YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   70 / 98

207K to 210K   out of 291.7K words

Bayan ta gama shirin kwanciyarta ta fito ta tarar da shi a parlour, "kin shiga zaki kwanta kenan?" Ya tambayeta yana sanye da vest da wandon kaftan na d'azu.
"Eh" seka shigo take son ce masa amman tasan ba shigowan zeyi ba. "Seda safe." Ta k'ara akai.
"Sleep safe and sound." Kai ta gyad'a mai ta koma d'aki. Tana kwance bisa kan gado kawai ta soma kuka, so take ta kira Lubiee ta sanar da ita but she wants to give Al'ameen some time ai yama yi k'ok'ari daya dawo da ita despite kalan rashin kyautatawa da rashin kunyan data mishi da a baya, yayi sacrificing virgin duk a kanta saboda haka zata basa some space. Da tunaninsa yau ma tayi bacci.

*MIEMIEBEE. Team #YGC!🎀*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*

*March, 2017*
6⃣2⃣

_Assalamu Alaikum y'all Beautiful people. I will first of all like to show my deepest appreciation fort the love and support you guys are giving to YGC!🎀 It really means so much, MIEMIEBEE na alfahari daku. I am head over hills in love with you, OneLove❣_
_So kamar yadda kuka sani d'an Adam ajizi ne, totally na mance ban sa an sake d'aura wa Maj-Gen. da Zeezee aure ba a last page saboda shagalin events ya tafi min da mind🤣 so ayimin afuwa. Lets fire on!_


As early as possible ta tashi yau ta had'a mishi breakfast had'ad'd'e sannan ta koma tayi wanka tayi kwalya tsaf abinta kaman a gudu da ita don kyau, ga kuma k'amshin dake tashi daga jikinta. Wajajen 8am Al'ameen ya fito daga d'akinsa yana sanye da vest da irin free size wandon exercise d'innan. Tana zaune akan kujera ta sauk'a har k'asa sannan ta gaishesa cike da ladabi.
"Me haka kuma Zainab? Bazan amsa ba sekin tashi." Kuma dagasken yak'i amsawa seda ta tashin sannan ya amsa suka gaisa. "Meya tada ke yau haka da wuri? Zaki fita ne?"
"A'a I made you breakfast."
"Uh-oh" zallah yace.
"Zaka fita ne?" Ta tambayesa.
"No zanyi Training men d'ina ne."
"Since before ka karya Ya Al'ameen?"
"It won't take long karki damu."
"A'a nikam ka karya please kafin nan already na kai musu nasu su."
"Zainab karki damu kinji? Actually yau ina azumi" Allah ya soshi yau Thursday ne.
"Oh is that so?" Tayi maganan sounding disappointed.
"Yeah thanks kinji?" Yana kaiwa nan ya fice, itama k'in karyawan tayi inda ta zarce d'akinta tana me kuka sosai bata san ya zatayi da ranta ba. Bayan Al'ameen ya gama training men nasa ya koma ciki yayi wanka ya shirya tsaf cikin k'ananun kaya da ya sake fidda shi sosai sannan ya nufi d'akin Zeezee inda ya tarar da ita tana bacci. Smiling kad'an yayi at her view sannan ya fice. Bayan Azahar Zeezee ta tashi inda take tambayan me gadi ko Al'ameen ya fita ne yake sanar da ita eh yace he won't take long ze dawo. Wani takaici ta jiyo. D'aki ta koma ta kirasa wanda bada jimawa ba ya d'aga "hello Ya Al'ameen?"
"Na'am Zainab har baccin ya isheki ne?"
"Ya Al'ameen baka dawo ba har yanzu?"
"Zan dawo soon karki damu."
"Toh kana azumi baka sanar dani me kakeson shan ruwa dashi ba."
"Actually, Zainab na karya azumin nawa kaina ke ciwo sosai d'azu." Tasan k'arya yake he is just looking for a reason karya ci girkinta. Danne zuciyarta tayi tace. "Ayyah Allah k'ara sauk'i toh se anjima."
"Yauwa take care." Sauk'e wayan tayi a hankali sannan ta shiga aikin kuka da k'yar ta samu ta idda sallah ta kira Mama suka gaisa inda ta nuna mata everything is fine. Bayan La'asr Al'ameen ya dawo a lokacin Zeezee na a d'akinta kayan duniya sun isheta, she can't tell how she is missing Al'ameen.

