Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
“A’a Ya Al’ameen dan Allah karka fita wallahi dukana zatayi” Zeezee tayi maganan tana sake matsesa a jikinta.
“Mama please kiyi hak’uri karki ta6ata zatayi wanke-wanken.”
“Naji bazan ta6a ta ba ka fita to mu samu mu had’a kitchen d’in.”
“Ya Al’ameen wallahi kafita duka na zatayi.” Seda Mama tayi dagaske tasamu ta fito da Al’ameen. “Maza kama yin wanke-wanken wawiya kawai.” Nan da nan Zeezee ta shiga washing dishes d’in sama-sama kaman yadda ta saba ashe duk kallonta kawai Mama take, ta gama zata fara jerawa Mama tace, “dawo dawo dasu nan” cup d’aya ta d’aga ta shafa jikin se maik’o kawai malam sekace be shiga cikin ruwan kumfa ba. Lafiyayyen mari Mama ta kai mata a baya kafin tasa ihu Mama ta aza hannunta akan lips nata tana mata alaman tayi shiru. “Wallahi kika bari Maj-Gen ya fito kinji na rantse sena gayawa Babanki har nan ya biki ya baki d’ankaren duka” jin haka ta had’iye ihun nata tare da shanye hawayen nata.
“Hakane kin wanke? Bazaki bar aikin cuwa-cuwan nan da kika saba bako? Kanki ma yanzu zaki cutar tunda tun chan agida haka kikeyi.” Mama na tsaye a kanta Zeezee ta sake bin wanke-wanken seda suka fita k’al sannan ta share kitchen d’in tayi mopping ta goggoge kan counter dasu gas cooker and microwave. Bayanta kan ze 6alle, tunda tasan kanta bayan aikin wankin da Ya Ibraheem ya ta6a sata bata sake aikatuwa kaman na yau ba. “Shara fa kinayi?”
“Mama dan Allah kiyi hak’uri ki tafi gida wallahi nayi shara yau bayana yana iya 6allewa.”
“Ma’ana bakiyi kenan?”
“Zan fara gobe dan Allah kiyi hak’uri.”
“Maza d’ago tsintsiya ki bini ashe ba sharri idona suka miki ba tun shigowana na karanci gidan naku da k’ura” haka Zeezee tana tura baki tana matse k’walla tabi bayan Mama, kap gidan ranan seda Mama ta sata ta share ta kuma yi mopping harda dusting sannan tabi gidan duka da turaren wuta. Tanayi tana kuka amman hakan besa Mama ta k’yaleta ba.
“Wayyo Allah zan mutu!” tayi maganan baje akan tiles tana riqe da bayanta.
“Tashi kije ki kiramin Maj-Gen. d’in.”
“Mama wallahi bazan iya tashi ba.”
“Aww na saki share cikin gidan naki kenan ko?”
”A’a zan tashi zan tashi” tana bud’e d’akin nasa ta tarar dashi akan laptop yana aiki “wai kaje Mama na maka magana.”
“My Princess ya haka da riqe baya?”
“Ban sani ba ai wallahi ka kyauta nikan kazo.” Bayanta yabi suka fice akan kujera opposite na Mama suka zauna “gani Mama.” yayi maganan gentlemanly.
“Yauwa Maj-Gen ka bud’e kunnuwanka da kyau ka saurareni don Allah nace.”
“Toh Mama.”
“Take a look at your house now what can you say?” Yadda Mama ta buk’acesa yayi. He couldn’t believe it ko ina se sparkling yake ga k’amshin turare na tashi. A rayuwa yanason yaga muhallinsa da tsafta kaman haka “wow” yayi breathing “its sparkling yayi kyau sosai.”
