YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   56 / 98

165K to 168K   out of 291.7K words

to d'akin Baba. Ganin haka Zeezee itama ta miqe zata bisu sede kafin takai da bakin k'ofan Omar yasa hannu yana kareta ayayinda Mama ta juyo in crying tone tayi stating "taya zakice zaki shiga Zeezee bayan kinsan kece silar rashin lafiyan nasa? Kiyi hak'uri ki tsaya anan kibari nida yayyunki mu shiga."
"Mama yanzu bazan iya ganin Baba ba? Don Allah kuyi hak'uri kubarni inga mahaifina na rok'eku please."

"Ya kike magana kaman baki gane abinda Mama ke nufi ba?" Cewar Mariam spitefully. "So kike mu barki ki shiga ki gama halaka mana shi?"
"Ya isa Mariam" Mama ta katse ta "mu shiga." Ba tare da ta sake cewa uffan ba suka shiga tare da shutting door a face na Zeezee. Nan fa baiwar Allah abin tausayi ta kuma sauk'a har k'asa tana kuka a yayinda Mrs Mukhtar keta bata hak'uri.

Kallo d'aya iyalan Baba suka iya suka mishi idanunsu ya cike dam da hawaye. Banda kuka ba abinda suke iya yi. Kallo d'aya za'ayi wa Baba asan da k'yar ya kwana yau Alhamis ya kwana da rai. Hakan ba k'aramin sake tayarwa family'nsa hankali yayi ba. Da gudu Mariam da Omar sukayi kansa, shi Omar na miji amman se kaman yama fi Mariam yin kuka musamman idan ya tuna fa just a while ago suke zaune a masallaci lafiya k'alau. Har Mama ta kasa barin kuka.

"Ya'yan albarka ina kuke?" cewar Baba in a low and cracky voice.
"Gamu nan Baba" cewar Mariam "sannu Allah ya baka lafiya."
"Ameen" Mama da Omar suka amsa in unison. Hannunsa dake ajiye a gefe yake son d'agawa amman ya kasa, da Mariam ta gano haka seta d'aga ta had'a da nasan, shima Omar ya miqo hannunsa duk suka had'a gu d'aya.
"Masha Allah suwa dawa ne anan?" Ya tambaya gashi de a zahirce idanunsa a bud'e ne sede ko bayi gani dasu ne masani se Allah.
"Mariam da Omar ne anan Baba" cewar Omar yana share hawayensa da d'ayan hannunsa.
"Sannu 'ya'yan albarka Allah yi muku albarka."
"Ameen Baba" Mariam ta amsa "sannu." Se kuka suke sosai saboda raya musu da zuk'atansu ke na cewa Baba baze kwana ba yau.
"Mariam" Baba ya kirata cikin dashasshiyar murya.
"Na'am Baba gani."
"Mariam 'yata ki yafemin rashin adalcin da nayi a tsakaninku tun kuna 'yan yara, ki gafirceni don Allah."
"Baba wace erin magana kake haka? You've never once offended me don Allah kabar seeking forgiveness d'ina, what we are after at is your health."
"Nasani Mariam amman inji da kunne na kin yafemin." Hannunsa ta sake matsewa gam cikin nata tana me sake kuka "Baba inhar abinda kakeson kaji kenan shikenan, ni Mariam 'yarka na yafe maka komi da 6oyayye da kuma bayyananne duniya wa lahira, Allah ya baka lafiya."
"Ameen masha Allah Mariam nagode, Omar Baba na kaima ka yafemin rashin ad-" be idar da maganan ba Omar ya katse sa in a crying tone yace, "na yafe maka Baba, na yafe maka komi Allah baka lafiya."
"Nagode 'ya'yan albarka, Allah ya albarkaci rayuwanku ya baku zuri'ah d'ayyiba, sannan kuma ya haneku dayin rashin adalci a tsakanin 'ya'yayenku kunga abinda hakan ya haifar min. Kumin alqawari ko akan layi kuka ga iyaye suna rashin adalci a tsakanin 'ya'yayensu zaku tsaya ku musu wa'azi."
"In shaa Allah Baba Allah baka lafiya." Mariam kije ki ibo su Hafsah daga islamiyya." Mama ta fad'a da k'yar.
"Mama bazan iya barin Baba haka ba."
"Karki damu nida Omar zamu kula dashi, tashi kije Mamana." Ba tare da tayi gardama ba ta share hawayenta, "toh Baba zanje in ibo su Ramlah daga islamiyya."
"Toh sannu Mariam d'ina."
"Yauwa Baba, zuwa anjima zan dawo Mama."
"A'a Mariam ki zauna da yaranki if not waze kula dasu mijinki bayi gari."
"Mama koda me aiki ne zan barsu."
"A'a ban goyi bayan hakan ba gani ga Omar duk abinda Babanku ke buk'ata ni da Omar zamuyi masa."
"Are you sure Mama?"
"Yes Mariam karki damu."
"Toh shikenan amman if something goes wrong please don't hesitate to call me."
"In shaa Allah ki shafa min kan takwara na."
"Toh Mama" nan ta juyo tana kallon Baba da hannunsa ke rik'e dana Omar har yanzu. "Baba gobe in shaa Allah zan dawo get well soon Allah baka lafiya." Kai zallah ya gyad'a mata, anan ne ta samu ta fita.
Zaune ta tarar da Zeezee kan bench tanata aikin kuka har yanzu, ko niyyan magana Mariam batayi mata ba hakan yasa Zeezee ta miqe tana kuka sosai takira sunan Mariam.
"Adda Mariam?" Banza da ita tayi tana me cigaba da tafiya.
"Adda Mariam don Allah kiyi hak'uri ki sanar dani halin da Baba yake ciki ba don hali na."
Kaman bazata amsata ba tace, "da sauk'i" sannan ta fice ba tare data sake sauraronta ba. Kasa daina kukan Zeezee tayi har seda Omar ya fito daga d'akin shima kasancewar aiken sa gida da Mama tayi domin ya ibo mata abubuwan dazata buk'ata don kwanan asibiti.