Kasancewar gobe Al'ameen ze koma Abuja yau bayan Sallan isha ya shigo d'akin Zeezee ya sameta zaune bakin gado ta zurfafa cikin tunani sosai. Seda yayi gyaran murya sannan tayi noticing shigowansa. "Uhn Ya Al'ameen I'm sorry banji shigowan ka ba."
"Tunanin me haka kike Zainab?"
"Babu" ta mai k'arya.
"Erm nazo sanar dake ne gobe zan yi resuming office."
"Har gobe Ya Al'ameen?" Tayi maganan sam bata ji dad'i ba.
"Eh Zainab kinsan sun kaimu Maiduguri."
"Ayyah, banji dad'i ba nad'au sun baka erin 2 weeks d'innan ne."
"No, kiyi hak'uri kinji?"
"What for?"
"Auren Soldier seda hak'uri Zainab, I can't stay with you for a long time."
"I totally understand you Ya Al'ameen Allah ya taimakeka ya kuma kare ka."
"Ameen thank you."
"Bazaka ci dinner ba?"
"Nasha black tea bana jin yunwa."
"Toh shikenan."
"Toh seda safe."
"Allah bamu alkhairi" ta fad'a hawaye na forming rapidly a idonta she don't think she can hide it anymore. Har ya bud'e k'ofa ze fita Zeezee ta kira sunansa chak ya tsaya tare da juyawa. A nitse ta miqe ta k'arisa gabansa kanta a k'asa ta fara da cewa "Ya Al'ameen am sorry."
"What for Zainab?" Yayi saurin tambaya.
"Ya Al'ameen stop pretending as if things are good between us nasan har yanzu kana min kallon dump, stupid, disrespectful and disregarded Zainab but thats not true, I've changed am not the Zeezee you use to know."
"Zainab what are you talking about?" Finally ta d'ago kanta tana kallonsa, "you don't love me anymore do you? Please be sincere and tell me the truth, ka dawo dani ne badon kana sona ba illa don kana tausaya min, am I right?" Shiru yayi ya kasa cewa komi a yayinda degree na rolling tears nata ya dad'u. "I should have known-" katse ta yayi "Zainab-" itama da sauri ta sake katse sa.
"You don't love me anymore, and I don't blame you Ya Al'ameen saboda laifi na ne, I was dense and stupid then I wasn't thinking straight, I failed to realize that you are my true and perfect love, I love you Ya Al'ameen ina sonka, I can go the whole day shouting I love you because I can't get enough of you." By now kuka take sosai "Zainab enough okay?" Yayi fad'a at last.
"Its not okay Ya Al'ameen tunda baka cin abincin dana dafa maka, baka iya kwanciya a inda nake, you don't call me your princess anymore taya kakeso in samu peace of mind? Wallahi da zan iya reversing time da nayi and make things right, I love you Ya Al'ameen" ta d'ago both hands nasa ta had'a da nata. "I love you so much, morethan you could ever imagine. I've never had this feeling with anyone not even Adeel. I love you Ya Al'ameen please ka tausaya wa rayuwa na kadena punising d'ina haka. Anytime kace bazaka ci girki naba ji nake as if in d'au wuk'a in kashe kaina, if only nasan ya zanyi maka describing just how much I love you I would have done it a long time ago."

"Zainab..." ya sake kiran sunanta a hankali gabad'aya ta bashi tausayi yadda take kuka.
"Please kar kace no, please don't." Hannun nasa ta sake kawai tayi hugging nasa gagam "I'm truly sorry" tayi stating cikin kukan. "Forgive me please, forgive your Zainab and kabani one last chance."
Tausayi sosai ta bashi he never expected these words from her a hankali ya zagaye hannunsa a bayanta "stop crying okay? Ya isa haka kukan." Kai ta kad'a "unless you tell me you love me also in ba haka ba bazan iya dena kuka ba, I need you to tell me please tell me." Da k'yar ya jata daga jikinsa sannan yayi cupping face nata "I love you Zainab, you know that already koba haka ba?"

