YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   50 / 98

147K to 150K   out of 291.7K words

masu kyau k'waya biyu again tasa, ragowan tasa a flask takai masa. Kafin yafito harta cinye nata ta kora da ruwa.

Fitowan Adeel ya nufi dining cike da zumud'insa ya bud'e flask d'in in search of cinyoyinsa biyu don yaci, sede ya gama dubansa amman d'aya kad'ai yake gani haka daya gwada neman other parts d'inma duk d'ai-d'ai yake gani. Danqaree!
"Ke Zeezee! Zeezee! Ina kike?" Seda ya kirata kusan sau biyar sannan ta fito batare da ta amsa ba.
"Ina kika kai min sauran parts d'in?"
"Cikina."
"Cikinki? Naki ne da zaki cinye? Kokuwa ni na baki?"
"Ko d'aya amman naga hak'k'i na ne dole inci tunda ni na girka."
"B'arauniya ba, toh kisani kinci haramun."
"Kanka akeji." Tana kaiwa nan ta koma d'akinta. Later during the night Zeezee ta fito sanye da bombshot da vest tana latsa wayar da Lubiee tabata. Zama tayi kan kujera tare da kunna power button tana kallon TV tana chatting. To 10:30pm Adeel ya fito sanye da pajamas nasa zasa d'auko ruwa a fridge. Tsayuwa yayi yana kallonta, yayi hakan na mintuna biyu ya kad'a kai ya wuce dining ya d'auko bottle na ruwa duk anan Zeezee bata san da halitta tsaye gun ba. Har ya kaiga shiga d'akinsa yaga baze iya hak'ura ba, "Ke a ina kika samu wannan wayan?"
"Sata nayi ina ruwanka tunda ba kai ka siya min ba?" tana gama amsa sa tasa dariya da alama da chatting da takeyin ne. Hakan ba qaramin 6atawa Adeel rai yayi ba shi bayison yaga tana walwala yafison yata ganin ta cikin hawaye kullum "Kuma da wa kike chatting?"
"Wai kam ina ruwanka? In kana waya da Ruky kowa take na ta6a yimaka magana ne? Please kadena cikamin kunne."
"Ajiye wayan kizo." Ya fad'a more like a command.
"Nazo kamin meh?"
"Kizo nace dont let me repeat myself."
"Bazan zoba in fad'an abu zakayi say it ina jinka."
"Kizo haqqi na nakeso."
"Lallai ko kayi 6atan kai in haqqin ka kakeso kana iya zuwa gun ita karuwar taka ta baka amman kasani bakada haqqi akaina."
"Zeezee karkisa na miki na k'arfi."
"Kayin ai dama abinda ka saba yi kenan." Fusata yayi lokaci guda wai ita waye da zece yanason haqqinsa tace bazata bada ba, goran ruwan ya ajiye ya nufi gabanta, ko tsorata bata yi ba hannunta yaja seda ya miqar da ita daga kan kujeran "ina ayi ta dad'i bakiya so?"
"Ka sakemin hannu mugu azzalimi kwai let me go." Janta ya shiga yi, ganin haka ta sulale k'asa "ki tashi nace!"
"Ai wallahi na gaya maka bazaka sake samun wani abun aguna ba, I belong to Ya Al'ameen."
Haka kikace? Bale ma shi Ya Al'ameen d'in me zeyi da wacce bata haihuwa? Mschww!"
Eh ka fad'i koma me, bashi zesa na baka kaina ba."
"Ajinki ko anan bazan iya yin abinda nakeso bane?" Sauk'a k'asan shima yayi ya had'e hannayenta biyu a sama yana wani erin shunshuna wuyanta wane ze had'iyeta "Adeel stop it banaso! Stop it already." Ko sauraranta beyi ba, dabara ce ta fad'o mata, ta seta k'afanta dai-dai kan abin nasa ta gullesa. Take yabar abinda yaken tare da sakar da wani mugun k'ara abin nasa ya riqe yana matse ido anan Zeezee ta samu ta tashi tareda rugawa d'akinta a guje.
"Wallahi you won't get away with this" yace da ita lokacin da take sa lock jikin k'ofar tata. Yafi minti biyu tsugune agun sannan finally ya miqe ya nufi d'akinshi.