"Ya Omar" ta kirasa tana k'ok'arin miqewa daga kan benchin.
"Na'am Zeezee." Ya amsata ba yabo ba fallasa.
"Ya Omar ya jikin Baba?"
"Da sauk'i."
"Ya Omar ka fad'amin gaskiya please, I tried to talk to Adda Mariam but she is so mad at me."
"Da sauk'i Zeezee addu'ar mu kawai yake buk'ata."
"In shaa Allah Ya Omar, how I wish I can see him also and hold his hand." Tayi maganan k'walla na cikowa a idonta. "I miss my Dad Ya Omar, I miss him so much. I can't ever forgive myself for letting him suffer like this, nice sanadin rashin lafiyarsa." Ta rushe da kuka sosai. Shi kansa Omar tausayi ta basa dukda kuwa haushinta yakeji saboda ita ta fara haifarwa Baba da wannan rashin lafiyar. Dan irin kukan da Zeezee take me tsuma zuciya yasa Omar yajata jikinsa tare da hugging nata yana bubbuga bayanta. Hugging nasa back tayi tana me cigaba da kukan.

"Ya isa, he is going to be alright in shaa Allah." Kai ta gyad'a seda tad'an yi shiru ya saketa nan ta shiga share hawayenta. "Ki zauna ina zuwa."
"Gida zaka?"
"Eh."
"Zan bika."
"Are you sure?"
"Yes please."
"Okay toh muje." Anan suka fice, Zeezee ce ta had'awa Mama dukkannin abinda zata buk'ata.