"Then why are you punishing me like this?"
"I'm not punishing you Zainab I just don't want to be a burden to you."
"Haba Ya Al'ameen! Taya zakace haka? I'm your wife remember?"
"I know bar kukan haka toh." Kanta ta sunkuyar sannan tace, "meaning zaka dawo nan da kwanciya?" Shiru yayi yana mamakin Zeezee yadda she can't hide how much she loves him anymore, shima he loves her as much saidai bayason ya nuna mata ne gani yake like har yanzu ba sonsa take ba, but now he does.
Jin yayi shiru tace, "baza ka dawo ba? Well, I'm sorry" ta k'are maganan tana share hawayenta. One step back tayi taking wanda da wuri ya kama hannunta "we'll do it anyhow *My Princess* wants it" ya sanar da ita yana murmushi. Kasa 6oye farin cikinta ta tayi, jikinsa kawai ta shige tana mishi wani irin hug cike da so da k'auna. "Thank you *My Soldier* I love you so much." _My Soldier_ yaji dad'in name d'in.
"I love you too My Princess" yayi maganan tare da hugging nata back. Sun d'au tsawon lokaci ahaka, se shaqan daddad'an k'amshin jikin juna suke barin ma Zeezee dake ji wane a aljannan duniya aka tsunduma ta, Ya Al'ameen is her world. Se chan Al'ameen yayi breaking hug d'in.
"My Soldier?" ta kirasa tana kallon hannayensa data rik'e a cikin nata.
"My Princess" yayi answering back.
"I so much love the name, call me again." Murmusawa yayi "and that smile also, I love it. Say it again please."
"My Princess."
"I love your voice, I love you in whole Ya Al'ameen, words can't tell how just much I love you."
"Zainab I love you as much also, you are my princess."
"I love you you more My Soldier and I don't think so, I love everything about you, your voice, smile, dimples, abs (packs), muscles, height, just everything about you drives me crazy." Ta fad'a sincerely. Murmushi yake sosai by now, "I love you also Princess, I love your pretty face, long hair, smile, charisma, and everything."
"Your Princess loves you more, muje kaci dinner kaji?"
"Princess am not hungry." Fuska ta maraice, "you call me your princess amman bazaka iya cin girki na bako? Shikenan." Fuskanta ya d'ago da hannunsa.
"Don't be sad kinji? You'll be the one to make me breakfast gobe."
"Amman bazaka ci na yau d'in ba?"
"Princess what part of I'm not hungry don't you get? Ko so kike se cikin nawa ya fashe tukun."
"Toh ina ma tunbin yake bale cikin ya fashe? Kai de kawai kace bazaka ci ba saboda ban iya girki ba."
"Shh! Kema kinsan thats a lie, har yau ina mafarkin rice and stew in kincan."
"Toh in haka ne muje ko kad'an ne ka ta6a."
"Princess tunbi kikeson inyi ne?"
"Ai jikinka is fit bazaka ta6a yin tunbi ba muje kaji? Ko kad'an ne seka ci, I need My Soldier to eat dinner before going to bed."
"As you wish Princess." Hannunsa ta kama cike da jin dad'i har suka isa dining d'in sannan ta ja mishi kujera yayi godiya tare da zama, na gefensa taja ta zauna itama sannan ta shiga serving nasa.

