Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
“Eh anan Hafsah ai na gaya miki jiki na na bani da daddare kuna barin yarinyan nan tai ta kuka da wannan muguwan yartan” ya galla wa Mariam harara yanzu kuma.
“Yo Alhj ba sena gama arba’in ba tukunah?”
“Ke kika sani, nide anan zan kwana Mariam fice kije ki d’ago Yasmeen daga d’akina ki kaita d’akinku achan zata kwana yau.”
“Toh” ta fad’i tana jin dad’i dama harga Allah ta gaji da tashi kullum da daddare tana yawo da Zeezee a hannu har seta koma bacci, “seda safe Mama, seda safe Baba” tace dasu tare da ficewa.
Bayan Mama taja comforter ta kwanta ta kalli Baba dake zaune gefen gadon yana ma Zeezee addu’a tana turo baki tace, “ni wallahi Alhj nasan yau hanani bacci zakayi in kasa wannan Zeezee agaba.”
“Ai dama nasani ignoring nata kike da daddare kuma daga yau hakan bare sake faruwa ba” nan ya miqe ya kashe masu wuta suka kwanta da Zeezee rigingine a jikinsa.
_2:47AM_
Cikin bacci Baba ya soma jin kukan Zeezee, take ya tashi tare da kunna wutan d’akin ya d’agata yana jijjiqata ganin tak’i yin shiru ya maido da kallonsa kan Mama da tayi kamar bataji kukan Zeezee ba tana ta bacci.
“Hafsah!” yayi whispering sunanta, shiru bata amsa ba.
“Hafsah tashi nasan kina jina tashi nace ko ba kijin kukan Zeezee ne?”
“Alhj dan girman Allah ka barni in huta, ka fa san irin hidiman da na sha jiya.”
“Meaning baraki bata mama ba kenan komeh? Tashi nace!” yasa hannu yana jijjiqata da k’yar ta miqe ta zauna tana galla mai harara har a nan Zeezee bata bar kuka ba. Chan ta miqa hannu ta d’ago feeder’n Zainab ta mik’a mai, “gashi bata ruwan tasha k’ishi takeji” kallonta kawai Baba ya tsaya yi totally speechless mah.
*© MIEMIEBEE*
PAGE 03
*December, 2016*
“Amshi mana Alhj bacci fa nake ji.” Ganin baida niyyan karb’a ta ajiye mai akan gadon ta juya zata kwanta, sede wani hanzari ba gudu ba kafin kanta ya dire kan pillown Baba yasa d’ayan hannunsa yaja “hab-” take ya katse ta;
“Bana son dogon surutu karb’eta nace ki karb’eta mana!” haka tana gunguni ta amshe Zeezee ta shiga bata mama da zaran tace zata cire Baba ya hanata, yau kam koda Zeezee tayi bacci Mama ta gwada zare maman daga bakin Zeezee seta sa kuka haka Baba ya sata gaba ta kwanta mamanta maqale bakin Zeezee, da zaran tace zata cire Zeezee tasa kuka Baba yahau mata surutu a takaice de a tak’ure Mama tayi bacci ranan.
*~ *~
Mu kwana mu tashi be ragar komi ba, a yanzu haka Zeezee nada 4 months a duniya, yarinya tana girma tana dad’a kyau ko kad’an hasken ta be gushe ba, ga gashi masha Allah. Gatan da Baba ke bata yasa har ita Mama kanta abin na bata haushi atimes, banda yayyun ta da suka d’au karan tsana suka aza mata dan duk wani abinda Baba yasamu Zeezee kad’ai ya sani komai Zeezee, Mama tayi tayi dashi a fara baiwa Zeezee madara amman yaqi haka har ta rame dan irin shan nono na Zeezee bata qi a yini ana shayar da ita ba. ‘Yan unguwa kuwa kowa yasan Baba da Zeezeen sa duk da 'Baban Zeezee' suke kiransa akoda yaushe da yamma ze zauna a harabar bakin gate na gidanshi da Zeezee ajikinsa suna shan iska, kap cikin yaransa ba wanda yake jinta a jikinsa kaman Zeezee kodan tanada sunan margayiya ne oho?