The following day, ba yadda Adeel beyi da Zeezee ta fito daga d'akinta ba tak'i, wanki ya loda mata bakin k'ofan yau harda iron "gashi in kika fito ki wanke min su duka kuma ki goge wallahi in bemin ba zaki sha mamaki." Yana kaiwa nan ya fice seda ta tabbata ya fita sannan ta fito baki ta sake ganin yawan kayakin da kaman bazata wanke ba sekuma ta tuna da abinda ta mai jiya muddin ta bari ta sake yimai wani abin yau yana iya zaneta sabida tsab ze rina. Kamar wacce zatayi kuka ta tattara kayakin nasa ta wanke mai suna bushewa tabisu da guga, bayanta wane ze 6alle. Seda ta gama mai nasa sannan ta shiga yin nata itama, se tunawa take time da take gidan Ya Al'ameen da zaran wankinta ya taru shi da kansa yake sawa a wanke akuma yi mata guga. She can't tell how much she is missing him.

_Few months later..._
***
Maganan aure fa ba fashi, gini har an kammala an soma jere, ba aikin Zeezee yanzu se kuka kullum, bazata iya zama da kishiya ba, kishiyan ma wai wacce taji boko fiye da ita. Tunanin kalan rayuwan da zata shiga muddin ta bari Adeel ya auro Ruky Mama kawai take tasani tamkar baiwa ze mai da ita, she can't take it.

Yau da misalin k'arfe d'ayan rana Adeel ya shigo gida da almajiri biye dashi yana riqe da akwati na tsakiya k'waya d'aya. A parlour ya umurci yaron ya ajiye mai sannan ya sallemesa. Anan ya shiga k'walla wa Zeezee kira "Ke Zeezee! Ina kike ki fito da Allah kina 6ata min lokaci."
Tana kwance bisa gado tana aikin kuka ta miqe tazota, da k'afa ya tura akwatin side nata "gashi wannan naki ne kayan fad'an kishiya kome ake kira." K'arisowa tayi a nitse ta tsuguna ta bud'e akwatin dududu befi atamfofi biyar ciki ba nan ma ba super ko makamancin haka ciki, seda wasu local inner wears k'waya biyar da shampoo na 'yan N350 guda d'aya aciki se dubu biyar a gefe. Kai ta kad'a sannan ta miqe tsaye tana kallonsa "Adeel koda tinkiya ce zaka auro mata wata bazaka kai mata wannan abu ba bale ni mutum. Meh wannan yanzu? Kana ganin kamin adalci kenan? Akwatuna nawa ka kai gidansu Ruky Mama 24 am I right? Amman ni dake ka miyar dani tamkar wacce ba haifanta akayi ba zaka kawo min wannan tsummakaran, Ahaka ne kake tunanin zakayi adalci tsakani na da wacce zaka auron?"
"LOL bakisan wani abu ba wannan d'inma banyi niyyan kawo miki ba, mutumin danayi siyayya a shagonsan ne yace lallai sena kawo miki wani abu, kuma tun wuri is better kidena had'a kanki da Ruky kinga na farko ita ba sadaqarta za'ayimin ba, da kud'i na zan aurota unlike ke da aka wulla min ke na biyu Ruky tafi minke tunda ita masters holder ce ke kuwa ko degree bakida, na uku garau take at any moment tana iya d'aukan ciki ta hihu ba kaman ki da bakida amfani ba, kinga ko anan ma zakisan matsayinku ba d'aya bane. Ki taimaka wa kanki kibar comparing d'in ku."
"Haka kace?"
"Haka yake ma so ni zan koma."
"Dan tsaya" ta buk'acesa. Kitchen ta nufa da wuri bayan second counts ta fito riqe da galon na kero da ashana. Baki ya saki yana kallonta lokacin da take bulbula keron akan kayakin, seda ta tsiyaye tas sannan ta kyasta ashana ta wulla akai balbal ya soma ci.
"Kasani koda a sadaqa ka sameni ba a wahala ka tsintoni ba da zaka kawomin k'ananun zannuwan dubu uku kayi tsammanin kuma zansa su."
"Ke!" Anan ne bakinsa ya bud'u "asaran dukiya zakiyi min? Dama inba zanin dubu uku-ukun ba ki gayamin wani zanin ne yafi cancanta da 'yar sadaqa?"