*****
"Hafsah?"
"Na'am Alhj" ta furta tana k'ok'arin shanye kukan dake neman kub'uce mata.
"Kina ina?"
"Gani nan Alhj" nan ta sake matsowa kusa dashi tare da had'a musu hannayensu.
"Hafsah ta ki yafeni kinji?"
"Alhj kuma wani irin magana kake?"
"Nide ki yafeni don Allah nasan sau dayawa nakan miki abubuwan da bakiso kiyi hak'uri ki yafemin please."
"Alhj please ka dena, kabar magana haka. Ya kake ta neman yafiya sekace mutuwa akace maka zakayi? Please ka bari ya isa haka."
"Hafsah ta inaji a jikina today will mark my last day, zuciyana namin ciwo sosai." Hawaye ne suka soma tsiyayowa daga kumburarrun idanunta. Jin shiru yace, "baza ki iya yafemin ba Hafsah ta? Yi hak'uri ki yafemin kinji?"
"Alhj me kayi min da zaka nemi gafara na? Ni nace kayi offending d'ina ne? Please kabar maganan haka lafiyarka ce a gaban mu yanzu."
"Baki fad'a ba amman nasan da hakan."
"Alhj inhar jin yafiya na kakeson ji toh ni na yafe maka duniya wa lahira."
"Nagode Hafsah."
"Nima nagode Alhj Allah baka lafiya, Hjy (Maman shi) ta kira d'azu k'afafunta ke ciwo taso fitowa yau amman tace zata bari zuwa gobe."
"Toh ba matsala, Allah kaimu."

**^^**
Har dare around 9pm Zeezee tak'i barin asibitin, ba yadda Omar beyi da ita ba ta ya kaita gidan Mrs Mukhtar amman tak'i ita tanason taga Babanta.
9:30pm Mama ta fito waje don yima Zeezee magana. Alokacin Zeezee na miqe akan benchi tayi lamo "Zeezee" Mama ta kirata.
"Na'am" ta amsa tare da miqewa a kid'ime.
"Me kike har yanzu baki koma gida ba?"
"Mama ya jikin Baba?"
"Da sauk'i yana bacci ma."
"Allah ya bashi lafiya."
"Ameen tashi Omar yayi dropping naki Mrs Mukhtar nata kira."
"Mama zan kwana anan."
"Anan a ina Zeezee?"
"Ko akan benchin I want to be anywhere close to Baba."
"Zeezee kiyi hak'uri ki koma gida."
"Mama don Allah kimin hanya, ina son inga Baba in gani da ido na wani halin yake ciki please Mama don't refuse my offer, I cannot forgive myself for what I've done to him."
"Zeezee dama Allah ya riga ya k'addara wannan rashin lafiya wa Babanku sede kice ta sanadin ki hakan ya faru Wanda dama komi seta sanadin wani yake faruwa, so kibar blaming kanki ki taya shi da addu'a Allah shi basa lafiya."
"Ameen Mama yanzu don Allah ba yadda za'ayi na gansa kafin na tafi?"
"Zeezee kin fini sanin abinda hakan ze haifar."
"Mama kince fa yana bacci."
"Even still Zee-"
"Mama please I beg you don Allah, this is all I ask." Zeezee tayi pleading abin tausayi. Mama zata sake magana Zeezee ta sake had'ata da Allah, she can't say no now. Muje.

"Nagode Mama, thank you so much" a nitse tabi bayan Mama suka shiga d'akin inda ita Zeezee ta tsaya daga bakin k'ofar a yayinda Mama ta k'arisa ciki ta sake duba fuskan Baba don ta tabbatar da baccin yake. Hannu tayi wa Zeezee nan ta k'ariso ciki.
Kallo d'aya Zeezee tayi wa Baba ta rushe da kukan zuci se hawaye kawai take tsiyayarwa. Binsa kawai take da kallo tana me sake tsanar kanta na sanya mahaifinta cikin wannan hali, duk anan kallonta kawai Mama take. Hannu Zeezee ta d'aga a hankali ta d'aura akan na Baba a hankali. Har Mama ta bud'e baki zatayi magana, ganin Baba be farka ba ta barta.
"Baba I'm so sorry, Allah ya baka lafiya, your daughter loves you so much if only I can take away your pain." Tayi kusan minti biyu akansa sannan da k'yar Mama ta samu ta turata waje "kije gida Zeezee, Omar na jiranki a mota in shaa Allah gobe seki dawo."
"Toh Mama take care of Baba please Allah bashi lafiya."
"Ameen seda safe."
"Allah tashemu." Tana kaiwa nan ta juya ta fice. Ciki Mama ta koma ta idar da shafa'i da wutr nata, ta shiga canza kayan sawanta tana cikin haka ne taji Baba yaja doguwar nishi. Rabin kayan na jikinta rabi ta cire ta k'arisa kansa "Alhj?" Ta kirasa cike da tashin hankali. "Alhj?" Tayi tapping nasa "na'am Hafsah." Ya amsa at long last.
"Alhamdulillah! Ka tashi kenan?"
"Eh" ya amsa sama-sama.
"Ya jikin toh?"
"Alhamdulillah."
"Barin canza kaya na ina zuwa." Da nod daya mata ta koma ta canza kayan nata zuwa na bacci sannan ta dawo ta zauna a gefensa.
"Hafsah ina Ibraheem da... da... da Yasmeen?"
"Ibraheem na Abj Yasmeen kuma Kd amman gobe in shaa Allah zasu d'auko hanya don dubanka."
"Ina son ganinsu yanzu kiyi musu magana kice suzo."
"Alhj ba gari d'aya fa muke dasu ba, Mariam, Omar da Zeezee ne muke gari d'aya dasu."
"Ibraheem da Yasmeen fah?"
"Suna chan Abj da Kaduna Alhj karka damu gobe zasu shigo."
"Inason yi musu magana Hafsah."
"Toh in kira maka su a waya?"
"Zamu samu muyi magana?"
"Sosai ma."
"Toh kiramin Ibraheem shine babba aiko?"

