Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
ya cigaba da raya Zeezee har takai matakin primary 2 a karatu tanada actual 6 years kenan, tana girma se dad’a kyau take sede wani hanzari ba gudu ba, hak’waran gabanta duk sun zube se gib’i kake gani in ta washe bakin hakan yasa siblings nata suke making jess of her suyi ta mata dariya itako tayita kuka tana jan Allah ya isa in Baba ya dawo ta gaya mai ya d’au mataki. Zeezee de kam ta gagari kowa a gidan rikicin yau daban na gobe daban, bata jin maganan kowa se na Baba.
_Saturday evening, 4:38PM_
Mama ce zaune tsakar gida tana gyaran farce Zeezee ta shigo sanye take cikin wani ‘yar kanti iya gwiwarta, kitson shuku biyu ne akanta wanda ya sha beads. “Mama!” Banza da ita Mama tayi “Mama!” Ta kira for the second time.
“Meh? Meh? Meh kuma kikeso yau?” Tayi maganar tare da d’ago kai tana k’ura wa Zeezee ido.
“Kibani d’ari cikin kud’in da Ya Zannah yabani ranan.”
“Wai shin an gaya miki kud’in naki haifafa yake ne? Dubu biyu ne kacal kuma a tambayan k’ananun canji duk kin k’arar da dubu biyun, d’arin dana baki jiya shine k’arshen kud’in naki.”
“Wallahi k’arya ne kina son ki kashe min kud’ina ne kuma wallahi bazan yarda ba” tayi maganan tana bubbuga k’afa. Dirty look Mama ta watsa mata sannan ta cigaba da yankan farcenta ganin haka Zeezee ta wuceta takai dab da shiga d’akin Mama kenan Mama ta sa mata kira “Zeezee! Wallahi kika kuskura kika tab’amin kud’i kinji na rantse dukan ki zanyi na gaya miki kud’inki ya k’are.”
“Wallahi zaki gani” cewar Zeezee in a very low voice hawayenta ta share sannan ta d’au hanyan barin gidan “kuma ki dawo ki sa hula kafin ki fitan.”
“Barin sa ba” ta murgud’a baki sannan ta fice. Gidan Ummu Mufeeda ta nufa bayan tayi sallama ta gaishe ta “yauwa sannu Zeezee yawo ba d’an kwali ko? Bakisan bakin mutane kad’ai ya isa ya karya miki wannan sumar taki ba?” Shiru Zeezee tayi batace komi ba as tana nazarin wani k’aryan zata mata chan tace, “yauwa Mama na ne ta turoni wai in kinada N500 ki bata in ta samu zata miyar miki, batada cenji ne kuma tana son ta sallami wani.”
“Ji Maman Zeezee de dawata zance meh d’ari biyar kuma?” Tayi maganan tana ciro d’ari biyar d’in daga lalitarta “gashi kai mata.”
“Toh nagode” ta amsa tare da ficewa, kantin Ya Wakeel ta nufa ta kashe d’ari biyar d’in tas cikin sayayyan shirmen banza sannan tadawo gida Mama na ganinta bata ce mata komi ba ta wuce da ledar parlour. Bajewa tayi kan rug ta tab’a wannan ta tab’a wancan tana cikin haka Mama ta shigo, ko d’ago kai ta kalleta batai ba se shan chocolates nata take “ke ina kika samu kud’i kikayo wannan siyaya?” Shiru... “Dake fa nake magana! Am very sure babu kalan wad’annan chocolates cikin na school naki.”
“Haaa’ah! Nikam ba kud’in ki na d’auka ba ina ruwanki?”
“Kinsan Allah zan mauje ki, ina kika samu kud’i nace?”
“Nima ban sani ba.” Ganin Mama tayo kanta da nufin bugin ta tasa ihu “zan fad’a zan fad’a.”
Oyya speak up!”
“Gidan Ummu Mufeeda naje nace kince ta ara miki d’ari biyar-”
“Ni?!” Mama ta dafe k’irji.