*MIEMIEBEE TEAM #YGC!*
beeenovels.blogspot.com
πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
πŸŽ€πŸŽ€β€˜YAR GATA CE!
*BY MIEMIEBEE*
Page 46
Febuary, 2017

_I solemnly dedicate this page in honour of my sweetheart in disguise *MAMAN FADEEL* Thank you for everything Big Sis your Lilly loves you so much, Allah yabar zumunci❀❀❀❀_



Tana hawaye sosai tace, "Adeel mena ta6a yimaka a rayuwa? Mesa ka tsaneni haka ka lalata min rayuwa? Don kai na rasa komi nawa har iyaye na na yafe saboda na kasance tare da kai amman kake wulak'antani haka? Wallahi a da ko had'e sama da k'asa za'ayi acemin ga abinda zakazo kamin bazan yarda ba." Sosai ta qare maganan tana kuka. Bayan ya samu yayi stopping fire'n da estinguisher yace, "toohhh!" cike da mamaki "yanzu kuma what lead to all these nonsense talks? Saboda zan miki kishiya? Wai tsaya tukun mata nawa Allah ya halitta min? One, two, three upto 4 dan nace zan k'aro d'aya bama biyu ko uku ba kike neman gayamin magana? Kuma fa auren nan da zan qara inada dalili na-"
"Meye dalilin naka Adeel?" Ta katse sa "Mene bana maka as a wife? Ina maka girki ina k'ok'arin baka farin cikin daya kamata a kullum, baka ta6a neman had'a kwanciya dani na hanaka ba koda kuwa am not in the mood me kakeso nayi maka again? Na lasa tafin k'afanka ko me kakeso?"
"Naji kinayin all the above stated activities amman zaki iya bani family ne? Nagaji yanzu haihuwa nakeso, kekuma bazaki iya ba your womb is damaged shikenan so kike dukan mu biyu muyi asaran auren da mukayi?"
Hannu tasa ta share rolling tears nata, "Adeel ji yadda kake magana as if daga halitta nane mahaifata batada kyau tun farko, kaine nan fa ka lalatamin mahaifa amman ji yadda kake magana kayi adalci mana."
"Kifa dena kawo min zancen adalci dan kema bakisan ma'anarsa ba, inhar da kinsani da bazakiyi wa Al'ameen abubuwan da kika mai ba."
"Hakane Adeel thank you so much for teaching me such a valuable lesson in life I shall never forget it. Tabbas na tafka babban kuskure rabuwa da Ya Al'ameen masoyi na na haqiqa na aureka."
"Sede nadaman kam dan se in a lahira keda ki sake rayuwa dashi zaman ki a gidan nan dindindin! Kafin na dawo kuma ki tattara nan ki dafa min lunch ni na gaya miki." Anan ya fice ita kuwa ta sauqa har qasa tana kuka na haqiqa bazata iya kwatanta kalan nadaman da tayi ba ashe Al'ameen shine masoyinta bata ta6a sani ba? Seda tayi ta godewa Allah sannan ta shiga had'a mai lunch.