“Good toh haka nakeson gidanka ya kasance a kullum, alk’awarin abu d’aya nakeson kamin, ka tabbata ko wani safiya Zeezee tayi shara tayi moppkng after each 3-4 days kuma tayi dusting, wanke-wanke kuma ban yarda wanke-wanke ya kwana a gidanka ba inba wai rashin lafiya take ba. Kar ya zamana takai sati bata wanke muku toilets ba. Zancen me aiki kuma banason ka d’au ma Zeezee me aiki dukkanin aikin nan dana lissafo ita nakeson tanayi can I count on you?”
“Uhmm Mama you see-”
“Bazaka iya min ba kenan?”
“A’a bawai haka bane-” saurin katsesa tayi “then can you promise me all that?”
“Yes Mama, I promise in shaa Allah.” wani mugun kallo Zeezee ke binsa dashi sannan ta sauk’a har k’asa tana kukan munafirci “Mama dan Allah kiyi hak’uri wallahi inhar na cigaba da aikatuwa haka kullum wataran gawa na zaku cire daga gidan nan, kiyi hak’uri dan Allah kibar Ya Al’ameen ya d’aukomin me aiki I promise tare zamuna yin aikin da ita Allah wallahi.”
“Zainab banason sakarci kina jina koh? In kinga Maj-Gen. ya d’au miki me aiki toh wallahi se in kin haifafa hidiman yara ya fara miki yawa, kana jina ai Maj-Gen?”
“Eh Mama naji.”
“Good ke kuma addu’a zan yita miki Allah shiryeki don zagi bashida amfani, amman kisani duk ranan da garin Allah ya waye baki aikata wannan aiki dana lissafo ba bakuma dan wani k’wararren dalili ba Allah ya isa na yana kanki.”
“A’a Mama please, kiyi hak’uri in shaa Allah ma zata nayi ba sekin ja Allah ya isa ba.” cewar Al'ameen.
“No ka barni da ita nasan halinta sarai ina barin nan bazata sake d’aga tsintsiya ba tunda kai na lura baka mata magana.”
“Kin jini ko bakiji ba?” Shiru Zeezee tayi not ready to talk.
“Aw in kira Babanki na fad’a
mishi.”
“A’a wallahi naji, naji karki kirasa dan Allah” tayi maganan fear na building a tare da ita. Da mamaki Al’ameen ke kallonta ashe duk rashin kunyarta tanada weak point, da kyau. Hak’uri Mama ta sake bawa Al’ameen akan rashin hankali irin na Zeezee sannan kuma a gabansa tayita yiwa Zeezee fad’a sosai sannan ta bisa da nasiha.
Bada jimawa ba tace zata tafi wanda Al’ameen yasa driver’n sa yayi dropping nata. Tana tafiya Zeezee ta zarce d’akinta tana me rusa kuka tsakaninta da Allah yanzu shikenan ita hutunta ya k’are kenan? Kukan ta cigaba dayi koda Al’ameen ya ganta be mata magana ba sabida yasan theres no point doing so in banda rashin kunya ba abinda zata masa don haka ya zarce d’akinsa shima.
*~ *~ *~
Washegari Zeezee ta tashi da sassafe ta gama ayyukanta tas, ji take wane bayanta ze 6alle dan azaba. Al’ameen na fitowa yaga ko ina sparkling clean ga kuma k’amshin turare d’akin Zeezee ya nufa ya sameta miqe kan gado tayi ruf da ciki. A nitse ya k’arisa ya zauna kan side drawer nan ta juya mai baya. “My Princess?”shiru ba amsa, “My Princess sannu da aiki kinji? Everywhere is sparkling clean ga wannan tukuicin aikin da kikayi.” ya ajiye mata bundle na N50.
Juyawa tayi don ganin meye tukuicin tana ganin kud’in ta d’aga bako kunya. “Bayanki na miki ciwo ne?” Kaman bazata amsa saba se kuma ta gyad’a kai. “Do you need a massage?” Tana so tana kaiwa kasuwa “ni banaso kafita min daga d’aki ai duk kaine.”
“Yi hak’uri toh.”
