kice you are not interested shikenan, I’ll go look for another date, hanging out fa za’ayi Ss2 Vs Ss3 kema kinsan you need to be there.”
“Haba Baby taya zakace am not interested wallahi I am naji zan shirya yanzu sekazo.”
“Yauwa Sexy, dress hottie kinji?”
“Yes Boyfriend, I love you.”
“I love you too Babe” yayi hanging.
Tana ajiye wayan ta shiga cin faracunta she’s all confused batasan me zatayi ba, what if lokacin da yazo Ibraheem ko Baba suke dawowa su kamata fah? Kai ta kad’a amman inhar banje ba Ammar will be angry infact ze iya cewa ma lets break up cause mata rushing akansa suke. Bayi ta fad’a tayi wanka a gurguje tayi applying medium makeup sannan ta ciro wani red strapless gown tasa ta d’aura kanta me kyau ta feffeshe da turare. In 3 minutes time Ammar ya kirata bayan ta rufo ko ina agidan ta fita exactly kalan motan Ya Ibraheem Ammar yake hawa, da wuri-wuri ta k’arisa gun motan, wani irin mayen kallo Ammar ke binta dashi musamman dayaga d’an cleavage nata awaje. Ta bud’e motar dai-dai zata shiga kenan sega motan Ya Ibraheem wane daga sama batasan alokacinda ta saki fitsari kad’an a panties nata ba. B’ari ta shiga yi tama rasa nayi “Ammar ka fito! ka fito please” alokacin da Ammar ya fito daga motar har Ya Ibraheem yayi parking motarsa shima yafito yana nufan gunda suke in a swaying motion tace, “koya tambayeka waye kai kace you are my classmate.”
“Sannu da dawowa Ya” tayi stating in a cracky voice hannunta se had’a gumi suke ayayinda zuciyarta keta harb’awa tana addu’a Allah ya sa karya mata abin kunya a idon Ammar.
“Ina kwana?” Ammar ya gaishesa, ko amsawa beyi ba yace in a serious tone, “ina zakije da wannan shirin? Sannan kuma waye wannan?”
“Ya ba inda zani, classmate d’ina ne yazo tambaya na materials da zai siyo mana na physics practicals namu ne” ta k’are maganan tana b’ari.
“Nace waye wannan kuma ina zakije da wannan d’an iskan shirin?!”
“Zeezee I’ll get going se mun had’u Monday at school zanje na siyo materials d’in” Ammar na kaiwa nan yaja motarsa ya tafi.
“Saurayi kika