"A'a'ahh Princess ya isa, ina zan kai wannann abinci?"
"Here" tayi pointing cikinsa.
"Karki k'ara ya isa, am full already." K'in jinsa tayi seda ta kusan cika mai plate sannan ta tura mishi plate d'in gabansa "eat ko nayi feeding naka?" Dariya sosai ya tsaya yi due to her statement in which Zeezee finds him cute. Zama tayi se kallonsa take, da k'yar ya tsagaita dariyan nasa ya mata apologising "I'm sorry."
"Keep on laughing, you have such a cute smile, I love it."
"I'm sorry" ya sake apologising.
"Toh ma dariyan me kake haka? Dan nace zanyi feeding naka?"
"Eh mana, tsoho dani." Baki ta sake wide in shock tana kallonsa, "waye tsohon?"
"Ni mana."
"Allah ka sake kiran kanka tsoho zanyi kuka."
"Aww ba tsohon bane toh?"
"A'a wallahi, don bana ce maka Baby shine zaka ce kai tsoho ne? Please kar ka sake banaso."
"Toh Princess bazan k'ara ba."
"Yauwa My Soldier finish your meal." With a nod ya kai spoon d'aya baki inda ya tsaya yanata exaggerating dad'in abincin, itako banda kallonsa ba abinda takeyi, he is way adorable cin abincinsa ma daban yake dana mutane. Spoons less than 10 yayi yace ya k'oshi.
"Har ka k'oshi My Soldier? Me kaci anan?"
"Are you kidding me Princess?"
"Yi hak'uri ka k'ara koda spoon biyar ne kaji?"
"Princess on normal basis ma naci 15-20 spoons na k'oshi bale yau da am already full."
"Yi hak'uri ka k'ara."
"Bakisan bana cin abinci sosai bako?"
"Aysha once told me amman Yi hak'uri ka k'ara. Kasan wani abu?" Kai ya kad'a nufin a'a. "Kai spoon d'aya tukuna se in fad'a maka."
"Am full Princess."
"Bakason kaji kenan."
"Inaso, tell me."
"Toh ka kai spoon d'ayan first." Haka tayita masa wayo har seda ya kai 5 more spoons sannan tace, "are you ready?"
"I am." Yayi maganan tare da picking cloth ze goge bakinsa inda da sauri Zeezee ta kar6e, "let me" ta fad'a tana yimai murmushi. Kallonta kawai ya tsaya yi a yayinda ta shiga goge masa bakinsa a hankali in a romantic manner "you are way handsome My Soldier, bana gajiya da kallon ka." Tayi informing nasa.
"Ban kai ki kyau ba ai Princess."
"Ka zageni de kaji dad'i."
"Uhm so me kikeson fad'amin duk kinsa na k'osa."
"I can die for you, you know?" Ta fad'a mockingly.
"Princess!" ya saki baki totally speechless yana kallonta "all these spoons? Kawai don kice min you can die for me neh? Kema kinsan I can die for you a thousand times if needed."
"I'm sorry kaga yanzu ko bakayi breakfast ba gobe bazaka ji yunwa ba, muje in had'a maka akwatinka."
"Na riga na had'a karki damu."
"Oh toh thats good." Daga nan kuma se duk sukayi shiru suna tunanin abubuwa daban-daban. Chan Al'ameen ya kirata, "My Princess?"
"Na'am My Soldier." ta amsa tare da d'ago kai tana kallonsa.
"Since when kuka rabu da Adeel?" Take yaga mood nata ya sauya.

"I'm sorry didn't mean to kiyi hak'uri, in bakiya son ayi maganan shi so be it." Hannun su ta ta had'a musu, "you are My husband Ya Al'ameen I have no hidden secret for you."
"Are you sure?" Kai tamai nodding sannan ta amsa, "getting to 10 months now."
"Wow!" Yayi exclaiming "kana son kaji sanadin rabuwan mu da kuma rayuwar da nayi living a gidan shi?"
"In har ze miki ruining mood naki and make you cry banaso." Murmushin takaici ta sakar masa sannan ta fara kaman haka "tun ranan da na rabu da kai na cuci kaina Ya Al'ameen..." labarin komi ta basa ba tare da ta 6oye mai wani abun ba, abinda ya kama daga kan fasa mata waya da Adeel ya soma, staying late at night, kula 'yan mata, sata yimai wanki, dad'o aure, forcing nata into bed, wulak'anta ta komi seda ta basa a yayinda take hawaye sosai. Shima Al'ameen sosai ya tausayawa Zeezeensa, just how bad have she suffered? Abinda Zeezee bata fayyace wa Al'ameen kad'ai ba shine na lalacewar mahaifarta, gudun karya ji ya tsaneta shima just like how Adeel did. Be k'arisa jin labarin nata ba ya mik'e tare da janta jikinsa yayi hugging nata yana bubbuga bayanta a yayinda volume na kukan ta keta k'aruwa. Da k'yar ya samu Zeezee tayi shiru se anan ya d'agota daga jikinsa yana share mata hawayen nata da hannunsa.

"You are forever free from him Zainab, I'll never let you leave my side, I will never torture you like that, I will love you like there's no tomorrow, I'll take care of you like an infant baby. I will never hurt you than to make you cry, I'll always be there as your Soldier to protect you Zainab, you are the love of my life, I love you so much." Hawayen jin dad'i

70 / 98