Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
ya basa d'an ze wahalar dashi, ki sani don Allah be baka haihuwa ba doesn't mean he doesn't love you, atimes yana hakan ne saboda yana sonka Zainab. And you can't even conclude that bakiya haihuwa, this is just your first year of marriage, lets have faith and pray for zuri'ah d'ayyiba okay?" Ya k'are maganan yana mata murmushi sede ta kasa smiling back masa, how can he be so sweet kawai take fad'a a ranta. Hannunsa ta d'aga a hankali ta had'a da nata "Ya Al'ameen I do believe in all that you've said amman ba wai haka ne kad'ai na yanke hukuncin bana haihuwa ba, I have a strong reason."
"What are you saying Zainab?"
"Ya Al'ameen ban ta6a fad'a maka bane but for six months Adeel yata d'ura min wani maganin hana d'aukan ciki ban sani ba." Salati kawai Al'ameen ya sakar a zuciyansa, wani irin mugun mutum ne Adeel da zeyi torturing precious halitta irin Zeezee haka? Kuka kawai tasa na sosai wanda tuni yayi hugging nata yana shafa kan gashinta soothingly. "Alokacin dana zo na gane maganin hana d'aukan ciki yake ban it was too late na riga na rasa mahaifata saboda side effects nasa."
"Shhh! Cry nomore Zainab, I love you for who you are I don't care ko kina haihuwa ko bakiya yi, ni ke nakeso and nothing else."
"Ya Al'ameen am sorry nasan yadda kakeson yara but I can't provide you your happiness which is a family, kayi hak'uri don Allah."
"Zainab stop apologizing, in akwai wanda ze bada hak'uri anan Adeel ne and no one, kibar kukan haka ai dama ba yarjejeniya mukayi dake ba kafin na dawo dake akan zaki haifo min yara ba so I have no right to be mad or furious at you."
"It'll be more happier idan muna da yaranmu muma, Ya Al'ameen in kai ka yarda zaka cigaba da zama dani haka what of Mama Babba? Don't you think tana da urge na ganin jikanta daga gareka?"
"Princess Mama is not like that, she'll totally understand everything."
"Are you sure Ya Al'ameen? Bana son in tauye maka chance naka na meeting da jininka, yaranka tamkar yarana suke kar kaji nauyi don zaka auro wata da zata iya baka wannan arziki I am totally okay with it."
"Zainab idan kika sake magana haka zamu 6ata dake am serious, I'll pack my stuffs and go back to Abuja na gaya miki ke kad'ai ce, kuma a hakan nake sonki bale ma ban yarda wai mahaifar ki ta 6aci ba gabad'aya. Which Dr told you so?" Kai ta kad'a mai nufin a'a.
"You mean to say ba Dr'n daya tabbatar miki da cewa your womb is damaged?" Yayi tambayan cike da mamaki.
"Babu but yabani labarin wacce tayi using drug d'in for just 2 months and seda aka cire mata mahaifar tata saboda yadda ta lalace."
"Princess that isn't enough reason kema kice naki ya lalace."
"It is Ya Al'ameen gashi kana gani har yanzu na kasa conceiving, ko 6ari ban ta6a yi ba."
"No I don't believe in that zamuje asibiti a duba ki only then zan yarda."
"No please."
"Yes Princess."
"No" ta fad'a tare da shigewa jikinsa tana rusa kuka sosai "please don't inhar kana sona kaman yadda kake fad'a you won't force me zuwa ganin wani Dr again, na yarda da k'addara na kuma na kar6esa hannu bibbiyu amman bazan je wajen Dr ba ya sake tayar min da hankali please don't force me Ya Al'ameen." A hankali ya shiga hugging nata back, "its okay Princess ni duk abinda kikeso shi zan miki, bakiya son zuwa ganin Dr so be it but I assure you mahaifarki bata lalace ba, you are still very young. I believe some day zaki kawo min little Soldier or Princess d'ina into this world okay?"
"I really do pray so also, ba abinda nakeso kaman inga nayi blessing naka da yara, tun akan Ramlah na gano kai kids lover ne."
"And you will Zainab, its just a matter of time, cry nomore."
"I love you Ya Al'ameen, I love you so much na d'au bayan kaji wannan sirrin nawa zaka tsane ni ka koreni gida a yinin yau."
"Subhanallah sekace wanda be san addini ba zanyi haka? Kina nan a gidan nan Zainab mutu kan raba." Dad'i sosai taji inda ta lume jikinsa tana shak'an daddad'an turaren jikinsa.