****
Zeezee ce kwance bisa kan gado da abin wasanta a hannu se wasan miyau take ayayinda Mariam ke k’ok’arin canza mata diaper (pampers) se wani tuttura baki take daidai ta cire ma Zeezee used diaper d’in tana k’ok’arin sa mata sabo kenan Zeezee ta tsula mata fitsari siiirrrr! a fuska. Ihu ta saki wanda yasa su Ibraheem shigowa da sauri ganin meke faruwa. Dariya sosai suka saki ganin fuskan Mariam na yoyon fitsari, Zeezee kuwa ganin yayyun ta na dariya itama ta kama dariyar, ba kaman Ibraheem da har yana dafe ciki, kusan a tare Mama da Baba suka shigo suna tambayan meke faruwa a zatonsu ba lafiya ba.
Kamar wacce zatayi kuka Mariam tace, “Baba wai dariya sukemin saboda Zeezee tamin fitsari a fuska.”
“Amman Mariam kema seda na fad’a miki kibar b’ata lokaci a duk lokacin da zaki canza ma Zeezee diaper saboda incasities haka ai ga irinshi nan.” Mama ta yi scolding nata. Baba daya k’arisa kan gadon ya d’aga Zeezee yana mata wasa yace, “shine zakiyi kuka dan Zeezee ta miki fitsari? Mschw! Banason sakarci fah Mariam.”
“Ayyi Baba kalli dariyan da Ibraheem kemin fah.” Idanun Baba da na Ibraheem na had’ewa Ibraheem yayi tsit tare da calming kansa. “Dariya ko? Nasan maganinka, Hafsah amsheta kisa mata pant tasha iska” nan da nan yaran sukayi waje se neman tsokanan Mariam suke.
Chan bayan Azahar su Ibraheem suna zaune a tsakar gida suna chin abinci Baba ya k’wala mai kira, ba tare da b’ata lokaci ba ya miqe ya je kiran “na’am Baba gani.”
“Yauwa zo ka amshi Zeezee kayi mata tsarki ka kuma wanke pant d’in tayi kashi aciki.”
“What?!” Yayi exclaiming batare da yasan yayi hakan ba.
“Meh kace?”
“Bb.. Babu banji me kace ba Baba”
“Cewa nayi kazo ka ma Zeezee tsarki ka kuma wanke pant d’in tayi kashi ciki.” Fuska Ibraheem ya maraice “Baba kayi min rai dan Allah, taya zan wanke wa Zeezee kashi? Ni wallahi ban iya ba.”
“Baka iya wanke kashi ba?”
“Eh wallahi ban iya ba Baba.”
“Tohhhh... In kayi naka wake wanke ma? Ni ko Mamanku? Will you come and carry her my friend!” Ya daka mai tsawa.
“Baba dan Allah kayi hak’uri.”
“Ba ka iya ma Mariam dariya ba? Nan gaba zakayi hankali.”
“Baba kayi hak’uri wallahi na tuba.”
“Ibraheem kaji na rantse kasake barina na nanata abinda na fad’i maka ranka ze b’aci” haka kan wanda zeyi kuka ya k’ariso ciki ya amshi Zeezee daidai nan Mama ke fitowa daga wanka idanunta basu sauqa ko ina ba se kan pant na Zeezee dake a cike dam “laaa bade pupu tayi ba Alhj? Shi yasa ban son barinta ba pampers kawota Ibraheem in wanke mata in mata wanka gabad’ai.” Dad’i sosai Ibraheem yaji wanda ya kasa b’oyewa bekaiga miqa wa Mama Zeezee ba Baba yace, “ka wuce nace!”
“Ayya Baba mana, Mama tace zata wanke mata.”
“Meke faruwa neh?” Mama ta tambaya, nan Baba ya labarta mata komai ta tab’e baki tace, “Alhj dade ka barsa zan wanke mata kai kuma nan gaba se kayi hankali.” Har b’ari bakinsa ke yace, “wwa...walla..wallahi nayi, nayi hankali Mama.”
“Hafsah ki basa waje ya wanke ma yarinyan nan jiki bakyau fa barin kashi jikin yaro akwai harmful acids ciki.”