“Amman karki damu tace ta baki a kyauta kinga ba sekin biya taba.” Bata hankara ba Mama ta fisgota ta hau nad’a mata na jaki bayan ta mata lik’is ta tattara chocolates d’in tayi sadaka dasu wa almajirai. Kuka kenan! Kuka Zeezee tayi tayi tana jan Allah ya isa har bacci ya isketa a garriage koda yaran suka dawo daga islamiyya suka ganta kwance gun basuyi ta kanta ba dan sun san halinta sarai daga tambayarta meya faru seta hauka da rashin kunya kokuwa in Baba ya dawo tace kai ka tab’a ta.
Cikin bacci Zeezee taji k’aran security’n motan Baba, firgit ta mik’e ta shiga rusa sabon kuka bayan yayi parking motar taje ta same sa tana hawaye “ya haka K’anwata keda waye?”
“Maamaa!” Ta fad’a a shagwabance.
“Me ta miki yau kuma?”
“Duka na tayi haka kawai” d’aga ta yayi ya share mata hawayen sannan sukayi ciki “Hafsah! Hafsah! Wallahi muguntan naki ya soma yawa kullum sede ba’a barki da ‘yar nan ba se kiyi ta dukanta sekace ganga? Ina kike fito nace!” Da confidence nata ta fito “ai bakaji me tayi yau ba...” nan ta kwashe labarin komi ta bawa Baba hoping he’ll back her today, to her suprise bayan ya gama sauraronta yace, “toh laifin waye? Da kin bata kud’in da ta tambayekin da duk hakan ya faru ne?”
“Lallai ma Alhj!” Mama ta fad’a short of words, “kana nufin tayi dai-dai kenan?”
“Bance tayi dai-dai ba amman you are partially to blame kuma karki sake tab’a ta dan wallahi zan soma jan Allah ya isa.”
“Wallahi sede kaja amman muddin ta sake tafka rashin hankali kaman na yau banga me hana ni dukanta ba abin kunya yarinya is 6 years old almost getting to 7 amma banda fatiha da nas, falaq and ikhlas ba abinda ta sani” tana kaiwa nan tayi ciki.
“Kar ki jita kinji K’anwa ta zan nemo miki malami yana miki karatu a gida islamiyya nede bara kije ba.”
“Toh Baba.”
Alwalan Sallan Maghrib suka shiga yi kasancewar yau Baba ne ze jasu a gida kowa na alwala banda Zeezee datayi cross leg kan kujera tana game a ipad, fitowan Mama daga bayi ta galla mata harara “ke bazaki tashi kiyi alwalan bane?”
“Barinyin ba!” daidai nan shigowan Baba d’akin kenan “ina yaran suke? Ku fito muyi sallah.”
“Zeezeen fah? Baza tayi sallan bane?”
“Ke ina ruwanki yarinyan nan is just 6 kuma ko a muslince ma cewa akayi se yaro yakai 7 a soma sasa.”
“Meh laifi idan an fara sata yanzu?”
“Kanki akeji Ibraheem ku fito.” Nan suka fiffito Baba yahau jansu bayan sun idar Baba yasa Zeezee ta d’auko school bag nata dan yin homework nata.
“Zab’i wanda ze miki homework d’in amman banda Ibraheem kinga yana aikin project nasa” (Ibraheem is now a petrochemical engineering student at ATBU) yana 400 level.)
“Ni shi nakeso.”
“Yi hak’uri k’anwata gobe shi ze miki amman yau ki zab’i daya cikin sauran kinji? Maza jeki su miki kizo mu kwanta” ba tare da tace komi ba ta fice k’aramin parlour, su Mariam ta tarar ba Ibraheem. “Ya Omar kamin homework d’ina.”
Omar dake jin dad’in chatting dayake ya d’ago kai tare da galla mata harara “bazanyi ba bakiga ina amfani da waya na bane.”
“Kana chatting da budurwa de kuma sena fad’awa Baba kema Adda Mariam naji ranan keda Ya Ibraheem kuna magana wai wani friend d’inshi na sonki duk sena fad’a.”
“Banza yanzu ma kije ki fad’a” cewar Mariam tare da watsa mata harara.
“Zaka min ne ko sena je na gayawa Baba?” tayi maganan tana hararsa da manya-manyan idanunta.
“Kawo in miki” yayi maganan full of sarcasm, wurga mai jakar nata tayi “Verbal Reasoning ne da Quantitative inka gama ka kaimin jaka na d’aki” ta k’are maganan tana harararsa.