"Tashi muje I need My Woman."
"I need My Man also" cike da so da k'auna ya d'agata in a bride like style ya direta kan gado achan na basu privacy nikuma.
Tun daga ranan da Zeezee ta sauk'e wannan maganan da take gani tamkar hak'k'i a gareta tad'anji iska. Yawancin kullum zata tashi cikin dare tayi ta nafilfilu tana miqa wa Allah kukanta. Rayuwa ta cigaba da kasancewa da dad'i wa Zeezee se gani ma take like seda Al'ameen ya gano wannan matsalar dake damunta ya fara nuna mata wani sabon son simply because he wants her to know shi ba don haihuwarta yake sonta ba. Prolonging zamansa yayi har na sati biyu Zeezee couldn't ask for more, kullum suna tare da Al'ameen nata, lectures ma ji take as if tabar zuwa saboda yadda bata son barin Al'ameen nata shi kad'ai a gida.
As always wannan tafiyansan ma seda tasha kuka abinta. Bayan tafiyan nasa kuwa ta cigaba da maida hankalinta ga karatu, ana cikin haka ne Lubiee ta haihu inda ta samu 'yarta suka yi wa Mama takwara, ita de Mama takwaran nata har sun mata yawa gana Mariam, gana Ibraheem sannan kuma na Omar. Ranan suna sun sha budiri sosai, 'yar sak Lubiee ba abinda ya rabasu.
Life moved on, a kullum dad'a son juna Al'ameen da Zeezee suke wane jiya-jiya akayi musu aure. Lokaci ba wuya Zeezee harta ci rabin karatunta or so, da auranta da Al'ameen shekara biyu kenan. Yanzu haka suna rubuta exams na 2nd semester'nsu for their second year, Lubiee kuwa this year tayi graduating, 'yarta Afrah dake nan sak ita ta girma sosai.
Ta fannin Adeel da Ruky Mama kuwa har yau gasu nan ne kawai, sam sekace ba mata da miji ba idan an gansu gu d'aya to hak'k'in d'ayansu ya had'a su, if not kowa kaman zaman kansa yake, hakan ba k'aramin damun Ruky Mama yake ba, tana son Adeel nata sosai amman abubuwan da tayita masa yasa ta fita daga kansa gabaki d'aya. Gashi har yanzu ta kasa ajiye d'a a gidan, da ta d'au ciki bayi kai 3 months yake zubewa, sau d'aya kuma ta sake haihuwa ta mace bayan kwana uku ta koma itama. Kukan da Ruky tasha yasa har asibiti sanda aka rik'e ta, sosai ta bawa Adeel tausayi kawai bai nuna mata ne saboda gani yake abin ma yafi damunsa akan ta. Tunani Ruky ta soma yanzu, anya ko ba alhak'in Zeezee ke binta ba? In haka ne ya zama dole taje ta nemeta ta kuma nemi tubarta.
*****
Karatu Zeezee take sosai, sanin sunkusa fara exams Al'ameen yak'i dawowa gida koda ya samu hutu sabida bayason yayi distracting nata he knows right Zeezee bata iya karatu idan yana kusa da ita. Labarin ciki de har yanzu shiru, Zeezee de ba k'aramin damunta hakan keba but idan taga yadda Al'ameen is care free yake kuma nuna mata so se itama taji damuwan nata ya gushe. Ko da wasa kuwa Mama Babba bata ta6a kawowa Al'ameen zancen haihuwa saboda tasan shi hakan daga Allah ne.
Cikin sa'a su Zeezee suka k'are exams nasu. A daren ranan Al'ameen ya kirata bayan sun gaisa yake tambayarta ya last paper.
"Alhamdulillah My Soldier wato kaje ka mak'ale a Abj kak'i dawowa ko? Ka mance da Princess taka."
"Ina ni! I might forget myself but you? Bazan ta6a mancewa dake ba Princess banso dawowa bane saboda time d'in kuna exams Princess, banason na zame miki distraction yanzu haka flight dina nake jira yau zan dawo." Ihu ta k'urma cikin wayan "yeyyy!!! Are you serious Sweetheart?Yau zaka dawo?"
"I miss you like hell."
"Awww I mis you more me kakeso in dafa maka?"
"Anything yummy."
"Toh wallahi sauran kuma kace min kaci abinci a jirgi a k'oshe kake."
"LOL kar ki damu yau kam da empty stomach zan taho."
"That's My Man so seka shigon ko? Kasan wani abu?"