“Jeka wanke mata Babana yi hak’uri.” Mama tace dashi a hankali.
“D’an banza kawai!” Baba ya fad’i yana hararansa, haka yasa kai cikin bayin yana galla wa Zeezeen dake ta faman masa dariya harara har yasamu ya wanke mata jikinta tsaf sannan ya riqo pant d’in a d’ayan hannunsa ya fito daga bayin akan gado ya direta ya fice nan qannensa da suke ta faman leqansu tin d’azu suka hau masa dariya banda kaman Mariam da har take sauqa k’asa tana hawaye, bece dasu komi ba ya nufa bakin famfo tare da neman kara haka yana yamutsa fuska ya samu ya wanke pant d’in ya shanya. Akan yayi wajen abincinsa seya hau yin d’akinsu.
“Ya Ibraheem abincin naka fah? Ka k’oshi ne ko Yasmeen ta kai ma d’aki?” Mariam ta tambayesa full of sarcasm.
“Wallahil azimu Mariam kika sake min magana me hanani dukan ki agidan nan se Allah hegiya kawai.”
“Oho dai! Allah ya rama min, daidan ka kenan nan gaba zaka sake min dariya.”
Har ya kama tafiya yaga bare iya hak’ura ba da gudu ya nufo inda take ganin haka ta miqe itama tasa gudu tanayi yana binta har suka isa d’akin su Baba. Bayan Mama Mariam ta k’arisa tana b’uya “ya haka? Meke damunku ne wai? Shin baku iya sallama bane?” Baba yayi scolding d’insu a yayinda Mama ke k’ok’arin k’wace kanta daga rik’on da Mariam ta mata.
A fusace Ibraheem ya soma magana, “Baba wallahi ka ja mata kunne ta dena shiga harkana in ba haka ba b’ab’b’allata zanyi into pieces.”
“Ehhh sannu fah, sanu ubanta” cewar Baba cike da mamaki yana mamakin k’arfin hali irin na Ibraheem. “Kai d’in ba dariyar ka mata d’azu ba? ” Shiru Ibraheem yayi bece komai as se harara n Mariam yake. “Da kai fa nake?!”
“Alhaji ya isa please, Ibraheem Baba na kayi hak’uri” Mama tace cikin sanyin murya sannan ta dawo da kallonta kan Marian “ke kuma ki shiga taitayinki kidena yima wan ki rashin kunya kina ji ko?” Baki Mariam ta turo “toh Mama ni d’azun bemin dariya bane?”
“Oya find your way out!” Baba yayi masu nuni da hannu. Ganin Ibraheem yak’i motsawa Mariam ma tak’i fita.
“Daku fa nake” this time a tsawace.
“K’el” cewar Ibraheem yana nodding kai yana kallon Mariam nufin ‘inya kamata d’innan’ daga nan ya fice ya b’oye bakin k’ofa Mariam na fitowa ya cafko hannunta tare da danna mata nank’washi me uban zafi akai, k’ara ta saki sosai idanunta auka ciko dm da hawaye, “Allah ya isa mugu kawai” ta murgud’a mai baki beyi ta kanta be ya wuce BQ ko a babu ya kusa sata kuka.
Bayan Sallan La’asr Baba ya shirya tsaf ze fita kasuwa, ganin haka Mariam tabi sahunsa Mama dake a kitchen tana had’a dinner tayi tsaye tana kallonsu ta window.
“Baba!” Cewar Mariam, chak Baba ya tsaya tare da kewayowa.
“Wani abu ne Miryaamu?” Ya tambayeta.
“A’a Baba” tace tana wasa da yatsun ta, “uhm Baba nace ko akwai kud’i zaka siya min jakar makaranta nawa ya tsufa.”
“Yaushe ne na siya miki jakan Mariam?”
“Baba tun last last year fa, tun primary 5.”
“Toh naji Mariam, Allah ya kawo kud’i.” Shiru tayi bata ce komai ba as tana nazarin wani irin kud’i Baba yake magana baida shi. “Ba kiji me nace bane? Allah ya kawo kud’i.”