Tsabagen tashin hankali ko yunwan ma bataji, tana baje a kan tiles a d'akinta wayarta ya shiga ruri tana dubawa taga Mama bazata iya tuna when last Mama ta kira taba don haka ta d'aga without wasting time.
"Assalamu Alaikum ina ini Mama?"
"Wa'alaikis salam ya kike Zainab?"
"Laf-" sekuma ta rushe da kuka.
"Helo Zeezee?" Cikin sautin kuka ta amsa da "na'am."
"Kukan me kuma?"
"Mama fa har ansa date na bikin nasu bakiga abinda ya kawo min as kayan fad'an kishiya ba. Mama ban gaya miki bane amman yanzu bazan iya concieving ba."
"Subhanallah! Aina aka tabbatar miki da hakan?"
"Asibiti Mama."
"Subhanallah! Are you sure matsalar daga kece kuwa?"
"Daga nine Mama for six months Adeel yata d'uaramin wasu capsules ban ta6a sanin na hana d'aukan ciki bane seda ya gama rusa min mahaifa."
"Ya Salam!! Wannan abu dame yayi kama? Amman Zeezee bakida wayo ne da zaki tashan magani har na tsawon watanni shida without asking him name ne?"
"Mama I trusted Adeel with all that I got ban ta6a tsammanin ze cutar dani haka ba gashi yanzu har gori yakemin yana kira na da 'yar sadaqa kokuwa wacce bazata iya haihuwa ba Mama inda nasan da haka da ko Ya Wakeel kukace in aura zan aura saboda za6in iyaye is always the best kuyi haquri ku gafirceni wallahi naga gwagwarmaya a rayuwa kuma bayan family mutum baida kowa again, nayi nadaman dikkannin abubuwan dana aikata muku tun ina k'arama."
"Ya isa Zeezee ki k'ara haquri wataran se labari no situation is permanent kinji?"
"Naji Mama nagode ya Baba?"
"Yana nan k'alau."
"Toh ki gaida min shi harda Ya Omar ma, Ya Ibraheem ma don Allah kibasa haquri, kona kirasa bai d'agawa he is still mad at me."
"Zan masa Allah rufa mana asiri ya kawo sauqi cikin lamarinki."
"Ameen Mama nagode sosai."
"Yauwa se anjima" anan ta katse wayar. Tunanin ya zatayi ta jawo hankalin Baba kan Zeezee take amman takasa saboda anytime ta taso mai da maganan Zeezee ko sauraronta baiyi.

*^*^*
Haka fa preparation na biki ya cigaba da gudana, Zeezee de aikin kullum itace ta kuka gashi sede zance be had'ata da Adeel ba seya zageta koya gaya mata baqar magana had'e da goranta mata ba. In banda dad'a rama ba abinda take yi. Ahaka har watan bikin Adeel da Ruky Mama ya iso, cikin ikon Allah aka soma biki aka gama lafiya wanda cikin duk events d'in ba wanda Zeezee taje kullum tana maqale a d'aki tana kuka.
A daren randa aka d'aura musu aure aka kawo amarya gidanta. Convoy ne sosai motoci se shiga ciki suke har ya zammana saura ba inda zasu samu shiga seda suka faka a waje. Zeezee na leqe ta window tana kuka se tuna time na bikinta da Al'ameen take itama yadda convoy ya had'u mata amman nata da Adeel wane akuya aka d'auko daga ita se shi aiko anan ma ya isa ya mata gori "why didn't I thought of this before?" Ta tambayi kanta. Daren ranan gabad'aya ta kasa samun sukuni ita rabonta datasa Adeel a ido ma tun kamin a soma wedding events nasun, any time tunanin yanzu haka Adeel na tare da wata suna shan soyayyansu yayi hitting nata se ta rushe da kuka haka seda garin Allah ya soma wayewa ta samu tayi bacci.

Some hours afterwards... Site na Ruky Mama @ 11:46am.
Kwance take bisa jikin Adeel hannunta d'aya akan chest nasa tana wasa da d'ad'd'aikun gashin k'irjinsa "Baby am hungry" ta fad'a a shagwabance. Ruky Mama ta kasance 'yar duma-duma za a iya cewa tana da k'iba dake a k'oshe take b'ul-b'ul tana da kyau dai-dai gwargwado uma tsayayyiyar mace ce.
"Toh ki tashi kiyi warming kanki kink'i." Yace da ita yana shafa fuskarta.
"Bazan iya ba the pain is too much."
"Yi haqur kinji? Nasanki fa da juriya."
"Toh Baby breakfast fah? Will I be the one to cook?"
"Haba! Meye amfanin Zeezee a gidan nan da har zakiyi girki?"
"Are you sure Baby? Zata fyarda ta girka mana?"