"No tell me."
"Mafarkin events na second anniversary'nmu nayi yau wai mun sake zuwa Washington amman wannan karan da kids namu wai mace da miji, na mijin ne babba, they both look exactly like you, it was so adorable."
"In shaa Allahu we will one day Princess zamu sake komawa Washington da kids namu kamar yadda kikayi mafarkin its just a matter of time."
"Allah yasa Sweetheart."
"Ameen so sena shigon ko?"
"Safe flight your Princess loves you so much."
"I love her way over." Yana katsewa Zeezee ta rage kayan jikinta ta shiga kitchen ta hau had'a ingredients na fried rice.
A lokacin da ta gama kwalyanta se k'amshi ke tashi a jikinta tana zaune a parlour tajiyo k'aran bud'e gate. Kamar yadda ta saba kowani dawowansan yau ma ta kasa jiransa ya shigo, tun a waje taje ta tar6esa. Se kallon Zeezee kawai Al'ameen yake yadda ta k'ara wani haske, cika da kuma kyau. Bayan ya watsa ruwa suka fito ta shiga feeding nasa da kanta. Suna cikin hakan ne ta lura da irin kallon da Al'ameen ke mata ita ta d'au ma ko wani abu ne ya faru, "Sweetheart?" Ta kira sa a hankali.
"Yes Princess" yayi maganan tare kawar da idanunsa daga gareta.
"Sweetheart is there a problem?" Maido da idanun nasa ya sakeyi a kanta. "Me kika ga?"
"You've been starring at me since, is something wrong with my makeup?"
"God No Princess, your makeup is perfect."
"Toh mene kake ta kallo na tun d'azu?"
"Tun shekaran jiya da mukayi video call naga kin k'ara haske se na d'au ko kawai camera ne but its not dagaske ne kin k'ara hasken, your skin is glowing Princess bakiga yadda kikayi kyau ba and har k'iba ma kin k'ara."
"Oh come on Ya Al'ameen don't tease me please exams fa na gama."
"Seriously Princess" yayi maganan tare da miqa mata hannunsa, tana grabbing ya jata ya zaunar da ita a cinyansa. "Me sirrin ne Princess?" Hannayenta ta zagaye a wuyansa. "Sirrin?" Ta tambayesa, nan take yayi nodding. "Saboda Sweetheart d'ina na bani all that I need and ask for. Kula danin da kakeyi yasa na k'ara haske harma da weight bakaji Mama na teasing d'ina ba ranan wai na kaita k'iba yanzu."
"Oh thats not true My Princess is slim and elegant." Lips nata ya lalumo a hankali ya shiga kissing nata inda take miyar mishi da martani itama daga chan suka wuce d'aki ganin nan d'in baze iya containing nasu ba.
Later during the day wuraren k'arfe 5:35pm Zeezee na mik'e akan gado tayi lamo wane wacce batada lafiya. Fitowan Al'ameen daga bayi kenan yana sanye da towel ya tsaya kallonta. "Ka fito?" Kad'ai ta iya tambayarsa a kasalance.
"Yes Princess are you okay?" Nan ma kai ta gyad'a mishi. "Sorry naso fito maka da kayan da zakasa amman banjin zan iya." Da wuri-wuri yayi grabbing shirt da trousers yasa ya k'araso kan gadon ta gefenta ya zauna. "Princess you are not okay" ya fad'a yana scrutinizing face nata, da sauri ta kawar da kanta "na fad'a maka I'm fine."
"No you are not you are looking pale and weak Princess."
"Karka damu zuwa anjima zan dawo normal."
"How sure are you?"
"Saboda kusan kwana hud'u kenan hakan kemin, da zaran yamma ko safiya yayi senaji banida lafiya cikin some hours kuma sena ji am back to normal karka damu."
"Yanzu Princess har na tsawon 4 days kike fama da hakan baki fad'a min ba? I'm very angry."
"Please don't" tayi maganan tare da rik'e hannunsa "ban gaya maka bane saboda banason ka shiga damuwa, its nothing to worry about." Hannunsa ya cire daga rik'on da tayi mar tare da shafa side na fuskarta "bakida lafiya kuma kice its nothing to worry about? Ya kika samu kika k'arisa exams nakin ma toh?"
"Cikin dare nake tashi inyi karatu ko da rana please kabar damuwa."
"I can't Princess we need to see a Dr."
"What for?"
"Ya dubamin ke saboda bakida lafiya."