“Kutcee! Ya Omar kana jinta take ma wannan rashin kunyan?” Cewar Yasmeen.
“A’a’hah! Barta kekam” yadawo da kallonsa kan Zeezee, “in nagama zan kai miki suke nan homwork d’in?”
“An bamu a handwriting ma shima kamin page 17.”
“Lallai! yanzu handwriting d’inma bazakiyi ba?” Yaseen ta fad’a.
“Ina ruwanki?” ta murgud’a mata baki “dan bance kimin ba kike da bakin magana koh?”
“Ahh ahh! Kekam Yasmeen barta mana, jeki kwanta ‘YAR GATAN BABA.” Dad’i sosai taji taje tayi ta game nata a d’aki koda Baba ya tambayeta assignment infa? K’arya ta mai tace sun gama.
“Omar I don’t trust you what are you planning on doing? Yau kai ne Zeezee ke ma rashin kunya haka baka ce komi ba” states Mariam.
“Bar ni da ita Adda Mariam ita ba hegiya ba, kwab’a mata homework d’in zan ta kama zero yadda gobe za’ayi punishing nata da kyau.”
“Pwhahhah!” Suka kwashe da dariya “wallahi amman ka burgeni da haka zamuna getting back at her fitsararriyar yarinya haka” Yasmin tayi maganan tana jin dad’i.
DON’T BE A SILENT READER TELL ME HOW U ACTUALLY FEEL, THINK ABOUT MY NOVEL
MIEMIEBEE
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 12
_Heres a page in honour of you sweetheart divas😻 *Maryam (Abmar), Deeylerhh* and *MeenoUr,* my boo thang thang, ILY'all!💕_
9:14PM Omar yayi sallama d’akinsu Mama ya ajiyewa Zeezee jakarta tare da yiwa su Baba seda safe. Bayan Mama ta fito daga wanka ta kalli Zeezee data d’ale tsakiyan gado tana shirin bacci tace, “jibi abin kunya” sannan ta k’arasa gaban mirror tare da jan kujera ta zauna ta soma shafa mai, jira take Baba ya tanka ta taji yayi shiru hakan ya sake bata daman magana “ace yarinya shekarunta shida almost getting to seven amman a tsakiyan iyayenta take kwana ko a ina aka tab’ayin haka oho.”
“Ji yadda kike magana kaman kinyi mata d’aki tak’i kwana ciki, bansani ba ko a parlour kikeson tana kwana.”
“Kamar ya a parlour? Baga d’akin su Yasmeen ba.”
“Wai kina nufin Zeezee ta soma kwana da su Mariam? Mugayen can!”
“Eh mana!” ta basa amsa take. “Ba yayyun ta bane?”
“A dalilin meh zan tura K’anwata kwana da wad’ancan mugayen? Ba abinda ze kai Zeezee d’akinsu Mariam kiji ki sani.”
“Lallai kuwa!” Tayi maganan tare da miqewa ta nufa gun wardrobe nata searching for her night gown “shikenan kullum damu zata na kwana?”
“Eh har sena mata d’akinta itama.”
“D’aki?! Ta zaro ido waje a ina zakayi mata d’akin?”
“Wannan kuma is for me to know and you to find out kin gama feshe-feshenki ki kashe mana wuta, Allah bamu alkhairi” yana kaiwa nan yaja musu comforter da Zeezee sukayi baccinsu comfortably as always.
~* ~* ~*
_Monday morning, 6:10AM_
“Ke! Zeezee wallahi ki tashi kona zuba miki ruwan sanyi iskancin banza shekaranki nawa da shiga makaranta amman ace kullum sekin bawa mutum headache kafin ki tashi a wani gidan ma ke za kina yin wanka da kanki, tashi!” Yasmeen ta k’are maganan cikin sautin tsawa ganin ko kad’an Zeezeen dake baccinta tana tsotsan thumb finger’nta bata motsa ba, hakan ya sake k’uludda ita “wallahi zan mareki tunda Baba bayi gida.”
“Mareta wallahi” cewar Mama ai tana jinki. Tas! Yasmeen ta wanke d’uwawun Zeezee da mari da force ta miqe zaune tare da sa ihu.