"Yes Sweetheart karki damu." Kissing nasa tayi passionately "I love you."
"I love you more."
"Nifa ban yarda da wannan I love you d'in ba nasan kaje ka sameta abinda zakana gaya mata kenan itama."
"Inji wa? Rabona dana sata a ido I can't even remember seriously wancan batada wani amfani I use her for sex and cooking kuma kinga gaki yanzu kin fita zuma da dad'i ba abinda ze sake shiga tsakani na da ita."
"Are you sure Baby?"
"Dont you trust me?"
"I do Love."
"Good tashi toh muje kiyi warming kanki." A hankali cike da so da k'auna ya samu tayi warming kanta sannan sukayi wankan sunnah suka fito. Nan ma da kansa ya shafa mata mai se wani binta yake sekace 'yar gwal sun gama shiri fes suka koma suka kwanta tana manne a jikinsa. Hannu ya miqa ya d'au Wayansa tare da kiran Zeezee sede har 2 missed calls bata d'aga ba se ana uku.
"Yauwa Ke Arrange breakfast for us ki kawo immediately kinji?" Lallai ma ta furta a ranta sannan ta kashe wayan. "Hello? Hello? This rascal wants to die" ya furta angrily.
"Babe ka barta kawai ka siyo mana."
"No way meye amfaninta? Excuse me kinji I'll be right back."
"Don't take long okay?"
"Okay Sweetie" nan yayi pecking lips nata sannan ya fice. Chan a d'akinta yaje ya tarar da ita tana aikin kuka bubbuga k'ofan yayi seda ta juyo tana kallonsa da swollen eyes nata. "Hanging call zakiyi a kaina?" kaman a kyaftawan ido ya nufi gadon tare da fincikota daga kai cike da mugunta. "Magana nake miki!" Ya fad'a a tsawace "ko sekinji sauqan mari zaki ansani?" Kai ta kad'a abin tausayi tana me cigaba da kukan.
"Zaki had'a breakfast d'in kokuwa sekinji na jaki?"
"Zan had'a muku" ta furta tana kuka sosai.
"Maza wuce ina kallonki" anan ya saketa and ba gardama ta nufi kitchen ta fere doyan ta tafasa sannan ta musu doya me k'wai a jiki sannan fried egg separate a gefe. Cikin food warmers nata tasa takai dining table ta ajiye duk anan Adeel na zaune a parlour yana jiranta.
"Ke anan kuma zaki barsu? Cemiki akayi Ruky zatazo nan?"
"Aina kakeson na ajiye?" ta tambaya a hankali abin tausayi.
"Site nata zaki kai mata."
"Adeel nida ita waye babba? Waye uwar gida?"
"Wannan kuma keya dama inma kece kakar gidan can ta matse miki nide ki kai wa matata breakfast natan."
"Wallahi Allah bazan kai ba kai bakada imani ne? In zakayi adalci nida ita waya kamata ya kawo ma wani abinci?-"
"Ke ya kamata ki kai mata" ya katseta "and sai kin kai d'in, ce miki akayi Ruky sa'ar kice?"
"Bazan kai ba abun kuma ai ya koma iskanci." Belt nasa taga ya zare yana nannad'awa a hannu "zaki d'auka kikai kokuwa?" Kallonsa ta tsaya yi totally short of words dagaske yanzu dukanta yakeson yi? "Kina kallo na ajinki bazan iya baki kashi bane anan in kuma saki ki kai matan?"
"Zaka iya tunda kai mahaukaci ne zan kai mata amman kasani wallahi kaima Allah baze barka ba Adeel idan baka gani akanka ba toh kajira akan 'ya'yanka."
"Aikin banza d'aga ki kai mata" one more look tamasa sannan ta

50 / 98