*MIEMIEBEE. Team #YGC!*
Beeenovels.blogspot.com
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
πŸ‘„Page 51
*FEBRUARY, 2017*

Blog readers how are you guys coping with this version? Lemmi know your opinions please, ILY'all❀


"Eh Alhj" nan da nan Mama tayi placing Ibraheem on the line. A lokacin wayan nasa na a hannun Hafsah 'yarsa wacce suke kira da Maamah tana game. 'Yar tasa sak shi ba abinda ya rabasu, haskensa ne kawai bata gama ibowa ba ta d'an had'a da duhun mahaifiyarta. Ganin hoton Mama yayi displaying akan screen d'in tayi saurin kai wa Ibraheem da Fateemah da suke zaune a d'akinsu wayar.

"Daddy! Daddy! Maman Daddy is calling you."
"Dagaske? Kawo in gani toh Maamah na."
"O'o Daddy ina game."
"Yi hak'uri muna gamawa zan baki."
"Ni o'o."
"Yi hak'uri Maamah ki basa kinji?" Cewar Fateemah dake lullub'e cikin bargo da alama laulayi ke damunta.
"Zan baki nawa."
"Ni banashon naki."
"Yi hak'uri kiban ze yanke, ga chan ice cream naki a fridge jeki d'auko."
"Yeyy!" Kai mai wayan tayi da gudu sannan ta nufa fridge ta d'au ice cream d'in ta shiga sawa a armpit (hammatarta) hakan ba k'aramin dad'i yake mata jin sanyi-sanyin. Fateemah na kallonta aman batajin zata iya mata magana saboda tasan 6ata lokacinta kawai zatayi dan kuwa ba jin magana Maamah ke ba, halinta sak na Zeezee dukda taka mata birkin da Ibraheem ke, gado ba gwaninta ba.