“Wallahi barin je makarantan ba muguwa kawai.”
“Huummm!” Yasmeen ta toshe hanci “ji warin baki sekace latrine, k’azama kawai tashi da Allah!” haka da k’yar Yasmeen ta samu tasa Zeezee toilet nan ma zama tayi kan toilet sit tak’iyin brushing da ya kamata tayin, bayan 2 mins Yasmeen ta dawo ready to bath her taga ko brushing Zeezee batai ba hasali ma bacci take comfortably kan toilet sit d’in, ruwan sanyi ta tsiyaya daga famfo ta fesa mata a fuska firgit har tana neman fad’i daga kan sit d’in ta farka “meh haka? Muguwa kawai, Allah ya isa” tasa ihu “Allah ya isa mumuna kawai.”
“Fad’i koma meh wallahi yau tunda Baba bai gida se kin gommaci kid’a da karatu, maza sauk’o daga kan sit d’in.”
“Toh kin min tsarki ne da zan sauk’on?” Ta watsa mata harara.
“Yanzu fitsarin ma se an miki tsarki?”
“Pupu nayi.”
“Mschww dirty girl kawai”
“Niba ke ce zakimin ba Ya Omar nakeso.”
“In zaki tsaya ki tsaya” aiko Zeezee ta bijire mata itafa se Omar ze wanke mata pupu. Mama ce tasa baki a k’arshe ta tura Yasmeen kirawo Omar.
***
Bayan ta samesa a d’akinsu ta isar masa da sak‘on.
“Wallahi bazan jeba kashin ya bushe a jikinta inde ni zan wanke mata.”
“Kaine kashi ze bushe a d’uwawunka ba ita ba d’an banzan yaro kawai maza tashi!” Scolded Baba “bazaka tashin bane sena gaggaura maka mari?”
“Allah sarki Baba yarinyan nan fa yaci ace ta soma tsarki da kanta she is almost getting to seven (7) years”
“Eh bazata wanken ba seta cika seven (7) d’in wuce nace mana!” Haka yana kumbure-kumbure yaje ya wanke mata pupun Yasmeen ta mata wanka. 6:40AM Yasmeen ta kawo wa Zeezee breakfast nata na chips and eggs aiko tana gani ta soma rigima “ni bance chips nake so ba ni indomie zan ci.”
“Kinga ba time yanzu K’anwata yi hak’uri kici wannan d’in.”
“O’o tahau shure k’afafu ni indomie nakeso.”
“Oya Yasmeen kiyi sauri ki dafa mata kiyi amfani da ruwan kettle seya dahu da wuri.” Kamar wacce zatayi kuka Yasmeen tace, “wallahi Baba ba ci zatayi ba yanzu da indomien aka dafa cewa zatayi chips takeso neman sa mutum aiki ne kawai.”
“Banason suratan banza kije ki dafa mata nace!” In 18 mins indomie’n Zeezee ya iso kad’an taci ta jagwal-gwala saura as expected, Mama ta zab’a wai ta sama ta uniform, bayan an sa mata ta d’ago socks nata ta samata anzo sa takalmi aikuwa Zeezee tace ba wannan zata sa ba yau bayan taga shi Omar ya mata polishing, haka yana ji yana gani Baba yasa sa sake mata polishing wani sam be damu ba saboda yasan meya shirya mata a school yau.
AT SCHOOL *~ *
“All stand!” Ordered Mrs. Audu (form teacher’n su Zeezee) nan da nan su Zeezee da sauran class members nata suka mik’e suna nan har yanzu class da seat nasu d’aya da Lubiee they must be best friends now. “Submit all of your homeworks row-by-row all at once.” Nan da nan d’aliban suka fiddo da homeworks nasu su kayi kamar yadda teacher’n sun ta buk’ata.
_7 minutes later..._
“Zainab Isma’il Yusouf!” Called Mrs. Audu angrily, “come here!” Zeezeen da batasan me tayi ba ta mik’e a sanyaye “yes Ma’am.”
“Whats wrong with you? How can you fail all of your homeworks?”
“Me?” Zeezee ta dafe k’irji.