“Amman fa Bab-” da sauri ya katse ta “in baki iya fad’in amin ba seki jira in Maman ku ta kwashe adashe ta sai miki.”
“Ameen” ta fad’a a hankali sannan ta juya ta basa waje. Seda Mama taga ficewar Baba daga gidan takira Mariam take mata magana.
~* ~* Da goshin Maghrib Baba ya dawo daga fitan da yayi, wasu manya manyan shopping bags ne k’waya biyu hannunsa wanda ya shige dasu d’akinsa nan da nan ya d’auro alwala ya fice masallaci. Ashe kam tun shigowansa su Mariam suke leqensa yana fita suka shiga d’akinsa ita da Omar suka soma neman inda ya dire ledojin daya shigo dasun, cikin wardrobe nasa suka samu suka zaro tare da bud’ewa kayaki ne bil adadi masu kyan gaske wanda ko ba’a gaya ba ansan masu tsada ne duk na Zeezee ba ko na Yasmin d’ai ciki, dam ledojin duka kayakin Zeezee ne ciki bayan ko wanda aka mata suna dasu ma bata gama sawa ba amman ya sake yimata siyayya, Mariam da tace a sai mata jaka ance mata ba a da kud’i.
Omar ya nisanta yace, “ai dama na sani when it comes to Baba and Zeezee expect more.”
“Amman Omar yanzu Baba ya kyauta? Wallahi su Bilqees, Khadija, Sadiya dasu Halima a class namu har dariya suke min akan jaka ta.”
“Hak’uri zakiyi Adda Mariam tunda aka haifo jarababbiyar Zeezeen nan kam ai namu ya qare” ahaka ya taimaka mata suka miyar da kayakin ledan. Bayan Mariam ta idda Sallan Maghrib taje tasamu Mama ta mata bayani, cike da mamaki Mama tace, “lallai Babanku! ina Zeezee zata zo ta kai kayakin? Karki damu Mama na zan mai magana za’a siya miki sabon jakar kinji?” Kai Mariam ta gyad’a “nagode Mama” nan ta nufa d’akinsu suka hau kallo.
Bayan dawowan Baba ya kinkimi ledoji yayi d’akin Mama dasu, zaune ya tarar da Zeezee cikin gadonta se wasa take, tana ganinsa ta soma tsalle nufin ya d’auke ta, bayan ya gama yimata wasa ya cire mata kayan jikinta ya hau gwada mata sabin daya siyo wanda duk suka mugun amsheta. Ana cikin haka Mama ta shigo da sallamarta ta zauna a gefensa tana kallonshi daga bisani tace, “sannu da k’ok’ari kaya sunyi kyau.”
“Sekin fad’a ma? Ai nan da kike gani duk kayan dubu hud’u da d’ari biyar (N4,500) yayi sama ne, a shagon Yusha’u na siyo su.” Baki Mama ta dafe da hannunta d’aya tace, “yanzu Alhj kayi adalci kenan?” Cike da k’in nuna damuwa yace, “name fah?” Yana me sake gwada wa Zeezee wani kayan.
Mama bata b’oye komi ba ta basa labarin dukkanin abinda tasani, shiru Baba yayi chan yace, “ni wallahi banason suratai yanzu me kikeson implying? Bana adalci tsakanin yaran nan ko meh? Jaka de baze kawo fad’a ba.” Hannu ya cusa a aljihu ya fito da dubu d’ai-d’ai ya irga biyar ya watsa wa Mama “seku siya mata jakan, da an sai wa yarinya kaya shikenan kowa idonsa na kai toh Allah kyauta.”
“Ameen koma me de ka bada kud’in jakan.” Cewar Mama tana k’ok’arin barin d’akin. Ko uffan Baba bece da ita ba ya cigaba da abinda yakeyi.
★★★
Gata mara misaltuwa Zeezee ke samu gun Baba a yayin da hakan ke tusa tsanar ta gun ‘yan uwanta. Sosai take girma wane kazan agric sam Baba bai barin Mama tabar ta da yunwa, aduk lokacin da Zeezee ta soma jinyan hak’ori kuwa Baba ji yake kamar shi ke rashin lafiyar duk yabi ya tada wa kowa hankali a gidan barin ma Mama da take yini tana shayar da Zeezee 24/7.