“Ni kafita min.” Besake ce mata komi ba ya miqe, ya kaiga bakin k’ofa ta tsayar dashi “kazo kamin wallahi bayana kaman ze 6alle” murmushi kawai ya saki yana kallonta da take rage kayan jikin nata, bajewa ta sake kan gadon tana jiran ya fara mata tausar. A hankali taji sauk’an hannunsa akan bare back nata, take heart nata yayi skyrocketing ita kanta ta rasa dalilin da yasa every single touch na Al’ameen yakeda strong influence akanta.
Massaging mata baya ya shiga yi a hankali wanda don dad’i har wani bacci Zeezee ta soma ji, hakan ya cigaba da mata har seda tayi bacci. Kwanciyarta ya gyara mata sannan yaja comforter ya rufeta da shi tare da rage speed na AC’n tunda batada kaya. Dawowa yayi ya zauna akan side drawer yana k’are mata kallo a yayinda wani irin wutan sonta ke sake ruruwa a zuciyarsa, he can’t wait for the day Zeezee zatayi accepting nasa as her husband, surely that day will come shiyasa baze gaji da trying to make her happy ba. What a gentleman!
Hannunsa ya d’aga a hankali ya aza akan fuskarta yana shafawa sam bata motsa ba seda yaja hancinta. Hannun nasa ta kama tasa k’ark’ashin kumatunta duk a cikin baccin, ta sake kuma tak’i ta sake hakan ya sanya Al’ameen murmushi sosai. Haka ya cigaba da zama a wajen yana k’arewa beautacious innocent while at sleeping face nata kallo, da k’yar ya samu ya iya ya zare hannun nasa tare da pecking forehead nata yayi whispering “I love you Princess” sannan ya fice.
_5 days later..._
Gabad’aya rayuwan kanta tabar yiwa Zeezee dad’i dalili kuwa shine wannan aiki da Mama ta aza mata shi na dole, domin haka tayi coming up da plan. Tana idar da sallan Asuba yau ta d’au towel ta tsoma cikin warm water sannan ta mammatsa a jikinta seda ya d’au zafi. Tana jin dawowan Al’ameen daga masallaci ta ruga gado ta kwanta tare da jan comforter ta rufe duka jikinta dashi harda kanta ciki tana kakkarwa. Not long enough ya shigo d’akin nata as usual don duba ko tayi Sallah tunda yanzu ba kwana d’aki d’aya suke ba.
“Princess kinyi sallah?” Yayi maganan some inches away from her bed har anan bata motsa ba. “Zainab?” Cike da kasala wane wacce batada lafiya ta leqo da fuskarta waje “Ya Al’ameen...” Ta fad’a cikin wani irin muryan dake nuni da mutum baida lafiya.
“Subhanallah! Princess are you okay?” Ya k’are maganan yana zaune akan gadon a gefenta. “Meke damunki Princess?”
“Zazza6i nakeji.”
“Zazza6i?” Ya miqa hannu tare da feeling body tempreture’nta extremely high ya jisa. “Subhanallah! Princess you are sick, sannu kinji?” Wutan d’akin ya kunna ya shiga toilet tare da fitowa da bowl cike da ruwan sanyi kad’an. Matsa mata jiki dashi ya shiga yi da towel d’in idan ya tsoma cikin ruwan. Ahaka har fake hot tempreture’n nata ya sauk’o se kukan shagwa6a take ta mai.
“Sannu kinji? First thing in the morning za muje asibiti, sannu koh?” Comforter yaja ya gyaggyara mata kwanciya, ya miqe ze fice kenan ta riqo hannunsa “Ya Al’ameen Mama nakeso, dan Allah ka kaini wajen Mama ita kad’ai zata iya taking care of me.”