“Yes or do you need some proof?” Mrs. Audu ta d’ago mata zeron da takama a duka homeworks natan “shame on you! class say shame on Zainab” nan ‘yan aji suka hau yima Zeezee shame shame shame illa Lubiee ce bata mata ba. Kuka Zeezee tayi tayi ranan ana fita break ta tarke wata Deborah a lungu tayi mata d’ankaren duka sannan tayi warning nata kan inta kuskura ta kai k’ararta seta mata wanda yafi wannan. Kuma badan komi ta daki yarinyan ba sedan wai ta lura da Aunty tasa su yi mata shame duk Deborah tafi yi da ihu. Baba na zuwa d’aukanta ta nuna mishi homework da Omar ya mata ta fad’i.
*** _Back home..._
“Omar! Omar! Zo nan!” Omar dayasan this was coming ya mik’e yaje “na’am Baba” wulla mai littafin Baba yayi, “explain this, meh haka?” Bayan ya k’are wa makeken zeron dake kan fejin kallo yayi k’ok’ari ya had’iye dariyan sa sannan yace,
“Jiya ina kiranta tazo muyi mata homework d’in tak’i ta gudu nikuma... Nikuma...”
“Kai kuma kayi deciding da kayi failing nata har kasa ayi mata wak’a gaban aji koh? Toh maza ka bata hak’uri.” Ai atapir Omar yace baze bada ba seda Baba yayi dagaske yabata hak’urin aka wuce wajan. Fita Baba yayi kafin nan yace, “kice Mamanku tayi miki homework naki kinji?”
“Toh ba-bye”
Mama dake kitchen ne ta fito tana yi mata sannu da zuwa se gani tayi fuskan Zeezee da alaman yak’ushi. “Ya haka waya miki wannan abu a fuska?”
“Babu” tabada amsa tana cigaba da tafiya.
“K’arya kike fad’a kikayi ko?”
“Nikam ki barni” daga nan ta wuce ciki, bayan tagama wulli da socks da takalmanta as always tabar vest da panties zallah sannan ta fito da school bag nata zuwa d’akin Mama “wai aji Baba kimin homework d’ina.”
“Yau kuma? Ki jira yayyun naki suka dawo su maki.”
“Ba kina gani ba Ya Omar ya jefar dani da gan-gan naci zero ni kimin.”
“Kawo toh” bayan ta fito da homework d’in Mama ta buk’aceta ta faddo da pencil pack nata sede wayam ba komi ciki.
“Ina pencils nakin suka je?” Shiruu ba amsa, “dake fa nake magana? Ina sabin pencils dana sa maki ciki jiya?”
“Haaa’a! babu sun b’ata ki d’auko min wani” hannu Mama takai bakinta ta bige da k’arfi seda Zeezee tasa ihu, “idan baki bar min magana da rashin kunya ba na riga buge bakin naki kenan.”
“Allah ya isa” ta fad’a tana riqe da bakin nata.
“Ina pencils d’in suke? Ko ki fad’a ko in miki d’ankaren duka.”
“Ni shikenam kullum kiyita duka na Allah ze sak’amin.”
“Ina pencils d’in?!” ta daka mata tsawa, itama a tsawacen ta miyar mata da amsar;
“Sun b’ata babu!”
“Toh wallahi ki bud’e wannan kunnuwan naki da kyau ki jini, zan sa miki wasu biyun kika b’atar da wayan charger na zan chod’e wannan k’afafun naki kinji na rantse” haka da rigima suka samu suka k’are homework d’in.
Baba na dawowa gida that was by 4:23PM kenan Mama taje ta irga mai kan Zeezee taje tana fad’a a school, atapir Baba yace be yarda ba a kira Zeezeen yaga fuskan. “Zeezee! Zeezee! Zo” Mama ta kirata, d’akinsu Mariam ta shiga da wuri ta lak’uto foundation da concealer nasu ta shafa gun ta rufe tabon yak’ushin sannan taje “meneh?”
“Zo ina gunda k’awar taki ta yak’ushe kin?”
“Nifa ba a yak’usheni ba.”
“Maqaryaciya kawo fuskan” ba musu taje Mama ta duba gun tarasa ciwon.
“Ina yake toh? Neman yima yarinya sharri kawai.”