Zazzab’in sati biyu Zeezee tayi ta mulmule ta sake komawa old self nata. Da yamma bayan yaran sun tafi islamiyya Baba kuwa tun fitarsa safe be dawo ba Mama tafito rik’e da Zeezee a hannu, d’ayan hannunta kuwa ribbons ne da comb da kifiya da alama so take ta kamawa Zeezee gashin ta bayan ta nemi kujera ta zauna ta shafa mai akan sannan ta soma tajewa a hankali, comb d’in na tab’a gashin, Zeezee tasa ihu a rayuwa in akwai abinda ta tsana shine a tab’a mata kai dai-dai nan neighbours nata su Maman Sudeis, Ummu HH, Maman Sultan da Maman Samha suka shigo dan duba jikin Zeezee dan ko basu da labarin ta warke. Sannu da zuwa Mama tayi musu a yayinda suka k’ariso kan daddumar dake a kusa da Mama suka zauna bayan gaisuwa suka tambayi ya jikin Zeezee Mama take cemasu jiki da sauk’i, anan suka soma hira. Da zaran Mama ta tab’a kan Zeezee seta sa ihu.
Maman Sudeis ce ta bada shawara kan asa ma Zeezee mama a baki zatayi shiru, hakan kuwa Mama tayi, kum Zeezee tayi tsit wane bata gidan sede Mama na sake tab’a gashin ta saki maman tasa ihu, dariya Maman Samha da Sultan sukayi suna mamakin wayo irin na Zeezee “wato ita de kar a tab’a mata kai.” cewar Ummu HH. Maman Samha ta tab’e baki tace, “ai kuwa de ga gashi har gashi amman bayason kulawa, ina ma ace Samha ta keda wannan gashin? Yanzu ya zakiyi toh Maman Zeezee?”
Mama ta kalli Zeezee da tayi lamo a jikinta sannan tace, “danne ta zanyi wallahi ai Baban nasu bai gida, ‘ya‘yan kowa ana masu kitso ni bance zan mata kitso bama, d’an kamawa da ribbon da zan mata tace baza ayi ba!” Nan tasa comb tana taje sumar, Zeezee na dad’a ihu kaman ana cire mata rai tasha mama ma tak’i se ihu take amman haka be hana Mama fara sa mata ribbon d’in aka ba. Daga sama kawai ta jiyo sallaman Baba, ko kad’an bataji k’aran honk na motansa ba kodan kukan Zeezee ne oho? Cike da tashin hankali ya nufo inda matan suke zaune. Ko ta kan gaisuwan da su Maman Sudeis suke mai beyi ba ya soma masifa.
“Ya haka? Meke faruwa Hafsah?!”
“Sannu da zuwa Alhj.” cewar Mama.
“Ba abinda na tambaya ba kenan” yayi maganar tare da d’ago crying Zeezee daga cinyan Mama yana lalashinta har ta samu tayi shiru, se anan ya amsa gaisuwan su Maman Samha.
“Ina jinki Hafsah me kike ma Zeezee kukanta ya cika unguwa haka?”
“Alhj me zan mata? Gashin nata na keson kama mata naga yayi tsawo dayawa ana barin sa haka.”
“Da kuma bata so fah?”
“Al-” yayi saurin katse ta;
“Nace da kuma bataso fa? Me ya kamata kiyi?”
“In bari” ta fad’a sounding humiliated a gaban k’awayenta yana scolding nata haka. Ido ta d’an mai ko zeyi shiru ya bari se bak’in nata sun tafi yaso se yayi scolding natan amman ina se kaman cewa ma tayi ya cigaba.
“Toh meyasa baki barin ba? Kama kan banza da wofi!” ya miqa hannu kan cinyarta yayi watsi da ribbons d’in, “kinsa yarinya kuka ba gaira ba dalili dududu yaushe yarinyan ta samu sauk’i neh? Wallahi Hafsah ki kiyaye ni.” Ran ta ne ya b’aci bata san a lokacin da tace, “shikenan kai Alhj ba’a