“Toh karki damu sleep now, later on semu kaiki gida kinji?” Dad’i kasheta finally her plan has finally worked out! Kai kawai ta gyad’a mai kaman dagaske. Yana barin d’akin tahau daka tsalle sauk’a tayi daga kan gadon tare da jan d’aya daga cikin trolleys nata tahau had’a kayakinta ciki. Ai ba jaka bace ita da zata riga shara kullum tana dafa farin shinkafa, spaghetti kokuwa macroni wa bak’in Al’ameen gwara taje gida chan ta huta abinta.
*© MIEMIEBEE ™YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
[1/20, 9:01 PM]
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*
*January, 2017*
3⃣8⃣
_09:34AM_
Zeezee ta gama shiri tsaf sekace wacce zata gidan biki. Tana kan pancaking face nata Al’ameen yayi knocking bisa k’ofa tare da shigowa “My Princess har kin shirya ne? I thought kina bacci ai.”
“A’a na tashi since.”
“Jikin da sauk’i kenan.”
“A’a wallahi kawai de na dage ne yanzu haka kaina ciwo yake min just now nayi amai ma.”
“Subhanallah sannu ko? Muje mu karya toh muje asibitin yaso daga chan se nayi dropping naki a gida zuwa Maghrib na d’auko ki.”
“Wai kai ka d’au yini kawai zanje inyi? Rashin lafiya fa nake” akwatinta ta fiddo daga lungu “ina kuma zakije da wannan?”
“Gida mana.”
“Lafiya daiko?”
“Kaman ya lafiya zanje gida Mama ta kula dani mana.”
“Zainab yanzu sabida fever’n da be kwantar dake ba shine zaki had’a akwati zaki gida?”
“Kamar ya be kwantar dani ba? Dan ya d’an sakeni yanzu sekace haka? Ai zuwa anjima ze dawo.”
“A’a baza ayi haka ba, tunda ina gida i’ll take care of you yanzu muje asibitin.” Bajewa tayi k’asa gun tahau rusa kuka haka kawai ze kama yayi mata ruining plan wallahi k’arya ne. “Wallahi ni se ka kaini gida, ni Mama nakeso ba kai ba wayyo Allah!!” Ihu ta cigaba dayi wajen tana kururuwa a yayinda yayi tsaye wajen kawai yana mamakin yarintarta.
“Is okay toh naji tashi mu kaiki gidan bar kukan haka.” Hannu tasa ta share hawayenta “anya kuwa Zainab ba faking rashin lafiyar nan kike ba?”
“Kaman ya faking? Ana k’aryan rashin lafiya ne? Kai kanka fa kaji yadda tempreture na yahau d’azu Allah banida lafiya.”
“Toh get well soon.”
“Yauwa kuma ni bazan je wani asibiti bafa Mama zata kula dani.”
“As you wish lets have breakfast” nan da nan suka karya aka fito mata da akwatinta, acikin mota Al’ameen ya kalli Zeezee daketa buga Candy Crush a wayanta sannan yace, “Princess sekuma yaushe zaki dawo?”
“Idan fever’n yayi sauk’i kaman nanda one week haka.”
“Har one week?”
“Wani har nema? Dan bance zanyi wata ba?” Bada dad’ewa ba suka isa gidan nasu. An bud’e mata k’ofa ta fita kuma seta k’i. “Any problem?” Ya tambayeta.
“Yanzu na taho gida bazaka d’an bani kud’i na rik’e a hannu na ba?”
“Yaushe ne na baki 20k Zainab?”
“Ni ba abinda na tambaya ba kenan in kud’in ne bazaka bayar ba shikenan.”
“Toh ni ban fito da kud’i ba” sarai da akwai kud’i a pocket nasa dakuma motar ma in whole amman baze bata ba tunda rashin kunya tasa a gaba.
“Kar Allah yasa ka bayar d’in.” Buga masa murfin motan tayi wane zata 6alla sannan guard yabita da akwatinta ciki, binta da kallo Al’ameen yayi tare da kad’a kai.