"Kasan me nakeso Sweetheart?" Kai yayi saurin kad'awa "just hold me, I want to sleep in your arms." Pecking forehead nata yayi sannan ta matsa mishi kad'an ya kwanta wajen tare da kwantar da ita a jikinsa. Ba k'aramin zafi ba jikin Zeezee yayi wanda har yabawa Al'ameen tsoro sosai, toh wani irin rashin lafiya ne wannan? Just earlier she was perfectly okay yanzu kuma batada lafiya? Ji yake ina ma ace ze iya kar6a mata rashin lafiyan shi yayi suffering instead.
"Princess jikinki yayi zafi in d'auko towel in matse miki to cool it down?"
"No just hold me please."
"Shhh! Get well soon okay? I'm here for you, I love you."
*MIEMIEBEE. Team #YGC!π*
Beeenovels.blogspot.com
ππππππ
πππ πππ
πβ£π
β£β£
β’Β°β’β
β’Β°β’ β’Β°β’β
β’Β°β’
Β°β’ β’Β° Β°β’ β’Β°
Β°β’Β° Β°β’Β°
*βYAR GATA CE!*πΈπ»
β’Β°β’β
β’Β°β’
Β°β’ β’Β°
Β°β’Β°
*_written by miemiebeeπ_*
*March, 2017*
6β£9β£
Kai zallah ta iya ta gyad'a mar saboda yadda takeji ajikinta. Sake rungumeta yayi gagam dukda yadda baya jin dad'in hot temperature'n tan amman don da tace he should hold her. A hankali bacci yayi gaba da Zeezee, Al'ameen kuwa har yanzu hankalinsa ya kasa kwanciya. Tun aurensu da yayi shekara biyu yanzu be ta6a Ganin Zeezee a irin wannan situation ba, duk rashin lafiyanta baifin ciwon kai kona ciki wato menstral cramp, he is so worried ganinta a irin wannan condition. A hankali da k'yar wahalallen bacci ya d'aukesa shima se Maghrib ya tashi ya kwantar da Zeezee a gefe sannan ya fice bayi yayi alwala ya fito. A hankali ya sake gwada temperature'nta inda yaji ya sauk'a sosai, dad'i sosai hakan ya sanya sa. A hankali ya shiga tada ita har seda ta bud'e idanunta tayi setting nasu akan handsome face nasa.
"Princess how are you feeling?" Kai ta gyad'a mishi as an answer.
"Kin d'an ji sauk'i ko muje asibiti?"
"I am feeling normal Sweetheart kawai wanka zanyi in warware."
"Are you sure?"
"Yes ai na gaya maka, fever'n come and go ne."
"Alhamdulillah toh tashi na had'a miki ruwan wanka kiyi se muyi sallah."
"Zamuyi a gida?" Ta tambaya murmushin face nata na dad'a bunk'asa a rayuwa tanason Al'ameen yana janta sallah.
"Yes Princess."
"Yeyy! Thank you." Da kansa ya d'agata chak a sama har bayin ya direta, da wankan ma cewa yayi ze mata amman tak'i don haka ya bata privacy. Tana fitowa tasa kayan daya cire mata suka idar da Sallan.
Wajajen 8:30pm Al'ameen ya fito daga d'aki ya samu Zeezee dake kwance a parlour bisa kan kujera. "Princess bazaki ci komi ba ke zaki kwanta?"
"Bana sha'awan cin komai Sweetheart don't worry, come over." Ba gardama yaje ya zauna gefenta inda ta kwanta a jikinsa before 9pm har bacci ya saceta. Yana gama kallon sports nasa ya d'auketa ya kaita d'aki sede mamakin lamarin Zeezee yake. Bata ta6a kwanciya bata ci abinci ba se yau, bayan nan kuma a kullum duk rananda ya dawo daga tafiya Zeezee bata barinsa as suna satisfying needs na junansu amman yau ko ta kansa bata yi ba. Da wannan tunani a ransa ya kwanta gefenta tare da janta jikinsa yayi bacci.
Washegari ma haka suka sake tashi Zeezee ba lafiya ta yarda suje asibiti kuma tak'i ganin ya dage se sunje tashiga yi mai kuka dan dolensa ya yarda sukayi zaman gidan kamar yadda takeso. Breakfast ma shi ya musu yau, taci ma ta kasa da k'yar ya samu tad'an ta6a ta sake komawa bacci. Ciwo kaman me aljanu, sha biyu na wucewa kuma ta dawo old self nata ta girka musu lunch se anan take neman