Kasancewar wayar ta yanke yayi calling Mama back.
"Assalamu Alaikum Mama."
"Wa'alaikumus salam Babana ina wuni?"
"Lafiya Mama ya gajiya? Kin kira wayan na hannun Maamah tak'i bani."
"Takwaran nawa ko? Ya jikin Fateemah kuma?"
"Alhamdulillah da sauk'i" ya amsa yana kallon Fateemar, daga nesan tamai whispering "kace mata ina gaisheta and ta gaida Baba da jiki." Nodding yayi sannan yace, "tana gaishe ki da Baba da jiki, ya jikin nasa?"
"Toh alhamdulillah de shi yace in kiraka ma yanzu yana son kuyi magana."
"Allah sarki ki bashi toh."
"Yauwa" a speaker phone ta danna sannan ta matso wa Baba da wayar kusa dashi "ga Ibraheem d'innan Alhj."
"Aina?" Ya tmbaya nan Ibraheem ya amsa "gani nan Baba sannu ko? Allah baka lafiya."
"Ameen Ibraheem Babana, Allah yayi maka albarka."
"Ameen Baba gobe in shaa Allah zan shigo in duba ka."
"Toh Allah ya kaimu Baba na nace ka yafemin rashin adalcin danayi a tsakaninku tunda kuke yara, Baba yayi kuskure ka yafe mishi kaji?" Jin haka Ibraheem ya d'au k'afa ya fice daga d'akin nan Maamah ta shiga binsa tana kiransa da wuri Fateemah ta tareta tare da dawo da ita cikin d'akin. Dining chair yaja ya zauna gabad'aya jikinsa yayi sanyi, "Baba wani irin magana kuma kake haka?"
"Yi hak'uri ka yafemin Babana."
"Baba nifa ba abinda kamin, ni yakamata in nemi tuba a gareka ba kai ka nema a guna ba."
"Bazaka iya yafemin ba Baba na?"
"Baba inhar yafiya na kakeson ji toh ni na yafe maka duniya da lahira, Allah baka lafiya kaji? Gobe da sassafe zan shigo in shaa Allah."
"Nagode d'a na Allah maka albarka ya baka ikon yin adalci a tsakanin 'ya'yayenka nan gaba."
"Ameen Baba nagode, sannu kaji?"
"Yauwa ina Yasmeen kuna kusa?"
"A'a tana Kaduna bari incewa Mama ta had'aku."
"Toh Babana nagode."
"Sannu Baba, Allah baka lafiya" nan Mama ta d'aga wayar tare da cireta daga speaker phone. "Hello Ibraheem?" Cikin wani irin murya cike da tashin hankali dakuma tsoro da fargaba Ibraheem yace, "Mama what is wrong with him? Jikin nasa yayi tsanani haka ne?"
"Ibraheem se addu'a."
"Innalillahi! Mesa baki sanar dani ba tun d'azu ko a yau d'in in shigo? Mama mesa Baba yake magana haka?"
"Ibraheem I don't know also" ta amsa hawaye na ciko mata a ido chan bakin k'ofa ta nufa tace, "Dr yace min chances na rayuwansa be kai 30% ba I don't know what to do Ibraheem." Shima Ibraheem besan a lokacinda idanunsa suka cike da hawaye ba "why didn't you tell me he is in a critical condition like this?"
"Banason hankalinka ya tashi kai kad'ai na sanar wa hakan k'annenka duk basu sani ba."
"Allah bashi lafiya Mama please take care of him."
"I'll Ibraheem sekun shigo goben ka gaishe da Fateemah" anan ta katse wayar tana me share hawayenta. "Hafsah? Hafsah ina kike?"
"Gani nan Alhj" tayi maganan tana dosan gabansa. "Hafsah Yasmeen fah? Ki had'ani da ita itama."
"Toh Alhj" ba musu ta shiga trying line na Yasmeen sede sam bata samunta saboda d'anta bayi bar mata wayarta kullum cikin siyan sabuwar waya take dan kuwa sede Suleiman be gani ba seya jefata cikin ruwa. Atlast dana mijinta ta kirata anan ne ta same ta haka itama Baba yayi ta neman gafararta a yayinda take ta zuba kuka cikin wayan da k'yar ta iya fad'i mai ta yafe mishi itama. Tana ajiye wayan ta fad'a jikin mijinta tana kuka sosai, hak'uri yayi ta bata yana assuring nata in shaa Allahu Baba ze samu sauk'i and first thing tomorrow morning zasu wuce Bauchi.
"All is going to be alright kinji Queen? Bar kukan haka ko kina son kisa Abba shima?" Kai zallah ta kad'a masa.
"King Baba bashida lafiya I don't want him to die."
"Subhanallah! Kiyi istigfaar wayace miki Baba ze mutu? Ze samu waraka in shaa Allah just have faith kinji?" Nan ma kai ta gyad'a mai. Pecking forehead nata yayi "tashi mu kwanta zuwa anjima mu tashi muyi Sallah mu rok'i Allah wa Baba koh?"
"Thank you My King, I love you."
"I love

56 / 98