****
Koda ta shiga ciki bata tarar da Mama ba saboda ta fita unguwa ana sunan ‘yar k’awarta. Sallama tayi Baba dake shirin fita kasuwa ya fito “a’a K’anwata ya da akwati? Lafiya dai ko?”
“Ina kwana Baba?” tayi maganan wane maras lafiya tare da tsugunawa har k’asa.
“Amsani de tukun meya faru?” acewarsa ma sakinta Al’ameen yayi, his biggest fear.
“Lafiya k’alau Baba nice bana jin dad’i zazza6i yasani gaba chan kuma bame bani kulawa Ya Al’ameen kullum bai gida shine yayi suggesting nazo nan nad’an huta.”
“Toh hakane? Amman don zazza6i shine har sekin dawo gida K’anwata?”
“Toh Baba bazan iya kula da kaina ba yanzu haka daga asibiti muke ammin allura.”
“Wai wai har allura? Sannu K’anwata sannu, k’ariso ciki toh.” Da kansa yaja mata akwatinta (iyayen d’aure ma k’arya gindi ba.) Bada jimawa ba ya fice kasuwa nan Zeezee ta samu kanta. Waya tahau yi da Adeel kaman ba gobe. Harda La’asr ba wanda yadawo cikin su Baba. Se chan 5:46pm Mama ta dawo gida all exhausted ganin Zeezee tayi a kitchen tana soya k’wai aikin kenan kullum, kafin tace zata 6oye plate d’in har Mama ta ganta. “Zainab!”
“Na’am Mama sannu da zuwa.”
“Sannu de tun yaushe kike nan?”
“Tun safiya fah Baba yace kin tafi gidan suna.”
“Eh wallahi Fateey’n Maman Fateey ce ta haihu.”
“Ayyah sannu da zuwa, arghh! wayyo kaina!” Tayi faking exclamation.
“Me kuma ke damun kankin?”
“Oh! Ban fad’a miki ba ko? Wallahi zazza6i ne yasani gaba for the past three (3) days shine Ya Al’ameen yace na taho gida zanfi samun kulawa.”
“Ban fahimci wai kidawo gida ba wai kina nufin harda akwatinki?”
“Eh toh achan bame kula dani.” Tafe hannu Mama tayi in suprise tana mamakin gut irin na Zeezee “yanzu don zazza6in k’aryan da am sure kika k’irk’iron shine kika dawomin gida da zama?”
“Mama wallahi ba k’ar-”
“Rufa min baki” ta katseta da wuri, “ni zaki raina ma wayo ko jinki bansan wannan d’an banzan halin da kuke developing bane ‘ya‘yan yanzu? Da zaran kunga kun fara aikatuwa a gidan aurenku seku d’ibo k’afa ku dawo gida da sunan wai bakuda lafiya ko ba haka ba? To ki bud’e wannan kunnuwan k’ashin naki ki saurareni da kyau wallahi ba a gidana za’ayi wannan iskanci ba kina jina ko? A da dabaki fara su shara ba ai baki ta6a cewa bakida lafiya ba se yanzu. Maza-maza ki had’a kayakinki kiyima Maj-Gen waya yanzu ya turo a d’aukeki.”
“Mama wallahi ba haka bane Allah banida lafiya ai Baba ma yaga shigowa na kuma ya amince na zauna anan har sena samu sauk’i.”
“Babanku kam dama ai komi ma amince miki yake tunda shi har yau be koyi darasinsa ba, maza ki kira Maj-Gen ba a gidana za’ayi wannan sakarci ba wallahi, kin ta6a ganin Mariam ta dawo gida da sunan bata lafiya ne? Koda ta haihu batace zata dawo gida ba nice naje na sameta mesa baza kiyi koyi da yayyun ki ba? Bazaki motsa bane?”
Kuka Zeezee tasa gun ita a dole batada lafiya. “Wai jiranki nake ne?” Tana tsugune